Showing 3001 words to 6000 words out of 110313 words

Chapter 2 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt

Hindu take, yayi tsaye ne kamar an dasa shi. A wahalce ta karaso wajen shi tana wani irin kuka kamar zata shide


"Baa... Baaba na"


Ta fadi muryarta na sarqewa, hannu Baba ya mika ya kama na Hindu da baya tallafe da cikinta, yanajin sanyin daya dauka kamar kankara, shi kan shi da baifi minti biyu da shiga ruwan ba yayi sharkaf, ledar dake hannun nata yake bi da kallo


"Ham... Hamza ya bani"


Ta fadi dakyar, karbar ledar Baba yayi ya saka cikin aljihun jallabiyar shi yana taimaka ma Hindu da takejin bayanta kamar zai rabe gida biyu, numfashi ma a wahalce take jan shi tana fitarwa, Baba ji yake tamkar zai kama da wuta saboda bacin rai. Mota ya bude yana taimaka ma Hindu ta shiga, dai-dai lokacin da wata motar ta tunkaro wajen, tsaye yayi bayan ya mayar da kofar ya rufe, Muhsin ne da Huzaifa suka fito suna karasowa inda Baba yake


"Ina Hindun?"


Huzaifa ya bukata dan inba ganinta yayi ba hankalin shi ba zai kwanta ba, murfin motar Baba ya bude mishi yaganta a zaune ta jike sharkaf, numfashi Huzaifa ya sauke cike da nutsuwar da ta saukar mishi


"In dai na isa da ku bana so kayanta su kwana a gidan marar mutuncin nan"


Baba ya fada yana saka Huzaifa kallon shi cike da tashin hankali


"Baba kayi hakuri dan Allah, ka isa Wallahi har kayi yawa ma, amman yanzun dare ne, gashi ana ruwa, ba lallai a samu masu motar da zasu fito ba"


Huzaifa ya karasa maganar da sigar lallashi, yana saka Muhsin dorawa da


"Kayi hakuri Baba, gobe tunda sassafe, kaga yanzun ya kamata muje gida ta sake kayan nan kar zazzabi ya kamata"


Kai Baba ya jinjina wani abu ya tokare mishi makoshi, bai ba Hamza auren yar shi dan yagaji da ita ba, duk da burin kowanne iyaye shine suga yaransu a gidajen mazajen su, amman idan babu kwanciyar hankali da nutsuwa gara ya dinga ganin yar shi cikin gida kullum, zai fi mishi wannan bakin ciki. Dakyar ya iya bude motar ya shiga, dan shima duk ya jike, sai da ya zauna tukunna ya kalli su Huzaifa yace


"Ku wuce gida kawai, goben idan an samu motar da zata kwashe kayan ku kirani"


Wannan karin su duka suka jinjina ma Baba kai, suna tsaye har saida sukaga ya bace musu, tukunna suka koma mota, gida Huzaifa ya fara sauke Muhsin, tukunna ya wuce nashi gidan shima.


*


Wani irin sanyi take ji yana ratsata har cikin kwakwalwar ta yana hana mata wani tunanin daya wuce na son rufa da katon bargo ko zataji dumi. Da suka karasa gidama, Baba ne ya bude mata bayan motar, amman tayi galabaitar da ta sakko kafafuwanta wajen motar, amman ta kasa raba jikinta da kujerar.


"Hindu?"


Baba ya kira ganin yanda take fitar da numfashi a wahalce yana dorawa da


"Ko mu wuce asibiti?"


Kai Hindu ta girgiza mishi, kwanciya kawai take so taji tayi, ba zata iya zaman motar ba har su sake nufar asibiti. Dakyar, hannunta daya dafe da cikinta, dayan kuma ta rike kofar motar ta raba jikinta da kujerar tana mikewa tsaye hadi da runtsa idanuwanta kafin ta sake budesu cike da gajiyar da take ji. Baba na tsaye yana kallonta zuciyar shi cike da tausayin yar tashi, a gefe daya kuma fal da bacin rai, ita ta fara yin gaba tana karasawa wajen kofar tasa hannu ta murza tana turawa ta saka kafafuwanta cikin falon. Tana karasawa kan kujera ta zauna, Baba kuma ya wuce cikin daki inda yabar Mama, ba bacci takeyi ba tun fitar shi, tana kwance ne tana tunane-tunane, ta kunna fitilar and wayarta tunda babu wuta dan ana ruwa har lokacin


Tana jin sallamar shi ta mike tana fadin


"Kun dawo? Ina Hindatun?"


