Showing 99001 words to 102000 words out of 110313 words

Chapter 34 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt

mutuwa ce gabaki daya ta rabasu. Tun kafin ta haihu take fadin yanda yara ba zasu taba zama dalilin da zata zauna a auren da batayi niyya ba.


Har Mama ca tayi bata da hankaline da taji hirar, bata dandana zafin naquda ba. Yanzun ba naquda ba, ga yarinyarta nan a hannunta, ga dayar nan a hannun Babanta, amman ba zata taba koma mishi ba


"Na miki alkawari na saba, nasani, zan canza saboda su, karkiyi tunanin zan kalli yarana inyi musu karya, wallahi zan canza Hindu, karki rabani da ke, kiyimun kowanne hukunci banda wannan..."


Kai ta sake girgiza mishi tana saka shi jin wani abu ya bude a zuciyar shi. Mikewa yayi, yana mika mata Suhana da tayi bacci a jikin shi yana juyawa. Idan abinda yakeji kuka ne zai balle da shi ba zaiyi a gaban yaran shi ba, ba zasu fara ganin raunin shi kafin suyi girman fahimtar karfin zuciyar shi ba. Ko daya kama hannun kofar ya bude yana fita, janta yayi a hankali, batare daya kalli inda yake tunanin su Appa suna tsaye ba ya taka yana nufar hanyar da zata fitar da shi daga asibitin. Ko babur ne zai hau zuwa gida, idan yaje ya nemi kudin da zai bashi, sam baima ji Abid da yake kwala mishi kira ba sai da yasha gaban shi


"Abid ka kaini gidan Fodio"


Ya furta, Abid din na daga mishi kai, suka karasa wajen motar shi, ya bude ya shiga ya zauna yana jan murfin. Har Abid ya zagaya ya shiga baima sani ba, dan ya nutsu yana jin yanda ba tsaga daya zuciyar shi takeyi ba, wajaje ne daban-daban yake budewa yana sanar dashi ba iya kirjin shi ciwon zai tsaya ba.


*


Babu kowa a gidan sai Fodio, yana zaune kan kujera a falo da Mug a hannun shi da Hamza baisan ko meye a ciki ba. Sallamar Hamzan ya amsa da wani irin sanyi murya. Shima baice mishi komai ba ya wuce daya daga cikin dakunan baccin gidan zuwa bandaki. Wanka ya fara yi yanajin kamar an sake mishi fatar jikin shi saboda iskar da yake ji tana shigar shi ta ko ina. Sai da ya fito ne ya kula da dakin Fodio ne, cikin kayan shi ya sami riga da wando, yasan su duka basa rabuwa da sabon kayan ciki ko dan abokai baqi, ko bukatar hakan ta taso a tsakanin su.


Har turare ya samu ya dan fesa, sai da ya dafe kirjin shi saboda ciwon da yaji yana mishi. Sannan ya samu ya fito yana dawowa falon. Waje ya samu ya zauna. Sai yanzun ya kalli Fodio da idanuwan shi sukayi zuru-zuru, abinka da mai hasken fata, kamar jini ne kwance kasan idanuwan shi da yake nuna alamar rashin wadataccen bacci, duk abinda Hamza yake ji bai hana shi fadin


"Fodio lafiyar ka kuwa? Kaga yanda ka rame?"


Kallon shi Fodio yayi


"Me kayi?"


Ya tambaya a madadin amsa tambayar da yayi mishi


"AbdulHafiz bai fada mana ba, yace ba hurumin shi bane ba, in kana so muji zaka fada mana da kanka. Me kayi Hamza?"


Numfashi Hamza yaja yana gyara zaman shi cikin kujerar, da wani irin yanayi a fuskar shi yace


"Kuskure, Fodio kuskure nayi"


Dan daga mishi kafadu Fodio yayi


"Rayuwar mu cike take da tarin kuskure Hamza"


Da sauri Hamzan ya kalle shi


"Ba za kai mun fada ba?"


