Showing 102001 words to 105000 words out of 110313 words
Chapter 35 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt
su Suhana, ko za'a dauko mata yar aikine da zasu dinga zuwa makaranta da ita tana tayata raino idan basa nan, kai ta girgiza ma Anty
"Zan kira Baban su yazo ya karbe su, shima ya dana yaji"
Ko abu ya kawo sai take tsintar kanta da fadin
"Baban su Suhana ne ya kawo"
Ya tashi daga Hamza a idanuwanta, saboda idan ta kira shi da hakan zai zamana akwai wani kusanci a tsakanin su da yake ita da shi kadai, amman idan tace Baban su Suhana, kusancin zai biyo ta kan yaran ne tukunna ya hadata dashi. Hakan kuma yayi mata har a zuciyarta. Bata bukatar wata mai raino, courses biyune ta ajiye daman ko da ta dawo makaranta, saboda tana tsoron ga ciki, kamar ba zata iya ba. Tunda project dinma a lokacin kaf zanen Hamza ne yayi mata su, har aka kusan kamata wajen kare kanta, danma yasa tayi rubutun da kanta, kuma yayi mata bayani da yawa a kai, da bata haye ba, tsaf za'a gane ba ita tayi ba.
"Muje sai in baka kayan su, suna mota"
Ta furta tana mika hannunta ta karbi Amna
"Nagode Faruk"
Ta furta tana yin gaba, Hamza ya bita a baya, har kasan zuciyar shi yake jin yanda ko arziqin gaisuwa bai samu ba wajen Hindu. Suna zuwa mota ta dauko jakar kayayyakin da tasan duk zasu bukata, har madarar su da sai sunga haza suke sha ta hada musu. Tasan yana da kujerun su a duka motocin shi, na tata motar ma shiya siyo ya kawo. Ta dai raka shi har mota ne ya zaunar da su
"Idan Suhana tayi fitsari baka canza mata pampers ba kuka zatayi, bata son jin lema a jikinta ko kadan"
Kai ya jinjina mata, yana kallon fuskarta, kewarta na danne shi, yanda take mishi bayani zakai tunanin ba zata sake ganin su Suhana bane ba, murmushi yakeyi
"Hindu..."
Ya kira a hankali
"Amna bataso a kwantar da ita akan bayanta, zata farka..."
Gyara tsayuwar shi yayi
"Hindu..."
Ya sake kira, sai lokacin ta kalle shi
"I got this, I got them... Na 'yan awanni ne, ki yarda dani, zan iya"
Kai ta jinjina mishi, yanayin fuskarta yana nuna mishi ko kadan bata yarda zai iya kula da su ba, kuma haka dinne, duk da tun suna jarirai suna awa har biyu tare da shi, wani lokacin fiye da haka. Kewar yaranta takeyi tun kafin subar wajen, ko a gida wani ya karbe su, alkunya kawai take, dan ji takeyi inba ita ba babu wanda yake fahimtar abinda suke so, babu wanda zai kula dasu kamar yanda ita din zata kula da su.
"Dana fito zan kira ka, in suna kuka ka kirani dan Allah, kaji"
Kai ya daga mata
"Ayi test lafiya. Allah ya bada sa'a"
Kallon shi takeyi kamar zai tafi da wani bangare na zuciyarta. Harya shiga mota yana kallon tana kokarin leqa su Suhana duk da tinted ne gabaki daya gilasan shi. Kai kawai ya girgiza yana dariya, da har yanzun tana karkashin ikon shi, da test din yau an hakura da shi, zai jata su shiga mota su tafi gida, saboda yasan da wahala ta sami nutsuwa harta iya rubuta wani abin kirki. Yana hanya ne yaga kiran Fodio, bai daga ba sai da ya sauka daga titi yai parking, ba zai amsa waya yana tuqi da su Suhana a motar ba
"Ina kaje?"
Fodio ya tambaya
"Hindu na da test a makaranta, shine naje na karbo su Suhana..."
