Showing 57001 words to 60000 words out of 110313 words
Chapter 20 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt
yana bata mamaki.
Ko dan itama in dai wanda take burine ta samu bataga jiran da zata tsaya yi ba. Da wannan tunanin ta koma Instagram tana shiga shafin Hamza. Ya saka sabon hoto yana wajen cin abinci, daga kasan hoton cikin harshen turanci ya rubuta
'I can't wait to be home'
Haka kawai sai taji zuciyarta ta kumbura ta cika fam, ba zai zauna acan kamar yanda duk wanda ya ketare daga Nigeria sukeyi ba, da alama Hamza na sha'awar dawowa gida Najeriya, hakan kuma yayi mata dadi da bata da dalilin shi. Hoton tayi liking ta shiga comment din tana ganin matan da suke ta cewa yayi kyau, kuma yayin, jar riga ce a jikin shi mai dogon hannu, da hula kamar ta sanyi itama ja, yadan turata baya, gashin kan shi ya fito, kunnuwan shi a rufe ruf da hular, sai dai kana ganin farin zaren earpiece din da alamu suka nuna yana manne cikin kunnuwan shi
"Shegu mayu"
Ta tsinci kanta da furtawa, a gefe daya tana jin dadin yanda Hamzan ko like bai danna akan comments din nasu ba ballantana ya kula su. Tana fitowa daga comments din tayi refreshing taga ya saka sabon hoto na wani gini, da alama shi yayi, bayan tayi liking sai tayi comment da hotunan zuciya har guda uku, dan duk yanda taso ta fadi wani abu daban ta kasa, ta rasa abinda ya kamata ta fadi da sauran mayun matan da suke ta mishi magana basu riga da sun fada ba. Ganin haka kawai comments din nasu yana neman bata mata rai yasa ta tashi tana some shirin fita makaranta.
Tana gama shiryawa tsaf, ta dora baya akan kayanta tana yafa mayafin abayar saman kanta, yar jaka ta dauka ta saka wayarta a ciki, tana da kudi, tunda Baba na sati daya yake bata ta rike a hannunta, wani lokacin kuma yana kara mata kafin satin ya kare. Sai da ta shiga dakin Anty dan tayi mata sallama ta samu tana bacci, fitowa tayi taja mata kofar a hankali ta wuce makaranta. Handout din daya kaita kawai ta karba, da yake batai breakfast ba, yunwa takeji har wani jiri-jiri takeyi, karasawa tayi restaurant din su Elizabeth da yake nan cikin makaranta, taci doya da kwai da plantain. Sannan taji tadan samu nutsuwa.
Ganin azahar har tayi yasa ta biya masallaci tayi sallah, tukunna ta fita daga makarantar zuwa gida. Tana shiga da sallama ta sami Anty zaune a falo
"Sannu da gida"
Ta fadi, Antyn na amsawa da
"Yawwa... Yau da wuri?"
Kai Hindu ta jinjina mata
"Ai bamuyi komai bama, Handout kawai na karbo"
Ta karasa maganar tana wucewa dakin su dan tasan da wahala Antyn ta sake cewa komai. Kayan jikinta ta rage, ta zauna kan gado tana zaro wayarta daga jaka, kiran Huzaifa tagani dayasa ta tunanin ko lafiya, dan haka ta danna tana bin kiran, yana dagawa da sallama
"Yaa naga kiranka ne, ina dawowa daga makaranta wayar na cikin jaka"
Dan jim yayi kafin ya amsa da
"Nabar miki sako a whataapp, ki duba"
Ya kashe wayar, da mamaki a fuskarta ta kunna data. Sakkonin ta bari suka gama shigowa tukunna ta bude na Huzaifa din tana soma karantawa:
'Akwai abokina Kamal, shagon shi kusa da nawa yake, ya taba zuwa gida, amman ba lallai ki gane shi ba. Tunda yaganki ya matsamun sosai, nayi miki magana ne yanzun saboda na yarda da hankali da nutsuwar shi. Duk da nasan shi wajen shekara hudu, sai da na kara bincike a kan shi kafin na yarda in hada ku. Bance sai kinso shi ba, amman ki bashi dama dan Allah. Zai zo anjima da yamma'
Sake karanta sakon tayi tana dakuna fuska, duk da yaune karo na farko da wata magana data danganci Samari ta taba hadata da Huzaifan, watakila shisa taji zancen yazo mata daga sama. A wani bangaren kuma tana jin Kamal din bai mata ba tun kafin tagan shi, saboda tana da yakinin ko kafar Hamza bai kamo ba, ita kuma yanzun a zuciyarta Hamza yayi mata setting din wani standard da ba zata dinga auna duk wani namiji da zai kalleta da sunan soyayya.
