Showing 9001 words to 12000 words out of 110313 words
Chapter 4 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt
sa ko kadan baya burgeta, ba ca yayi yana son ta ba, kwata-kwata a tunaninta data kwatanta idan yace yana sonta dinne baiyi mata ba. Ba sau daya ba, ba sau biyu ba, babu wani dalili tana jin mutum baiyi mata ba, amman kiyayyar da takewa Musa dabance, kuma sai ya dinga abu kamar baisan gajere bane, yana daddaga kafadun da takeji kamar ta kwantara mishi wani abu akai dan takaici
"Hindun Baba....Ya kike?"
Ya fadi cike da iyayin da ita kadai take gani a tare da Musan, ta tsani yanda ta karfi da yaji yake nuna akwai wani kusanci a tsakanin su, sai yashe mata baki yakeyi. Mama tace Baban shi qwara ne, da Hindu ta dauka a bakaken fata kawai akafi samun guntaye, amman saiga Musa ya fito a qwaran shi sak, amman tana hango tsakiyar kan shi
"Lafiya..."
Ta amsa can kasan makoshi, da Halima bata wajen ko inda yake ba zata kalla ba, amman tasan halin Halima, ta kwada mata mari ba abu bane mai wahala, ko Yayarsu Salma basa tsoro haka kafin tayi aure, Halima bata wasa dasu, a haka sai kaganta kamar tana da sanyi, sai kaji saukar mari akan kuncinta, dan bata son raini, bata kuma so taga kana wulakanta mutum, shisa ba sosai suke shiri da Hindu ba, sau daya ta taba cewa Musa gajere a gaban Halima ta kusan kwada mata mari
'Ko gawayi ba zaki iya yiba, kina kushe halittar da Ubangiji yayi kamar bakije islamiyya ba, idan gajartar shi batai miki ba, sai a samo tsani kihau sama kiji dalili. Wallahi Hindu ki iya bakin ki, ba tun yau nake jin yanda kike kushe halittar mutane ba, idan baki haifa ba, zaki iya aura'
Shine abinda Halimar ta fada mata, a ranta ta dinga zabga addu'a kar Allah ya amsa, dan taji haushi sosai. Tunda bakin cikine, ita ta sami me kyau tana mata fatan auren gajere. Ko maza sun kare sai ire-iren Musa gara ta hakura da auren, yanzun ma dakinsu Khadija ta wuce dan taga Musa naso ya karayi mata wata magana. Halima ce taje ta kawo mishi ruwa bayan ya zauna tana fadin
"Bari in kira maka Mama"
Kai Musa ya daga mata, ba wani dalili bane ya kawo shi gidan sai Hindu, tun randa ya fara dora idanuwa akan yarinyar ta kwanta mishi, yayiwa Mama magana akanta tace ya dakata ta kammala sakandire, amman sosai yaso ace ko sanar da ita Hindun Mama ta bashi dama yayi kar wani yazo yayi masa shigar sauri. Mace irin Hindu ba'a saka wasa a neman auren su, amman duka kasa da shekara daya ya rage musu. Har kasan ranshi yake jinta, lokutta irin haka yakan kasa hakuri sai yazo gidan yaganta sun gaisa, kullum kyau yake kara ganin tana yi mishi da yan matancinta da yake kara fitowa. Dan haka Mama na fitowa suka gaisa yace zai wuce.
Murmushi Mama tayi, ba tun yau ta kula yakan zo gidan bane da sunan gaisuwa dan kawai yaga Hindu
"Ka gaishe su, dan Allah kace ma Hajiya ta shirya da wuri jibin zuwa sunan yar wajen Jummai... Nima da wuri zan fito in shaa Allah"
Kai Musa ya jinjina mata sukayi sallama ya wuce. Zata so yaron da Hindu saboda hankalin shi, kuma duk a gidansu babu wadda ta shaku da ita sama da Hajiya, mahaifiyar Musa, ga Baban shi ma mutum ne na kirki dayake samun shaidar mutane a duk rana, tace ya bari tagama sakandire ne sanin tsarin Baban su Hindun, kuma yaran yanzun ba'a yanke musu hukunci, gara shi Musan ya fara neman soyayya a wajen Hindu kafin manya suce zasuyi katsalandan su sha kunya.
