Showing 69001 words to 72000 words out of 110313 words
Chapter 24 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt
tana barin kofin nan kan mudubi, ta mike ta karasa kan gado ta sami waje tayi zamanta, tana kallon yanda Aunties dinta suke shigowa sunata tsokanarta da fadin
"Yarinya zuwa sha biyu zamu tattaraki mu kai ki"
Da sun fadi haka sai taji zuciyarta tayi wani irin tsalle, ba'a fadi wannan fargabar da tashin hankali na tunanin barin gida ba a littafi, kwanciya tayi jin alamar zazzabin tashin hankali da yake shirin rufeta.
*
Bai taba gajiya da daukar hoto ba sai yau, babbar rigar da take jikin shi ta ishe shi, yana fitowa daga motar da tayi parking cikin gidan Fodio ya fara cire babbar rigar jikin shi, yana cire hular ya rike hannu ya taka zuwa bakin kofar da zata shigar dashi gidan, yana jira AbdulHafiz da mukullin yake a hannun shi ya karaso yazo yana bude gidan. Shigewa Hamza yayi hadi dayin sallama, ya jefe babbar rigar akan kujera ya samu waje ya zauna. Tun karfe goma aka daura aure, amman azahar ma a hanya suka tsaya sukayi, sai yanzun ne suke shigowa gida. Ko karin kirki bai tsaya yayi da safe ba, tun jiya yake jin shi a hargitse
Daya motsa sai yayi kamar wasu sarqoqi ne suke biye dashi suna jiran lokaci ya cika su daure shi waje daya, zuciyar shi taki aminta da cewar auren shine aka daura, badan sarkokin da yakeji sun dabaibaye shi ba, zai dauka ko mafarki yakeyi, da suka fito daga wajen daurin auren ma, yana kula da kallon da Fodio yake yi mishi, kamar shima yana mamakin yanda akayi Hamza yai wannan wautar, yanda ya yarda ya daukar ma kanshi gagarumin nauyi kamar aure. Har a kasusuwan jikin shi yakeji bai shirya ba, shine abinda yasa shi sulalewa ya fice daga gidan jiya ya nemi yarinyar da Hindu bata tashi kiran shi video call ba sai da suna tare.
Ba kuma zaice ya akai ya dangwalo wayar ya amsa video call din ba, ga kan shi da yakeji da nauyi sosai tamkar an dora dutse, giya ta fara dira cikin shi a safiyar yau, sai shayin daya kurba dakyar, kamar kayoyi ne a cikin shi ko wasu itace haka yakeji. Ana fadin
"Amin"
Sai da yaji wani abu ya tsirga mishi har zuciya yana sa hanjin cikin shi kullewa waje daya. Shikenan an daura, shikenan an mishi katanga da abubuwa da yawa a rayuwar shi, abubuwan da bai shirya bankwana dasu a yan wasu shekaru masu zuwa ba, yanzun ma mikewa yayi yana nufar kitchen, AC din dakin bata hana zufa tsatsafo mishi a goshi ba, yana shiga kitchen din fridge ya nufa ya bude, giyar ta gwangwani ya dauka ya bude yana dagawa ya kwankwada, sanda ya sauke gwangwanin yasha fiye da rabi, numfashi yake mayarwa kamar wanda yayi gudu.
Yasa hannu ya balle maballin rigar shi guda biyu, dan yanajin kamar sun taimaka wajen shaqe mishi wuya suna barazana da kaikawo na iskar numfashin shi. Motsin da yaji sai da ya zabura, juyawa yayi yaga AbdulHafiz da yake kallon shi, gwangwanin ya daga yana karasa shanye abinda yake ciki, saida ya matsa shi da hannun shi tukunna ya jefa cikin kwandon shara, yana kallon AbdulHafiz din ya saka hannu a cikin aljihun shi ya zaro wata farar takarda yar karama yana karasowa ya ajiye mishi akan kantar kitchen din, ya mika hannu ya bude fridge din ya dauki ruwa yana ficewa.
