Showing 45001 words to 48000 words out of 110313 words

Chapter 16 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt

shima yana tashi yabar wajen, dan ya fita zaiyi ya siyo musu abinda zasuci, shi kam yunwa ta fara naniqar shi, har tara da wani abu. Sakon da AbdulHafiz ya amsa Hamzan ya duba yana shiga profile din Hindu, hotunanta ya shiga yana tsayawa kan wani da take sanye da farin Hijab


"Woow"


Ya tsinci kan shi da furtawa, ta mishi kyau badan bai tana ganin yan matan da suka fita din ba, kawai ya manta ranar karshe da mace tayi mishi kyawu a idanuwan shi har haka.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 3


Kamar yanda Zahra Tabi'u, marubuciyar Mai Tafiya, cikin alkalamin ta a rubutun Farin wata:


"_Kowane labarin duniya yana da tushe. Kowanne yana da mafari. Me ke nan? Wani abu da ya faru har ya zama sanadin wanzuwar jirkitattun al'amura_"


Labarin Hindu ya fara a shekarar 2012 a lokacin tana aji biyar a sakandire. Tun bayan haihuwar ta, tun ranar da Baba ya dora idabuwan shi a kanta tana a cikin shawul, aka mika mishi ita dan yayi mata hudu ba, Anty zatace taga wani yanayi a fuskar shi da bata taba gani ba a game da sauran yaran nashi, ba wanda ta haifa tare dashi ba kawai, har wanda suka haifa da abokiyar zamanta, dan tana wajen duk yawanci sanda ake bashi yaran yayi musu huduba. A lokacin da yake rike da Hindu zaka iya rantsewa ita ce yarinya ta farko da Allah ya nufe shi da samu bayan tsayin shekaru, kuma a lokacin yana da yara bakwai kafin ita. Ya kuma kara samun yara hudu bayan ita din, jimlar yara goma sha biyu da Allah ya albarkace shi da samu.


Amman ya riketa a jikin shi ko bayan daya gama yi mata huduba, daga ranar kuma har zuwa yanzun zaka gane yanda wajen Hindu daban yake a zuciyar Baba. Akwai dalilin da yasa Malamai da yawa suka karkata ra'ayin su da kafa hujjoji masu karfi akan cewa iyaye su boye yaron da yafi soyuwa a ransu, karsu nuna a fili saboda hakan zai iya saka kishi a zukatan sauran yan uwan su, idan da kaddarar shaidan ya darsa musu wani tunani zasu iya cutar da juna ma. Sai dai a gidan Baba hakan bai faru ba, saboda bokon shi ta rinjayi ilimin addinin shi ba kadan ba. Duk yanda Anty taso ta nusar dashi akan yanda yake nuna kaunar Hindu karara sai ya nuna mata bacin ran shi, ya nuna mata shi duka yaran shi yana kaunar su.


Da dukkan gaskiyar shi yakan yi maganar, yana kaunar yaran shi, zai iya komai a kan su, yana kula dasu, yana kare musu duk wani hakki har wanda bai rataya a wuyan shi ba indai zasuyi farin ciki. Da iyayen su mata basa tsaye akan tarbiyar su, tabbas da yaran gidan Baba zasu taso cikin wata irin sangarta taban mamaki, dan shi in ba Hindu aka taba ba, baisan ya kwabi yaro ba, wannan itace kalar fahimtar da Baba yayiwa kaunar yara. Ita kanta Hindu tana girma tana kara fahimtar yanda ita dince raunin Baba, ko da ana so a roke shi abinda ba ayi tunanin zaiyi ba, ita din ake turawa, da ta shagwabe fuska tace


"Baba na"


Kamar yanda take kiran shi, ko wacce bukata zata furta bayan kiran sunan nashi, dai-dai kun ranaku ne yake iya ce mata a'a shima badan zuciyar shi taso hakan ba. Ba zaka ce babu kishin kalar kaunar da Baba yake ma Hindu a tsakanin yan uwanta ba, dan lokutta da dama a fuskokin su zaka gani. Sai dai su kansu akwai wata irin kauna da shakuwar zaman yau da gobe hadi da karfin jini ta saka musu akan junan su, shisa kishin kaunar da Baba yake mata din baya damun su na tsayin lokaci, zasu nuna a lokacin da hakan ya faru, ita kuma tayi musu dariya dan har ranta take jin Baban nata, idan kaunar shi a gareta daban ce, tana da yakinin kaunar da take mishi daban ce da ta sauran yan uwan ta.