Hanyar waje Baba ya nuna mata, babu shiri ta sakko da kafafuwanta. Tana daukar wayar ta wuce falon ya rufa mata baya, kallo daya taiwa Hindu taga yanda take a galabaice, tana karasawa taba fuskarta tayi zuwa wuyanta tana jin yanda zazzabi ya rufeta ruf


"Alhaji da asibiti aka wuce da ita ai, kaji zazzabin da yake jikinta?"


Mama ta fadi kafin ya amsa tana dorawa da


"Tashi muje ki cire wannan jikakkun kayan"


Saida Hindu ta sa bayan hannunta tana goge hawayen da taji ya zubo mata, tukunna ta kama hannun Mama data riko kafadarta dan taimaka mata, ta mike, dakin Mama din suka nufa tana bata kayanta, ta sake a wajen, dan wata kunyar Mama ce karshen abinda takeji. Sake kama hannunta Mama tayi suka fito daga dakin zuwa dakin baki da yake gyare tsaf, har sauri Hindu take karawa dan so kawai takeyi tajita a kwance, har wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke data kwanta, Mama ta rufa warware katon bargon da yake dakin tana rufa mata. Gefen gadon ta zauna tana kallon Baba daya biyosu ya kasa samun nutsuwa shima tace


"Kaje ka sake kayan jikinka kaima ka kwanta, zan zauna da ita zuwa safe in Allah ya kaimu"


Dan jim yayi kamar zai musa, tukunna ya jinjina kai yana wucewa ya fita daga dakin, duk da shine karshen abinda yake so yayi. Yafi so ya samu waje ya zauna sai yaga Hindun ta warware tukunna. Da tunanin ko da Hamza ne namijin daya rage a duniya Hindu tagama auren shi har abada Baba yake sake kaya. Shi da an sami mota ma cikin daren za'a kwashe kayan, tunda shi bashida mutunci.


Mama kuwa da taga ya fita, jikin Hindu ta sake tabawa taji da zazzabi har lokacin, tana kallon duk da idanuwan Hindu din a rufe suke, hawaye ne kawai yake zubar mata yana sauka ta gefen karan hancinta zuwa kan pillow din da take kwance


"Kiyi hakuri ki daina kukan nan Hindu, kinga bake kadai bace, karki jama kanki wani ciwon kinji ko?"


Kai kawai Hindu ta daga mata badan tana da wani iko akan zubar hawayen nata ba, su suke fitowa da kansu saboda kwanciyar da tayi da dumin bargon da ya rufe jikinta ruf yaba kwakwalwar ta damar tunanin asalin halin da take ciki. Ba tayi mamaki dan Hamza ya koreta tsakiyar dare da tsohon ciki, ana kuma ruwan sama ba, tana da tabbacin yana can kwance yana baccin shi a nutse, dan babu wani abu da yake shiga tsakanin shi da baccin shi. Yakan ce


'Koma meye zai iya jira, bacci na ba zai jirani ba'


Sake runtsa idanuwanta tayi gam, har radadi suke mata da tasan kukan da tasha ne a daren, kukan da ba yanzun ta fara yin shi akan Hamza ba, bata dai san ranar karshe da zata daina ba, da gaske takeyi lokacin da tace mishi


'Na manta ranar karshe da hawayena suka zuba akan wani abu da ba kai ba'


Sai takejin kamar tun tana yarinya rabon da wani abu ya sakata kuka sai bayan ta hadu da Hamza, daga ranar ta fara kukan da ya kawota inda take yanzun


"Ko dai sai munje asibiti a daren nan?"