Idanuwan shi Hamza ya runtsa yana bude su akan yar takardar da take dauke da rubutun da akayi da pensir
"Isra'i:32"
Runtsa idanuwan shi Hamza ya karayi, fassarar ayar na yawo a cikin su
"KADA KU KUSANCI ZINA, DOMIN ITA ALFASHA CE KUMA TAFARKI NE MUMMUNA"
Bude idanuwan shi yayi yana ganin rubutun da yake kasan na farkon
"Nur:02"
Wannan karin numfashi Hamza yaja mai nauyi yana fitarwa
"MAZINACIYA DA MAZINACI, TO KUYI BULALA GA KOWANNE DAYA DAGA GARE SU, BULALA DARI. KUMA KADA TAUSAYI YA KAMAKU GAME DA SU A CIKIN ADDININ ALLAH IDAN KUN KASANCE KUNA YIN IMANI DA ALLAH DA RANAR LAHIRA. KUMA WANI YANKIN JAMA'A DAGA MUMINAI, SU HALARCI AZABAR SU"
Yakai mintina biyar yana kara jin shi a hargitse, tun jiya AbdulHafiz yake mishi wannan abin, yana kara hargitsa mishi lissafi, ya manta ranar karshe dayaji zunuban shi nabin shi kamar zasu kayar dashi sai bayan yarinyar jiya. Daga ayoyin da sukayi magana akan hukuncin zina, sai kuma wanda sukayi magana akan muninta da yanda take ragargaza imani tare da ayyuka. Yau tunda safe ya ajiye mishi ayar da tayi magana kan a jefe wanda yayi zina da aure.
Yana da tabbacin da yawa AbdulHafiz din ya samo ya rubuta yana ajiye mishi duk wadda hannun shi yakai ya dauko. Baiyi magana ba, baice mishi komai ba, saboda bashida abin fada, tunatarwa ce AbdulHafiz yake yi mishi, kuma daga ranar daya fara bin mata ya rigada ya hango barin hakan duk ranar da aka daura mishi aure, saboda bai shiryama daukar wannan gagarumin zunubin ba, da kan shi dai bayajin yana da karfin daukar hukuncin zina da aure, a lokaci daya kuma yanzun shaidan na kallon shi a gefe, yana saka shi tunanin yanda zai kare gabaki daya rayuwar shi da mace daya tal.
Tunda aka furta Amin din data kulle shi karkashin inuwa daya da Hindu ya kiraya ta amsa shi da
"Okay"
Ta kashe sai ya kara jin duk wani zumudi da yake ya fita kan shi, tsoro da firgici sun maye gurbin shi, ga AbdulHafiz da bai taimaka wajen samun nutsuwar shi ba, asalima so yake ya karasa firgitar da shi. Dakyar ya iya dafa bango ya fito daga falon, ya samu Abdallah ya dawo, tunda shi gidan su Hamzan ya wuce, Anna ta kira suzo su karbi abinci, har ya fara zuzzuba musu, waje Hamza ya samu ya zauna. Yanajin hirar da suke kamar zasu tashi dakin, amman sam hankalin shi ba'a kansu yake ba, abincin kawai yake kaiwa bakin shi yana hadiyewa badan yana gane dadin shi ba.
AbdulHafiz ne ya mika mishi robar ruwan daya dauka da sauri yana budewa ya sha, sai lokacin yaji abincin da yaketa hadiya ya karasa cikin shi inda ya zauna da wani irin yanayi.
"Ka ajiye idan ka koshi"
AbdulHafiz din ya fadi da harshen fulatanci, yana saka Hamza dagowa ya kalle shi
"Kamar ka damu da lafiyata"
Ya amsa yana cigaba da hadiye abincin shi, yayi niyyar ajiyewa, maganar da AbdulHafiz din yayine ta saka shi karasa cinye abincin da yake cikin plate din, aikam ji yake kamar zai mutu saboda cikar da cikin shi yayi, ga shinkafar tayi mishi tsai-tsaye. Ajiye plate din yayi yana mikewa
"Ina zaka je?"
Arafat ya bukata
"In da ka aike ni"
Hamza ya amsa shi yana tsallake Fodio ya wuce kitchen, gwangwanye hudu ya diba na giyar shi yana dawowa ya wuce daki, ya doko kofar kamar zai karyata, yana saka Arafat runtse idanuwan shi da karar
"Ni kadai ne ko yanayin Hamza da gaske ya canza tun da aka daura auren nan?"
