Showing 48001 words to 51000 words out of 110313 words

Chapter 17 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt

ku Wallahi, kuyi chatting dinku, bashida wani aibu in dai kuka tsarkake zuciyar ku, duk da hanya ce ta shagala da ta same mu, yana dauke hankali sosai daga muhimman abubuwa, dan Allah ku kula"


Kai Hindu ta jinjina mishi, nasihar tashi na zauna mata


"In shaa Allah Yaya"


Wayar ya mika mata, ta karasa tana nuna ma sauran, kafin ta wuce bangaren su ta nuna ma Anty, fadan da Huzaifa yayi mata shi Anty ta sake maya mata. Caji ta saka tana komawa suka ci abincin dare, ko da akayi isha'i anan sukayi. Baba yace jikin shi ya mishi nauyi a gajiye yake, Junior yaja musu sallah, shine ustazun gidan, ya kusan hada haddar shi ta Qur'ani, yaro ne da kallo daya zakai mishi ka fahimci nutsuwar da take tattare dashi da annurin fuskar shi wanda hasken karatun Qur'ani ne kawai yake zaunar dashi.


Huzaifa ana idar da sallah ya fita, baifi mintina sha biyar ba ya dawo, ya mika ma Hindu katin dari biyu, sosai tayi mishi godiya tana jan hannun Khadee suka nufi bangaren su


"Dan Allah kizo ki turamun..."


Hindu ta fadi, nan suka zauna suka kunna wayar, Khadee ta tayata suka saita komai. Tukunna ta fice daga dakin, kan gado Hindu ta koma, tana jin ranta kal, ta siyi go credits daman, shiga 2go din tayi tana fara saka user name din duka kawayenta tayi adding dinsu. Biebee ta fara ansa mata tana turo sakon


"Kawata kin shigo gari, kice Baba ya miki komai yau"


Dariya Hindu tayi a bayyane suna fara hira da Biebee din. Kafin ta shiga Kaduna room1 din, yar kallo ta zama saboda tayi magana tafi sha biyar babu wanda ya kalli ko inda take, abin daya kona mata rai sosai. Dawowa private tayi tana fadama Biebee data turo mata kawunan dariya


"Banza baki ga star dinki a Novice take ba, waye zai kula ki? Haka zaki ci gaba da dagewa har adan fara ganin ki"


Jikinta Hindu taji yadan yi sanyi da maganar Biebee din, da tayi mata sallama dan tace bacci take ji zata kwanta. Fita daga room din Khadee zatayi taga an turo mata friend request. Da kamar ba zata amsaba ganin Elias aka rubuta a jiki. Sai kuma ta amsa, sannan ta fita daga room din. Sallama yayi mata da tasa ta duba profile din shi, zuciyarta na dokawa saboda ganin hoton nashi, ya hadu iya haduwa, bashi da hasken fata, amman yana da kyau, ga kasumba luf-luf kwance a fuskar shi, yasha shadda ruwan kasa da hula. Da alama a zaune yake da mota a bayan shi, sosai yayi ma Hindu kyau.


Sallamar shi ta amsa suna gaisawa, yake ce mata sunanta yayi mishi dadi da harshen hausa, dan tunda suka fara hirar da turanci sukeyi


"Kana jin Hausa daman?"


Ta tambaya, tana saka shi turo mata dariya


"Sunana Illiyas Abdallah. Bahaushe ne ni, ko dan kinga Elias, haka abokai suke kirana"


Dakuna fuska Hindu tayi, sam sunan nashi bai mata ba, dan ita tafi son sunan yan gayu. Meye wani Iliya?


"Yayi kyau, sai da safe"


Ta fadi tana sauka daga kan 2go din batare da ta jira amsar shi ba, WhatsApp din da bata bude ba, ta shiga ta saka lambarta tana yin register. Tukunna ta sauka da kudirin da taje makaranta da safe zata amshi lambobin yan ajin su, itama su san ta faso gari yanzun. Danne-danne ta shiga yi na son ganin komai na wayar. Da Asma ta shigo dakin dakyar ta bata wayar tagani na wasu yan mintina. Har wajen sha daya na dare tayi kuri tana danna waya. Jin motsin Anty yasa ta tura wayar karkashin pilo zuciyarta nayin tsalle har cikin makoshin ta saboda tsoro.


