Showing 6001 words to 9000 words out of 110313 words
Chapter 3 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt
ji yana zufa, Aliyu haushi ya gama ƙume shi
“Ai ba nan gizo ke saƙar ba, yanzu me wannan yarinyar zatayi dakai? Jibe ka fa. Rigar ka kwara ɗaya, gashi duk ta koɗe bata kama omo"
Aliyu yai maganar, Adam da sauran yan shagon na bushewa da dariya.
Bai kula suba, ya koma gefe ya soma chatting da Hindu gadan gadan. Sai ya zamana a duka satin babu abinda Jalil yake banda hira da Hindu da ta saki jiki ta biye mishi, duk yanda Dimples tayi mata kashedi tabi a hankali, sai ta bagarar da zancen Dimples din na cewar a low-key Twitter tabbas akwai attajiran masu kudi, akwai kuma attajiran amman tantiran yan duniya masu bin mata, kuma zai iya yiwuwa akwai yan yankar kai ma, tunda yanar gizo yanzun ta zama abinda ta zama. Sai Hindu ta alakanta maganar Dimples da rashin son mutanen ta, in da mutane zasu biye mata sam zata wuce su wuce kamar ba daga jinsi daya suka fito ba.
Ko kadan bata da yarda, zaku shekara tare da ita kafin ta sakar maka fuska, kullum girarta a sama take, bata shiga harkar kowa, ba kuma zataki kowa karya shiga harkarta ba, shisa sai ta daina mata zancen Jalil din, duk da tana so ta tambayi Dimples ko zata iya cema Jalil ya turo mata da hoton shi kar a karayin ta Elias, amman kuma nan ba 2go bane ba, Twitter ne, bata taba ganin wata ta fito tace ta hadu da gurgu ba, kuma tana ganin suna ma juna bangajiyar ziyara da kuma godiya a tsakanin su. Ga ajin Jalil din ya burgeta, har lokacin ko lambar wayarta bai karba ba.
Wata safiyar asabar da ta kasance bata da aikin makaranta sosai, ta kuma tambayi Anty Dimples zata zo suje gidan Maman Amrah Yayar Dimples din batajin dadi zata dubo ta, sanin kusancin da ke tsakanin Hindu da Dimples shisa Anty ta amince da kashedin kar Hindun ta kai dare. Ranar kuma tayi dai-dai da lokacin da Jalil ya bukaci yana son ganinta su gaisa. Nan ta shaida mishi cewa bata gida yau zasu fita ita da Kawarta. Ya tambayi unguwar tace mishi wajen Lagos Street ne, kafin wani lokaci Jalil ya amsata da cewa shima zaiyi ta area din sai su hadu 'Briefly' su gaisa, yanda yai amfani da kalmar a gayance ya kara burge Hindu.
Sosai taji daɗin wannan maganar, a cikin rana ɗaya tayi babban kamu. Watau Jalil shiru shirun twitter zai ziyarce ta. Kwalliya ta fesa sosai, data karbi jikin ta, tasan cewa harga Allah tayi azkar da kyau. Kuma dama Allah yana tare da mai hakuri. Wulakanci da Hamza yake ta mata ne, da kuma kalar tarkacen Samarin da tayi yau Allah zai wanke mata duk wani bakin ciki da ta kwasa. Tunani kala kala ya rinƙa rikito mata. Ita bata san gajeren namiji kamar an kifa kwando. Fata takeyi kada Jalil ya zamto gajere. Sai kuma ta tuna cewa yanzu kai ya soma wayewa, tsawonka shine aljihun ka. Idan dai yanada kuɗin sa kawai zata aure shine ne amma bazata taɓa barin ƙawayenta suga mijinta ba.
Zata ce mashi bata san snatching, kafin ayi mata dariya ace taci baya. Haka tayita tunani kala kala tana kokarin ta kawo kamannin Jalil wanda take kyautata zaton shine zai zama mijinta. Da wannan tunanin Dimples ta sameta, suka yi ma Anty sallama suka fice, a hanya ne take ba Dimples labari
"Ba zaki rufama kanki asiri da mazan Twitter ba ko Hindu? Bakiji me nace miki ba"
Kai Hindu take girgiza ma Dimples
"Wallahi ina ji a jikina Dee"
Ta kirata kamar yanda take ce mata tana dorawa da
"Ki yarda dani, zuciyata ba ko yaushe take mun karya ba, ina da good feelings akan Jalil. Ina jin kamar shine zai zama mijin da zan aura"
Wani irin kallo Dimples takeyi mata, su duka sunsan halinta, ba akan komai take magana ba, amman idan taji bata yarda da abuba to karshe sai abin nan ya zamana baizo musu da dadi ba
"Hmmm..."