'Allah ya kaimu'
Ta amsa Huzaifan da taga yazo online
'Nagode Kanwata. Allah ya tabbatar mana da alkhairi'
Sauka tayi kawai, ba zatace Amin a abinda bata gani ba, babu wani alkhairi ita idan ba ganin shi tayi ba. Tashi tayi ta fito tana fadama Anty zatayi bako da yamma
"Daga ina? Waye shi?"
Anty ta tambaya tana tsare Hindun da idanuwa
"Bansan shi ba nima, abokin Yaa Huzaifa ne, yanzun yake fadamun"
Kai Anty ta jinjina, fuskarta na saki da alamun yarda, tasan sukan taba kishin su a tsakaninta da Mama, amman babu ayar tambaya a kaunar da ke tsakanin yaran, Huzaifa ba zai taba aminta da yazo wajen Hindatun ba sai idan ya yarda da tarbiyar shi. Yanzun Hindun ce matsalarta, dan haka fafur duk yanda Anty taso ta da Musa kai tsaye tace bata son shi guntu ne. Tana kula da yanayin 'yartata, zuwa yanzun kuma addu'a take mata babu dare babu rana, Allah yai mata zabin alkhairi ya tsayar da hankalinta akan mutum daya, tagaji da dauka da saukewar da Hindu takeyiwa Samari, zata so tayiwa Baba maganar amman zai goyi bayan Hindu ne, tunda bata laifi a idanuwan shi.
"Ki bashi dama Hindu, karki duba wani kyawu na halitta, ina fada miki bashi yake rike aure ba"
Kai kawai Hindu ta jinjina ma Anty tana wucewa ta koma daki,bawai dan maganar ta shigeta ba, kyawu kam shine ginshiqin komai a wajenta, ita kanta Antyn Baba ta zabo, kuma bashida muni. Babu dalilin da zaisa ta saurari mummuna, shisa ma take addu'a babu gajiyawa. Kyakkyawa, fari, dogo, mai kudi na fitar hankali. Ba zata zo tana kwana a duhu ba, ko ta fito tana kikiniyar shiga kitchen, gara tasan aure tayi, taga banbanci daban dana gidansu, tana daki a dafo a kawo mata. Ba zataki ta auri mijin daya iya girki bama, tana bacci ya tasheta ya hada musu breakfast yanda akeyi a littafin Hausa. Ai soyayya dabance, in batajin shi har bayan zuciyarta babu abinda zaisa ta aure shi.
*
Karfe biyar taga kira da bakuwar lamba, dagawa tayi tana karawa a kunnenta
"Assalamu alaikum..."
Muryar shi ta daki kunnenta da wani irin sanyi da yasata gyara zama tana amsa mishi sallamar
"Kamal ne, ya kike?"
Sosai muryar shi tayi mata dadi, da dan murmushi a fuskarta tace
"Alhamdulillah. Ina wuni"
Amsawa yayi yana dorawa da
"Afuwan, kinganni sai yanzun. Ina cikin gidan ku"
Mikewa tayi
"Gani nan fitowa"
Ta fadi tana neman Hijab din data fito da ita, ta Asma ce ma, ita ba ma'abociyar saka hijabi bace, lokaci zuwa lokaci takan saka, bata dasu da yawa ma, tafi saka abaya, yanzun da zamani yazo saita dora Kimono wasu lokuttan. Bata dai san dalilin da yasa ta zabi hijabin ba yau. Ruwan toka ce da ta haskata ba kadan ba, fita tayi zuwa falo tana zira takalmanta da suke kofar daki, tana fita ta kitchen din gidan ta zagaya, dan akwai hanya ba saita bi ta falon Mama ba, daga nesa ta fara hango shi kan machine roba-roba a zaune
"Tafdin...Machine..."