Baima karasa maganar ba Fodio ya katse shi da fadin
"Ka zo dasu gidana dan Allah, mu ma can zamu tafi yanzun"
Numfashi Hamza ya sauke yana daga girar shi
"Me yasa? Ni gida zan wuce"
Shi suke shama kamshi, duk da yasan su duka suna zuwa ganin yaran, lokutta da dama sai sun dawo su fada mishi, ko Hindu ta dauki hotin abinda suka kai mata ta tura mishi ma yake sanin sunje din. Rayuwa ta hada shi da abokan da mutane da yawa suke addu'ar samu
"Bana so inyi zagi saboda kana tare da su Suhana, dan Allah ka kawo mana su, kaji"
Dariya kawai Hamza yayi yana kashe wayar. Gidan Fodio din ya nufa kan shi tsaye, sun ma riga shi karasawa, saboda sunfi shi kusa da gidan daga Office, tunda yai parking, yana budewa ya fito yaga Fodio harya bude murfin motar yana rankwafawa ya kwance Amna daga cikin kujerarta ya dauketa, sai yaga kamar ta kara kiba, kumatunta kawai na saka dariya kwace mishi, tafi Suhana haske, yanda yaran suke kama da Hindu suna kuma kama da Hamza batare da sunyi kama da junan su ba yana matuqar bashi mamaki.
Hamza kuwa Suhana ya dauka, yana juyawa AbdulHafiz na miko hannu ya karbeta, da Nabila batayi bari ba da yanzun yana rike da nashi shima, amman haka Allah ya tsara, komai na da lokaci. Su Amna dinma jin su yake kamar daga jikin shi suka fito. Wani abu Suhana tayi da baki
"Allah karkiyi mun rashin kirki Suhana, ke kullum sai munyi fada ne?"
AbdulHafiz ya karasa yana dangwale mata hanci, sake kwabe fuska tayi
"Ko kinyi kuka ba ajiye ki zanyi ba...."
Yai maganar yana gyara mata zama a kafadar shi, tare suka shiga gidan su duka. Kan su bai dauki caji ba sai da yaran biyu suka kaure da kuka. Su hudun sun rasa yanda zasuyi da su, musamman Suhana da ko fida taqi kamawa. Hakan yasa Hamza fadin
"Ko Pampers take so a sake mata"
Wani tsalle Fodio yayi yana komawa gefe
"Ku cireni a lissafin nan"
Ya fadi, yana son su Amna, amman ba zai taba kashin yara ba. Shi a nashi tsarin rayuwar ma sam bai hango yara ba har yanzun, aure ne abinda ya fara sakawa a ciki yanzun, shima ya kasa furtawa a fili wani yaji saboda tsoron da yake ji, amman ya san yana bukatar mace ko dan karya komawa neman su ta hanyar da bai kamata ba. Amman yara kuwa yana da sauran tafiya a gaba kafin ya fara hasaso rayuwa da su
"Bari kuga Husband material, yadi goma, riga harda yar ciki"
Arafat ya fadi yana fara kokarin cirewa Suhana skirt din da yake jikinta. Su duka tsayawa sukayi suna kallon ikon Allah, batama bata pampers din ba, rigima ce kawai da take ji, yana sabata a kafada kafin a miko mishi wani pampers din tana tsula mishi fitsari
"Inalillahi... Suhana kinsan wanne kayane kikai wa fitsari? Kinsan dubu nawa kika fitsare?"
Ya fadi kamar zai fashe da kuka, dole Hamza ya karbeta suna mishi dariya. Sai da suka samu duka yaran biyu sukai bacci tukunna Hindu ta kira shi
"Na fito yanzun"
Kai yake girgiza mata
"Wallahi ba yanzun zan dawo dasu ba, kinsan wahalar da muka sha kafin suyi bacci..."
Yana jin tayi jim kafin ta kashe wayar, shima pillow ya dauka daga kan gadon yana kwanciya kasa, gefen katifun su Suhana da suke kwance a kai suna baccin su, kamar basu da wata damuwa a duniya. Idanuwa ya kafa musu yana kallon su har shima baccin ya dauke shi.