Arafat ya tambaya yana kallon su
"Kai mun alfarma daya Arafat, da kaji na fara maganar aure, ka kamani, ka girgizani, idan banji ba, ka daukeni ka tsoma kaina a bokitin ruwa, kayi komai daya kamata, amman ka duba abokantakar mu, karka barni inyi kuskuren da Hamza yayi"
Dariya Abdallah yayi yana kallon Fodio
"Auren nan fa dadi gare shi, ka koma gida a gajiye ka samu wadda zatayi maka sannu ma da dadi, koya aka bata maka rai a waje in ka koma gida yaranka zasuyi wani abin da dole saiya sakayi dariya"
Zuciyar shi Fodio ya dafe yana girgiza kai
"Abdallah ina magana da wanda zasu fahimta, gabaki daya rayuwar ka akan iyali ta kare, duk zaman da zakayi maganarka kenan"
Murmushi Abdallah yayi yana ajiye plate din abincin shi, dan ba wani mai yawa yaci ba, zai koma gida suci, bayason ya cika cikin shi. Fodio ba zai taba fahimtar yanda aure yake ba, in zai kwana yana mishi bayani, kuma yasan rayuwar gidansu Fodio din ta taimaka sosai wajen saka mishi kokwanton nan.
"AbdulHafiz ba zakace wani abu ba?"
Abdallah ya tambaya, AbdulHafiz din na girgiza mishi kai
"Bazan bata bakina akan Fodio ba, zan mishi addu'a da maganganun"
Ya karasa yana mikewa shima, gara ya watsa ruwa ya canza kaya, yanzun zasu kara fita daukar yan kai amare, inya dawo saiya duba Hamza, bashi da kalaman da zaiyi amfani dasu ne, har ran shi yakejin kamar akwai kuskure a auren nan da Hamza yayi, saboda ta kowacce fuska yau Hamza ya nuna sam bai shirya daukar nauyin daya dorama kan shi ba.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 23
Tunda Hamza ya tashi wajen karfe hudu tana jin shi, sai da ya fice daga dakin tukunna ta bude idanuwanta, akwai wani abu da yazo yayi mata tsaye da bashi da alaqa sam-sam da abinda ya faru shekaranjiya. Tasan jiyane ya zame mata daren farko, da shima yazo mata ba'a yanda ta tsammata ba, har ranta taso jin yanda ita din take daban da sauran matan da take da tabbacin Hamza yayi mu'amala da su a baya, taso ya fada mata ita din daban ce, ko dan mutuncin ta da ta kawo mishi, ta so jin tarin alkawurra a bakin shi, a kasan irin wahalar da tasha, kunnuwanta a bude suke cike da shirin jin duk wannan abubuwan.
Batace sai ya bata kujerar makka kyautar kawo mutuncinta ba, duk da tasan yana da halin hakan, amman idan ya fada mata yanda ita din daban ce, yanda baisan abinda ya dingayi da rayuwar shi kafin ita ba zataji dadi, gaya mata ya samu duk abinda yake nema a jikin mace a tare da ita, yayi mata alkawari cewa tunda gata, shi da wasu matan sai dai kallo daga nesa, yanda ta tsammaci zai rikice a kanta ba haka taji abin ba sam-sam. Ga labaran da ta dinga ji da wanda ta dinga karantawa kala-kala, sam basu ko da kusan karya gado yanda ta hasaso ba, bata majin idan akwai mutum a dayan dakin zaiji su.
Jin shigowar Hamza yasata saurin lumshe idanuwan ta. Shikam kaya yaje ya dauko daga bangaren shi, a kan gadon daga gefe ya ajiye su yana wucewa bandaki. Da gaske ne akwai nutsuwar da tazo mishi tare da macen da ta kasance ta shi, halalin shi, bai tashi da Hindu manne a kirjin shi yanajin wata irin dauda ba, kuncin da kan jiyarce shi duk lokacin da yabi sauran matan da dana sanin da yakeji sam babu su yau, asalima sai yake jin shi daban, ita ma Hindun sai yajita daban. Ba sai wani ya fada mishi dan ita din halalin shi bace ba. Sai dai a kasan duk wannan yana tunanin ace ya sami mata masu yawan gaske da zasu zama halalin shi.