Bawai dan Anty bata da halaye masu nagarta ba, ba kuma dan batajin mahafiyarta har karkashin zuciyarta ba, haka kawai ta taso da son zama kamar Baba, ta taka matakin karatu kamar shi, taso yaranta kamar yanda Baba yake son su, dukkan rayuwarta tana kwatanta ta akan son zama kamar mahaifin nata.


Yau tun da akaje daukosu daga makarantar su ta Zamani College dake nan garin Kaduna, Hindu take jin ranta kal, farin ciki takeyi tunda satin ya kama, bawai dan kasancewar yau din ranar alhamis ba, ranakun da take matukar so fiye da kowanne a cikin satika shine Alhamis da juma'a, dan babu islamiyya, zata samu tayi kallo yanda ranta yake so. Musamman idan Allah ya dora ta akan Yaa Zaid ya ara mata kwanfutar shi kirar laptop tayi kallon a ciki. Akwai faifan cd din data siya har biyu, daya fina-finan indiya ne da baka raba rayuwarta da kallon su, dayan kuma korea ne da bata jima da fara kallon fina-finansu ba, ta kuma sami sunyi dai-dai da ra'ayinta.


Zuwa yanzun tana da tabbas duk kudaden da zata samu wajen siyo su zasu kare. Tana son soyayya, tun bata kai haka ba take hasaso kalar mijin da take so, ballantana yanzun da take kan ganiyar shekarun yan matancin ta. Duk da kullum saita canza ma mijin da take ra,ayi siffa ko launi a cikin kanta, amman dai a kowanne yanayi, kyakkyawa ne na kwatance. Sai dai alhamis din yau ba murnar kallo bace kawai a ranta, harda murnar Baba zai cika mata alkawarin wayar da yayi mata. Kusan duk kawayenta a makarantar boko suna da wayoyin hannu, shekarar da tazo ana yayin Nokia daga kan Express zuwa C2 da kuma X2 da take tashe tsakanin yan mata, samari harma da masu aure, idan kuma akazo wayoyin Nokia na symbian series da bakowanne bama yasan darajarsu balle yagane dadin amfanin da suke dashi da yanda a lokacin suka shallake ma duk wani samfuri na wayar hannu da kamfanin Nokia suka kaddamar.


Saboda haka dai-dai kun mutane ne suke da ita. Ita kam Hindu ba wannan tunanin bane a ranta, waya take so ta mallaka kawai. Yanda yan ajin su ke hirar manhajar sada zumunta ta 2go bata so a barta a baya. Dan haka ta addabi baba cewar suna duba aikin gida da za'a basu a makaranta a wayar ta google. Kuma yana da kyau ace ta mallaki tata saboda jarabawar da karshe da zata shirya su shiga aji shidda da take gabato musu. Kuma ta fada mishi idan ya hado mata da memory card har karatun Qur'ani kamalalle za'a tura mata, zata dinga kunnawa tana sauraro saboda haddar da sukeyi a islamiya. Duk da Baba yaso sai Hindun ta gama sakandire, dan shine tsarin shi ga matan na rike waya.


Mazan kuwa kusan yanzun da wayar ta yawaita duk ya siya musu, har Khalil da Junior suna da yan Nokia dinsu kananu. Ita ce mace Babba a gidan tunda Amna da Asma'u yanzun suke tasowa, wayar hannu ita ce karshen abinda yake ran su. Sosai Khadija take mata yanga da Nokia Express dinta, tana kara kwadaita mata son wayar, kawarta Zainab da duka suke kira da Biebee, makociyar su ce, tare suka taso tun yarinta, duk da ba makarantar bokon su daya ba, amman islamiya daya suke zuwa, itama satin daya wuce Babanta ya sai mata X2 yar yayi.