Mama ta tambaya cike da damuwa, dan ita kam bataso taga mai ciki a wani hali. Tunda tasan shi kanshi daukar nauyin cikin idan aka barka dashi batare da an kara maka wani ciwon ba ya isheka. Cikin disashiyar murya tace


"A'a Mama, bacci nake so inyi"


Bawai dan tana jin baccin ba, kai Mama ta jinjina


"In kawo miki ruwa"


Kai kawai Hindu ta iya girgiza mata da alamar a'a. Kyaleta Mama tayi a zuciyarta tana mata fatan samun sauki, ta hau kan gadon tana jan mayafi ta rufe kafafuwanta sannan ta kwanta, dan kanta harya fara ciwo, gara ko baccin kasa da awa biyune ta samu kafin asuba, fitilar wayar ta kashe tana lumshe idanuwanta.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 7


Shekara daya bayan gama diploma dinta, ta sake samun gurbin karatu na HND ana Polytechnic din ta Kaduna, duk da Baba yaso ta gwada Direct Entry ana KASU, amman sam makarantar ta gama fita daga ranta, haka kawai take son cigaba dayin Poly din saboda tana sakata jin wani kusanci na daban da Hamza. Ita kanta zuwa yanzun tasan inda a kasar wajene idan Hamza zai kai kararta tsaf za'a kamata da laifin bibiya, wato stalking a turance, a shekara daya da wani abu duk wani hoto da Hamza zai saka akan idanuwanta, tana liking ta kuma yi mishi comment a shafin shi na Instagram, dan ta tabbatar Hamza ko dan wasan film ne ko kwallon kafa, yanda take bibiyar shi yaci ace ya kula da ita, ko da sau dayane ya tanka.


Amman ko inda take Hamza bai taba kallo ba, har haushin kanta take ji wasu lokuttan idan ta gama yi mishi dogon sharhi musamman akan gine-ginen da yakan dora. Ranar da taga ya dawo Najeriya ji tayi kamar an mata albishir da kujerar Hajji, kamar Hamzan zai kulata saboda suna jaha daya, kuma taga dan Kaduna ne daga yanayin wajajen cin abincin da suke hotuna a ciki shida abokan shi. Amman ko like bai taba dannawa akan comments dinta ba. Ta kuma kasa daina yi saboda yanda yake bala'in burgeta.


Zuwa yanzun Samari takeyi kala-kala, ta kasa tsayar da hankalinta akan guda daya, dukkan su saita sami abinda ta kushe a jikin su, duk nasiha da Anty take zaunar da ita tana mata, ta kunnen dama take shiga ta fita ta haggu, daman ita kadai ta rage a gidan da take mata magana akan maganar tsayar da Saurayi daya, Baba kam da Anty ta gwada yi mishi zancen, ca yayi


'Ki kyale yarinyar nan dan Allah, duka Hindatun nawa take da kikabi kika dami kanki akan ta? Ba karatu takeyi bane wai? Ko kin manta shi auren nan lokaci yake dashi?'


Daga ranar kuwa Anty bata kara daga mishi zancen ba, amman yana damunta matuka, tana kuma addu'a akai. Ita kanta Hindu abin na damunta, yanda har yanzun ta kasa tsayar da hankalinta akan saurayi daya, ta kasa samun wanda zai kwanta mata. Ba sosai take hawa manhajar WhatsApp ba, balle kuma facebook da take dauka sai gidadawa suke yinshi yanzun. Dimples ta koya mata zaman Twitter ba kadan ba. Da yake ita Dimples can tafi ganewa, ko kace ka mata magana a whatsapp bata amsa ba zata ce maka


'Baka dubani a Twitter bane ba'


Itama Hindun tunda tagane kan Twitter tasan cewa nan din wata duniya ce ta daban, ta hada duk wasu manyan gayu da kake tunani, babu kuma karya kamar yanda akanyi a Instagram. Akwai manyan yaran da suke burgeta sosai a Twitter, yaran attajirai ne daga yanayin shigarsu da motocin da zaka gansu a ciki, duk da kyawun su bai kai mata inda take so ba. Takan shiga wasu lokuttan a dama da ita, kusan tafi Dimples shige-shige a Twitter, ita Dimples idan ma bata sanka a gaske ba, ba zata taba sakar maka fuska har kuyi wata hira ba, ko kabita ma, ba zata amsa gayyatarka ba.


