Showing 63001 words to 66000 words out of 110313 words
Chapter 22 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt
suke suka karasa, har wajen motar Hamza ya raka shi
"Zaka iya tuqi?"
Ya tambaya, Hamzan nayin wani irin shiru, saboda ya nisa cikin tunanin da bazaice ga na menene ba, dan taba shi Fodio yayi tukunna ya daga ma Fodio din girar shi duka biyun
"Hamza, Hamzaaa"
Fodio ya karasa cike da roko
"Nayi yarinta da ciwon zuciya, Hamza ka bari in mayar wa AbdulHafiz kai lafiya sai kayi duk abinda zakayi"
Sai lokacin Hamzan yayi dan murmushi
"Bana son iskanci Fodio"
Sharce goshin shi Fodio yayi
"Kana tsoratani yau din nan"
Murfin motar shi Hamza ya bude yana shiga, saida ya rufo tukunna Fodio ya wuce yana shiga tashi motar, su duka suna fita daga gidan, dayake Fodio baima dade da samun maigadi ba, su suke jigilar bude gate dinsu da rufewa da, yanzun ko gidanma bai damu daya kulle ba. Malali suka nufa dan su zasu dauki su Hindu, gudun da Hamza yakeyi da mota, Fodio addu'a kawai yake a ran shi su dauke su, su karasa wajen dinner din lafiya
"Karka bari yayi wani shirme"
AbdulHafiz ya jaddada mishi kafin ya fita, bayajin yasan wani abu shakka, ko kuma shayin wani tun tasowar shi, ko Yayyen shi tunda ya kawo karfi babu wanda zai daga mishi dan yatsa bai lankwasa ba, amman AbdulHafiz na mishi wani irin kwarjini naban mamaki, akan AbdulHafiz din yasan me ake nufi da samun Babban Yaya da har ranka kake da tabbacin zai kula dakai da duka zuciyar shi, har a kullum yana godema Allah daya kadarta kasancewar AbdulHafiz din a rayuwar su, dan shi Alheri ne tare dasu gabaki daya.
Suna karasawa, Hamza ne ya fara shiga da motar, ya samu waje cikin harabar gidan yayi parking dinta, a jiki yabar mukullin yana fitowa, cikin gidan ya shiga kanshi tsaye, duk da bazai ce ga dakin da Hindun take ciki ba, amman yaji hayaniyar su, dan haka ya nufi dakin da yake anan kasa, tunda gidan hawa biyune. Kwankwasawa yayi, yana tattaro duk wani karfi daya rage mishi ya dora murmushi akan fuskar shi
"Waye?"
Yaji muryar Dimples da yanajin ita kadai zai iya ganewa duk a kawayen
"Ku fito"
Hamza ya fadi, yana gani aka murda hannun kofar ana budewa
"Ango kasha kamshi"
Dimples ta furta, murmushi ya karayi
"Ku fito ko zasuyi wata magana, kafin suce mun saka musu ido"
Dimples ta fadi tana raba Hamza ta wuce, su Biebee ma wucewar sukayi, Hamza ya taka yana shiga cikin dakin, hadi da mayar da kofar ya rufe, a tsaye ya hangota, tayi wani irin kyau naban mamaki, jira yake yaji abinda yakeji duk idan ya ganta, musamman yanzun da take halalin shi, amman sai takeyi mishi kamar abincin da ya dade yana jira bayan matsananciyar yunwar da har taci shi ta cinye, saboda haka duk wani zumudin da yakeyi ya fita daga kan shi. Takawa yayi ya karasa inda take, kamshin da takeyi na saka shi lumshe idanuwan shi, kafin ya kara bude su a kanta.
Itama yawatawa takeyi da nata idanuwan akan fuskar shi,duk da sai da ta daga kanta saboda tsayin shi, yayi mata kyau matuqa, hular kan shi kalar kayan jikinta. Magana take sonyi, amman batasan abinda ya kamata tace mishi ba, ga zuciyarta da take ta dokawa kamar tana son fitowa ta nuna ma Hamzan abinda harshen Hindun ya kasa furta mishi, hannun shi ya dago yana saka yatsan shi ya taba janbakin da yake kan lebenta da yayi mishi kyau matuqa, kafin ya sauke hannun yana amfani da duka biyun ya kamo kowanne cikin nata.
Dago dasu yayi, ya ware tafukan hannuwanta yana dorawa kan kuncin shi hadi da runtse idanuwan shi yana sauke numfashi
"Lafiyar ka?"