Naci da rokon da ta dinga yiwa Baba ne yasa shi amincewa. Yace har sim da memory duk zai hado mata dashi, ran alhamis yace mata, tana kuma lissafe da ranakun. Yau a sama take jinta tana yawo kan gajimaren farin ciki. Har fina-finai ma sai ta dinga bayarwa ana tura mata a memory dinta, kallo zata dinga yi a nutse babu takura, bamai zuwa falo yai mata iko da rimat. Sosai take cikin nishadin da ko fuskarta kagani saika fahimta. Suna shiga gida kai tsaye bangaren su ta wuce tana shigewa dakin su ita da Asma. Kai tsaye bandaki ta wuce dan babu wutar lantarki, ga wani irin zafi da taji ya saukar mata, ruwa ta watsa tunda tayi sallah a makaranta, tana fitowa ta saka riga da zani na Atamfa tukunna ta fice daga dakin zuwa kitchen dan ta zuba abinci.


Duk da batajin yunwa, cikinta a cike take jin shi da murna, tuwon shinkafa ne da miyar taushe da tasha lawashin albasa tana ta zuba kamshi, ga wadataccen naman rago da ya kara taimaka mata wajen yin kyau. Rabin malamala ta zuba tana saka miya a kai ta dauka ta fito falo ta zauna, bata nemi Anty ba dan tasan bacci take a irin wannan lokacin, ko da zata tashi sai zuwa la'asar. Asma kuma tana da tabbacin tana bangaren Mama. Ta fara cin abincin kenan Khadija da suke kira da Khadee ta shigo falon, duk da yanda suke furta nasu sunan a gayance Kha din daban sai Dee din da take fitowa a gajarce D, in wasu suka kira sai suna gyara musu da cewar ba haka bane ba.


"Banza ashe kin dawo, yau Baba zai kawo miki wayarki ko?"


Khadee ta fadi tana samun waje kan kujerar da Hindu take ta zauna, kai Hindun ta daga mata dan ta cika bakinta da tuwo, hadiyewa tayi kafin tace


"Eh yau yace in shaa Allah... Zaki tura mun 2go"


Dan karamin tsaki Khadee taja


"Ke ba zakiyi addu'a ba ya siyo miki mai yin WhatsApp, yanzun shi ake yayi ba wani 2go ba"


Dan turo baki Hindu tayi, duk da yanayin ya zame mata jiki, fuskarta kusan ko da yaushe a shagwabe take, da harda muryarta kafin tsokanar yan makaranta yasa tayi kokarin gyarawa, amman duk da haka, magana kawai zatayi ka fahimci tsantsar sangarta a tattare da ita


"Ni dai ina son 2go"


Ta fadi, dan kuwa shi yan ajinsu suke labari kullum, suna hirar rooms, Nigeria room1, Kaduna room1, da Comedy room1. Duk da shi Comedy room din monitan ajinsu taji yana maganar shi, akwai masu account biyu ma a ajin, da garin Kaduna da kuma garin Kano, dan ance sosai ake buga dirama a BUK room1. Tama ji kawarta Yasmin na fadin zata bude, dan rannan wasu yan Kano su B2 sun shigo Kaduna room din sunyi fadan turanci da akafi sani da brawl da su Curious su Zeegee, dan daga baya fadan ya koma BUK room, taso ta kalli yanda aka kare.


Labarai irin wannan su suke kara kwadaita ma Hindu 2go din, ita whatsapp din bawani burgeta yake ba, dan taji Khadija tace yafi rashin hayaniya. Saima kana da lambar mutum tukunna zaka gan shi. A kunnuwan Hindu hakan ba abu bane da zaiyi mata dadi, tunda duk kawayenta sunfi yin 2go, bata da waya amman duk wata dirama da za'ayi suna bata labari, da yanda suke fadar turancin samarin Kaduna room1 tasan dole akwai hadaddu a cikin su. Zata je itama a gabza da ita, a santa a Kaduna room1 dan duk wanda yai mata ba barin shi zatayi ba, da alama Yasmin yar kallo take zama dan ta cika tsoro, takan ce mata tana gudun tayi turanci su Qwaro ko Curious suja mata layi alamar batayi dai-dai ba.