Hindu ta fadi tana tabe baki, lallai zata sallame shi ya koma inda ya fito, karasawa tayi tana mishi sallama hadi da kare mishi kallo cikin raini, bataga dalilin da zaisa shi zuwa mata da jallabiya da hula tashi da kwakwa kamar sabon ladani ba, ga wani gemu da zata iya kirgawa tsai-tsaye kamar dole akace saiya ajiye gashin da yaki bashi hadin kai. Murmushi yayi hakoran shi na bayyana, guda daya ya karye, bashida muni, amman sam baiyi mata ba. Duk da jallabiya ce a jikin shi tana iya gane siririne ba kadan ba. Duk yanda tayi kokarin ganin tayi mishi fara'a ko dan Huzaifa saita kasa.
Dan gaisawa sukayi, Kamal duk yanajin wani iri, shi yana zaune akan Machine ita tana tsaye, hakan yasa ya sauko daga kan Machine din shima ya tsaya, duk da yaga kujeru irin na robar nan a cikin gidan, amman Hindu batayi mishi tayin zama ba, yana ganin kamar baiyi mata ba daga yanayin fuskarta, ko kuma dan zuwan farko ne shisa, shi yake ta kokarin janta da yar hira, amman sai amsa shi take da
"Umm..."
Ko
"Ai kam"
Duk jinshi yake a takure, Hindu kuwa daya sauke daga Machine din taga hannuwan shi kamar bulala, dogone babu laifi, amman bazai kai Hamza tsayi ba, sai dai sam batason ganin namiji siriri haka, ita da take son dirarren namiji da zai dauketa bai sauke numfashi ba, faffadan kirji da zata kwanta luf kamar jaririya a kirjin mahaifiyarta. Ina zata kai irin Kamal, bai cire rigar shi ba, amman tasan babu komai a kirjin shi banda kasusuwan da intayi bacci akai zata tashi da tambarin da kasusuwan shi zasu bar mata a kunci kamar bagobura.
Ganin da Kamal yayi ya rasa gane kan Hindu, ga yamma na karayi yasa yai mata sallama da fadin
"Zamu yi waya"
Shima kai ta jinjina mishi, tana kallo yaja jak din Machine din shi da bata tsaya ya tayar ba ta juya tana nufar cikin gida, badan Huzaifa yace mata yana da shago kusa da nashi ba, in a hanya tagan shi zatace Malamin Islamiyya ne, ko kuma irin matasan nan masu jan baqi a wajen tafisir. Yanzun ma tanaji a jikinta robobi yake siyarwa a shagon...!
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 22
Yafi mintina goma da bude idanuwan shi, amman sam yaki ko da motsawa ne, komai nauyin shi yakeji, dakyar yayi sallar asuba, itama a cikin daki, sabo ne kawai abinda ya tashe shi a yanda yakejin shi kamar marar lafiya. Karatun Qur'ani ma, da kai ya karanta abin da ya sawwaqa, yaja jikin shi ya koma kan gado ya kwanta. Baya gane hasken rana ta cikin dakin saboda gabaki daya labulayen a sake suke, kuma ya kashe wutar dakin, akwai dalilin da yasa yayi zanen taswirar dakin a haka, saboda bayason haske sam idan bacci yake son yi.
Dakyar ya iya juya kwanciyar shi, yana daukar wayar shi ya latsa, sha biyu saura mintina tara. Dan ware idanuwan yayi ganin rana tayi har haka, sako yagani ta saman wayar, ya cire daga mukulli yana budewa. AbdulHafiz ne
"Basu dauki yarinyar su sun baka dan sun gaji da ita ba. Kamar yanda wani bai maka dole kaganta kace kana so ba, karka wulakanta musu yarinya Hamza, karka ci amanarta da ka dauka. Allah ba zai barka ba, ka zauna da ita kamar yanda kake so mijin Auta ya zauna da ita, ka riketa kamar yanda kaga Appa ya rike Anna, ka kula da ita kamar yanda zaka so a kula da naka yaran wata rana. Allah ya baku zama na aminci, Allah ya kauda fitina a tsakanin ku, Allah baka ikon fin karfin zuciyarka a kowanne yanayi"
Wani abu Hamza ya hadiye da yazo yai mishi tsaye a makoshi, yanajin jikin shi ya kara nauyi da maganganun AbdulHafiz din, a lokaci daya kuma suna bashi karfin gwiwar mikewa zaune. Dan dafa kan shi yayi, kafin ya sauke wani numfashi mai nauyin gaske yana mikewa gabaki daya ya nufi bandaki, ruwa ya watsa ya fito, zuwa wani dan lokaci ya shirya kan shi tsaf cikin wani yadi ruwan kasa mai haske, sai kamshi yake bazawa. Idan kagan shi zakace wani waje zaije, dan har hula ya saka a kan shi, ya daura agogo a hannun shi, takalma ya zira da za'a iya kira da silipas, bakake, tukunna ya fito daga dakin, a hankali yake sauka kasa.