Kawai ta furta suna cigaba da takawa zuwa titi inda zasu hau adai-daita sahu da zata kaisu gidan Maman Amrah
*
"Nifa inada abin yi, ku ce ma Kawu na fita"
Jalil yace tareda miƙewa. Su Adam kallonsa sukayi sai suka cigaba da hirarrakin su. Gida ya koma yana cire kayan jikinsa, wankewa yayi sosai da omo dan yayi haske clean ya saka. Daman ya siyo bula domin ya ƙara ma dan yadin da yake matukar ji dashi armashi. Dayake yadin mai laushi ne kuma ana iska nanda nan ya bushe. Aikam saiya goge da kyau yana mishi karin guga na mutunci.
Takalmin sa wanda ya ɓare ya soma dariya ya ɗauko, yana saka gam da baya rabuwa dashi dan yan liqe-liqe, nan ya gyara tareda gogewa fes. Yanayin Hindu bai mashi kamar wadda zatayi wulakanci ba. Kuma ai ba santa yace yanayi ba, idan sun haɗu bayan yau zai soma binta da kalamai wanda zai sa ta soshi. Bai taɓa budurwan kirki ba, ya dai saba cema yan talla yana sansu saboda su rinka bar masa kaya kyauta. Musamman masu doughnut ko gyada. Su kuma idan suka gane halinsa su zage shi tas suyi gaba.
Karfe huɗu Hindu ta bashi damar ya ziyarce ta, inda ta faɗi yanada ɗan nisa da inda yake. Maimakon ya hau mashin sai Ustaz yace bari yaje da ƙafa tunda akwai sauran lokaci, yan kudin Machine din yayi amfani dasu ya kara siyan data. Inda yake gani babu nisa saida ya kwashi fiye da awa ɗaya yana takawa. Ga rana ana barbaɗawa ranar kamar zai soye. Duk zufa yakeyi ta ko'ina hammatar rigarshi duk tayi dabbara-dabbara da wajen wuyan sa musamman tunda kayan akwai bula.
Ya isa inda ta faɗa mishi sai nishi yakeyi zufa tana karyo mishi. Sai yayi mata text ta twitter ta fito gashi. Hindu kuwa har nuna ma Dimples tayi tana wani murmushi dan taga kalar ajin da Jalil yake dashi, mikewa Dimples tayi batare da tace komai ba ta dauki mayafinta, daman Kimono ta dora akan riga da wandon da yake jikinta, sukace ma Maman Amrah zasu ga wani a waje, yanzun zasu dawo.
Jalil yana cikin jira ta fito sai gari ya juye hadari ya haɗu, anan iska ta ɗauke mishi hular da ta Kawu ce ta aro ta kuwa cilla cikin unguwa. Haka yayita bi yana
“Wait! Wait!!”
shi kaɗai kamar mahaukaci. Dan ya san halin Kawu tunda ya hana shi taba mishi kaya, Hular bata tsaya ba saida ta shiga cikin wata muguwar kwata. Haka ya saka hannu ya tsamo ta. Nan yayi dama dama da hannunsa. Zare ido yayi ya soma dube-dube. Sam baisan nan ne kofar gidan Maman Amrah ba, dama Dimples ta hana Hindu bashi asalin address din tace mata kada ta bashi asalin address ɗin, koda baiyi masu ba zasu iya yi mishi fuska kamar basu bane.
Nan su Hindu suka fito suka ganshi tsaye kamar mahaukaci sai zufa yakeyi ga kaya duk datti, balle kuma kayan sunyi mugun koɗewa. Bai gane Hindu ba tunda hotuna kan bambamta. Balle ita da tafi kyau a fili fiye da hoto. Saiya ƙarasa wajensu yayinda suka fito domin su taimaka mashi da ruwa ya dauraye hannun shi harma da bakar leda ya samu ya saka hular kar Hindu ta fito tagan shi
Yana isa wajen su, bayan yayi sallama yana ajiyar zuciya saboda gudun dayayi. Dimples na watsa mishi wani irin kallo daya saka shi shan jinin jikin shi, a daburce ya soma magana
“Dan Allah kuyi haƙuri, ruwa zaku taimaka mun dashi in wanke hulata data fada kwata...”