Dan Anty ta mata kashedi banda chatting din dare, tasan kuma tsaf zata iya dinga karbe wayar duk dare inta kula Hindun bata ji maganar da tayi mata ba, Anty na sakar musu fuska yanda ya kamata, amman suna bala'in shakkarta, bata da wasa ta fannoni da yawa. Baccin da bata shirya ba ya dauketa cike da mafarkin wayar tata.


*


Cikin sati biyu yanayin surutun da Hindu take da kuma tsoma baki a cikin duk wani fada da zata gani yasa aka fara ganeta a Kaduna room1 harma wanda ake ji dasu a group din kanyi mata magana, zuwa lokacin request take samu kaca-kaca. Takan amsa wasu, wasu kuma bata amsawa, tunda wanda take so suyi mata request din su Curious ne da su Rugi, amman taqi samu, dan ance mata Rugi ma zaku iya shekara kuna hira a room bai maka request ba. Gashi turancin shi na tafiya da ita.


Duk a tarkacen da tayi babu wanda suke magana dashi sosai kamar Elias, wata irin shakuwa sukai a satika biyu, har sun koma da hirar su ta WhatsApp, yakan kirata da daddare ta shiga bandaki ta amsa a tsorace kar Asma ta farka taji ta, tasan bakar shaida irin tata, tsaf zata kwashe ta gayawa Anty, tayi mata sanadin wayar gabaki daya. Hankalinta a tashe takanyi wayar na mintina ta kashe. Dan dai taga hotunan Elias din, ya tuttura mata, ya kuma yi mata kyau sosai, dan ya iya daukar wanka.


Cikin wata daya kuwa, kaf kawayenta babu wanda baisan labarin Elias ba, wasu suna dan ganin shi a room, amman da yake bai cika magana ba, ba wani sanin shi akayi ba. Sosai sukan yi hira, wani lokaci tana assignment suna taba hirar su. Lokaci daya Elias ya nuna ma Hindu yana so su hadu, hankalinta ya tashi, amman bata so ta nuna mishi ita din ba babbar yarinya bace kamar yanda ya dauketa. Ranar juma'a da daddare yai mata maganar, washegari Asabar tace ma Anty zata shiga gidansu Biebee dan suyi assignment din Nahwu, tunda anyi hutun kwana uku a islamiyar, daya cikin Malaman su ya rasu, sai ranar Monday za'a koma.


Anty bata hanata ba, gidansu Biebee dasu kusan an zama yan uwa, tana shiga suka gaisa da Hajiya mahaifiyar Biebee din Hindu tajata suka shiga daki


"Ke wajen ki nazo fa, Elias naso mu hadu, wallahi na rasa yanda zanyi"


Wani irin kallo Biebee takeyi mata da yasa ta fadin


"Dan Allah Bie, ki fadamun me ya kamata inyi"


Gyara zama Biebee tayi


"Me ya kamata kiyi banda ki fada mishi ba'a barinki zance a gida, sai kin gama secondary, in zai iya jira ya jira. In bazai jira ba yai gaba"


Dafe kai Hindu tayi, Biebee ba zata gane ba, matsalarta daya da ita kenan, komai a tsaye takeyin shi babu wata kwana, yanzun ma dorawa Biebee tayi da fadin


"Ni nace miki baiyi mun bama, hoton shi duka a waje daya, kuma yanayin pattern daya, me yasa ba zai turo miki hoton shi a tsaye ba? Ke ni bai mun ba"


Langabar da kai Hindu tayi


"Bie ki rufamun asiri dan girman Allah, so kike yaje room yana fada musu yarinya ce ni, ina tunanin da mu hadu wani wajen... Sai muje dake kice ma Anty zamuje dubiya... In dake ne ba zata hana ba"


Tunda Hindu ta fara magana Biebee take girgiza mata kai


"Ku hadu ina? Idan dan yankar kai ne fa? Hindu ki rufama kanki asiri"


Hannunta Hindu ta kamo tana fadin


"Bie mana.... Dan Allah kimun wannan abin daya. Ki taimaki rayuwata"


Hannunta Biebee ta fisge tana mikewa, bada ita za ayi wannan rashin hankalin ba, ko bakomai tana jin tsoro, yanzun duniyar babu gaskiya. Shisa inda duk tace zataje bata biyawa wani guri, tana tsoron kar taje wani abu ya sameta, ko babu mutuwa akwai hatsari, akwai rashin lafiya da take dirar maka babu sallama. Idan tace zataje tudun wada a gida, sai ta wuce Malali, wani abin ya faru, ko mutuwa haka iyayenta zasu kasance cikin tunanin me ya kaita malali har karshen rayuwar su. Tunani irin wannan yana hanata abubuwa da dama.


