Showing 60001 words to 63000 words out of 110313 words

Chapter 21 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt

kawai zai saka maka AbdulHafiz"


Hamza ya fadi yana godema Allah da kyautar AbdulHafiz a rayuwar shi. Sai yakejin kamar AbdulHafiz bai taba mishi wani abu da yaji dadin shi irin yau ba. Mikewa tsaye yayi yana zaro wayar shi daga aljihun shi, AbdulHafiz ya kira da bugun farko ya daga yin sallama


"AbdulHafiz...."


Hamza ya kira yana rasa abinda ma zaice, yanajin karamin tsakin da AbdulHafiz din yaja


"Menene?"


Ya bukata, yar dariya Hamza yayi


"Nagode, Nagode AbdulHafiz"


Yanda yayi maganar yasa AbdulHafiz fadin


"Kai kam baka da hankali dama"


Ya kashe wayar daga dayan bangaren


"Kamshin me nakeji?"


Hindu data fito ta fadi yawunta na tsinkewa


"Abinci AbdulHafiz ya aiko mana"


Hamza ya bata amsa, abayar da ta saka a jikinta ta cire tana cillawa kan kujerar dake falon, tare suka tattara kulolin suna dawowa falon, suka zauna dirshen, babu wanda yake maganar dauko plate, akwai cokula a ciki, da babu hannuwan su zasu saka, ita kam Hindu batasan ko yunwar da takeji bace ba, amman ta kwana biyu bataci abinda yayi mata dadi ba haka.


"Hindu mun kusan cinyewa"


Hamza ya fadi da mamaki a muryar shi


"Kasan yunwar da nake ji kuwa?"


Hindu ta amsa shi tana saka nama a bakinta


"Bamuyi Bismillah ba, ko ke kinyi?"


Ya sake tambaya, kai ta girgiza mishi, dariya yakeyi yana sakata dariyar itama, cikin nishadi suka karasa cin abincin, suna zaman su a falon dan su dan sami natsuwa, kowa da tunanin da yakeyi a ran shi.


*


Tare sukai sallar azahar, Hamza yayi ja musu sallar. Suna gama azkar dinsu ta gyara zamanta, tanajin wata gajiya na saukar mata, Hamza take kallo da yake karatu a hankali da wayar shi, muryar shi na nutsar da abubuwan da batasan suna tashe ba a zuciyarta, tana kara jinjina ikon Allah da kalar jarabtar Hamzan. Gashi yayi mata wani irin kyau, sai da ya idar tace mishi


"Kayi kyau"


Kallon kanshi ya danyi, yana kashe mata ido daya


"Kwalliya nayi miki"


Murmushi ta danyi, duk da taji dadi har ranta


"Ko dai zaka fita ba"


Kai ya girgiza mata


"Babu inda zanje Allah, sai za'a je wani waje ake kwalliya?"


Ya tambaya, shi zai iya yin wanka ya saka manyan kaya harda hula kuma yayi zaman shi a daki. Mikewa yayi yana hawa kan gadon ya zauna ya mike kafafuwan shi, itama Hindu mikewa tayi, inda taga jakar system dinta su Anty sun ajiye mata ta nufa ta dauko, akwai socket ta gefen Hamza, ta fara saka cajar, sannan ta hada da system din tana janta zuwa kan gado ta ajiye, ta dayan bangaren ta zagaya ta zauna.


"Me zakiyi?"


Ya bukata cike da son sani, yasan tana da sauran sati biyu kafin ta koma makaranta, zangon karshenta.


"Kallo..."


Da ido yake binta harta kunna system din, tana zama a gefen shi, matsawa yayi kusa da ita sosai, ta kunna korean film din da bata fara kallo ba, Biebee ta tura mata shi.


"Bride of the century"


Hamza ya karanta sunan, yana mamakin inda suke samo sunaye haka, kashi na farko Hindu ta kunna, tana gyara zama, ta kwantar da kanta a kafadar Hamza, tasha mafarkin faruwar hakan, har a ido biyu tana hasasota zaune da mijinta suna kallo haka a system suna taba hira. Yanzun da abin ya faru sai take ganin kamar a mafarki, kamar wani zaizo ya tasheta. Hannun Hamza taji ya kama nata yana hade yatsun su waje daya ya dumtsa, tana jin yanayin har cikin zuciyarta. Kallon suke a nutse suna son fahimtar inda film din ya dosa, har kashi na farko ya kare, Hamza ya mika dayan hannun shi ya shigar musu na biyun, film din ya fara daukar hankalin shi sosai


"Yarinyar nan na da kyau"


Ya furta a fili, shiru Hindu tayi mishi batace komai ba, sai da akayi wajen mintina sha biyar a tsakani aka sake nuno jarumin film din tukunna tace


"A haka ba lallai kaga kyawun shi ba, sai ka natsu tukun..."


