Showing 12001 words to 15000 words out of 110313 words

Chapter 5 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt

Me ya faru?"


Tsaki Hamza ya sake ja, duk satin nan baya rabuwa da ciwon kai, akan Hindu ne kuma, ita ce sabon ciwon kan da ya shigo rayuwar shi


"In kaga mazan da suke DM dinbHindu suna mata magana zakayi mamaki wallahi, kamar basu da wani aiki banda bin yaran mutane"


Shayin AbdulHafiz ya kurba, sannan ya ajiye kofin a nutse, ba sosai yake saka kananun kaya ba, yanzun ma dan suna gidane, anan suke ta aikinsu tun safe, tracksuit ne a jikin shi, riga da wandonsu, yaja zif din rigar har wuyan shi a rufe yake ruf, dago da idanuwan shi yayi yana saukewa kan Hamza da yake girgiza kan shi cike da dana sanin subutar bakin da yayi akan Hindu din. Banda Fodio babu wanda yasan da maganarta, shima Fodio din ya dauka Hamza ya sami abinda yaje nema ya barta.


"DM? Screenshot ta turo maka?"


AbdulHafiz din ya fara tambaya, Hamza ya riga yasan ba zai iya kaucewa maganar ba, ya riga yayi subul da baki, kuma yanayin fuskar AbdulHafiz din ya nuna mishi ba zai bashi wannan damar ba yau, gashi su kadai ne, Arafat da su Fodio suna kamfanin su. Daga shi sai AbdulHafiz din a gidan, da saiya sake maganar, AbdulHafiz zai dauka bayason yayi a gaban su Arafat a lokacin, zai kyale shi.


Kai ya girgiza ma AbdulHafiz din


"Da kai na nake gani"


Shayin AbdulHafiz ya sake kurba yana ajiye kofin


"Abu biyu zan fada maka, ban san me kakeyi a Instagram ko Twitter din ta ba, amman hakan zai saka rashin yarda a tsakanin ku, idan ka yarda da kanka, ka yarda da soyayyar da take maka, sauran mazan bai kamata su dame ka ba"


AbdulHafiz ya fadi yana dorawa da


"Ka zama Sarki a masarautar yarinyar da kake tare da ita, sauran mazan duk da zasu zo fadawa ne, ba su da wani muhimmanci, da kanta zata baka labari kuyi dariya. Karka fara dora alamar tambaya akan zaman ku, in bata baka dalilin yin hakan ba"


Yana jin kalaman AbdulHafiz dinne, amman bai yarda dasu ba, badan bai yarda Hindu tana son shi ba, kawai dai yana so yaga dawa take magana ne.


"Wacce Hindu din?"


AbdulHafiz ya tambaya, tunda maganganun da yayi basa bukatar amsa, kawai saurare ne, idan Hamza yaga dama ya dauka, idan baigani ba ya rigada yayi nashi bangaren.


"Yarinyar da ka amsa a DM dina"


Kai AbdulHafiz ya jinjina, yagane ta, yana son yaji tabbaci ne daga wajen Hamzan. Sosai ya gyara zaman shi yana tattara duka nutsuwar shi da hankalin shi akan Hamzan, dan maganar da yake son fadi na da matuqar muhimmanci a wajen shi


"Nasan kaddara zata hadaku idan Allah ya rubuta hakan ko da ban amsata ba, kaddarar tazo da ni ne sanadi. Ka jini Hamza, saboda zan fada maka sau dayane, kamar dan uwa kake a wajena, kasan hakan, ba yau ne na farki dana fada maka ba, ina maimaita maka ne...."


Numfashi Hamza yaja yana fitarwa, tun kafin AbdulHafiz din ya karasa maganar ta tsinci kanshi da son tashi ya gudu yabar dakin, dan ya kauce ma jin koma meye zai fada


"Kusancin da yake tsakanin mu ba zai sa ka darsa mun kokwanto a neman lahirata ba Hamza. Kana jina, idan ba da niyyar aure kake tare da yarinyar nan ba, idan babu alkhairi a tare da niyyar ka, ka yanke koma menene a tsakanin ku, bazan zama silar baka ticket din da zaka sakata a layin matan da kabi ba. Baka isa kai mun haka ba, wallahi baka isa ba, kaji na rantse, ban isa in hanaka abinda kakeyi ba, shisa nake binka da addu'a, amman banda ita, banda Hindu....ba rokon ka nakeyi ba, fada maka nayi. Bazan yafe maka ba wallahi..."


AbdulHafiz ya karasa maganar yana so Hamza ya fahimci da gaske yake, idan ya bata musu yarinya zai yanke alaka da shi, maganar farko tayi mishi yanayi da Nabilar shi, batayi kama da matan da Hamza ya saba bi ba sam, ba zai zama sanadin da zata lalace ba. Ba zai yafe ma kan shi ba idan Hamza ya taba ta, kamar yanda ba zai yafe ma Hamzan ba. Kofin shayin shi ya dauka yana tura kujerar da yake kai baya, hadi da mikewa dan yaje ya karo wani shayin da yake kitchen cikin kettle.


Nan yabar Hamza a zaune yanajin kamar an mishi wanka da ruwan kankara. Shi bai shirya yin aure ba, sam babu wannan tsarin a rayuwar shi nan da shekaru biyu ma, ko gidan shi bai gama ba. Bai san yanda AbdulHafiz din yake so yayi ba, yanajin dai yanzun ko Hindu bata isa ta raba shi da kanta ba, balle kuma wani. Har ran shi yanzun ba zaice ga abinda yake da niyya akan ta ba, yana son kasancewa da ita, amman shi bai shirya aure ba sam. Kamar yanda bai shirya yanke alakar da take tsakanin shi da AbdulHafiz ba, zai iya hakura da Hindu ko da aurenta zai idan hakan zai shafi alakar da take tsakanin su da AbdulHafiz, yana jin shi kamar dan uwan shi, sun wuce matakin abokantaka.