"Ke kika sani, meye a 2go banda hayaniya, da shirme, kowa sai yace zai turo maka friend request, aita maka shirmen banza da wofi"


Cewar Khadee dan sam bata san hayaniya, duk gidan ita da Zaid sun fita daban. Gara ita Khadee ma ana hira da ita idan taso, Zaid kuwa zuciyar shi a wuya take kullum, da wahala ayi hirar mintina goma bai watsama wani zagi ba, dan zaka fadi wani abin da bai mishi ba sam-sam. Kusan a yayyen maza yan gidan sunfi shakkar shi, yana musu dariya, amman hakan baya hana shi hukunta su idan bukatar hakan ta taso. Karasa cinye tuwon ta Hindu tayi ta dauke plate din takai kitchen ta wanko hannunta, dai-dai lokacin da suka kawo wutar da ta sakata wani ihun murna tana fitowa daga kitchen din da gudu.


"Allah ya sambada muku albarka yan nepa"


Yar dariya Khadee tayi


"Kafin anjima ki tsine musu in sun dauke ba"


Kayan kallon dakin Hindu ta kunna tana dauko remote ta dawo ta zauna, kafin su gama kawowa tace ma Khadee


"Anya akwai wanda suka fi yan Nepa shan tsinuwa a kasar nan?"


Kai Khadee ta girgiza mata


"Bayin Allah, ko yan sanda basu kaisu shan zagi ba, duk in suka kawo wuta suka dauke fa sai kinji an zage su, ko kwana nawa wutar zatayi"


Dariya sukayi su biyun, suna mayar da hankalin su kan tv din, Hindu na canza channel din zuwa ta indiya sun saka film din Ishq, duk da ta kalla, tana son film din har lokacin, saboda soyayyar da aka shimfida a cikin shi, ita ta saka Ajay ya kara burgeta matuqa, daman yanayin miskilancin shi ya mata, haka take son namiji karya cika dariya ta rashin dalili, abu kadan ya bude hakora cike da rashin aji. Kallon sukeyi suna dan taba hira kan film din, kafin a kira sallar la'asar data tashe su, Khadee na wucewa bangaren su, ita kuma Hindu tayi daki abinta.


*


Da yake sun saba cin abincin dare tare da Baba, yamma nayi suka tattaru bangaren Mama kasancewar ranar ta fada girkinta. Su biyar ne a dakin. Huzaifa, Khadee, Jafar, Hindatu sai Junior da ya shigo da sallama yana zama gefen jafar da ya lafe cikin kujera mai mazaunin mutum biyu da wayar shi makale a kunne, da alama ya gama nutsuwa cikin wayar da yakeyi, banda murmushi babu abinda yakeyi, muryar shi ma can kasa, Junior din ma da yake kusa dashi ba zaice ga abinda yake fada ba.


Muhsin ne ya fito daga bangaren su, da sai daga baya aka gina musu, boys quarters din da yake bayan gidan ne Baba ya rushe aka sake ginin ya hade bangaren da cikin gida, a ra'ayin shi bai yarda shi yana cikin gida yara dan maza ne suna can wani bangare kofa ta raba su ba, duk da a ko ina suke cikin gidan ba zai hana abinda Allah ya kadarta samun su ba. Amman zasu iya fita yawon rashin dalili sukai dare a waje bazai sani ba, ba lallai maigadi ya fada mishi ba. Idan anan ciki suke, dole zai san karfe nawa suka dawo, in fitar dare ce zasuyi sai da sanin shi, hakan yafi mishi kwanciyar hankali.


Kallon Jafar yayi da yake ta zabga murmushi tukunna ya kalli Huzaifa yana fadin


"Shi kuma wannan me yake yi?"


Cike da rashin kulawa Huzaifa yace


"Waya"


Girgiza kai Muhsin yayi dan yana da tabbacin da budurwa Jafar din yake waya, rigimar yaran na bashi mamaki, idan yana da yarinya kamar su Jafar na zuwa wajenta, da kan shi zai fito yace ya turo manya. Yasan daga nan bazai sake ganin shi ba, yara basu da ko sisi wai soyayya.