Bata karasa ba saboda zungurinta da Hamza yayi da gwiwar hannun shi a hakarkarinta


"Wallahi zaki fasa kallon nan, me yasa zaki natsu kina kallon shi?"


Dariya Hindu tayi


"Oh ashe babu dadi"


Hararta yayi kafin ya mayar da idanuwan shi kan laptop din


"Ni ai ba har zuciyata na fada ba, kinga kinja banga me aka ce ba"


Ya karasa maganar yana mika hannu yadan mayar da episode din baya. Kallon suka cigaba dayi, ko da sukayi sallar la'asar ma kallon sukaci gaba dayi, suna tattauna abinda yake faruwa a film din, batasan yanda akai Hamza ya koma jikinta ba, ita da take jikin shi a kwance, wajen biyar da rabi ta miqe ta sauka daga kan gadon


"Ina ka kai mana kazar mu ta jiya?"


Saida ya tsayar da film din tukunna ya kwashe da dariya


"Menene abin dariya? Bakajin yunwa kai?"


Kai ya girgiza mata


"Ina ji wallahi, tun dazun"


Kallon shi takeyi


"Bana so in fara yin magana ne kawai. Tana cikin fridge a kitchen..."


Ya karasa maganar yana sauka daga kan gadon, tare suka fita kitchen din, komai na mata bakunta, tana mamakin kitchen dinta ne haka. Tukunya ta dauka tana daurayewa ta dora akan gas ta kunna dan ta dunduma musu kazar


"Kisa a microwave mana....ina da a kitchen din sama"


Hamza yai maganar, ita ta manta da wani abu microwave, akwai a gidan yayarsu Babba, amman basu da shi a nasu gidan, shisa tunanin tayi amfani da shima baizo mata ba, duddubawa takeyi a nata kitchen din ko itama an kawo mata. Bata gani ba, tasan wasu kayan sai a hankali zata dinga fiffito dasu. Aikam saman suka hau, lokacin duk da tagama dumama musu ana kiran magriba, anan bangaren Hamza sukayi sallah, suka dauki kazar da sauran shawarmar su da burger suka sake komawa kasa, fita Hindu zata sakeyi yace mata


"Me kuma zaki dauko? Allah zanci gaba da kallo idan kika dade"


Murmushi tayi


"Lemo fa zan dauko mana"


Ta fadi tana ficewa, wani irin sama-sama take jinta saboda nishadin da take ciki, gabaki daya yau din ya wanke mata bakin cikin data kwasa a daren jiya. Shi kan shi Hamzan yau da sauqi yake jin shi, kamar zai iya zaman auren, kamar babu wani abu mai wahala a ciki kamar yanda yake tunani. Kallon sukaci gaba dayi har isha'i, da suka idar ne ya sake jansu sukayi nafila raka'a biyu ta godiya ga Allah daya kamata su gabatar tun a jiya, amman hakan bai faru ba. Kallon suka ci gaba dayi har wajen goma na dare, kafin zancen ya fara sauyawa.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 20


Hannu tasa tana kara gyara qullin lafaya din da yake daure a kugunta, hawayene da batasan inda suke sauka ba, saboda kanta da yake a sadde. Har Anty ta gama mata maganar da takeyi mata, sam bataji komai ba, hankalinta baya jikinta, bata kara shiga tashin hankali ba sai da taganta tsugunne a gaban Baba, sai da taji muryar shi ta dira kunnuwanta cike da bankwana, tabbas aure ba mutuwa bane ba, amman tana jin kewar Baba har cikin kasusuwan jikinta


"Haka muke cinye kwanakin mu Hindatu, sai makusanta cikin jimami suyita ganin kamar munyi gaggawa, suna manta yanda su dinma basuyi jinkiri ba"


Baba yayi maganar yana kasa yarda yau shine Hindu take tsugunne a gaban shi, yau shine zaiyi sallama da ita, ya mika kulawarta da amanarta a hannun Hamza. Iyaye mata kance rana irin tayau kanzo musu da farin ciki hadi da firgicin rashin sanin makomar gobe akan auren yaran su mata, abinda basu sani ba, shine firgicin yafi yawa a tattare da iyayensu maza, ka dauki amanar 'yarka da tayi shekaru karkashin kulawarka, kana duk wani kokari da kake da iko a kai na ganin wani abu bai cutar da ita ba, rana daya zaka mika ma waninka ita, duk kuwa da tarin kokwanton da yake ranka na ganin babu wanda zai iya kula maka da ita kamar kai.