*
Satin bikin Halima yayi dai-dai da satin da Hindu ta fara kallon film din korean da yayi tashe a shekarar 2010 mai suna Secret Garden da ita sam bata san yanda akayi sai yanzun take kallon shi bayan shekara uku dayin shi ba. Daga farko film din yaso yayi mata wani iri, dan ta saba ganin Lee Min Hoo da ya samu wajen zama a zuciyarta yayi kane-kane yana saka duk wasu sauran jaruman fina-finan korea sai take ganin su daban, tamkar kyawun su da soyayyar su bata kai tashi ba. Sai da ta rasa abin kallo, da yake yanzun a wayarta take yin kallon, sai ta saka earpiece ta dade kunnuwanta yanda babu wanda zai dameta.
Yanzun ma saida ta tabbatar har wanke-wanke tayi, tayi sallar isha'i, bata da wani assignment tukunna ta saka earpiece tana kwanciya kan kujera dan daren jiya har mafarkin film din ta dinga yai saboda yanda ta saka shi a ranta. Soyayya ce irin wadda take so, zuwa yanzun ta daina ganin fuskar jarumar, dan ta jima da daukar tata fuskar ta makala a jikin jarumar, ya zamana tanajin kamar da ita ake zuba madarar soyayyar da take faruwa cikin film din. Daman haka rayuwa take, sai kaga mijinka ya fado ta inda baka tunani. Tasan hakan na faruwa a Najeriya, kawai ba sosai ba. Yanda jarumin duk kudin shi, da ajin shi ya bada kai bori yahau wajen soyayya ya gama tafiya da Hindu.
Haka take so ta kasance da ita, dukkan kudin shi ya zama nasu ne, store dinsu da ya kusan rabin barnawa jarumin ya dauki jarumar dan ta zabi dukkan kayan da take so, amman ta watsa mishi kasa a ido tana nuna bata so, ta juya tana fara tafiya, amman duk irin wulakancin da tayi mishi sai ca yayi
'Nal tteona jima (Karki barni)'
Cikin yanayin daya burge Hindu, bata san lokacin da ta mike ba, tana tsayar da film din, idanuwanta ta lumshe tana bude su, tana jinta tamkar a kasar Korea lokacin data maimaita kalaman da jarumin ya fada, tana watsa hannayenta, ji tayi kamar ba dai-dai tayi ba, haka ta shiga maimaitawa, sai ta girgiza kanta ta sake maimaitawa, ko kadan bata kula da Zaid daya shigo ba yanata magana dan ta tare mishi hanya, sai da taji ya dala mata wani duka a gadon baya hadi da tureta
"Dalla matsa...wawiya kawai"
Ya furta a kufule yana shigewa ciki, dan zai tambayi Anty aron wayane ya kira Baba, katin shi ya kare, kuma yana bukatar magana dashi kan lemukan daya aike shi siyowa da za'ayi amfani dasu wajen bikin Halima din. Sosai dukan ya shigi Hindu, saida ta cire earpiece din ta samu waje kan kujera ta zauna, tana tuna yanda ko kusa batayi hanyar Korea ba, da Zaid bai dala mata dukan da yayi mata ba yanzun, shisa komai na kasashen ketare yake burgeta, yanayin 'yancin da suka samu na rashin kwaba kansa ta hasashen itace a wannan matsayin. Ka kwanta sanda kaga dama, ka fita lokacin daka ga dama, amman duk gidan Khadee ta dauka zata fahimci wannan fannin, data gwada mata magana tsaki taja tana fadin
'Sai a sakeka kamar tunkiya, shisa kike ganin ga rayuwar su nan, babu kan gado, musulunci ma Rahma ne wallahi'
Shiru Hindu tayi ta kyaleta, dan ita ba maganar musulunci takeyi ba, maganar zamantakewar rayuwa takeyi. Wayaki irin wannan 'yancin, ka kula duk kalar saurayin dakaga dama, kaje party babu wanda zai hanaka, har tsakar dare fita sukeyi. Amman sukam a gidansu, mazan ma akwai shekarun da zaka kai kafin ka fara fita bayan Magriba idan ba masallaci zakaje gabatar da sallar isha'i ba. Balle su kuma da in suka dawo daga islamiyya shikenan sun gama fita sai dai in su duka gidan zasuje wani waje. Ko aiken su ma ba'ayi tunda akwai maza a gidan.