Kai Fodio ya girgiza mishi


"Zan maimaita maka abinda kasani ne, kayi kuskure, baka kyauta ba...duk kasan wannan Hamza"


Fuskar shi Hamza ya saka a cikin hannuwan shi yana jin duniyar tayi mishi tsaye waje daya


"Kana da sa'a daya, in dai zaka tsarkake zuciyar ka, idan zaka roki Allah da dukkan zuciyar ka zai yafe maka"


Bude fuskar shi Hamza yayi, Fodio na jinjina mishi kai


"Haka AbdulHafiz yace mun, tunda raina bai zo wuyana kafin in gane kuskuren da nayi ba ina da sauran rabo. Kasan AbdulHafiz, ya jamun ayoyi da Hadisai yana kara kashe mun zuciya"


Murmushi Hamza yayi mai sauti, badan ya samu saukin abinda yake ji ba, sai dan AbdulHafiz ne, kaunar shi a wajen su mai girma ce, shisa yake jin abinda AbdulHafiz din yayi mishi har kasan zuci, shi kan shi Fodio din da murmushin a fuskar shi


"Hindu ta haihu"


Hamza ya furta muryar shi can kasan makoshi, wannan karin murmushin da Fodio yayi har cikin idanuwan shi ya kai


"Kace mun ba wasa kake mun ba"


Hamzan kan shi baisan murmushi ya kwace mishi ba, murmushi tun daga zuciyar shi


"Amna da Suhana..."


Yatsun shi biyu Fodio ya daga ma Hamza da ya jinjina mishi kai yana murmushi


"Congratulations Man... Allah ya raya mana su"


Abinda bai taba faruwa da Hamza ba yaji yanzun, yanayi ne daya dauka bakowa Allah yake halitta da shi ba, kunya, kunyar ma ta Fodio


"Amin"


Ya amsa da wani yanayi da yasa Fodio kwashewa da dariya, har ran shi ya dauka zai jima wani abu bai saka shi nishadi ba, amman daya daga cikin kyautar da Allah yayi wa dan Adam ita ce mantuwa


"Kunya ta kake ji yau?"


Hararar shi Hamza yayi, zai magana kenan wayar Fodio da ta hau ruri ta hana shi. Dagawa Fodio din yayi, kwata-kwata Hamza bai gane kan maganar ba tunda bayajin me ake fada daga dayan bangaren


"Dan Allah daga nan zuwa gobe ku nemomun duk kauyukan da akace suna cikin wahalar neman ruwa, ko guda nawa aka samu kuyi mun magana ina jira"


Shine ma dan abinda ya fahimta a maganganun Fodio, kafin ya sauke wayar daga kunnen shi. Ganin yanda Hamza yake kallon shi yasa yanayin daya gani cikin idanuwan shi tun zaman shi ya dawo, kamar maganar da yake shirin yi na da ciwo tun kafin ya fito da ita


"Ina son gina iya rijiyoyin da nake da hali a madadin Ashir...banda wani abu da zan mishi, Hamza ban da shi"


Fodio ya karasa maganar muryar shi na karyewa, cikin idanuwa Hamza ya kalle shi


"Idan ka gina rijiya ko da daya a madadin Ashir, ina da tabbacin da zai dawo duniya ko na rana daya zai nemoka, zai fada maka yanda kake daya daga cikin masu kaunar shi da bai tabbatar ba sai da ya rasu"


Kai Fodio yake girgiza ma Hamza, yanajin idanuwan shi na cikowa da hawaye


"A wajen na bar shi, a wajen, Hamza ko gawar shi ban tsaya an dauke ba, wacce irin kauna ce wannan?"


Numfashi Hamza ya sauke, shima yana bukatar lallashin nan, ba Fodio bane kawai cikin yanayi


"Ban sani ba....ban sani ba Fodio...."


Cewar Hamza a gajiye, yana dorawa da


"Kawai nasan ina fatan in rigaka mutuwa, abinda ban tabayi ba, saboda ina so in samu abinda Ashir yake shirin samu yanzun... Zunubaina masu yawa ne"


Shiru ya biyo bayan maganar Hamzan, ba dan basu da sauran abin fadi ba, sai dan su duka kowa da tunanin da yakeyi, wayar Fodio din ce ta sake yin ruri, wannan karin daya duba mikawa Hamza yayi ganin Mansy ce, ajiyar zuciya ya sauke yana karbar wayar hadi da daga kiran ya kara a kunnen shi


"Hello..."


Ya furta, jin muryar shi na sa Mansy fadin


"Alhamdulillah, ina kaje? Inata kiran wayarka a kashe, na maka text yafi a kirga baka karanta ba ma, lafiya dai ko?"