"Zance kiyi hakuri saboda yana daya daga cikin manyan jigo a cikin zaman aure, amman bance kiyi hakuri idan ya hada da cutarwa ba, na dage akan islamiyar ku saboda ki fahimci darajar da musulunci ya baki a matsayinki na 'ya mace, idan har hakurin da zakiyi a gidan aure ya nemi taka wannan darajar, Hindu ina da wajen zamanki, karki taba bari al'ada ta tauye danne miki 'yancin da addinin ki ya baki..."


Cewar Baba, yana dorawa da


"Allah yai muku albarka..."


Yanayin muryar shi da yanda ta sauka ya kara haduwa ya karyama Hindu zuciya, batasan ta zauna ba, saida taji kanta ya jingina da kafafuwan Baba, kafin wani kuka daya fito daga kasan zuciyarta ya kwace mata, kuka take na barin gida, kuka take cike da firgicin rashin tabbas din da take cikin aure, kuka takeyi saboda yanzun ne take jin kamar bata shirya ma zama da Hamza ba, yanzun ne takejin wani bayanannen tsoro ya lullubeta. Sai da Mama da wata kanwar Baba sukazo suka janyeta dakyar suna fitowa da ita daga bangaren Baba. Kuka takeyi har yanzun da aka fito da ita.


Ko da kanta ba'a lullube yake da lafayan jikinta ba, ba lallai taga hanya ba saboda kukan da takeyi, batasan waye ya kamata yana sakata a mota ba. A wani irin gigice take jinta har suka karasa gidan da yake a unguwar Malali, ta wajen KAD Academy. Batasan waye yake ce mata tayi addu'a kuma ta fara saka kafarta ta dama ba, ita banda sallama babu abinda ya iya zuwa kanta, addua kullum cikin yinta take, fiye da yanda zasu taba fahimta, saboda haka su kyaleta kawai taji da abinda takeji. Tanajin suna rike da ita har aka shiga wani daki, tukunna aka zaunar da ita akan gado.


Har lokacin fuskarta a rufe take, danma tanajin sanyin AC din da ya gauraye dakin yana ratsata, banda ajiyar zuciya babu abinda take saukewa, kayansu da zasu saka anjima wajen zuwa Dinner yana wajen su Aina'u, su suka harhada komai, tasan kuma sun taho dasu, kilanma suna cikin gidan. Tana jin shige da ficen mutane da masu yi mata fatan alkhairi, da masu yi mata nasiha, ita kam banda hayaniya batajin komai, ba zatace ga awannin da aka dauka a haka ba, sai da taji muryar Hauwa data kama mayafin da yake rufe da fuskarta tana fadin


"Ke bude kisha iska, duk sun tafi"


Numfashi Hindu ta sauke hadi da ajiyar zuciya, tana kama mayafin ta kara goge fuskarta da shi, kafin Dimples ta shigo da plate din abinci a hannunta tana kallon Hauwa


"Ba zakici abincin ba? Bie na kitchen..."


Dan yatsina fuska Hauwa tayi, ita ba wata yunwa take ji ba, amman taga kamar da hadin salad, zataci wannan


"Jiba gulma, yanda kike damun uban kowa da Hamza shine kika garji wannan kukan, kinga fuskarki? Ki tashi ki wanke ko zai sauka kafin lokacin Dinner"


Dimples ta karasa tana zama gefen gadon, ta fara juya abincin da yake rike a hannunta


"Wallahi duk fuskarki ta kumbura"


Hauwa ta fadi tana nufar hanyar da zata fitar da ita daga dakin, ta fice


"Ki tashi Allah, kinsan dai dole a zageki tunda ango yafiki kyau, gara ki wanke fuskar ko zai taimaka miki"


Dan murmushin karfin hali Hindu tayi tana saukowa daga kan gadon, sai dai kofa biyu tagani a cikin tanqamemen dakin baccin, na farko ta fara budewa tana ganin dakin sake kayana, saita rufo ta dawo ta bude dayan, dan ware idanuwanta tayi ganin kayatuwar da bandakin yayi


"Ke kinga toilet din nan kuwa?"