Amman Allah yayiwa Hindu wata baiwa ta samun abinda take so a wajen mutane, bai dauketa mintina talatin ta shawo kan Biebee ba, amman da sharadin inda sukace zasuje nan zasu. In yaso sai Elias din ya same su a bakin hanya su gaisa su wuce. Hakan yayi ma Hindu, hira suka dan karayi tana tashi ta wuce gida ta fadama Elias gobe zasu hadu, amman zata fada mishi ko karfe nawa da safe, sukayi hira dashi tukunna ta kwanta tana jin yanda zuciyarta take lugude, gani take kamar Anty zata shigo dakin ta dauki wayar in tayi bacci, tashi tayi zaune ta dauki wayar tana goge chats dinsu duka, ta goge kiran wayar sannan hankalinta yadan kwanta. Ta samu bacci ya kwasheta.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 11


"Na hango ki"


Hamza ya fadi yanda ya sauke kalmar 'G' din da take cikin 'Hango' din na fito da fulatancin da yake harshen shi, ita kam ta cikin tabaran fuskarta take yawatawa da idanuwa ko zata hango shi


"Ban ganka ba ni kam"


Cewar Hindu tana danne tambayar da take sonyi mishi ta kowacce irin mota yake ciki. Bataso ya fassara tambayar da ko tana so tajini dan tasan darajar da zata dora motar tashi a kai


"Zaki ganni nan da mintina biyu, zan yo kwana ne..."


Titi take kallo sosai, zuciyarta na lugude kamar zata fito daga kirjinta


"Gani nan afuwan....yanzun nan"


Hamza yake fadi cikin sigar da yasata yin yar siririyar dariya, tana jin wani irin shauqi na lullubeta da batasan daga inda yake tasowa ba. Kafin ta hango wata mota ruwan madara kirar Range Rover da baqin gilasai da akema laqabi da tinted, ta tsaya a gabanta


"Gani nan na karaso"


Taji muryar shi a kunnenta ta cikin wayar, kafin ya sauke gilashin motar hadi da sauke wayar daga kunnen shi, yana saka Hindu jan wani numfashi da taji yaki kai mata inda ya kamata. Da alama suspenders ne a jikin Hamzan, dan tana ganin belt din kayan dayake a kafadun shi ya zagaya zuwa bayan shi inda take da tabbacin yana maqale a mazaunin shi jikin wandon shi, rigar shi fara kal mai dogon hannu, ya dora hular hat daya dan tura baya, idanuwan shi kal-kal dasu kamar bai taba cin karo da hayaqi ba, tamkar hawaye basu taba zama a cikin su ba balle su bata asalin hasken da suke dashi.


Yanayin fatar shi yafi komai ba Hindu mamaki, batasan ko idanuwanta bane kawai suke ganin salqin da yakeyi saboda kyawun da yai mata. Bata taba yarda da cewa mutum na maka kyau har kaji numfashinka na tsai-tsayawa ba sai yau, sai yanzun da ta rasa yanda zatayi ta dauke idanuwanta daga kan Hamza


'Kice wani abu mana Hindu'


Wata murya ta fada mata a cikin kanta


'Ki daina kallon shi kamar wata sakarai, kice wani abu'


Muryar ta sake fadi, amman ta kasa ko motsin kirki balle ta iya furta wani abu. Hamza kuwa tun da ta fada mishi kalar Hijab din da take jikinta ya fara hangota, daga farko zai karya idan yace kalmar 'Hijab' din data furta bai mishi wani iri ba, fita yace zasuyi suci abinci, ba wajen wa'azi yace mata zasuje ba. Duk da hotunan da take dorawa da Abaya a jikinta, banda dankwalin kanta wasu lokuttan ba zaice ga kalar kayan da yake kasan Abayarta ba. Amman 'Hijab' ta mishi wani iri sosai. Bayason harkar rashin wayewa, tashin farko da suka fara magana batayi mishi kama da local ba.