Numfashi Hamza yaja yana fitarwa a hankali


"Lafiya kalau..."


Yana jin itama ta sauke numfashi


"Motar ka zan kawo maka daman, ina kofar gidan Fodio, ko ina zan kai maka?"


Mikewa Hamza yayi


"Ki shigo ciki"


Jin ta danyi shiru yasa shi sake fadin


"Ni nace ki shigo..."


Sannan ya kashe wayar yana mikawa Fodio daya karba ya ajiye a gefe shima yana mikewa, kitchen ya nufa dan ya ajiye mug din da yake hannun shi. Hamza kuma ya fita daga gidan. Mansy harta shigo da motar ciki, ta bude ta fito. Ganin shi yasa ta karasowa tana samun shi. Sai dai yanayin fuskar shi ya tsorata ta, sosai yanayin fuskar shi yasa zuciyarta dokawa, hannu ya mika mata tana saka mishi mukullin a ciki


"Yau ne rana ta karshe da wani abu zai hadamu Mansy, zaki tafi, zaki goge lambata, zaki gogeni a duk wani shafi na sada zumunta da kike dani, kamar yanda zanyi dana dauki wayar ta...."


Cikin bayanannen tashin hankali da firgici take kallon Hamza


"Ina da yara Mansy, ina da yara har guda biyu yau da safen nan. Ba zan koma baya in goge rayuwar da nayi ba, bama ni da tabbacin laifukana ba zai taba su ba..."


Hamza yake fadi wani irin tsoro na shigar shi


"Me kake ce mun? Ta ina kake so in fara? Ni bance zaka aureni ba tuntuni, ka fadamun da bakinka ba zaka aureni ba. Bance kai ka fara bata ni ba, amman kana da hannu a ciki..."


Mansy tayi maganar hawayenta na zuba, itama tsoron ne bayyane a fuskarta, firgicin inda zata fara daga nan, badan Hamzan ne kawai namijin da ta taba bi ba, ba kuma dan shi kadai ne take tare da shi ba. Duk da ya sha fada mata yanda ba zai taba aurenta ba, ta kuma dauka har zuciyarta ta yarda da hakan, sai yanzun, sai yanzun da yake tabbatar mata rabuwa da shi take jin akwai bangaren zuciyar ta da yake ganin kamar Hamza zai kasance a rayuwar ta har karshe


"Ina da laifuka da yawa na yarda, amman ba zan bari ki doramun na bacinki ba Mansy, ba zaki karamun da wannan ba, babu abinda ya faru a tsakanin mu da babu amincewar ki, zamu raba laifin ne dai-dai..."


Hamza ya fadi yana dorawa da


"Wa'azi ya kamata in miki, amman banda wannan kalaman, laifukana ba zasu barni ba. Karki sake nemana, idan har akwai wani bangare na zuciyar ki da ya taba mutunta abotar mu zaki bar rayuwata"


Hannu tasa tana goge fuskarta


"Nagode, nagode da komai"


Ta karasa muryarta a karye tana juyawa, shine namiji na farko a rayuwar ta da ya taba kokarin kareta batare da alhakin hakan ya rataya a wuyan shi ba, namiji kwara daya da tasan zata kira a kowanne lokaci ya taimaka mata idan bukatar hakan ta taso, namiji na farko da ta jingina kanta da shi batare daya tureta ba. Ko bata ba Hamza jikinta ba a idanuwanta taga yanda zai taimaka mata idan da ta roke shi. Shisa yanzun rabuwa da shi yake jijjiga rayuwarta. Sai dai da gaske akwai bangaren daya wuce zuciyar ta da zai cigaba da mutunta abokantar su har karshen rayuwarta. Zata bar shi, zata bar shi kamar yanda ya roketa, duk da batasan inda rayuwa zata kaita daga nan din ba, zata bar shi.