Ran Hindu yayi mugun ɓaci saboda bata ƙaunar rainin wayau, kar mutumin nan ya ja mata bad luck, batason wani akasi da zai faru kafin taga Jalil, Dimples ce ta riƙe mata hannu domin su saurare shi, bata son mutane, amman kuma hakan baisa tana da wulakanci ba, musamman taga zai girmesu nesa ba kusa ba, ganin haka yasa Jalil murmusawa cikin yanayin da duk idan yayi a mudubi yakan ga yayi matukar kyau
“Dan Allah ruwan zaku taimaka mun sai yar bakar leda in saka hulata..."
Yai maganar yana dorawa da
"Nazo wajen wata abin begena ne Hindu shine hulata ta faɗa kwata"
Da yake Allah yayi mishi surutu na rashin dalili
"Me?"
Dimples ta tambaya tana son taji ko kunnuwanta yaji 'Hindun' da Jalil ya furta. Yana dan fadada murmushin shi ya sake maimaitawa
"Hindu, ko kinsanta ne?
Wannan karin Hindu da take jin jiri na shirin kwasarta ce tace
"Jalil?"
Muryarta cike da matukar shakku, dago idanuwa Jalil yayi yana karema Hindu kallo, sai yanzun da ta kira sunan shi tukunna ya ganeta, yanda take kallon shi ya tabbatar mishi da kiris take jira ta kwada mishi mari
"Kan uban can"
Cewar Hindu tana dorawa da wata ashariya da bata tabayin irinta ba, kafin ta sake wani motsi Jalil ya ari takalman kare ya yanki Hanya da wani irin gudu cikin yadin shi da yake kwasar iska yana hura shi kamar zai tashi sama. Cikinta Dimples ta rike saboda da dariyar da take tattaruwa kafin ta fito fili da wani irin yanayi da yasa Hindu taji idanuwanta sun cika taf da hawaye.
'Wannan wacce irin rayuwa ce'
Ta tambayi kanta, me yasa na rana daya abinda yake karbar mutane ita bazai karbeta ba? Me yasa duk wani abin arziqi da idan wasu matan sukayi dangane da samun Mijin aure na gari ita idan ta kwatanta sai yazo mata a baibai? Wacce irin rashin sa'a ce take bibiyar rayuwarta har haka?
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 4
Zatai karya idan tace gabanta baya faduwa. Asali tunda suka fito daga gida wata zufa take tsatssafo mata a saman goshi har zuwa tafikan hannunta, da sukaje gidan su Ummi sam kasa samun sukuni tayi. Biebee na kula da ita, batai mata magana ba saboda ta fada mata daga farko bataji ba, sau daya take gaya maka gaskiya ta koma gefe ta saka maka ido, yanda zataji dadin cewa ta fada maka baka dauka ba idan komai ya kwabe. Bata sake shiga tashin hankali ba sai da Elias ya kira wayarta, jikinta har bari yake
"Bie muje...Anty ta fara kirana"
Hindu ta furta muryarta na rawa, kai Biebee ta jinjina mata, Ummi ce tace
"Wai tun yanzun zaku tafi? Kai dan Allah.... Hindu ba Anty tasan nan kuka zo ba"
Murmushin karfin hali Hindu tayi
"Zata fitane zan dora girki, yamma nayi shisa"
Kai Ummi ta jinjina tana fadin
"Bari in dauko Hijab dina in rakaku"
Wannan karin Biebee ce ta girgiza mata kai
"Dan wahalar da kai? Mu biyune fa, kiyi zamanki dan Allah"
Duk da haka saida Ummi ta rakasu har bakin kofar gida, sannan sukayi sallama, da sauri Hindu ta daga kiran Elias daya shigo a karo na ukku
"Haba Hinduna, inata kira sai an mun sarautar za'a daga?"
Dan murmushi Hindu tayi
"Kana ta ina?"
Sai da yayi jim tukunna yace
"Bakin wani saloon Umtaz..."