"Jafar da muryarka na sauka haka kake mana hayagaga"


Cewar Muhsin din cikin jimami, dariya Huzaifa yayi


"Me yasa zai kashe maka murya?"


Dan rausayar da kai Muhsin din yayi yana samun kujera ya zauna


"Hakane kuma..."


Ganin zasu dame shi yasa Jafar mikewa har lokacin da wayar a kunnen shi dan yabar musu falon, yana kan fadin


"Jiya ko baccin kirki banyi ba ina tunanin ki"


Suna cin karo da Mama da tayi karaf tace


"Kaji shegiyar karya, ba ina jin Babanku harya dawo masallaci ba yana faman tashin ka..."


Da gudu Jafar din ya wuce dan yasan Mama zata ballo mishi aiki, gabaki dayan su dariya suke, Mama kam kai take jinjinawa


"Haka kuke samun yan mata kuyita gillara musu karya, sai kiji yaro yana fadin ya kasa cin abinci, bayan ya share faranti biyu yana neman kari"


Sosai Huzaifa yake dariya


"Mama banda ni fa"


Hararar shi tayi


"Kai din? Allah dai ya shiryaku kawai"


Ta karasa maganar tana shigewa kitchen ta dauki kofi ta koma daki abinta. Hira suke dan tabawa kafin ayi kiran sallar magriba, mazan su wuce masallaci, su Hindu duk anan bangaren Mama sukai sallah. Kafin Baba ya shigo da sallamar da suka amsa su dukan su, dan sauran mazan ma sun dawo sanin Baban na gab da shigowa, murmushi ne najin dadin ganin yaran nashi bayyane a fuskar shi da take cike da dattako, kasumbar da furfura ta fara fitowa ta kara mishi wani kwarjini naban mamaki, kallo daya zakaiwa Baba kasan dan boko ne, ga gayu ya samu wajen zama tattare dashi. Yakan saka manya da kananun kaya duk randa ra'ayin hakan ya motsa mishi.


Su duka sukayi mishi sannu da zuwa, ya amsa yana dorawa da


"Hindu"


Murmushi Hindu take ganin ledar dake hannun Baban, cike da shagwarta ta amsa


"Baba na"


Karamin tsaki Zaid yayi


"Wai Baba na, kamar ke kadai kike da Baban"


Shagwabe fuska Hindu tayi sosai, dan Zaid ne shiya hanata furta wani abin, ko a gaban Baba ne zai iya kwadeta sai dai yayi mishi fada, ledar hannun shi Baba ya mika mata yana dorawa da


"Ga alkawarin ki"


Cikin hanzari ta mike tasa hannuwa biyu tana karba hadi dayin wani ihun murya tana rungume Baban kamar zata karya shi


"Nagode Baba na, Allah ya kara arziqi ya kare mana kai"


Wani karamin tsakin Zaid yaja yana takaicin yanda Hindu ke abubuwa kamar wata yar shekara hudu, ita kuwa bata ma bi takan shi ba, Baba ya gama mata komai yau. Nan Baba yabar su yana shigewa ciki, Muhsin ya kalli Hindu da fadin


"Zo muga wayar Yar Baban ta"


Kamar yanda yakan kirata in yanajin tsokana, da sauri ta karasa wajen shi


"Babban Yaya ai kaine ma zaka bude min daga kwalin"


Hadi da mika mishi ledar, ya karba ta fito da Nokia C2 dal a kwalinta. Murmushi yakeyi, da gaske Hindun yar Baban ta ce, dan ko shi wayar hannun shi bata kai tsadar wannan ba, shiya bude ya saka mata sim din da memory ya mika mata. Murna fal ranta, inda Huzaifa yake ta karasa


"Yaa Huzaifa kaga"


Karba yayi, wayar ta mishi kyau yana fadin


"Ma shaa Allah, aikam idan na fita zan siyo miki kati. Sai a kiyaye banda abinda bai kamata ba, nasan ban isa in hanaki chatting ba, ki dai saka Allah a duk wani abu da zakiyi da wayar nan Hindu..."


Huzaifa ya fadi yana kallon sauran kafin ya dora da


"Ku dukan ku ma, wayar nan da kuke rainawa zata iya halakar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login