Showing 30001 words to 33000 words out of 110313 words

Chapter 11 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt

tsintar kanta da duba wayarta ko ya mata magana, itace bataji karar wayar ba. Har kallo ta fara data kwanta, ko zai dauke mata hankali, amman ta kasa, tunani ne kala-kala a ranta, musamman yanda zatayi ma Hamza magana karya sake tabata, ya hakura suyi aure tukunna, kafin ta fara tunanin ai har yanzun baima ce yana sonta ba ballantana magana irin wannan ta shiga tsakanin su.


Ganin tunani zai dameta ya sata shiga Instagram, tana ta kallon kwalliya tunda tana da wadattaciyar Data, Hamza na tura mata kati har ta rasa abinda zatayi da shi. Sai dai ta siyi data ta shiga YouTube ko taje Instagram taita kallon shagalin bukukuwan da ake sakawa a shafin 9ja weddings. Abin yana kayatar da ita, wasu bukukuwan kan sata hasaso yanda nata zai kasance. Yanzun din ma abinda takeyi kenan, tana hango dinkin da za'ayi mata, sai taga notification na cewa an mata sako, da sauri ta duba ko Hamza ne, dan sha biyun dare, sai taga Ahmad ne yayi mata sallama, duk sai taji haushi ya kamata, dan har ranta ta saka ran Hamza ne.


Kamar ta share shi, saita bude ta amsa sallamar


'Wai kinga abinda ya sami Mike?'


Da sauri ta fara bashi amsa


'Wallahi Ahmad karka bani labari, karka batamun kallona, ka kyaleni'


Kawunan dariya ya turo mata, kafin suci gaba da hira, yana dan debe mata kewar Hamzan da takeyi. Batasan lokaci na ja bama, dan in suka fara hirar films ita da Ahmad din, ko waya sukeyi hakan ne yake kasancewa, kan abu daya daya faru a film din zasu iya kwanaki suna gardama a kai, kamar yanzun da ta dake babu abinda Mike zai nuna ma Harvey sai kwakwalwar shi, amman Ahmad din yaki yarda. Wajen daya saura, taji idanuwanta sun fara mata yaji, ta fita daga chat din su da Ahmad din taga Hamza yayi mata magana a Instagram din, kuma baifi mintina biyu da sauka ba. Amsa Hello din shi tayi, sakon na shiga tana ganin ya turo mata alamar tambaya a whatsapp.


Sai ta koma can din, kafin ta amsa shi ya sake turo


'Bakiyi bacci ba? Me kike yi? Zane?'


Ya jero mata tambayoyin yana sakata yin murmushi


'Aa, ina kwance ne ma, yanzun dai zanyi baccin, kai ma bakayi ba, ko aikin ne?'


Tana kallon yana rubutu


'To me kikeyi? Bakiyi bacci ba har yanzun'


Ya turo yana share tambayar ita da tayi mishi, tasan halin rikicin shi


'Naje Instagram ina kalle-kalle, sai kuma na tsaya muna hirar film ni da Ahmad'


Tana ganin ya dauki lokaci yana typing


'Ahmad? Waye shi din? Har tsakiyar dare kina hira da shi? Me yasa zaki dinga magana da shi da daren nan? Akan me? Shi me yasa zaiyi hira dake da daren nan?'


Yau kam ji tayi tagaji da kishin da yake nunawa a kanta ba soyayya suke ba, baice yana son ta ba, amman ya dinga tsareta da tambayoyi, yanzun bata isa ta amsa wani a comment section ba sai sunyi rigima, ko hoto ta saka nata sai yace ta cire.


'Kai ga shi ina hira da kai, menene dan nayi da shi? Abokina ne'


Gani tayi yana typing, yakai mintina biyu, amman sako bai shigo mata ba, har tayi tunanin ko network dinta ne, kafin taga kiran shi na shigowa, sai da taji gabanta ya fadi, da sauri ta danna gefen malatsin wayar tana sakata a silent, tashi tayi ta sakko daga kan gadon tana zuwa ta duba kofar dakin, taga Asma bata rufe ba, ita ta murda mukullin, sanda ta koma kiran harya yanke, saiga sakon shi ya shigo


'Ki daga wayar nan Hindatu'


Kafin ta amsa ya sake kira, dagawa tayi muryarta can kasa tana fadin


"Hello"


Ta dan runtsa idanuwanta jin yanda muryar shi ta daki kunnenta a fadace


"Ni da shi daya ne? Me yasa zaki hada mu kamar muhimmancin mu a wajen ki iri daya ne? Akan me zaki ce dan kina magana dani ko da yaushe shima zakiyi magana da shi haka?"