Sai da ya zagayo ya hangota sosai, sai yanzun kuma daya sauke gilashin mota yake kare mata kallo, bai taba tunanin mace zata saka Hijabi tayi mishi kyau har haka ba, duk da zaiyi komai dan ya daga hijabin yaga abinda take boyewa a kasan shi, amman tayi mishi kyau babu karya. Tabaran da ta sakane ya hana mishi ganin idanuwanta. Murmushi ya tsinci kanshi da yi hadi da fadin


"Muje?"


Sai lokacin Hindu ta iya daga mishi kai, tana samu ta motsa kafafuwanta dakyar ta zagaya ta bude murfin motar ta shiga. Wani irin kamshi mai sanyi na dukan hancinta. Haka kawai ta tsinci kanta da yin murmushi, zuciyarta take so ko yayane ta tsagaita da dukan da takeyi. Amman kamar da Hamza yaja motar ma zuciyarta kara dokawa tayi


"Kin san yunwar da nake ji? Banyi breakfast bafa"


Hamza ya fadi saboda shirun motar yayi mishi yawa. Kuma da gaske bai karya ba, wani irin bacci yayi, sanda ya tashi kuma ana jiran shi a wajen aiki. A gurguje ya shirya ya fita, yanzun ma sai da yazo zai taho yaga AbdulHafiz ya daukar mishi mota yabar mishi wannan da yake ciki, baisan me yasa yake son daukar mishi mota ba, ta AbdulHafiz din har tsada da komai tafi, sai yace ta mishi girma, dan Yayan shine ya bashi kyauta shisa yake dauka, bawai dan yana so ba.


"Me yasa?"


Hindu ta tambaya tana wasa da yatsun hannuwanta, rage gudun motar Hamza yayi yana dan kallonta kafin ya mayar da hankalin shi kan tuqin da yakeyi


"Ba zamuyi haka dake ba, ba zaki fara mun kunya-kunya ba, bana so, ba zamu shirya ba idan kikace zaki fara jin kunyata"


Wannan karin dago kai tayi tana dan juyar dashi ta kuwa yi sa'a shima ya juyo da nashi kan suka hada idanuwa, nata zata sauke yadan girgiza mata kai


"Bance kunya ba abu bane me kyau, bana sone kawai. Don't be local mana Hindatu"


Dan tari tayi kadan tana hadiye yawu saboda tunda take ba'a taba furta sunanta cikakke da yanayin da Hamza ya furta ba, tsallen da zuciyar ta tayi sai da tajita a makoshinta. Har wani zazzabi takeji yana shirin saukar mata. Kuma shi gaskiya ya fada mata, shisa duk tunanin shi, duk yanda ya hango da wahalar gaske ya iya auran cikakkiyar bahaushiya, bayason gidadanci, idan tace wannan sunkuyar da kan, amsa mishi magana dai-dai zata dingayi, yaune ranar karshe da zata sake ganin shi, zai kokarin hadiye kwadayin shi a kanta dan ba zai iya ba.


Kuma zai karya idan yace bata burgeshi ba, kominta yayi mishi, komai nata yasa shi son daga hijabinta yaga sauran sirrikan da suke tattare da ita. Amman hakan ba zai yiwu inta fara da jin kunyar shi ba. Itama kokari takeyi taga tadan ce wani abu, amman yaune karo na farko da ta taba kebewa haka da wani namiji da ba muharraminta ba, a mota su kadai suna nufar inda bata ma sani ba


"Ina zamu je?"


Ta bukata, tana saka Hamza sauke numfashi, yadan daga mata kafadun shi


"Ina kike so muje? Na fada miki yunwa nake ji ko?"


Yar dariya tayi tana daga mishi kai


"Good... Ina ya kamata muje?"


Dan jim Hindu tayi, ita ba wani wajajen cin abinci ta sani ba


"Duk inda kake so"


Dan kallonta yayi yana daga girar shi duk biyun


"Kin tabbata?"