Hindu ta fadi, tana saka Dimples kusan shakewa da shinkafar da take bakinta


"Banza yanzun ranki har yayi sanyi, saboda bandaki"


Dimples ta karasa tana kwashewa da dariya, itama dariyar Hindu tayi, tana shiga bandakin, komai ta karewa kallo, kamar an ciro shi daga film an ajiye mata, har bango saida ta dafa, yanayin tayal din ruwan gwal yayi matuqar daukar hankalinta, lokaci daya ta nemi damuwar da take ciki ta rasa, alwalar magriba ta dauro, dan bata lokacin da aka tsaya yi, sai bayan la'asar aka taho kawota, tasan inba dai babu masallaci a kusa dasu ba, tabbas ana gab da kiran sallar magriba, kuma karfe bakwai sukayi da mai kwalliya zatazo tayi mata, kafin su fara kama hanyar zuwa wajen dinner.


Tana fitowa ta sami su duka ukkun a dakin suna cin abinci


"Ke ba zakici wani abu ba? Tun dazun kike yawo kamar ganga"


Kai Hindu ta girgizawa Biebee, ko yunwa bataji ballantana taci wani abinci. Tana zama ana fara kiran magriba


"Wai Magriba har tayi?"


Hauwa ta fadi cike da mamaki


"Saiku tashi kuyi sallah, ni nayi sub"


Hararar Biebee din Dimples tayi


"Abin nan baimun dadi ba, yanda na wanke kwalliyata naso kowama ya wanke tashi wallahi"


Dariya Biebee tayi sosai


"Dan bakin ciki dai baiji dadin rayuwar shi ba"


Dimples din bata ko kulata ba, ta mike, ita ta tattara kwanonin da su duka sukaci abinci


"Allah sarki Kawata, dadina dake baki da matsala"


Biebee din ta fadi tana sake kwashewa da dariya, fita daga dakin Dimples tayi tana kin biye mata, tana dawowa itama alwala ta dauro ta fito, duk sallah sukayi banda Biebee da take zaune tana danna wayarta. Basu dade da idarwa ba saiga mai kwalliyar na kira tazo kan street din, Hauwa ta karbi wayar Hindu ta fita tana dawowa da ita. Batare da wani bata lokaci ba ta tsarama Hindu kwalliyarta da tayi matukar karbar fuskarta, suma yi musu aka sakeyi, Biebee kuwa dan gyara mata akayi, tunda bata bata tata ba. Kafin kace wani abu har sun kammala shirinsu tsaf, Hindu na sanye da material da dinkin doguwar rigar kawai zaka kalla kasan amarya ce.


Wine color kamar yanda bature yake kiran kalar kayan da suke jikinta, tayi wani irin kyau da har Hauwa sai da tace


"Oh Allah, Hindu kinga yanda kikayi kyau?"


Murmushi Hindun tayi, tana mata godiya, hotuna suka dinga yi mata, ta mika musu harda wayarta, su material dinsu ruwan madara ne, duka dogayen riguna.


"Ni kadai ce nayi kama da muburkin miya"


Dimples ta fadi tana saka dukansu kwashewa da dariya


"Zan tayaki addu'a kawata, yar kibar nan Allah ya dubeki"


Tsaki Dimples taja


"Bie bana son iskanci, kuma anma fi yayin kalata kiji, yarinya siririya, ga kyau ga dimples"


Wata dariyar Biebee ta sake kwashewa da ita, Hauwa nata kallon su da murmushi a fuskarta, yanayin kawancen su yana burgeta, tun jiya sunyi fada yafi sau ashirin, kamar kaji haka suke, Dimples saurin kulewa, Biebee kuma tsokana. Hindu kuwa kiran Hamza ta daga, tun bayan wayar da sukayi da aka daura aure, sai da suka zo gidansu akayi hotuna, shima magana ko daya bata hadata da shi ba, sai take ganin wani nisantaccen yanayi shimfide a fuskar shi da batasan na menene ba, basu wani dade ba suka wuce, basu sake neman juna ba kuma, yanzun ma tana karawa a kunnenta yana furta


"Kun shirya?"


Kai tadan daga mishi tana dorawa da


"Eh..."


Cikin sanyin murya


"Kaji wai sun shirya..."