Tashi zaune tayi dan taga alamar rigimar Hamza yake so suyi, abinda bai sani ba shine ita kanta ta iya rigimar, kawai dai bata nuna mishi ne, tana lallaba shi, idanuwan shi kawai idan ya kafa mata sai taji duk jikinta yayi sanyi, amman yanzun bata ganin shi, zata iya tattaro kwarin gwiwarta ta fada mishi duk abinda take son fada


"Kasan ko bashi ba dole zan kula wasu ai..."


Tana jin hucin da yake har ta cikin wayar


"Saboda me?"


Numfashi ta sauke


"Saboda ni macece, budurwa kuma, ko ba abokai ba, zanyi samari"


Tana jin shirun daya biyo bayan maganarta, dan saida ta ciro wayar daga kunnenta dan taga bai kashe ba, tana ta reading, kawai shiru yayi da yasa zuciyarta cigaba da dokawa kamar zata fito daga kirjinta


"Bana so"


Ya fadi can kasan makoshi, yana sa ta sauke muryarta


"Haka zakayi hakuri... Dole zanyi samari Hamza, kaima abokina ne"


Tayi maganar da wani irin ciwo da taji ya fito daga zuciyarta, tasan karya takeyi, tana kuma addu'ar baiji yanda muryarta take rawa ba, yanda ya wuce matsayin aboki a wajenta, tana son shi, tana son shi fiye da yanda take tunanin soyayya take, tana son shi har mamaki abin yake bata.


"Kibari, bana so, karki sake hadani layi daya da abokan ki"


Cike da gajiyar da takeji har a kasusuwanta, da kuma kukan da take son tarbewa tace


"Ina kake so in ajiyeka? Ka fadamun inda kake so in ajiyeka"


Shirun ya sake biyo baya, fiye da na dazun, kafin kamar wanda aka shaqe yace


"Ki ajiyeni a saurayin ki, karki hadani da kowa, bana so, karki hadani da kowanne namiji. Wallahi zamu sami babbar matsala"


Murmushinta da wasu hawaye masu zafi ya bayyana, tasa ka hannu tana share su, tana jin yanda zuciyarta take tsalle-tsalle


"Ahmad da wa kike hira cikin daren nan?"


Kai ta girgiza tana danyin gyaran murya kafin tace


"Shi kadai ne"


Da sauri ya amsata da


"Ban yarda ba"


Kafin ta amsa ya sake cewa


"In gani"


Yana kashe wayar, Hindu ta sauketa daga kunnenta tana binta da kallo, kafin sakon shi ya shigo mata ta whatsapp


"Menene Password dinki?"


Tsintar kanta tayi da tura mishi


'HAlamin'


Tana cigaba da kallon wayar, baifi mintina biyar tsakani ba, ta sake ganin ya mata magana


"Jibi tarin mazan da kike magana da su, Hindu kina so ki kasheni ko?"


Murmushi tayi, bata san abinda zatace mishi ba, can ta sake ganin yayi magana


"Kina Twitter daman? Me yasa wannan banzan yake tambayar handle dinki?"


Batama san waye yake magana akai ba, ikon Allah kawai take kallo, kafin taga notification din twitter alamar anyi following dinta, tana dubawa taga Hamza dinne, shisa ta neme shi bata gan shi ba a Twitter, HAbuAbbas ya saka a handle din. Bin shu tayi itama, tana fara duba tweets din shi, duk yawancin hirarrikin shi da abokan shine, sai wata Mansy_ da taga suna magana, ta bude profile dinta tana duba hoton ta, sai da taji gabanta yayi mummunar faduwa ganin hoton jikin Avi din Mansy din ita da Hamza ne, da alama ita ta dauka, dan Hamzan yana bayanta ya daga girar shi duka biyun da murmushi a fuskar shi.