Kai Hindu ta jinjina dan ta gane wajen
"Gani nan karasowa to"
Ta fadi tana sauke wayar daga kunnenta batare data jira amsar shi ba, ta kalli Biebee
"Wai yana wajen Saloon din Umtaz"
Biebee ta jita, bata dai ce komai bane, suka dan kara sauri kowa da abinda yake sakawa cikin zuciyar shi. Suna karasawa kwanar da zata kaisu titin da Elias yace yana tsaye Biebee ta riko hannun Hindu
"Zuwa zakiyi, ki kira shi kice yana cikin wacce motar, ki fara hango shi tukunna"
Shawarar Biebeen ta zauna mata, wayarta ta danna tana kiran Elias da ya daga a bugun farko
"Ban ganka bafa... Kana cikin wacce mota?"
Hindu ta fadi kafin ya numfasa
"Cikin wata jar golf"
Elias ya amsata ta dayan bangaren
"Golf?"
Hindu ta maimaita cike da mamaki, daga ita har Biebee suna zira kansu suka hanga wajen saloon din, akwai motoci jefe a wajen, amman jar golf din da suke hangowa tayi kama da motar da ake dibar jogon kaji ana cin kasuwar kauyuka da ita, ga wata irin kura da ba zasuce ta kasa bace ko qoqewar da fentin motar yayi bane ba, kallon juna sukayi, Biebee na kokarin ganin bata kwashe da dariya ba, a hankali tace
"Kice bari mu duba"
Hakan Hindu tace tana sauke wayar da wani irin yanayi da yake fassara 'akwai matsala' bayyane a fuskarta, dariya Biebee takeyi harda rike ciki
"Wanne irin iskanci ne wannan Bie? Ya zanyi ni yanzun... Jar golf yace, ni kuma waccen motar kadai ce ma golf a duk motocin titin nan, anya shine? Ko dai wasa yake mun? Aike kinga motocin gidan su"
Kai Biebee take girgiza mata
"A gidan ubanwa naga motocin gidan nasu?"
Tsaki Hindu taja
"Ban nuna miki hotunan shi ba?"
Wani kallo Biebee tayi mata
"Da kika nuna mun hotunan bance miki ni ban yarda dashi ba?"
Numfashi Hindu taja ranta a bala'in bace
"Ni yanzun ya zanyi? Juyawa zamuyi wallahi..."
Kai Biebee take girgiza mata
"Zai yiwu wasa yake miki, ki sake kiran shi kice ya fito ko shi zai hango mu, kice kin saka hijabi ruwan toka"
Duk da taso su juya din tunda Elias yai mata wannan rainin hankalin, amman kuma ita taga hotunan shi, ta kuma ga kalar motocin da yake hotunan a jikinsu, maganar Biebee zata iya zama gaskiya, kilan shima yaga golf dinne yake so ya gwadata, yaran masu kudi kanyi haka wani lokacin dan suga ko tsakani da Allah kake son su. Shisa ta sake kiran Elias ta fada mishi abinda Biebee din tace su duka biyun suna labe jikin katangar da zata hadasu da titin da Elias din yake. Sai dai ga mamakinta murfin motar aka bude ta mazaunin da bana dire ba bane, kafin taga an ziro kafa daya, ana kama murfin motar, sannan taga ya saka dayan hannun shi kamar zai tattaro wani abu ya fito dashi, a tare suka ware idanuwa ita da Biebee
"Butar shayin buzaye..."
Hindatu ta fadi dan shine karshen zaginta idan abu yakaita makurar mamaki, Biebee na karbe zance da fadin
"Inalillahi... Ke Hindatu mun shiga uku....La haula wala quwwata ila billah.... Kinga me nake ce miki ko?"
Cewar Biebee da take a tsorace ganin shanyayyar kaface Elias din ya tattaro ya fito daga ita daga motar yana jingina jikin shi da murfin motar, sannan yai amfani da dayan hannun shi yana fara kiran wayar Hindu da batasan lokacin ma data sauketa daga kunnenta ba, sai da taji ringing dinta, dagawa tayi batare data kara a kunnenta ba, tana hango Elias daya bude baki yana fadin abinda bataji ba ta cikin wayar. Tana godema Allah da duk yanda Elias yayi naci hotonta daya yagani wanda yake a dp dinta na WhatsApp, ca tayi shida zai ganta wata rana harya gaji.