Kalar hotunan da Hindu take sakawa a Twitter yasa take da tarin Mabiya, duk da shigace ta mutunci a jikinta, duk da abaya, sosai ake mata kallan Babbar yarinya. Watan nan daya kama aure akeyi kaca-kaca a twitter, sai kaga matan sunce daga mazan sun tura musu DM wato sako ta inda su kadai zasu iya gani, su kuma suka amsa shikenan soyayya ta ƙullu tsakanin su, yanzun gashi har dunyi aure. Kuma sai taga mazan sun haɗu, ga kuɗi suna dashi, inta duba shafin su sai ta samu basu da wasu mabiyan kirki kuma basa saka hoto ko ɗaya. Abin na matuƙar burge Hindu, ita duk wanda suke mata DM tarkace ne.


Haka kawai saita fara ji a jikinta kamar itama mijinta zai fito daga Twitter ne,tunda taɗan rage burin nata, tanajin kamar ko gajerene indai yana da kuɗi sosai wataƙila ta haƙura taga abinda Allah zaiyi. Lokaci ɗaya ta fara ganin Musbey da suke following ɗin juna yana kwaso mata shafin wani Jalil idan yayi retweet ɗin posting ɗin Jalil ɗin da yake siyar da kayan sawa na maza wato kaftan. Daga yanayin kayan zaka fahimci irin kuɗin da yake dasu, duba shi tayi taga mabiyan shi kaɗan, ko data duba hotunan shi duk tallar kayane da suka ji sirfanin hannu da alamu suka nuna zaiyi tsada matuƙa. Saita tsinci kanta da following ɗin shi kafin ta sauka daga kan Twitter ɗin.


*


"Usztaz kasan dai ya kamata kayi aure ko?”


Abokin sa Adam yace mishi.


"Wai meyasa kuke ce mishi Usztaz ne? Bafa ustazu bane, rashin kaya ne kawai ke ɗawainiya dashi."


Aliyu yai maganar yana takaicin Ustaz din da ake kiran Jalil dashi, saboda ko kusa bai hada hanya da Ustazai ba. Jalil wanda aka fi sani da Ustaz baice komai ba, maganar mutane bata damunsa. Ba yau bane rana ta farko da mutane da abokan sa suke mishi maganar aure. Amma ta ina zai iya aure tunda ba shida sana'ar kirki. A shekaru arba'in da biyu sana'ar aikin hannu yakeyi. Yana saƙa design a riguna. Shima shagon ba nashi bane. Na wani wan mahaifinsa ne wanda ya gaji da ganin sa yana zaman banza.


“Haka kurum kuyita ce mishi Ustazu kamar abin arziki, daga namiji yana saka manyan kaya shikenan ya zama na kirki?”


Aliyu ya cigaba da sababi. Da Adam da Aliyu yan biyu ne yan shekaru ashirin da bakwai. Sabbin zuwa ne a shagon kuma jininsu ya haɗu dana Jalil, saidai idan ka fita kace mishi Jalil babu wanda zai sani. Anfi saninsa da Ustaz wanda ba'a san inda ya ɗauko laƙabin ba. Shi Jalil yana san gayu amman bashida hanyar da zaiyi, haka ya haƙura abinshi. Tunda yake jikinsa bai taɓa marhaba da English wears ba, toh saidai na haihuwa. Tun tashin shi ya saba saka kwabɗa kwabɗan yadi ko mai kwabo kwabo. Duka kayansa sunyi mishi girma. Gashi bala'in siriri baida faɗin kirji. Yana yanayi da ɗan shekara talatin da biyu yasa yake yarintar sa babu kama hannun yaro. Dan Jalil irin mutanen nan ne da sun girma basu san sun girma ba. Gashi idan yana tafiya saboda girman kayan shi da rashin kiba sai yayi maka kamada tuta.


Cima zaune ne na bugun jarida. Yan kuɗaɗen sa dayake samu baya komai dasu sai siyan data domin yaga kyawawan mata sannan kuma idan an dace ya samu wanda zata aure shi a yadda yake. Yanada NCE wanda yayi a FCE Zaria inda ya karanta English and Literature. Wannan ɗan turancin ne yake ma yan mata bagu dashi. A manhajan Twitter yaji labarin cewa akwai wasu manyan yaran attajirai, tun lokacin ma ta Web yake shiga, bashi da wayar da take sauke application, sai dai yana cikin mutanen da ake ma laqabi da Low-key a Twitter. Baya shiga duk wani rikici ko drama da za'ayi, kawai dai idan abu yayi mishi, sai yayi liking ko retweet, mabiyan shima basu da yawa, amman akwai wanda ake ganin girman su a Twitter da suke bin shi, sosai Jalil ya iya kama girman shi a Twitter ba kamar a fili ba.