Da sauri ta koma tana sake duba hirarrikin nasu da bata fahimta, dan yawanci da yaren fulatanci duk maganganun da sukayi yake. Handle din Mansy din ta sake komawa tana shiga gabaki daya hotunan ta da sun kai dari takwas, tana kuma matuqar mamakin ganin wajen kala talatin duk tare da Hamza ne, sai wasu da yawa kuma nashi ne shi kadai. Zuciyarta ta so gaya mata kanwar shi ce, amman kuma yanayinta ya nuna zata iya zuwa shekaru daya da Hamzan, dan ba yarinya bace ba, kuma kanwar shi ba zata saka hoton su da caption din 'Me and Mine' ba. Ta kira shi nata a yawancin duk hotunan da ta saka nasu, kuma bata ga inda ya gyara mata ba.


Kanta taji ya fara sarawa saboda tashin hankali, tsintar kanta tayi da dawowa Whatsapp inda Hamzan yabar mata tarin saqonni yana mata tambayoyi akan mazan da suke DM dinta na Instagram din


'Wacece Mansy?'


Ta tambaya, bai ko numfasa ba ya dawo mata da amsa


'Qawata ce'


Yana dorawa da


'Mariya24'


Kafin ya sake cewa


'Shine password dina na Twitter, ki duba kigani, banda abinda zan boye miki'


Numfashi Hindu ta sauke da batasan tana rike da shi ba, duk da ta sami waje a layin mutanen da ta tsana ta saka Mansy a saman dukkan su, zata hau twitter din tagani kamar yanda yayi ikirarin bashi da abinda zai boye mata. Gara ta tabbatar dai, amman ba a daren nan zatayi haka ba. Sai da safe, zuciyarta gara ta nutsu waje daya. Kar ta buga da irin tsallen da taketa faman yi, yau zata kwanta da nasara guda daya, zata iya nuna ma kowa Hamza ta kuma kira shi da saurayinta, wannan kadai ya isheta, shine kuma abinda zatayi tunani, Mansy da komai zasu iya jira sai da safe. Hakan kuwa tayi tana lumshe idanuwanta, ko sallama batai ma Hamza ba, bacci yayi gaba da ita cike da mafarkin shi.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 13


Idan akace maka a kasa da wata daya Hindu da Hamza sukai kalar shakuwar da sukayi zaka karyata hakan. Idan basa manne da juna ta waya, suna manne ta chatting, dan ma lokutta da dama karatu yake tayata yi, amman ko zane takeyi, maimakon ta saka waka ko karatu yanda takanyi wani lokacin, sai suyi waya. Ko aiki yake yakanyi mata text. Sai dai kamar yanda tagani tun a haduwar su ta farko, yana da rigima, sosai yana da rigima fiye da yanda take tunani. Zuwa yanzun Hauwa kadai tasan suna tare da Hamzan, batason ta cika yawan magana akan shi din, tunda bawai yace yana sonta bane ko wani abu.


Ko kadan bata wasa da addu'a kan hakan ya kasance. Dan har ranta take jin Hamzan. A lokacin kuma sau uku kadai suka hadu, zai wuce hidima ne sai ya biyo makaranta yaganta, ko mintina biyar baya cikawa, saboda yace mata sosai aiki ya rincabe musu. Yaune dai sukayi dashi zaizo har gida ya ganta. Dan ta ma sanarma da Anty, ta kuma gaya mata baya tashi aiki da wuri, ba zai samu zuwa da yamma ba. Ita kanta wani sama-sama take jinta, duk da yana kokarin kiranta video call, ba kamar tana ganin shi ba, yayi mata alkawarin ana idar da Magriba, zai bata awa biyu cikakku


"Ina so in ganki"


Shine abinda ya furta mata


"Da gaske ina so in ganki, Video call din nan baya mun"


Dariya kawai tayi, sai gashi kuma ya samar musu lokaci. Yau kam kwalliya tayi sosai, tana saka Abaya, a harabar gidan ta same shi a tsaye jikin motar shi. Jikin shi sanye da shadda sai maiqo takeyi, fara kal da ita, sai hular shi da takalmin kafar shi ruwan toka, yayi mata kyau kamar ta sace shi ta boye kar wata ta kallar mata shi. Murmushi yayi mata


"Sannu da zuwa"


Ta furta tana ajiye mishi kujerar data dauko, ta rabasu da yake guda biyune a hade, itama ta ajiye daya a gefe.