Sai dai tunda shi ba basarake bane ba, musulunci hudu ya halarta mishi zai iya samu ta wannan hanyar, ko a mafarki kuwa bai hango kan shi da mata hudu ba, yana da halin rike su, amman ba zai iya ba, da ace kwana bibbiyu ne, idan yayi hudun za'a kwashe su a zuba mishi wasu kamar yanda ake kiwon kaji zai so hakan. Har cikin kasusuwan jikin shi yake jin wani irin tsoro na ziyartar shi, sau daya ya kasance da Hindu, amman kamar ba zata rike shi ba, ita din kadai ba zatayi mishi ba. Ba kuma yason inda tunanin shi yake kai shi, shisa ya sakar ma kanshi ruwan sanyi, yana yin tsalle gefe babu shiri, hadi da mika hannu ya kashe shawa din yana maida numfashi. Ruwan yayi mishi bala'in sanyi, dole ya dai-daita zafin.
Bai fito ba saida ya dauro alwala, ya zame towel din jikin shi yana sake kaya, zuwa lokacin yana jin kiran sallah kasa-kasa. Kafar Hindu ya fara bubbugawa a hankali, su duka ba wani baccin kirki suka samu ba, amman idan tayi sallah sai ta sake komawa, shima idan ya dawo ya gama tilawa da azkar din shi bacci zai koma.
"Hindu..."
Ya kira a hankali yana sake dan dukan kafafuwanta, tana jin shi tunda ba bacci takeyi ba, wani malolon bakin ciki ne taji ya taso mata, ya za'ayi a darenta na farko ya dinga tashin ta kamar tana gidan su, ko Asma tasan ta tsani a bubbuga mata kafa in za'a tasheta, tama tsani a bubbuga mata ko ina, tunda ba nauyin bacci gareta ba, idan ka kira sunanta ma zataji. Ya yake so tagane banbancin auren da tayi da kuma gidansu, ita yanzun tana da miji, yanda ta hasaso zai dinga tashin ta daban da yanda yazo yana tashinta yanzun.
Ta dauka daya fito wanka zaizo gefenta ya zauna, saukar ruwan da yake digowa daga sumar shi zata fara ji a wani bangare na fuskarta, kafin lausasan labban shi kan goshin ta yana kiran sunanta cike da soyayya, bayazo yana bubbuga mata kafa yana kiran sunanta gatsau irin haka ba.
"Hindu..."
Tana jin shi sarai, idanuwanta sun fara tara hawayen bakin ciki
"Hindu ki daure ki tashi, in kikayi sallah saiki koma baccin"
Hamza ya fadi yana balle maballan jikin rigar shi, kafin ya kara matsawa yana zama gefen gadon, taji shi, ashe ya iya irin wannan zaman yai mata qerere.
"Hindu..."
Ya kira a hankali yana dora hannun shi a jikinta hadi da dan girgizata, sai lokacin ta bude idanuwanta a hankali tana sauke su cikin nashi, kwan fitila daya ya kunna, babu wadataccen haske a dakin, amman ya isa taga yanda yayi wani irin kyau, fuskar nan fayau da ita, kamar ta kai hannu ta shafi sumar da take kwance luf-luf akan fuskar shi
"Wani abu na miki ciwo?"
Ya tambaya cikin taushin murya, kai ta dan daga mishi a hankali
"Sannu, tashi ki samu kiyi sallah"
Ya karasa maganar yana mikewa, hadi da kama hannunta, ya taimaka mata ta mike daga kan gado, hannunta na cikin nashi harta tashi, tana kokarin langabewa a jikin shi ya tare ta
"Karki karyamun alwala Hindu"
Shagwabe fuska tayi, idanuwanta cike taf da hawaye, bai kamata sam yace ta samu tayi sallah ba, ina laifin ma tunda ta tashi ya dauketa ya kaita bandakin, wankan ma daya jirata sunyi tare
"Ni jikina ciwo yake mun"
Kallonta yayi, yasan dole jikinta zai mata ciwo, amman ba kamar yanda take nuna mishi ba, shagwaba ce kawai take son yi mishi ba wani abu ba, yasan me yakeyi, ba ita bace cikakkiyar macen daya fara kasancewa da ita ba. Hannunta ya dumtsa yana janta zuwa hanyar bandaki, gabaki daya sai langabe mishi takeyi, a dole dakyar take iya taka kafafuwanta.
"Hindu masallaci zan tafi fa..."