Tsaye yayi bakin kofar dakin Hindun yanajin jikin shi a sanyaye, ko kadan bayason tuna abinda ya faru a daren jiya, yasan shi din mai tarin laifuka ne, amman laifukan shi tsakanin shine da Ubangiji, nauyin da yakeji yau na da alaka da rashin kyautama Hindu da baiyi ba, ko kadan bayason hada laifukan shi da hakkin kowanne mutum, musamman ita, musamman matar shi. Numfashi ya sauke da kalmomi biyun karshen "Matar shi". Shi dinne yau karkashin inuwar aure da wata, shine da mata, da gaskiyar Hausawa da sukace "In da ranka ka sha kallo".
Kwankwasa dakin ya farayi, sannan ya tura a hankali, a tsaye ya hangota, daga inda yake baya iya ganin fuskarta, bata kuma juyo ba, jikinta na sanye da doguwar riga ruwan kwai, bayan a bude, bata kai da zage zip din ba, tanata kokarin daura dankwalin ta, takalman shi ya zare daga nan inda yake tsaye, ya saki kofar yana rufeta, a hankali ya taka har inda Hindun take tsaye, hannun shi yasa yaja mata zip din, kafin ya mika shi yana kama dankwalin da take kokarin daurewa, yana kallo ta sakar mishi, dubawa yake yana tunanin ta inda ya kamata ya fara daurawa dan baisan me take son yi ba, baima san me yasa yayi kokarin tayata ba.
Tunda ya shigo taji shi, taji shigowar shi, wani irin wahalallen bacci tayi tun bayan asuba, ta kuma tashi da wata irin yunwa, ga alamar zazzabi da takeji, ta dai godewa Allah da kanta baya ciwo, duk da ta kwanta da shi, amman bata tashi da shi ba, da sanyi-sanyi take komai tun tashin nata, sai da ta fara gyara gadon tukunna ta shiga wanka. Ba zatace ga halin da zuciyarta take ciki ba, balle kuma kalar tunanin da takeyi, a karo na farko da hatta tunaninta ya kwace mata, bata da karfin kokawa da komai, dan haka batayi kokarin janyo shi ba.
Shisa tana fitowa wanka ta shafa mai, ta sami riga ta saka a jikinta, Hamza ya kwace mata abubuwa da yawa a daren jiya, ba zata bari ya kwace mata shigar da tayi niyyar yi yau ba, dan bata cikin walwala baya nufin ba zatayi kwalliya ba, ko ba komai shirin zaisa kadan cikin ranar yau tayi mata saurin wucewa. Da taji shigowar shi sai da zuciyarta ta doka, wani sabon tashin hankalin daya daga mata kafa tun tashinta taji ya dawo, jikinta ya fara bari, tana rasa yanda tayi niyyar daura dankwalin kafin shigowar shi. Badan bataso juyawa bane, kafafuwanta taji sun daskare a waje daya, har ya karaso yana kama zip din rigar da take jikinta yayi sama da shi.