*


*Littafina na siyarwa ne. Akan #250 kacal*


Account details:
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank


Whatsapp Number
08074545149
9/19/20, 9:46 AM - mmn khalid: 31


Ba kirga kwanaki yakeyi ba yanzun, saboda wani irin tsayi da suke mishi wajen wucewa. Rayuwar ma gabaki daya bayajin dadinta, saboda cikin watanni ukun nan ta kowacce fuska rayuwar ta hade mishi waje daya. Su Anna basuce suna fushi da shi kai tsaye ba, amman bayan gaisuwa babu wata magana mai tsayi da take hada su, bai samu fuska har a wajen Appa da zai roki su sake zuwar mishi wajen Hindu ba. Hatta AbdulHafiz har yanzun bai huce da shi ba, ko yayi kokarin fada mishi damuwar shi baya saurare, satin daya wuce ma kai tsaye AbdulHafiz din yace


"Ka daina wahalar da mu biyun Hamza, kaga abotar nan mun gwada a baya batayi wani amfani ba, tunda ko shawara ce na baka banda kimar da zaka dauka.....shisa na daina maka shishshigi a lamurranka, kai dai muci gaba da maganar aiki ana gaisuwar mutunci zaifi"


Shisa ya kyale su, ya barma Allah lamurran shi. AbdulHafiz ne yake sa ran zaije ya taya shi bama su Anna hakuri daman, shima kuma ta bangaren shi babu wani sauki. Gidan Fodio din ma da yakan kwana yabari, tunda in dai ba yana falo zasu fita shi da Arafat ba sai dai ya fito yaga basa nan. Ko abinci suka siyo basa tahowa da shi


"Mantawa nake ka saki Hindu... Sai ina dauka kana da aure har yanzun zaka koma gida kaci abinci"


Arafat yace mishi ranar karshe da yai magana sunyo take away basu taho da shi ba. Abin yayi mishi ciwo ba kadan ba, a fuskar shi suke sake goga mishi laifin da ya riga daya karbi yayi, kuma gani yake duk AbdulHafiz ne ya zuga su suke mishi wannan abubuwan. Wai a ciki harda Abdallah ma, jiya da yazo wajen aiki a makare yake tsokanar shi magana ya danqata mishi


"Ba zaka gane dalili ba, wanda ya rike auren shi da kyau ne kawai zaifi fahimtar dalilin makarata"


Komai ya hade mishi waje daya, babu wanda yake kokarin fahimtar shi, kafar sada zumunta ta WhatsApp kawai yakan hau, shima idan ya roki Hindu yana son ganin yaran shi da zai rantse duk ganin da zai musu a kullum kara girma sukeyi, sai ta turo mishi hotunan su, duk maganar da zaiyi bayan hoton ba zata taba amsa shi ba. Ko kiranta yayi maganar su bata wuce ta wasu dakika, da yaji lafiyar su Suhana take kashewa, har mamaki yake. Hindu da aiki idan ya fita a tsayin rana bai kirata ba sai tayi mita


"Idan baka so kaji muryata, ni ai ina so inji taka"


Amman yanzun kamar bataso ma take amsa wayar shi, text baisan adadin wanda ya tura mata naban hakuri ba, bayajin ya taba bada hakuri a rayuwar shi mai yawan wanda ya ba Hindu, amsa daya ya samu a tsayin watannin nan


"Na fada maka komai ya wuce, wallahi komai ya wuce har raina"


Amman kuma taqi amsa tayin auren shi da yake sake yi mata. Idan gidansu yaje dan yaga yaran shi, Asma take bama su ta kawo mishi, harya gama zaman da zaiyi ba zata taba fitowa ba. Idan ma daukar su yayi ya kaiwa Anna, harya dawo dasu sai dai tasa aje a amso su. Ita kanta Anna yafi ganin fara'arta yanzun duk idan ya kai mata su Amna. Yau ma yana zaune a Office shi kadai, daga inda yake yana jin hayaniyar hirar su Fodio, zuciyar shi ciwo takeyi, duk yayi zuru-zuru ya fita hayyacin shi.


Wayar shi da take ajiye akan tebir ta fara ruri, jikin shi har kyarma yake wajen dauka da yaga Hindu ce


"Hello"


Ya furta kafin ta amsa yana dorawa da


"Ya kuke?"


Yanajin kukan da baisan na waye ba


"Amna ce take kuka ko Suhana?"


A gajiye Hindu tace


"Waka sani rigimammiya?"


Murmushi yayi


"Suhana..."