*
Links din hannuwan rigar shi ya dauko yana ajiye su akan gado, sannan ya dauki daya ya saka a hannun, yana daukar dayan ma. Cikin wani lokaci ya fito tsaf, cikin yadin shi ruwan madara. Da wahalar gaske ka kalle shi baka kara kallon shi ba. Kallo daya zakayi wa fuskar shi kaga kwanciyar hankalin da take shimfide, zuwa yanzun bayajin shi cikin kuncin da baisan dalilin shi ba, bayajin kirjin shi kamar an danne. Bai dauka zai iya shekara daya batare da mace ba. Azumin shi yake duk Alhamis da litinin yana rokon Allah daya kare mishi zuciyar shi. Da kan shi ya goge Twitter da Instagram. Baice zai daina gabaki daya ba, amman sai ya yadda da fin karfin zuciyar shi da yayi
Sau biyu yana kusan komawa ruwa sanadin Instagram, na biyun hotunan su Suhana da Hindu ta turo mishine ya taimake shi, hotunan yagani yasa shi goge manhajojin biyu gabaki daya. Temptation bala'i ne, idan kana fama da kanka abu kalilan, abinda kake ganin bai kai ya kawo ba zai dawo maka da komai baya. Shisa ya goge, babu yarinyar da zata saka shi karya alkawarin daya daukar ma Ubangijin shi, alkawarin tuba sahihi, tuban da yake fatan ba zai koma ruwa ba, bazai karya alkawarin da yayiwa su Suhana na ganin basuyi dana sani kona rana daya daya kasance sun fito daga jikin shi ba.
A hankali kwanaki suka tafiyar mishi suna juyewa watannin da suka cike shekara, a cikin wannan lokacin yaga kokarin da yayi ya samar mishi yafiyar su Anna, a cikin lokacin ne ya ajiye duk wata izza da yake ji ya roki AbdulHafiz ya yafe mishi dan yagaji da yanda yake mishi kamar bare, kamar basu da wata alaqa data wuce aiki. Shekara daya daya dauka yana bin Hindu kamar babu zuciya a kirjin shi kan ta sake bashi dama, amman tayi biris da shi, ita kanta harta kammala bautar kasarta.
"Ni karatu zanci gaba, ba aure bane a gabana Hamza, na farkon da nayi kaine shaida akan yanda ya kare..."
Shine abinda ta fada mishi, ya roki Anna tayiwa Appa magana a taya shi lallashin Hindu, tace mishi
"Ba zan shiga maganar nan ba, ba zamuyi amfani da girman mu da yarinyar nan take gani mu tirsasata ba, ka lallabata da kanka, idan kuna da rabon sauran zama zata dawo. Amman kam kayi hakuri, ni da Appan ka mun yanke hukuncin ba zamu shiga zancen ku da Hindu ba"
Maganar Anna ta kara kashe mishi jiki, duk da har a zuciyar shi yana son Hindu, yana azabtuwa da rashinta, musamman yanzun da yake ganin yanda ta kara kyau, ba a gane hankali ta fuska, tunda ba'a rubuce yake ba, amman zai iya rantsewa akwai hankalin da yake gani a fuskarta da baya gani a da. Duk da shima AbdulHafiz yace mishi su Suhana sun saka har kunyar mutane ya fara ji yanzun, duk da rikicin shi na banza yana nan babu inda yaje. Yanzun ma Fodio ne ya bashi karfin gwiwar sake tunkarar Hindu, ya dauka yagama ganin abin mamaki sai daren jiya da wayar Fodio na hannun shi yana duba design brief din wani abokin wasan Fodio din da yake son ayi mishi zane ya turo, kiran waya ya shigo.
Sosai Hamza yake kallon wayar, ganin Mansy, mikawa Fodio wayar yayi, ba ya manta da ita bane ba, yakan tunata lokaci zuwa lokaci, amman tunani ne na inda rayuwa ta kaita, ba wani abu ba, har ranshi yana mata addu'ar shiriya, ta samu dalilinta kamar yanda ya samu nashi, sosai yake kallon Fodio da yanayin yanda yake wayar da Mansy
"Tun yanzun zakiyi bacci kibar ni?"