Kasancewar Ustaz Jalil a Twitter yasa shi kara wayewa ta fannin da baka tunani, duk da rashin gayun na nan, kafin Twitter yaji yanda ake fadin fararen kaya girma ne, daga lokacin ko dan yadi zai siya sai ya siyi fari, naya saka wani kaya face fari, kuma idan aka ce farin kaya bawai ana nufin farin da mutane suka sani ba. Duk sun koɗe sunyi dariya ta wajen wuyan. Gashi yanada wani farin half cover wanda ya koma kalar madara. Ya saba idan manyan mutane sun kawo ɗinki saiya ɗauki hoton kayan ya wallafa, sannan yace shagon sa ne yanzu yaran ciki sukayi mishi aikin.


*


Zata ce kusan sati biyu da tayi following ɗin Jalil amman baiyi follow back ba, hakan ya sakata tunani barkatai, sai taita ganin kamar ita ce take bin arziƙi shikuma yana ƙinta. Hindu bata taɓa mashi magana ba, tunda dai duk matan da takeji dun sami mijin aure a Twitter duk mazan ne suke fara musu magana, amma tana kallon duk wani rubutun da zaiyi, ya kuma iya turanci ba kaɗan ba. Yanayin sa yana burgeta. Babu ruwan shi. Saidai ya watsa hotunan da yaran shagon sa suka yi kamar yanda yake cewa ya tafi.


Akwai wani kwarjini dayake mata na rashin dalili, bawai ta taɓa ganinsa bane tunda yana cikin mutanen da ko kadan basa saka hoton su,amma kuma yana bala'in birgeta. Wata Isha datayi aure kwanaki tace mijinta a twitter suka haɗu kuma baida followers sosai. Watau attajiran ba'a sansu ba. Gashi kuma mijin Isha ya haɗu cikakken namiji, Allah bai rage shi da komai ba ta fannin halitta. Hindu ta kasa gane dalilin daya sa take ganin cewa Jalil yana cikin wannan sashen. Kuma idan wannan manyan kayan dayake wallafawa daga shagon sa ne. Toh ai kakanta ya yanke saƙa. Dan kullum da kalar wanda zai saka.


Yau haka kawai ta tsinci kanta da yin liking ɗin hoton kayan da ya saka. Ko wayar bats ajiye ba taga yayi following ɗinta, wani irin murmushi taji ya ƙwace mata.


Shi kuma Jalil ana shi ɓangaren dan ƙarfin hali su Adam suna mashi magana ko jinsu baya yi dan sam sai yau ya kula da Hindu tayi following ɗin shi,satin ba'a sami wani aikin kirki ba, yanata lallaɓa data din shi karta ƙare da wuri,shisa baiyi wasu shige-dhigen rashin dalili ba sai yanzun da yaga tayi liking hotunan daya saka, nan take yai follow back yana shiga profile ɗinta. Bin hotunan Hindu yayi yana kallo, ta bala'in birge shi. Bawai aurenta yakeso yayi ba, kawai dai ko gaisuwa su rinƙa yi ana mutunci. Tunda shi kanshi yasan bakin rijiya ba wajen wasan makaho bane.


Sallama yayi mata, abin kuma yayi mugun bata mamaki. Kamar yasan yanzu tayi tunanin ko ita tayi mishi sallamar, Har ga Allah nan take Hindu ta fara hasaso yanda bikinta da Jalil zai kasan ce, tasan shine zai zamo uban yaranta. Batayi jan aji ba ta amsa.


“Wohoho... Maraba garsarshe!”


Jalil yace da ƙarfin tsiya. Yana saka Aliyu ɗagowa cikin ƙunar rai


“Ya dai Ustaz meye haka muna aiki kana mana ihu, kamar wani ƙaramin yaro"


Dama cikin tagwayen yafi zafin kai. Kuma bayason yanda Ustaz bashida kamun kai


Kallonsa Ustaz yayi yana dariya, saiya kara masa wayan a fuska


“Kalli abinda ya faru, nayi kamu jama'a"


Yace sannan ya miƙe ya soma taka rawa. Irin rawar nan da Ibro keyi da kafa ɗaya bayan yaci ɗammara. Haka yayita

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login