Hamza yayi maganar daga dayan bangaren da alama wani yake yiwa magana, kafin taji ya kashe wayar a kunnenta, saukewa tayi tana kallon su Biebee a zahirance, a badini kuwa batama ganin su, wani abune yazo dai-dai kirjinta yai tsaye, ba tasan akwai wani yanayi a tsakanin tsoro da tashin hankali ba, sai yanzun data tsinci kanta a cikin shi male-male.


"Sauran yan gidan su Hindu fa? Wa zaije ya dauko su?"


Fodio ya bukata


"Dan Allah Fodio ka kira AbdulHafiz, nifa ban sani ba, bana ji yace ya tura ba?"


Hamza ya fadi yana kara saka comb cikin sumar kanshi ya taje, kafin ya dora hular shi, farar Getzner ce kal a jikin shi sai daukar ido takeyi, duk da babu aiki a jikin riga da wandon da yake sanye dasu, kallo daya zakayiwa yanayin dinkin saiya burgeka, zaman agogon shi ya gyara, yana daukar babbar rigar shi ya rike hannu, dan bazai sakata tun yanzun ta yamutse ba. Turarukan da suke baje kan gado ya shiga dauka yana kara feshe jikin shi da rigar da take hannun shi.


"Ka cakar dani Hamza"


Fodio ya fadi yana mikewa tsaye, kan shi harya fara juyawa saboda karfin turarukan, ko kallon shi Hamza baiyi ba, ya mika hannu ya dauki wayar shi da mukullin mota, ficewa yayi daga dakin yana shiga kitchen, yanda yake jin shi idan baidan kara shan wani abu ba, rayuwar shi zata shiga wani yanayi kafin a gama dinner din nan. Kwakbar vodka ya dauka yana samun kofi ya zuba fiye da rabi a ciki, ya rufe kwalbar ya mayar, duk da akwai dan sanyi, saida ya dibi kankaru ya zuba, tukunna ya kwankwade.


"Uban me kake sha? So kake ka fara slow cikin jama'a?"


Fodio ya karasa maganar yana dariya


"Kaina yamun nauyi ne, kawai abinda zai taimaka mun a gama dinner din nan"


Dariyar Fodio ya sakeyi yana girgiza kai kawai


"Idan nace maka kayi kuskure kamar na makara ko? Tunda an riga an daura"


Numfashi Hamza ya sauke yana kara bude fridge din da nufin dauko kwalbar ya sake kwankwada, Fodio yayi saurin karasowa yana mayar da fridge din ya rufe


"AbdulHafiz zai kasheni wallahi, ka wuce mu tafi..."


Runtsa idanuwan shi Hamza yayi yana sake bude su, yanda kanshi yayi dim yana da tabbacin gab yake da fara buguwa fiye da misali


"Ya isa Hamza, ya isa haka, ba a karkashin kulawata zakayi wannan shirmen ba"


Yasan da gaskiyar Fodio, amman a wani irin takure yake jin shi kamar ya saka ihu. Duniyar ta hade mishi waje daya, ga wuyan shi da duka jikin shi da yakeji kamar an shaqe, tamkar wanda aka garkame a dakin da babu window, kofar ma an kulle an cillar da mukullin haka yake jin shi, iskar da yake shaka tun bayan da aka daura auren kanta da kauri yake jin tana mishi zirga-zirga. Kafin ya fara neman mukullin da zai warware wannan kullin da ya jama kanshi yake so yasha giyar shi harsai ya daina gane komai. Amman hakanma ba zai yiwu ba saboda zaije dinner, dinner din bikin shi


"Me nayi haka?"


Ya tambaya yana kallon Fodio


"Komai zaiyi dai-dai, calm the fuck down Man. Ka natsu fa"


Fodio yake fadi muryar shi na rawa saboda yanayin Hamzan ya fara bashi tsoro kuma, tun yana dariya, yanzun abin tsoro yake bashi, da AbdulHafiz yana nan shi yasan yanda zaiyi da Hamza, amman koma meye bazai barshi ya bugu ba tunda taro zasu shiga.


"Kazo mu tafi"


Numfashi Hamza yaja yana fitar dashi da nauyin gaske, kafin ya jinjina kai, yana saka Fodio sauke numfashin da baisan yana rike da shi ba


"Nagode"


Ya furta yana nuna ma Hamza hanyar fita daga kitchen din, baiyi musu ba ya fito, harabar gidan inda motocin su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login