Yanayin yanda Fodio ya ajiye maganar nasa wani abu tsirgama Hamzan da bashi da alaka da kishi, sai tsantsar mamaki da tsoron da baisan dalilin shi ba, har Fodio ya sauke wayar daga kunnen shi Hamza na mishi kallon tuhuma
"Karka tambayeni yaushe ya fara, nima ban sani ba"
Fodio ya furta yana samun waje ya zauna. Suna dan hira da Mansy sama-sama lokacin da take tare da Hamza, ko in tazo wajen shi, ko idan ya raka shi wajenta. Abu daya yasani tun a lokacin, da badan yarinyar Hamza bace zai taya shima, sai dai su din basa hada nema ko da na banza ne. Ta kitchen din gidan shi ranar da ta dawoma da Hamza mota yaji duk maganganun su. Baisan me yasa ya kirata a ranar ba, yasan labarinta, yasan rashin iyaye har biyu na daya daga cikin tushen lalacewar ta, zai fahimci wannan bangaren fiye da kowa.
Bai kirata ba sai karfe goma na dare a ranar, amman kuka takeyi har lokacin, ko muryarta bata fita sosai
"Ina tunanin rayuwata Fodio...ina tunanin abubuwan da zasu faru da na tashi da iyayena duk da ba zai taba zama hujja a gareni ba"
Har zuciyar shi yaji maganganunta, saiya tsinci kan shi da kiranta a kullum dan yaji lafiyarta. Sai ya sake tsintar kan shi da takawa har inda take dan ya dubata da idanuwan shi. Ya fahimci dalilin Mansy da yayi mata maganar tayi aure
"Wa kake ganin zai aureni batare da bincike ba? Wa kake ganin iyayen shi zasu yarda ya aureni bayan sun san rayuwar da nayi? Sirri irin nawa baya boyuwa komin gyaran da akai mishi..."
Shisa da yawan karuwai wa'azi baya shigar su, saboda in basuji ba sunga yan uwan su da tuba baiyiwa rana a duniya ba, duk da inda za'a tonosu a basu ikon magana zasu bada labarin yanda tuban ne zabi mafi alkhairi da sukayiwa rayuwar su, duk da mutanen da suke yawo da zunubai mabanbanta basu karbe su ba, ko da malamai suka zama akwai mutanen da zasu furta
"Abin da a baya kowa yasan tsohuwar karuwa ce"
Kamar zunuban su ba zasu yafu ba, suna manta yanda ba'a shiga tsakanin bawa da Ubangijin shi, suna manta yanda Rahma ta Ubangiji ce, wanda yaso a cikin bayin shi yake nufa da samunta. Shisa da yawa suke zabar zama inda suke tunda ko sun tuban baya wanke laifukan su na baya a idanuwan mutane. Akwai irin su Mansy da yawa, akwai iyaye da yawa da ba zasu taba barin yaransu su auri irin Mansy ba
"Ba zaka hadamun zuri'a da karuwa ba"
Sukan kafa hujja da zance irin wannan, sosai suke manta a cikin mummuna Allah yana fitar da me kyau, a cikin me kyau Allah yana fitar da mummuna, dan da yawa idan aka bincika asali, iyayen su mutanen kirkine, kaddara ce kawai basu tsallake ba. A ranar Fodio yasan idan aure zaiyi ba zai samu macen da yaji ta dace da rayuwar shi kamar Mansy ba. Bashi da wanda zai damu dayai bincike a kanta ballantana bayanta ya dami wani, indai tana da wakilan da nashi zasu samu da maganar aure shikenan. Yasan rayuwar shi ta baya ba zata hana shi samun macen kirki ya aura ba.
"Ka san wacece Mansy, Fodio ka sani"
Hamza ya fadi yana son karin tabbacin Fodio din yasan abinda yakeyi. Ya tuba shikam, shisa yake addu'ar Hindu ta dawo mishi, ya yarda da nagartarta, ba zai iya wahalar neman wata matar ba, ba zai iya duk wannan fargabar ba, dariya Fodio yayi da bata da alaka da nishadi
"Da in auri macen da zata canza mun, gara in auri macen da zata canza mun"
Kallon shi Hamza yayi, dan magana daya ce ya maimaita, kai Fodio ya jinjina mishi
"Canji biyu nake magana, mata nawa ne zaka aure su a kintse sai bayan auren su canza maka? Canjin da sai kayi dana sanin auren, gara in auri Mansy da halayenta da zata canza mun, nasan dukan mu da zuciya daya zamuyi, Allah zai taimake mu ba zamu taba dana sanin auren juna ba"
Yakinin da yake muryar Fodio shi ya taba zuciyar Hamza fiye da maganganun shi, dan ba fahimtar su yayi ba, har ranshi baiga dalilin da zaisa ya auri Mansy ana zaune lafiya ba. Allah ya shirye su duka ya hada kowa da rabon shi
"Sai dai in kana da matsala da aurena da ita, matsala daban da bata shafi halayenta ba"
Da sauri ya girgiza ma Fodio kai, daga ranar daya karbi mukullin motar shi ya yanke alaka da Mansy gabaki daya
"Bani da wata matsala da Mansy"
Numfashi Fodio ya sauke
"Mansura, sunanta Mansura"
Murmushi kawai Hamza yayi yana girgiza kai, sosai Fodio ya bashi karfin gwiwar sake tunkarar Hindu. Yau zasu gama maganar nan duk yanda take kauce mata, hular shi ya dora saman kan shi yana daukar mukullan mota ya sauko kasa yana ficewa daga gidan.