Ko ta cikin mudubin ta kasa kallon shi, zuciyarta dokawa take har zazzabinta ya bayanna sosai, dan tanajin zafin da jikinta ya dauka. Tana jin shi ya kama dankwalinta, shisa ta sakar mishi, sai yanzun ta sami karfin gwiwar kallon shi ta cikin mudubi, da yanayin fuskar shi daya nutsar akan dankwalin, zaka rantse bashida abu mai muhimmanci daya kamata yayi, numfashi ta sauke, tana mika hannunta ta dora akan nashi cikin son karbar dankwalin, makale mata kafada yayi yana saka dayan hannun shi ya tutture nata
"Kibar ni, ina tunanin style ne"
Yanda yayi maganar sai ta tsinci kanta dayin dan murmushi, yafi mintina biyar, har saida taji kafafuwanta sun fara gajiya da tsayuwa, sannan ta dan tsugunna tana zame kanta daga cikin dankwalin, ta sake mikewa, ta mika hannu ta fisge dankwalin daga cikin hannuwan Hamza, bude baki yayi ta riga shi da fadin
"Ka kyaleni, kafafuwana sun gaji da tsayuwa"
Ta karasa maganar tana daura dankwalinta mai sauqi ta hanyar lanqwasa shi, ta kuma tura ta baya, daurin da akanyiwa laqabi da ture kaga tsiya. Ya kuma yi mata kyau, ta cikin mudubin suka hada idanuwa, tayi saurin sauke nata, tana sa Hamza zagaya hannuwan shi a qugunta ya rikota jikin shi hadi da lumshe idanuwan shi
"Idan nace kiyi hakuri yayi kadan, idan nace ba zai sake faruwa ba zanyi miki karya...na rasa abinda ya kamata ince miki, kiyi hakuri, ban kyauta miki ba, kiyi hakuri Hindu"
Ya karasa maganar yana bude idanuwan shi cikin nata da take kallon shi ta mudubin, nata idanuwan cike taf da hawaye, batasan ko yanayin muryar shi bane ba, ko hakurin da yake bata, amman koma meye yayi tasiri a zuciyarta, tunda bata tsammaci hakan daga wajen shi ba, asalima batayi tunanin komai ba, dan a tsorace take
"Kiyi hakuri..."
Hamza ya fadi da dukkan gaskiyar shi, yana sakinta, hadi da kamata ya juyo da ita ta fuskance shi, yasa hannuwa ya tallabi fuskarta
"Dan Allah karkiyi mun kuka"
Ajiyar zuciya ta sauke, hawayen na zubo mata
"Ka bata mana daren mu na farko"
Ta fadi muryarta na rawa, kai yadan daga mata, yasani ba saita fada ba, shisa yasan bai kyauta mata ba
"Shisa bansan ya zan fara baki hakuri ba, naji dadi da muna da darare da yawa a tare damu, I will make it up to you, na miki wannan alkawarin"
Wannan karin ita ta daga mishi kai, yasa hannu yana goge mata fuska, kafin ya rankwafa ya sumbaci goshinta cike da ban hakuri, tukunna ya rungumeta tsam a jikinta. Ta zagaya hannuwanta a bayan shi, tasani daman, jiya dai zuciyarta ta fara karyatata, amman yanzun Hamza ya tabbatar mata ita yake bukata a rayuwar shi dan ta canza shi, tasan zata iya canza shi daman. Ba zaizo da sauqi ba, saita jajirce, amman tana ji a jikinta ko bajima ko ba dade hakan zai faru. Sunkai mintina biyu a hakan kafin yace
"Yunwa nake ji sosai..."
Tana lafe a kirjin shi ta amsa shi da
"Nima haka"
Dagota yayi
"Dauko mayafin ki mu fita"
Itama sai taji ya kara mata yunwar, gani yake kamar bata sauri saboda hanjin shi da yake kullewa
"Nikam bari in fito da mota, kafin ki karasa shiryawa"
Hamza ya fadi yana juyawa ya zira takalman shi ya fice daga dakin, hanyar waje ya nufa, ya kama kofar ya bude, ga mamakin shi, katon kwando mai hannuwa yaci karo da shi a bakin kofar dakin, tunanin farko daya fara zuwa ranshi ko jaririne a ciki, yanda kwandon yake a lullube, sai da kirjin shi ya doka, dan yasha ganin haka na faruwa a fina-finai, amman inda jaririne zaiyi kuka ai dole. Ganin yar takarda a maqale yasa shi tsugunnawa ya dauko takardar yana dubawa, kafin ma ya karanta yagane rubutun AbdulHafiz ne.
"Eng. AH"
Kawai aka rubuta a jiki, daukar kwandon yayi yana shigowa dashi cikin gidan, cike da mamaki, tsugunnawa yayi ya fara bude ledar da akayi amfani da ita aka lullube kwandon, yana cin karo da kuloli a shirye tsaf. Fiffito dasu yayi, ya bude na farko, dankaline soyayye da wainar kwai sai kamshi ke tashi, yana kara mishi yunwa, ya sake bude wata, farfesun kayan cikine
"Allah ne