Hindu ta bukata a tsorace, yanayin shi yana saka gwiwoyinta yin sanyi, hannun shi yana kan nata da yake kuncin shi, har lokacin idanuwan shi a lumshe suke, ya girgiza mata kai
"Ko ma maka wani abu?"
Ta bukata cike da son gano inda matsalar take, dan wannan ba Hamzan ta bane ba, Hamzan da yake nuna mata ya kasa jira hannuwan shi su sauka a kanta, yanzun gata a gaban shi a matsayin tashi, amman ta nemi duk rawar kan nan ta rasa, sai lokacin ya bude idanuwan shi yana sauke su cikin nata
"Bake bace ba, babu abinda kikayi mun"
Kai tadan daga mishi tana sauke numfashi, kafin a hankali ya sauke hannuwanta daga kan kuncin shi, yana dan dumtsa yatsunta, kafin ya saki hannuwan nata, wani irin mayafine yake gani kamar alkyabba, amman daga kafadarta yake manne, ya sauka har kasa yana baje, yayi mishi kyau, kamawa yayi yana kara gyara mata
"Kinyi kyau"
Ya furta da wani irin sanyin murya da yasa kai kawai ta iya daga mishi
"Muje?"
Ya bukata, ta daga mishi kai, jakarta ta dauka tana rikewa a hannunta, wayarta na hannun Biebee. Tare suka fita, Hamza ya bude mata mota ta shiga, yana tayata tattare rigarta da mayafin ta shigar cikin motar sosai, kafin ya zagaya ta dayan bangaren yana shiga shima. Tayar da motar yayi, yana fita daga gidan, a hankali yake tuqin, su dukan su babu mai cewa komai, kowa da abinda yake sakawa a cikin zuciyar shi har suka karasa wajen dinner din.
*
Littafina na siyarwa ne, #250 da hamsin ne kawai, zaka iya samu idan kai mun magana ta WhatsApp dina a lamba: 08074545149.
#250 baya nufin ka siya ka karanta da wasu, yana nufin ka siya ka karanta kai kadai, zabinka ne idan hakan yayi maka ka biya. Idan baiyi maka ba dan girman Allah, dan darajar iyayenka idan kasanta kana kuma mutuntata, ka barmun littafina.
Nagode.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 18
Ta dauka lokaci zaiyi mata tsaye,kalaman AbdulHafiz da Nabila bayan saka ranar su ya zauna mata daram, amman sai tasha mamaki, dan lokaci bai taba yi mata gudu irin wannan karin ba, ko dan jarabawar da sukayi da gujumniyar project din karshen zangon, duk da lokacin Hamza ya karba yayi mata tracing. Ta samu sauki, amman sam ta kasa yarda da cewa kwanaki kasa da ashirin suka rage a daura aurenta, sai take ganin komai ya cakude mata, ga Hamza sam aiki ya wani irin rike shi, komai ya bari a hannunta.
Dan Dimples da Biebee su sukayi hidimar fito da anko, sun sha wahala kafin su yanke hukuncin anko kala biyu, atamfa da za'a saka wajen Kamu, sai kuma leshi da za'a saka a wajen dinner. Wannan ma batabi ta kansu ba, nata kudin ma su taba, Ita tun sauran wata biyu bikin take duba leshina a Fabrique Castle, harma ta dauki lambar Waheedah Shu'aib Haroon da itace mai mallakin shafin, kuma da alama mutane sun yarda da kayanta, taga hotunan amare da dama da suka siyi kaya a wajenta cewar abinda suka siya shi aka aika musu da shi.