Gajiya tayi da tunani kan abinda ba zata canza ba, hakan yasa ta mike tana nufar daki, da niyyar idan Allah ya bata aron rayuwa, ta sami kalar mijin da take mafarki, zasu gina rayuwar su kamar ba daga yankin Najeriya suka fito ba, har yaransu zasu zamana daban, zasu taso cikin yancin duk da ta rasa a yanzun. Shisa Baba yake da waje daban a zuciyarta, shi kadaine mutum daya a yanzun da yake da cikakken ikon da zai takurata amman baiyi hakan ba. Kwanciya tayi tana fasa yin kallon, gara tayi bacci kawai, dan bama lallai tunani yabarta ta nutsu kan kallon ba.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 15
Cikin sati daya, ko idanuwanta ka kalla sai kaga yanda tayi zuru-zuru. Anty da ta tambayeta haka kawai tace mata
"Karatun ne ya kara zafi Anty"
Jinjina kai kawai Anty tayi, da damuwa a cikin idanuwanta
"Ki dinga hutawa dai"
Murmushi ta tsinci kanta da yi, Anty na daya daga cikin iyayen da basu cika bayyana kaunar su a fili ba, amman a cikin duk wani motsi da zatayi sai ka karanci tsantsar kaunar da take yiwa yaranta. Su kansu suna mamakin yanda take gane wani abu yana damun su, ko ya canza a tattare dasu. Hindu ba zata iya gayawa Anty asalin abinda yake damunta ba, batasan ta inda zata fara ba ko da zata iya. Jaruman litattafan hausa kan sha gwagwarmaya a ciki labaran su, kafin su samu cimma burin su, amman sunayin hakanne tare da Samarin, suna nuna musu wata irin zazzafar kauna a duk wani motsi da zasuyi.
Samarin basu taba zama matsalarsu ba, sai dai dangi, ko wani abin daban. Amman cikin sati daya, Hamza ya zame mata matsalar da ki a mafarki bata hango faruwarta ba, ga soyayyar shi da ta samu waje tayi mata zaune. Ta dauka tana da rikici, ta dauka ta iya rigima, ta kuma dauka ta gama gane cewar shi Hamzan yana da rikici, sai a satin nan daya, tunda ya fara kiranta da budurwar shi, ko wayarta ya kira yaji busy saiya tsareta da tambayoyi akan wa take magana da shi, idan wani da ba dan uwanta bane ya fara tashin hankali kenan, wani irin kishi take gani tattare da shi daya fara bata tsoro.
Yanzun kiri-kiri yayi mata blocking din Ahmad daga Instagram har Twitter din ta, harda fadin
"Allah ya isa idan kika kara magana da shi, dan bakya son shi baya nufin shi din baya jin wani abu a kanki, ko da bayaji ni baimun ba, bana son shi, bana so kina magana da shi"
Ahmad din har kiranta yayi, bata daga ba saboda batasan me ma zatace mishi ba, taga text din shi
'Naga kinyi blocking dina Hindu, bansan ko nayi miki wani abu bane ba, na kira baki daga ba'
Goge text din tayi saboda kunyar Ahmad din da takeji, yana da hankali da matuqar kirki, da ta gwada cewa Hamza
"Ba zai yiwu ka dinga mun blocking din mutane ba, wasu abokan karatuna ne, idan ina bukatar tambayar su wani abu fa?"
Yanda ya fadi
"Ni? Ni kike fadama ba zai yiwu ba?"