"Ina zuwa"


Cewar Hindu tana komawa, a bangaren Mama ta tsaya tana shiga kitchen ta dauko mishi ruwa roba daya, sai coke da tagani a ciki, batasan waya zuba ba. Ta dai dauki guda daya ta sami plate mai kyau, sannan ta koma. Plate din ta ajiye a kasa, tana dora ruwan da coke din a kai.


"Ga ruwa"


Hannu Hamza ya kai yana daukar coke din dan lemon shine


"Ke dai ki sha ruwan, nikam na dauki coke"


Yai maganar yana bude robar yakai bakin shi ya kurba


"Kin san yanda nayi kewar ki kuwa?"


Sadda kanta kasa tayi a kunyace, tana jin dadi idan yace yayi kewarta, sai taji kamar tana da wani muhimmanci mai girma a wajen shi


"Nima nayi kewar ka ai"


Ta tsinci kanta da furtawa, tana saka shi girgiza mata kai


"Da kinyi kewata da kin kalleni, tunda kika fito idanuwanki suke a kasa"


Dariya ta danyi, ba kallon shi bane batason yi, kunya take ji, yayi mata kyau na gaske, idan bai sani ba.


"Hindu..."


Ya kira can kasan makoshi, saboda ganinta ya birkita mishi lissafi gabaki daya. Ba karamin kokari yayi ba wajen kokawa da zuciyar shi ganin bai rungumeta a cikin harabar gidan su ba. Yanzun ma kokari yakeyi na ganin bai kamo ko da hannunta da take ta wasa da wayarta da shi bane ya rike a cikin na shi. A hankali ta dago kai tana sauke idanuwanta cikin na shi, amman yanayin da take gani a cikin su ya sakata sauke nata babu shiri. Numfashi ya sauke yana runtsa idanuwan shi hadi da bude su a kanta


"Me yasa duk wanda yai miki magana sai kin amsa shi a Instagram?"


Ya tambaya da wani yanayi a muryar shi yana kuma tsareta da idanuwan shi, tambayar tayi mata bazata, Hamza kuma amsarta yake jira, har ranshi yake jin wani irin kishin yaga garadan banzan nan suna mata magana. Bayaso sam, ba wai soyayya suke ko wani abun ba, amman yanajin tashi ce shi kadai, har kuma ranar da zai daina jin hakan, bayason kowanne namiji a kusa dashi, shisa sam bayabin mace sau biyu, saboda ba zai taba iya rabata da wani ba, yanada wannan kishin, ballantana kuma Hindu da ta sami waje tayi kane-kane a rayuwar shi.


"Haka kawai"


Ta amsa dan batasan me ya kamata tace mishi ba


"Bana so, bana so kina magana da su"


Ya furta cike da ikon da ya bata mamaki, a gefe daya kuma yana mata dadi, dan ya daga mata burin da take da shi a kan shi, a cikin muryar shi take son karantar kamar kishi yake son nunawa. Dan murmushi tayi


"Ki kalle ni Hindu... Da gaske nakeyi bana so, ki daina magana da su"


Kai ta jinjina mishi, ya sauke numfashi, kafin yace


"Nagode..."


Hadi da mika mata hannun shi, bataga komai da take rike dashi ba sai wayarta, dan daga mishi wayar tayi cike da alamar tambaya, ya jinjina mata kai, daga mukulli ta cire sannan ta mika mishi, Instagram dinta ya shiga yana goge hoton da ta saka jiya, baka ganin komai sai fuskarta da hular da take kanta, ta saka da caption din 'Work, work, work'. Sai dai alamun bacci da gajiyar da take cike da idanuwanta yasa tayi mishi wani irin kyau kamar ya lasheta. Tarin mazan da suke kasan comment section dinta yasa ya tabbatar shi kadai yaga tayi kyan ba.