Hamza ya fadi, haka kawai yaji dariya nasan kubce mishi, inda yasan wannan rainin hankalin zatayi mishi, daya bata dalili mai karfi nayin hakan. Kallon shi tayi, sosai idanuwanta suke cike da hawaye, shi da yake da sabuwar amarya ina yaga ta fita masallaci
"Ban hanaka ba ai"
Ta karasa maganar muryarta na karyewa, numfashi ya sauke, yana rasa abinda ya kamata yayi, after care din nan sam ba sabon shi bane ba, mace ma bata dade mishi harya tsaya yana lallabata, bai saba ba, komai yana mishi wani iri. Hannun shi ya zare daga cikin nata tunda yana da tabbacin babu abinda ba zata iyayi da kanta ba
"Yanzun zan dawo, kisa ruwa mai dumi sosai kiyi wankan"
Ya karasa yana juyawa, cike da mamaki Hindu take binshi da kallo, da gaske ficewa Hamza yayi daga dakin, da gaske ba zai tayata yin wankan ba, balle tasa ran zai nadota da towel ya daukota ya kawota ya kwantar. Hawayen da suka silalo mata tasa hannu ta share, ta lallaba tana shiga bandakin, shawarar shi ta dauka tayin amfani da ruwa mai dumi sosai. Kafin ta fito kam har jikinta yayi mata dadi. Doguwar riga ta samu ta saka, ta gabatar da sallar asuba, tana zaune tana azkar, harta idar ta karanta Qur'ani shafi biyu Hamza bai shigo ba. Hakan yasata jan jikinta ta mike, hijab din ta cire ta ninke, tana komawa kan gado ta kwanta.
Duka yanda ta hango safiyar yau ba haka tazo mata ba, itama ta hango bayan Hamza ya nadota ya fito da ita, ya sami kaya ya saka mata ya kums gama lallashinta, ta mike tayi sallah, kanta tsaye gaban mudubi zatayi ta tsantsara mishi kwalliyar da zata sake rikita shi, amman ko mai bata shafa ba, turare ma sabo dayine yasa tadan fesa ta cikin rigar jikinta tun kafin tayi sallah. Amman baccin da takeji a idanuwanta da kuma disappointment din da ya danneta bai barta da wani zabi ba. Zata dora laifin akan Hamza, daya bata kwarin gwiwa da tayi kwalliyar, tana wannan mitar a ranta bacci yayi awon gaba da ita.
*
Sosai take jinta daban, komai nayi mata wani iri, da sanyi-sanyi takeyin komai, jiyan batazo mata da wani yanayi ba. Sun fita da rana sukaci abinci ita da Hamza, amman fitar da sukayi da dare tayi mata dadi ba kadan ba, har Havila ya biya da ita ya kwaso mata ice cream. A bangaren shi suka kwana, bata samu dukkan abinda tayi tsammani ba, amman ta sami wani abu daban. Yau kuma tunda sukayi asuba suka koma bacci, basu tashi ba sai wajen goma da rabi, dukkan su wanka sukayi, tunda da dare ya fada mata zasu je su gaishe da Anna. Haka kawai sai zuciyarta ke mata rawa, fargaba na saukar mata.
Ta zabi kaya sunfi kala biyar tana mayarwa, har saida Hamza yace mata
"Ki kwantar da hankalin ki, Anna bata da matsala"
Kallon shi tayi
"Me zan kai mata? In kai mata turare?"
Dan jim yayi, kafin ya daga ma Hindu kai, yasan Anna da kamshi, zataso turare. Kai Hindu ta jinjina mishi
"Dan Allah ki saka kowanne kaya, kinga yunwa nakeji ni..."
Riga da skirt ta dauka na atamfa, ta wuce tabar shi a zaune, sakawa tayi, ta fito da wata Abaya da Baba ya siya mata, baifi sau biyu ta saka ba, saboda tana bala'in ji da ita, natsuwa tayi ta daura dankwalinta, ta feshe jikinta da turaruka masu saukin kamshi, shi kanshi Hamzan kallonta yakeyi saboda yanda tayi mishi kyau, banda jan janbaki da eyeliner babu wata kwalliya a fuskarta. Saida ta samu leda ta zuba turarukan wuta da aka kawo mata, dana sakawa a cikin kaya, da ma wasu ta ajiye a gefe tukunna ta dora abaya din, tana daureta ta zauna mata das,