Sai da tadan raba wayar da kunnenta, kafin ta mayar tana jin shi yana cigaba da fadin
"Kome zaki tambaye su, ni ki tambayeni, ni kadai na isheki, banda yan uwanki, ni kadai ne namijin da zai kasance a rayuwar ki, gara ki saba tun yanzun"
Kafin ma ta sami fadin wata magana harya kashe wayar shi. A kwanaki bakwai rana daya ce basuyi tashin hankali da shi ba, sai ya hau Instagram dinta, ya zaqulo tsohon chat ya tisa mata rigima a kai, ba karamin tashin hankali tagani wajen shi ba, akan hirar su da ya gani da Jalil, inda yasan yanda zancen ya qare ma da bai tashi jijiyar wuya a kai ba. Ita kam tunda ya bata password din shi ta hau sau daya, bata ma sami nutsuwar da zata koma ba. Sai yanzun da batada abinda zatayi, bata da wani assignment saboda jarabawa data qarato, sai project din zangon kawai, da a hankali take bin zanen.
Da yake asabar ce, a daki ta wuni, Anty ma bata sakata aikin komai ba, dan yanda taga tayi zuru-zuru sai ta kyaleta, taji dadin hakan har ranta. Yanzun ma tunda ta idar da sallar la'asar ta koma kan gado tayi zamanta. Hamza yace mata yana da aiki, idan anyi Magriba zai zo ya ganta, tunda duk satin basu hadu ba, sai dai video call kawai da sukeyi. Yau din ma tun safe, sai text din shi bayan la'asar
"Azkar din yamma"
Ta amsa shi da tayi, ko tana makaranta ne haka yake mata wannan tunin, yanzun da Asuba duk baccin da yake idanuwanta in batayi karatun Qur'ani ba sai yasa ta tashi, wani lokacin video call zai kira yaga ko ta tashin, yakan ce mata
"Ranar ki zata tafi dai-dai idan kika fara ta da sallar Asuba a kan lokaci, kiyi karatunki koya ne, kiyi azkar, sai ki rufe da sallah raka'a biyu idan rana ta fito"
In ta nemi yi mishi musu saiya ja mata ayoyin da zasu kashe mata jiki, sosai da duk rana Hamza yake kara samun waje a zuciyarta, lamurran shi kuma na bata mamaki sosai da sosai. Twitter din ta hau tana cin karo da tarin notifications da ta fara budewa, taga Mansy ce da tayi ma Hamza magana, ba gane me tace tayi ba tunda da fulatanci ne, wani irin tsaki taja, tsanar da tayi mata na dawowa farko
"Tsohuwar banza mai tallar goro"
Ta furta a fili tana kara dorawa da wani tsakin, ta tafi DM din Hamzan ta bude, nan ma na Mansy ne a farko
"Nawan ina kaje ne yau haka?"
Ta karanta sakon da tayi da harshen Hausa, wato munafunci ne yasa take mishi yare a bainar jama'a, anan kuma takeyin magana da wanda kowa zai iya fahimta. Shiga sakon tayi, zuciyarta nayin tsalle ta dawo makoshin ta, kafin ta koma kirjinta inda taci gaba da dokawa da wani irin ciwo da yasata yin tari, idanuwanta har yaji suke da abinda ya wuci hawayen da taji sun taru cikin su, hotunan da Mansy ta turo mishi ne tana dorawa da
"Wanne yafi kyau?"
Rigar mama ce mai hade da wani wando da Hindu takan ga turawa sun saka a bakin ruwa, bata ga dalilin da zaisa Mansy ta turo ma Hamza irin wannan hoton bane ba, ko da soyayya sukeyi abune da bai kamata ba sam-sam. Amman kamar yanda Dimples kan fadane
"Ni banga dalilin da zaisa mata suje suna fada da yan matan mazajen su ba, ko ke budurwa da bakima shiga gidan shi ba ki fara tsanar matan da suke tare da shi ba, saboda koma me yake faruwa a tsakanin su, shi ya bada fuska"
Amman hakan bai hanata jin kamar ta soka ma Mansy mashi ba, sama tayi tana karanta hirarrakin su da ko kadan babu kintsi a ciki, sam batasan hawaye take ba sai da taga digar su saman screen din wayarta, sosai kirjinta yake mata zafi, bata taba jin ciwon zuciya irin wanda takeji ba yanzun. Kwata-kwata tashin hankali bakonta ne, fitowa tayi daga hirar, tana cigaba da bude sakonnin sauran matan, da suke ma Hamza tallar kawunan su, sai dai amsar shi daya ce ga duk wadda ya amsa
"Digits"
Ma'ana lambar wayar kenan, in suka ajiye kuma babu wani abu da yake sake hadasu, amman hirar su da Mansy ta gama tabbatar mata da abinda yake faruwa a tsakanin Hamza da sauran matan.