Dan ba sosai take yarda da siyayya online haka ba, amana tayi karanci a cikin mutane yanzun. Amman tabbas akwai kayayyaki daga leshi zuwa atamfofi irin wanda bako ina ake samun su ba, yanda take son komai nata ya fita daban. Anan tayiwa Waheedah magana ta tura mata kalaluwan leshina da atamfofi, Hamza ya tayata zabe, tunda shima duk shaddojin daya siya tare suka zabi wanda zai dace da kayan da zata saka. Babu yanda Anty batayi da ita ba kan a siyi kayan anan Kaduna, itama tasan mutane, amman Hindu taqi
"Anty harfa nayi magana da Baba, yama bani kudi"
Cewar Hindu, dan Baba ya kirata yaji ita dame-dame ta zaba, ta kuma nuna mishi, da Antyn tayi mishi magana ca yayi
"Ki kyale yarinya da zabinta dan Allah, ke abinda zaki so ba lallai yayi mata ba, kuma kinsan kayansu na zamani"
Shisa Anty ta koma gefe ta saka musu ido, kiri-kiri Baba yake nuna yanda Hindu tafi mishi kowa a gidan, har saida Antyn ta dinga jin babu dadi, tunda da Hindu da Khadee za'a yi bikinsu lokaci daya. Amman kai tsaye Baba yake kiran Hindu yana tambayarta zabinta akan abubuwa da dama, ko da Khadee take nuna hakan ba komai bane, Anty tasan Mama ba zataji dadi ba, kawai dai in akace Baba da Hindu ne, babu wanda ya isa yace wani abu. Shisa kowa ya dauki ido ya saka musu.
Yanzun ma Hindu na daki a zaune ta shiga Instagram, wani biki ta fara cin karo da shi, ita yanzun gabaki daya bikin AbdulHafiz ya dakushe mata kyallin duk wasu bukukuwa da take cin karo da su, badan bata taba ganin bikin da yafi nasu AbdulHafiz ba, tunda Allah yayita da bin shafukan manyan mutane, amman nasun ne anyi shi cike da natsuwa, ga kuma irin kalar shigar da sukayi. Akwai kudi dan kudi, amman sarautar da take tattare da shagalin bikin na daya daga cikin abinda ya qawatar sosai da sosai.
Kuma lokacin dan rashin tausayi, duk da a Kaduna yake da zama da matar shi, amman sai su Hamza suka bashi sati biyu, tunda aiki suke a Kano lokacin, shi yake kular musu da sauran ayyukan su na nan Kaduna, shida Abdallah. Ita Hindu sai take ganin sati biyu yayi kadan, dan tana so idan nasu yazo a basu fiye da haka. Tasan yanda Hamza yake rawar kafa a kanta, ko wata daya aka basu wuni zaiyi cikin gida, yanda zata zuba sangartarta, tafiya ma a cikin gidan ba sosai zata dingayi ba, sai dai ya dauketa. A ganinta idan mata basu more wannan damar da Allah ya basu ta lokacin amarci ba, ai an gama sha dasu, indan Hamza ne yanayin soyayyar su ma, harsu tara yara ba zata wuce sunguma a wajen shi ba.
Murmushi tayi ita kadai tana dan sadda kai cike da kunyar kalar tunanin da sake-saken da take yawan tsintar kanta a ciki tun bayan da aka tsayar da lokacin auren su, balle kuma yanzun da abu ya matso kusa, sosai take hasashen yanda rayuwar auren nasu zata kasance. Ta gama da maganar dinki, Doka plaza takai, da aka lissafa mata kudin dinkunan gabaki daya sai da taji kanta ya sara, dan har kasan ranta take tausayin Baba, balle taga kudin da yake kashewa, tun daga kayan kallo dana kitchen, komai aka shigo dashi gidan guda biyu ake siyowa.
Ranar tana shigowa gida sunayin waya da Hamza, yake tambayar me tayi ranar, ta fada mishi takai dinki, sukai hirar, sai gashi ya turo mata kudin dinkin, taji dadi har ranta. Idan baba ya bata kudin dinki, ko nawane sai tayi maganar kwalliya dasu, taga yanda abin zai kasance. Ta dai ajiye lambar Nadine da Meemie Beauty, amman ranar Kamu dai zataje colors of Meena da yake safaha plaza anan kwato road, tayi gyaran kai, wankin kafa sai kuma suyi mata kwalliyar fitar bikin ranar acan. Khadee tayi musu booking din mai kunshi da zatazo tayi musu har gida.