Wayar ta kashe gabaki dayanta
"Na shiga ukuna ni Hindatu"
Ta fadi tana kallon Biebee da mamaki ya hanata dariya, hannun Hindun taja suna komawa baya
"Mu zagaya ta baya mu wuce gida"
Bata bari Biebee ta sake fada mata ba, da sauri suka nufi inda suka fito dan suyi zagaye zuwa gida. Sauri suke kamar zasu tashi sama, basu fara tsagaita tafiyarsu ba saida suka sha kwanar da zata kaisu gida, sannan Biebee tace
"Elias..."
Tana jan sunan kamar yanda Hindu takan fada kar suyi mata iskanci cewar sunan shi Iliya, kafin ta kwashe da wata irin dariya tana dorawa da
"Yar banza... Daman nabari kin karasa wallahi"
Hade rai Hindu tayi tunda ita bataga abin dariya a cikin wannan al'amarin ba, tana da yakinin ita kam yarda da wani namiji da zasu kara haduwa a 2go zai mata wahala, daman Khadee ta fada mata itace taki ji. Tace mata babu kalar tarkacen da babu a 2go
"Yanzun meye abin dariya?"
Ta bukata tana kallon Biebee din da taci gaba da dariya kamar haduwa da Hindun tayi da gurgu shine abu mafi nishadi da ta taba cin karo dashi a duniya. Dogon tsaki Hindu taja tanayin gaba, Biebeen nabin bayanta da fadin
"Haba Kawata ta Eliass"
Shiru Hindu tayi mata, duk tsokanar da Biebee take mata bata kulata ba, ko sallama batayi mata ba ta shige gida. Kai tsaye dakin su ta wuce ta cire Hijabinta tana ajiyewa akan gado, ta ajiye wayar da takejin duk yanda ta saba da ita zatayi kwana biyuma bata dauka ba, idan Elias ya kirata ya gaji zai hakura. Zatayi amfani da lokacin tayi karatun jarabawar da yake gabanta. Amman duk da haka bayan ta fito dan taya Anty hidimar girkin dare sai da taji zuciyarta na lugude kamar Antyn zata gane abinda ya faru, a tsorace take har suka gama aikin, duk surutunta ko magana bata son yi sosai.
*
Duk da girkin Anty ne, bangaren Mama ta shiga tana idar da sallar Magriba, ta kasa hakuri, tunda Huzaifa ya karbi memory dinta yace zai turo mata fina-finai, tun safen bata kara ganin shi ba har yanzun. Halima tagani, batama san ta dawo ba, dan taje gidan Yayan Mama din da yake Unguwar rimi, akwai yar shi da suke KASU tare, suna karatun shirye-shiryen jarabawar su ta zangon karshe a shekararsu ta uku. Dan abokin Baban ne ya manne ma Halima, da Baba yaso sai ta kammala karatunta, Hindu batasan meya faru ya amince aka saka rana ba, gashi yanzun bikin sai kara matsowa yake, sauran watanni biyu, tana kammala jarabawarta da sati daya.
Sosai Hindu take fatan samun mijin da yafi Yaa Ahmadi kamar yanda suke kiran shi, zatayi karya idan tace sanda yake zuwa gidan baya burgeta, duk da bai karasa irin tsayin Mijin da take so ba, amman ya iya gayu, gashi yana shigowa zaka fara jin kamshin turarukan shi na tashi. Magana daya zuwa biyu Yaa Ahmadi kan jefa turanci cikin kwarewa. Amman taji dadin auren Halimar da zaiyi, ko ba komai basuyi asarar hadadden gaye ba, a nata tunanin ya zama nasu, ta kuma ji dadi ba kadan ba
"Yaa Halima yaushe kika dawo?"
Numfashi Halima ta sauke, cikin sanyin muryarta ta amsa da
"Da yammacin nan, Anty tace kunje duba kawarku ke da Biebee"
Kai Hindu ta daga mata, tana jin yanda zuciyarta tayi tsalle data tuna fitar da ta saka Elias fadowa a ranta, duk saurin karbar memory din ma babu amfanin da zai mata yau, dan ba zata kunna wayar ba.
"Eh kam... Yaa Huzaifa ya shigo?"
Kai Halima ta girgiza mata, sallamar da sukaji na saka su juyawa su duka suna amsawa, Hindu na dorawa da
"Ina wuni"
A dakile ganin Musa ne dan Kanwar Mama, ta dauka tana son farin namiji, sai akan shi ta fara gane kalar namiji itace karshe cikin jerin abinda take so a tattare dashi, gajartar Musa ta