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Ta tsinci kanta da furtawa tana sauke wata ajiyar zuciya saboda kukan da takeyi. Hamza na bin mata, ko baya bin sauran matan yana tare da Mansy. Wannan ba zargi takeyi ba, hirar su ce ta tabbatar mata da hakan. Wayar ta ajiye kan cikinta, tana saka tafukan hannuwanta duka biyun ta rufe fuskarta da su. Kuka takeyi da ba zata tuna ranar da tayi irin shi ba, sosai zuciyarta take ciwo kamar zata fito. Tana nan kwance, tayi kuka har fuskarta ta kumbura, kafin ta iya mikewa tana shiga bandaki, ta wanke fuskarta, tana dauro alwalar Magriba. Tana fitowa ana kiran sallah, lokacin da yayi dai-dai da shigowar Asma dakin da sallamarta da Hindu ta amsa murya a dishe.
Tana kuma yin sauri ta kabbara sallah, tana jin Asma ta shiga bandaki, tana fitowa kuma ta fice daga dakin. Tana idar da sallah, dakyar ta iya yin azkar, da ta daga hannuwanta sai ta rasa addu'ar da zatayi, tana tsaka tsakiya neman wani canjin ba Hamza ba, ko kuma nema mishi shiriya, kafin ta yanke hukuncin tsayawa a nema mishi shiriya, dan zuciyarta ta karyatata wajen tunanin cewa abinda tagani akan Hamzan ya canza abinda take ji, yana nan daram a ranta kamar komai bai faru ba.
Wayarta data fara ruri ta mika hannu ta dauka tana ganin shine, dagawa tayi ta kara a kunnen ta
"Ina cikin gidan ku"
Ko magana batayi ba ta sauke wayar daga kunnenta, tana mikewa. Ko fuskarta bata duba a mudubi ba, hijabin jikinta kawai ta sake, tana daukar ruwan toka, da ta Asma ce ta zira a jikinta. Ba zata tsaya shafa wani abu ba, shiya sakata kuka, ya kamata yaga haka, ba zata boye mishi tana cikin yanayin damuwa ba.
*
Komai sabone a wajen shi, inda wani a cikin abokan shi zaice mishi a shekarar nan zai kira wata yarinya da budurwar shi zai karyata. Ba zaice ga yanda akayi ya ce Hindu ta saka shi a layin samarinta ba, yafi ta'allaqa hakan akan yanda tunaninta da wani saurayin yasa shi ganin wani hadarin kishi na gilma mishi ta cikin idanuwan shi, kirjin shi har zafi yakeyi. Bayason kowanne namiji a kusa da ita banda shi, bayason wani yaji muryarta, balle yaji yana son ya riketa kamar yanda yakan ji duk idan tana magana.
Aikin daya sakko su gaba bai hana shi tunanin halin da take ciki ba, da wa tayi magana a makaranta, wayai mata magana, waya tare ta a hanya. Shi kadai sai ya tsinci kan shi da jan karamin tsaki, yanzun tunda ya shiga Instagram dinta rabon daya shiga nashi, yana kai kullum yana ganin yanda ta sake tana hira da maza da yake bala'in bata mishi rai. Yau ma duk da ya yanke hukunci ajiye komai yaje ya ganta, haka ya shiga Instagram yana dudduba sauran chats dinta, dan duk wanda ya karanta saiya goge gabaki daya, yayi blocking idan namiji ne. Matan baya bi ta kansu sam, tsaki yaja ganin wani yayi mata sallama tafi biyar
"Wawa kawai"
Ya fadi yana saka AbdulHafiz da yake shan shayi yana aiki a system din shi ya dago da ido ya kalle shi
"Me yasa maza basu da aji ne?"
Hamzan ya tsinci kan shi da tambaya, yana saka AbdulHafiz yin murmushi
"Me yasa wasu mazan basu da aji zaka ce.