*Littafina na siyarwa ne. Akan #250 kacal*
Account details:
3029530320
Lubabatu Sufyan
Polaris Bank
Whatsapp Number
08074545149
9/20/20, 1:04 PM - mmn khalid: 32
Wata irin mummunar dokawa zuciyar shi tayi ganin Hindu zaune akan kujerun da suka saba zama, a wajen da suka saba yin zance, amman bashi bane akan kujerar, wani ne zaune a inda ya saba zama, yana magana da Hindu, har tana mishi dariyar nan tata da yake ji a ko ina na jikin shi. Dakyar ya iya yin parking saboda ko gani bayayi sosai, yasan yana da kishi na fitar hankali, ba tun yanzun ba, akan ta yasan kishin shi ya wuce duk yanda kalamai zasu fassara, dan nan take zazzabi mai zafi ya saukar mishi, ko murfin motar bai rufe ba daya fita.
Karasawa yayi inda suke yana addu'a kar ya nuna ma Hindu yanda akwai wasu daga cikin halayen shi da ba zasu taba canzuwa ba. Tsaye yayi a kansu yana mayar da numfashi kamar wanda ya sha gudu
"Hindu waye wannan?"
Ya bukata yana kare mishi kallo, kafin ya tsayar da idanuwan shi da suke cike da tsantsar rikici a cikin nata. Idan zata saurari wasu ma baiga dalilin da zata kula irin mutumin da yake zaunen nan ba, in ba kawai so take zuciyar shi ta buga ta tarwatse ba. Duk da a shekaru bayajin zai girmi mutumin, idan ma bai fi Hamzan ba to zasu zo daya. Numfashi Hindu ta sauke tana dauke idanuwanta daga cikin na shi
"Bello ga Baban su Suhana"
Ta fadi tana kallon mutumin da ta kira Bello, kafin ta kalli Hamza da fuskar shi har tayi wani ja saboda kishi tace
"Hamza ga Bello, shine wanda zan aura"
Bude baki yayi da nufin yin magana, yaji wani yawu ya sarqe shi, yana fara tari babu kakkautawa, sosai yake kokawa da numfashin shi, ko bai sarqe ba, maganganun Hindu barazana ne da rayuwar shi. Murmushi Bello yayi
"Bari in barku kuyi magana. Zamuyi waya ko?"
Kai Hindu ta jinjina mishi, kafin ya mike, Hamza da har lokacin tari yake ya samu dakyar yana furta
"Kar... Karka kirata wallahi"
Murmushin dai Bello ya sakeyi, Hamza na bin shi da wani irin mugun kallo harya karasa ya hau machine din shi da Samari sukafi yiwa laqabi da roba-roba yana ficewa daga gidan. A nutse Hindu take kallon Hamza da tarin shi ya tsagaita
"Ka zauna..."
Wani irin kallo yake binta da shi, tabbas ta sami tabin hankali idan tana tunanin zai dora mazaunan shi inda Bello ya tashi
"Ba zan zauna ba, Hindu kasheni kike so kiyi? Bana baki hakuri ba? Ya kike so inyi? Titi kike so in bi ina taro mutane dan su tayani baki hakuri ko meye?"
Ya karasa maganar idanuwan shi har sun sake launi saboda bacin rai.
"Sau nawa zance maka na hakura? Sau nawa kake so in fada maka komai ya wuce a wajena?"
Hindu ta fadi a gajiye, dan tagaji