Shiga tayi tana duba masu yin cake din biki, dan Hamza yayi mata maganar jiya, amman shi ba wasu abubuwa yakeyi da yawa ba, dinner ce kawai da zasuyi, kuma Fodio da shi kadai take da lambar wayar shi duk a cikin abokan Hamzan, da bikin ya gabato
"Nikam kaina na ciwo, haka biki yake da wahala daman? Kuyi magana da Fodio ni dai, nagaji wallahi"
Hamza ya fadi ranar da suke maganar wanda zai musu hotuna a wajen bikin. Yanzun ma alamar shigowar sako tagani ta whatsapp, tana budewa taga Fodio dinne yayi mata sallama, ya tura mata wasu hotuna da ta bude, wajen event ne har guda uku. Yana dorawa da
"Ki zabi daya"
Zabar kuwa tayi, inda yafi kowanne yi mata kyau a cikin hotunan, tana hasaso yanda zasu kawatu sosai, har saukowa daga gado tayi tana tashi tsaye, dan sosai wajen yayi mata kyau
"Castle event center, daman nima duk yafi mun kyau"
Ai bata ma ba Fodio amsa ba, ta sauka daga whatsapp din tana shiga Instagram dan ta duba su, wani irin tsalle tayi ganin sosai yanda wajen ya qawatu, tana da tabbacin zaiyi tsada sosai da sosai. Dan Big city events center ma nawa aka ce musu, dan anan zasuyi kamun bikin, da yake wajen babu laifi shima ya qawatu, da wuri sukayi booking, kar a fara gaya musu labaran da zasu karya musu zuciya. Murmushi kawai takeyi ita kadai, a tsayen Asma ta shigo dakin ta sameta
"Ke zo kiga inda za'ayi dinner din bikina"
Tace ma Asma cike da farin ciki, da gudu Asma ta karasa tana karbar wayar daga hannun Hindu
"Inalillahi.... Kai... Wallahi wajen nan yayi mugun kyau, amman da tsada ko?"
Kai kawai Hindu take dagama Asma, murmushi take har kumatunta sun fara mata ciwo, amman ta kasa dainawa saboda tsantsar nishadin da take ciki, wayarta ta soma ruri, kafin tayi wani yunkuri Asma ta daga, muryar Hamza na dukan kunnenta da fadin
"Babe..."
Cike da gajiyar da yake tattare da ita, dariya Asma tayi
"Ba ita bace ba"
Shima dariyar yayi, tun bayan saka ranar su da Hindu sukayi wata irin shakuwa da Asma din, dan Hindu batajin a gidan akwai mai yin Hamza bayan ita, sai Asma, takance yana da kirki sosai, haka kawai zai turo ma Hindu kati yace taba Asma, tayi sub ta duba assignment, ko zuwa yayi wajenta yakan taho da kayan ciye-ciye yace a bata, sosai in kana tare da shi zaka fahimci yanda hannun shi yake a bude kamar ganyen magarya, ba kamar samarin yanzun ba da Dimples kance
"Ki godema Allah Hamza nayi miki kyauta, yanda samari suke kamar kwalta, sam basa banbaruwa"
Godiyar Allah kullum a cikinta take dan ta sami cikar burinta, addu'arta bata fadi a banza ba, jinkirin da ya sameta yazo da alkhairi
"Asma, ina Babyna?"
Hamza ya fadi, dariya Asma ta karayi, kafin tace wani abu Hindu ya fisge wayar tana kai mata dukan data kauce tana fita daga dakin, dan har lokacin dariya takeyi
"Hello..."
Hindu ta fadi, tana jin yanda Hamza ya sauke numfashi
"Nagaji sosai, Fodio yake cemun kun zabi wajen da za'ayi dinner ko?"
Kai ta daga
"Eh yanzun ya turomun, sannu da gajiya, su AbdulHafiz ba zasu kyalemun kai kadan huta ba ko?"
Numfashin ya sake sauke mata cikin kunne
"Kibarsu, kuma wai zamu shiga Kano gobe, gashi yanzun suna so su kara jana mu fita, ni zan watsa ruwane inyi Magriba inzo wajen ki"
Zama Hindu tayi, jin kafafuwanta sun fara gajiya
"Dan Allah zaka zo? Karka sakamun rai fa"
Yar dariya yayi
"Jibi yanda kike magana kamar da gaske kinyi kewata, bayan nine nace zanzo"
Itama dariyar tayi
"Da gaske ina kewar ka, bana so ince yaushe zan ganka dan kar in kara takura ka"
Tunda tasan aikin da yake fama dashi
"Sau nawa zan fada miki duk aikin da nakeyi idan da gaske kina son ganina zan ajiye in zo? Sai dai in bana garin"
Murmushinta ya fadada, tanajin yanda soyayyar shi take kara cika mata kirji
"Sauran 'yan kwanaki dai, duk mu huta da wannan wahalar"
Ya fadi, yar dariya tayi a kunyace
"Ba zaki daina mun wannan kunya-kunyar da kika san bana so ba ko?"