Dan jim Hindu tayi


"Mama da Anty zasu fita yau ana wani suna haka. Ni yanzun ina makaranta, ina da test amman bansan ya zanyi ba"


Hindu take fada mishi, baima san ta koma makaranta ba, sam bata bashi labarin komai daya shafi rayuwarta yanzun. Motarta ya jima da kai mata abinta harda takardun, kuma yana jin dadi duk in yaje gidan yaga motar, bayan su Suhana yanzun bashi da wani abu nashi da yake tare da ita sai dai motar. Yana tura mata kudi saboda su, duk da kullum cikin siyayyar duk wani kaya da zasu burge shi yakeyi. Ya gwada sai mata sau daya tai wani irin warware shi, bai kara gwadawa ba. Yanzun tsoronta ma yake ji, tsoron yai wani abu da zai sake tunzutata taqi hakura ta dawo mishi yakeyi sosai.


"Karki damu, bari inzo in dauke su"


Yanajin numfashin da ta sauke


"Nagode..."


Kafin ta kashe wayar, mikewa yayi yana fita da sauri, kan shi tsaye ya nufi mota ya bude yana nufar hanyar da zata hada shi da makarantar su Hindun.


*


A bakin ajinsu ya hangota, takawa yake yana son tabbatar da abinda idanuwan shi suke hango mishi tun daga nesa. Rabon daya saka ta a idanuwan shi tun a asibiti. Watanni ukku cir bai ganta ba, tayi wani irin kyau, tayi jiki. Sai yake ganin kamar ya shekara ukune bai ganta ba, gashi tayi mishi wani irin kwarjini, banda jan jambaki babu wata kwalliya a fuskarta, sosai tayi mishi kyau cikin shigar abayarta kamar ko da yaushe. Sai wani da yake tunanin cikin yan ajin su na yanzun ne yana rike da Amna, ita kuma ta rike Suhana da take jijjigawa a hankali.


Ko da ake ce mata raino abune mai wahala bata tabbatar ba sai da yazo kanta, raino harna yara biyu. Danma kowa a gidan yana tayata hidimar su, shisa take samun sauki, Suhana ce take da wata irin rigima, gashi inta fara kuka kome zakai ba zatayi shiru ba sai tayi niyyar hakan da kanta. Amna kuwa in ba yunwa take ji ba ko batajin dadin jikinta da wahalar gaske kaji kukanta. Amman Suhana ko wanka za'ayi har makota sai sun sani. Hannu Hamza ya mika yana karbar Suhana ya sabata a kafadar shi yana jijjigata, magana yake mata a hankali cikin harshen fulatanci yana shafa bayanta, kamar haka take jira kukan ta ya fara rissina.


Cikin mintina kasa da biyar hartayi shiru, da alama bacci take shirin yi ma, kallon su Hindu takeyi, tana kallon yanda Hamza yakeyi da Suhana kamar raino na daya daga cikin abinda aka haife shi da iyawa. Suit ne a jikin shi mai guda uku, bai saka ta saman ba, daga ta cikin mai dogon hannu sai kuma yar jacket din saman. Dan murmushi tayi, da gaske takeyi ranar da tace mishi komai ya wuce mata, saboda a sujjada ta dinga zubar da hawayenta tana rokon Allah daya yaye mata dukkan damuwa.


Yanzun kam hamdala kawai takeyi saboda yanda komai ya nutsar mata, ita ce yau take kallon Hamza, gashi a gabanta amman kyawun shi bai mata wani abu ba, asalima salaf take jin zuciyarta a kan shi. Sai takejin kamar ba kalar kaunar da ake fadi taiwa Hamza ba, kamar dai-daito da yayi da kalar mijin burinta ne abinda ta so a tattare dashi ba komai ba, yanzun kuma da ya bude mata idanuwanta sai take kallon shi a shi kadai, take kallon shi babu tarin dukiyar nan, babu izza da kyawun shi. Hamza take kallo, Hamza da yai wasan cikar shekara da auren su, Hamza daya shigo mata a buge a darenta na farko.


Hamza take kallo daya sa kirjinta daukar zafi kamar ana hura wuta a cikin shi, sosai yanzun idanuwanta suke a bude tana ganin Hamza da yasa ta kuka kamar ba zata daina ba. Sai takejin kamar ba watanni uku bane da rabuwar su saboda inda take hango shi da matukar nisa a rayuwarta. Shi din bakomai bane a wajenta yanzun sai Baban su Suhana, ko dazun da zata fito da Mama take mata maganar yanda zatayi da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login