Ta jinjina mishi kai, yanda yake kallonta duk da na wasu dakika ne ya sa gwiwoyinta kamar an bubbuge su da guduma, duk sunyi mata wani irin sanyi. Yanda yake abubuwa kamar baisan komai kara mishi kyau yake ba na kara sakawa ya burgeta matuka. Numfashi ya sake saukewa, yana yanke hukuncin zuwa Byblos Restaurant da yake Abakpa, ta wajen Waziri Ibrahim Crescent. Suna da abinci kala-kala na kasa Najeriya, Lebanese harma da Mediterranean. Indai ba sauri yake ba yakan zo nan, wasu lokuttan kuma yai order tunda suna kaiwa har gida.


"Kin gama assignment din jiya?"


Kai Hindu ta girgiza mishi


"Na ajiye, Electric nake son karasawa in huta"


Murmushi Hamza yayi


"Oye ko?"


Hindu ta daga mishi kai suna dariya su biyun


"Mutumin nan ya bata mana lokaci ba kadan ba"


Idanuwanta ta juya


"Kai ma kenan daka gama, kuma ance zai mana Settlement ne ko meye next semester"


Sai da Hamza yadan kalleta cike da tausayawa yana girgiza kai sannan yace


"Hindu"


Wannan karin ita ta dan kalle shi


"Oye zai kashe ku"


Yanda yayi maganar ya bata dariya sosai, hira suke zaka rantse da Allah sunyi shekaru da sanin juna, ba yau bane haduwar su ta farko. Hamza na cikin mutanen da zasu sa ka sake dasu lokaci daya, bashida wahalar magana, kuma yasan yanda zai jaka da hira ko da bakayi niyya ba. Ba Hindu kadai taga haka ba, abokan shima sunfi so yayi magana da mutane a wajen aiki, musamman idan akace cinikin kudin aikinsu za'ayi. Sai kayi mamakin kudin da Hamza zai caji mutane kuma su biya suna fara'a. Yana da wannan baiwar ta samun abinda duk yake so a wajen mutane, saboda zai nuna maka kana da wani irin muhimmanci da bakasan kana da shi ba.


Yanzun a yan mintina kasa da ashirin daya dauke su zuwa Byblos Restaurant, Hamza yasa Hindu tanajin kamar tana da wani muhimmanci mai girma a wajen shi, a cikin hirarsu ya tabbatar tasan irin aikin daya tsallake ya fito, har saida taji kamar bata kyauta ba, kamar ita dince ta roki ya fito bashi da kanshi ya nemi ganinta ba


"Da ban sa ka fito ba, ba zaka sami matsala a wajen aiki ba dai ko?"


Hindu ta tsinci kanta da fadi lokacin da Hamza ya sami guri yayi parking din motar, dan gabaki daya yasa taji bata kyauta mishi ba daya fito. Sai da ya murza mukullin motar yana kashewa, ya daga gilasan tukunna ya girgiza mata kai


"Karki damu, it's worth it, nagan ki fa, shine abu mai muhimmanci yanzun"


Murmushin jin dadi Hindu tayi, tana kallo ya bude murfin motar, itama hakan yasa ta bude nata bangaren tana fita. Sosai take jinta sama-sama. Tunda take babu wanda ya taba fada mata magana mai dadin wanda Hamza ya gaya mata yanzun. Ta jira Hamza ya zagayo, tana karema shigar shi da tayi matukar burgeta kyau, duk da takalman da suke kafarta ko kafadun shi kanta bai kai ba, dogone, tsayin shi fiye da wanda take mafarkin samu, hannun shi ya mika mata yana kankance idanuwan shi kamar yana so taga yanda girar shi take a ciki, da mamaki ta dakuna fuskarta, dan batasan me zata bashi ba, sai da taga ya matso dab da ita yana saka zuciyarta wani irin dokawa


Jakar da take sakale a hannunta yadan kama, tana amfani da dayan hannunta ta zare jakar cikin sauri, dan batason abinda zaija ya tabata, sosai zuciyarta take mata wani irin lugude. Hamza nazarin duk wani motsinta yakeyi, amman baya iya ganin idanuwanta ta cikin tabaran balle ya fahimci kadan cikin abinda take tunani. Da dayan hannun shi ya rike jakar yana jerawa da ita hadi da fadin


"Muje?"


Kai Hindu ta daga mishi, duk da bugun da zuciyarta yakeyi a cike take taf da wani irin yanayi. A film kadai ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login