Tasan yanda yake a gajiye, rigima zai iya yi mata, tana kuma cikin farin ciki, sam batason abinda zaija suyi rikici
"Ka tashi ka watsa ruwan, yamma na karayi, nima alwala zanyi"
Zata rantse kai ya girgiza mata
"Ni um um, ban gama jin muryarki ba"
Mikewa tayi
"Yi hakuri, kai da zaka zo muyi hira ma, tashi ka watsa ruwa dan Allah, kaji"
Shiru yayi na yan dakika kafin taji ya sauke numfashi me nauyi
"Baka tashi ba fa"
Ta fadi
"Yanzun zan tashi ai"
Yayi maganar yana karasawa da hamma
"Bacci ko?"
Ta bukata muryarta na sauka kasa, cike da kulawa
"Ummm, bari dai inyi wankan"
Ya karasa maganar yana kashe wayar, kan gado ta cillata, itama tana shiga bandaki.
*
Zuwa yanzun Hindu gani takeyi kamar da ta tashi da safe dare yake sakeyi ta kwanta, saboda yanda lokacin yakeyi mata sauri. Gidansu Biebee taso shiga, amman suna wajen suna, zaifi mata sauqi akan zuwa unguwar su Dimples, amman babu yanda zatayi, dole can din ta tafi, saboda za'a kawo lefen su, gidan ma akwai wasu cikin yan uwan su, tacewa Anty a can zata kwana, idan ta kira Hamza tsaf zaije ya dauketa ya mayar da ita gida. Ko Baba Abba ma Yayan Dimples idan yana gida, dare kuma yayi tasan zai taimaka ya sauketa. Tunda taje suka gaisa da Mama tana dakin Dimples suna zuba labari, tana kwance akan gado, ita kuma Dimples din tana kan keken dinkin ta
"Dee rashin mutuncin ki bashi da na biyu, jibi rigar da kike dinkawa kan ki"
Idanuwa Dimples ta juya mata tana cigaba da abinda takeyi kafin tace
"Kinfi kowa sanin ban koyi dinki dan kowa ba sai kaina, kuma nama tsani abin yanzun wallahi, sam baya raina. Su Mama ma sun cire rai, tela suka samu suna kai dinkin su"
Dariya Hindu tayi, tasan halin Dimples, tunda Mama ce ba zata ce mata ba zata dinka ba kai tsaye, amman ayi watanni ko yankawa batayi ba, Mama kuma irin mutanen nan ne da basa son a ja musu rai, tunda ta gwada sau biyu, bata kara bata dinki ba.
"Allah ya shiryeki wallahi, amman ke banza ce, da kudin da zaki samu Allah kadai yasan yawan su"
Dankwalin da Dimples ta karasa lafewa ta jefa kan gado tana fadin
"Naji...yanzun zamuyi wata maganar mai muhimmanci ko baki gaji da bata bakin ki ba?"
Sosai Hindu take dariya, kafin ta daga wayarta da Hamza ya kira
"Nifa ina inda kika ce, ki fito, tun dazun nake kiran wayarki ban samu ba"
Mikewa tayi tana fadin
"Dee bari inga Hamza"
Kai Dimples ta daga mata
"Ki gaishe da shi"
Wucewa Hindu tayi, tasan Dimples, ko catayi ta fito su gaisa ba zataje ba, haka ma zatace
"Bana son shegen gulma, kibarni"
Shisa batayi asarar maganarta ba, fita tayi tana kuwa ganin motar shi da yayi parking a gefe. Karasawa tayi ta bude tana shiga, ya jingina sosai da jikin motar, ya juyo da kanshi yana sauke mata idanuwan shi da take ganin sun sake launi, takan ga hakan wasu lokutta, sai yace mata bacci ne da gajiya. Murmushi tayi mishi, yana sake shagwabe mata fuska
"Gajiya?"
Ta tambaya, ya daga mata kan shi da yakejin yayi wani irin nauyi, kuma yasan abinda yasha ne, da bacci zai kwanta yayi, kawai yaji yana son ganinta. Shisa ya kara bulbula ma cikin shi vodka, ko zai samu ta dishe mishi abinda yake ji, yanzun sosai take mishi rigima idan ya nemi ko hannunta ne ya rike, kuma ran shi na baci ba kadan ba, shisa yake kokarin ganin yayi controlling din kan shi, kamar yanda tace ne
"Saurin me kakeyi?"
Kuma AbdulHafiz yace mishi
"Idan