Hindu kuwa tsayawa tayi tana kallon ikon Allah, dan Hamza ya wuce Mijin Novel, duk yanda take hasaso mazajen, shi yana nuna mata kyawun shine kawai yayi dai-dai da nasu, amman ya fisu rikici da baudadden halayya. Kawai shi ba miskili bane, ba kuma shuru-shuru bane. Yana magana sosai sosai, duk wani hoto da bayason wasu kartin banza suna gani, suna kalle mishi ita suna hadiyar miyau yabi ya goge. Tukunna ya mika mata wayar da fadin


"Bana so, bansan me yasa kike yawan saka hotunan ki ba"


Duba Instagram din tayi taga ya goge mata hotuna masu yawan gaske


"Duk ka cire mun hotuna, wasu fa bani da su a wayar yanzun"


Hindu ta fadi kamar zatayi kuka, akwai hotunan da ta dora ne ko da zata rasa wayar. Kafadu yadan daga mata yana hade fuska. Akan ta yake mamakin kan shi sosai, bai taba daukar wayar ko da cikin abokan shi ya goge musu wani abu ba, amman ikon da yakeji akan Hindu mai girma ne


"Ki dinga turo mun kafin ki saka, kowanne wawa zai bude bakin shi yayi magana kinyi kyau. Bana so"


Kallon shi tayi tana sauke numfashi, tama rasa abinda ya kamata tace mishi


"Kina jina kikayi shiru"


Ya sake fadi, kai ta iya daga mishi kawai, dan lamarin ne take ganin yafi karfinta.


"Thank you"


Ya furta yana kai hannun shi ya dan murza goshin shi, kafin ya sauke shi yana kamo na Hindu da zuciyarta tayi wani irin tsalle kamar zata faso kirjinta ta fito, kar wani ya fito yagan su, ko wani ya shigo yagan su


"Na cika rigima ko?"


Ya fadi yana lankwasa yatsun hannunta hadi da sake budesu ya hada cikin nashi ya dumtsa, kafin ya sauke idanuwan shi cikin nata da yake ganin bayanannen tsoro a cikin su, kome tayi kara birkita mishi lissafi takeyi


"Haka zakiyi ta hakuri dani"


Ya fadi muryar shi can kasan makoshi. Hannunta take son zamewa daga cikin nashi, so take tace ya sakar mata hannu kar wani ya fito, amman sam ta kasa. Bakinta yayi mata wani irin nauyi, kuma kallon da yake mata batajin zata iya tabuka wani abin kirki, da kan shi ya sakar mata hannu bayan yadan dumtsa shi, hadi da sauke numfashi yana mikewa, da idanuwa Hindu ta bishi, motar ya bude ya mike hannu yana dauko agogon daya siya wajen Mansura. A status dinta yaga ta dora, yayi mishi kyau sosai. Bata tsare shi da tambayar wa zai bama ba, dan tasan halin shi da kyauta.


Dawowa yayi ya zauna, yana jin dadin samun wani dalilin da zai rike hannunta. Agogon ya fara kwancewa sannan ya kama hannunta yana dago shi, ya daura mata agogon, sai yaga hannun yayi mishi kyau. Yana ganin agogon ya hango shi cikin hannunta. Itama dago da hannun tayi, zuciyarta ta shiga wani yanayi da ba zata iya misaltawa ba


"Nagode..."


Ta furta a hankali, kai kawai Hamza ya iya daga mata, yanajin dadin sallar isha'i da yaji an fara kira


"An kira sallah"


Ya furta yana saka Hindu ware mishi idanuwa kafin ta shagwabe fuska


"Tafiya zakayi ko?"


Ta bukata tanajin kewar shi na danneta tun kafin ya tafin


"Ki kasheni kawai, Ki kasheni"


Ya fadi cikin yaran fulatanci yana sakata dakuna mishi fuska cike da rashin fahimta


"Zan dawo ai, in kina da lokaci gobe zanzo muje muci abincin rana tare"


Kai ta jinjina mishi, a cikin kanta tana tunanin lakcocin da take dasu goben. Hamza daya mike yana katse mata tunanin da takeyi


"Da gaske tafiya zakayi ko?"


Tai maganar cikin muryar da ta saka shi son sumbatarta, amman hannunta ya rike ta fara zare mishi idanuwa kamar yana zare mata rai, zai dauke shi lokaci mai tsayi kafin yazo wannan matakin, lokacin da bayajin yana da hakurin jiran shi, saboda yanda komai tayi yake kara kwadaita mishi ita.


"Hindu so kike ki hanani tafiya ko?"


Yar dariya tayi tana girgiza mishi kai


"Zan ganki gobe In shaa Allah"


Mikewa tayi itama, kawai saiya tsinci kan shi da sake kamo hannunta, yana share tsoron da yake gani a cikin idanuwanta, hannun yakai yana goga shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login