Sosai kan shi yake mishi ciwo, AbdulHafiz ne ya dawo


"Kai ba zaka sha shayin ba?"


Ya tambaya kamar bai gama hargitsa mishi dukkan lissafin shi ba, ammam AbdulHafiz ne, ya riga ya gama maganar kenan, ba zai maimaita ba. Yabar komai a hannun Hamzan, zabin nashi ne. Kai kawai ya girgiza mishi da yake jin yana kara ciwo. Su dukan su aikin da sukeyi suka cigaba. Kafin AbdulHafiz din ya fara waya da Nabila, ya saka earpiece a duka kunnuwan shi, hirar tasu na saka Hamza jin kewar Hindu da ta danne shi, tun la'asar rabon daya ji motsinta. Aikin da yakeyi yai saving yana kashe laptop din ya mike, zuwa yai yadan watsa ruwa ya dauro alwalar magriba ya fito, kaya ya sake zuwa manya, wani farin yadi daya karbi jikin shi, bakar hula da takalmi ya saka. Ya dauki mukullin mota yana fita falon


Wayar shi ya dauka da take kan tebirin da suka ajiye daga can gefe inda suke ayyukan su, dining ne ba zama suke suci abinci ba, ya zame musu kamar Office din gida. Harya kai kofa AbdulHafiz yace


"Hamza..."


Juyawa yayi


"Allah yasa alkhairin ka ce"


Dan murmushi Hamza yayi yana ficewa daga gidan,wasu lokuttan AbdulHafiz kanyi mishi kamar babban Yaya, duk da watanni biyar ne tsakanin su, shisa yake kasa zagin shi kamar yanda yake zagin su Fodio. Yanayin kusancin su daban ne, kuma su dukan su yana musu kamar Yaya fiye da yanda yake aboki a wajen su. A hanya ya tsaya nan masallacin da yake station round about, yayi sallar magriba, kafin ya karasa gidan su Hindu, maigadi na bude mishi kofa ya shiga da motar shi, bai fito daga motar ba ya kira wayarta, tana dagawa yace


"Ina cikin gidan ku"


Batace komai ba, shima bai jira amsarta ba, ya kashe wayar daga bangaren shi, yana ajiyeta a cikin motar. Wani irin sama-sama yake jin shi, ga kan shi da yake ciwo har lokacin, duk da wani bangare na zuciyarshi na cike da jin dadin zaiga Hindun, yau maganganun AbdulHafiz da yake ji sun dabai-baye shi sun kashe mishi jiki tsaf, a karo na farko tun daya hadu da Hindu da yazo wajenta batare da yanajin kamar inta fito bai riketa ba zai mutu.


Bai fito daga motar ba, sai da yaga Hindu da ta ajiye musu kujeru bayan motar shi, da murmushi a fuskar shi ya zagayo yana jan kujerar ya zauna. Sai dai tana zama ya sauke idanuwan shi kan fuskarta, murmushin da yakeyi ya dishe


"Hindu..."


Ya kira ganin fuskarta da take a kumbure har cikin idanuwanta, ai kamar hakan take jira taji wasu hawaye da ta kasa tarbewa sun zubo mata, yana fitowa taji kamar ta rufe shi da duka, kallon da yake mata cike da damuwa shiya karya mata zuciya yasa hawayenta zuba


"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un... Me ya faru? Menene?"


Hamza ya fadi yana kai hannu ya riko na Hindu data fisge tana goge hawayen fuskarta


"Dan Allah kiyi mun magana"


Numfashi taja tana sake goge fuskarta, zuciyarta take ji tana ciwo kamar zata fado


"Me yasa kabani Password din ka?"


Ta tambaya tana tsare shi da idanuwanta da suke cike da wani yanayi da yaji bayaso


"Saboda bani da abinda zan boye miki"


Ya fadi da dukkan gaskiyar shi


"Har hirar ku da Mansy?"


Ta bukata tana jin kirjinta na gab da budewa, numfashi Hamza yaja, yana huro iska ta bakin shi, ya dauka wani abinne daban akayi mata, ko shi yayi mata bai sani ba. A hankali ya daga mata kai, tunda ta rigada tagani baiga dalilin da zai mata wani boye-boye ba. Cikin sanyin murya saboda kan shi da yake ciwo yace


"Me kike so ince miki?"


Dariya Hindu tayi da bata da alaka da nishadi


"Kana da karfin halin yimun wannan tambayar Hamza? Bakasan abinda ya kamata ka ce mun ba? Akan abinda kukeyi da Mansy har kana ce mun baka da abinda zakace mun?"


Idanuwan nan nashi ya kafa mata, irin wannan dalilin na daya daga cikin dalilan da zasu saka shi kinyin aure nan kusa, ba zai yiwu ana tsare shi da tambayoyi haka ba


"Karkiyi mun ihu, karki fara cewa zakiyi mun fada. Dana baki password dina nace ki karanta mun chats? Na aikeki karanta hirar mu da Mansy? Da kika fara karantawa kikaga ba zaki iya jurewa ba me yasa kika ci gaba?"


Bakinta a bude yake tunda ya fara magana, dariyar ta sakeyi duk da idanuwanta da suke cike taf da hawaye


"Kana da karfin hali, wallahi kana da karfin hali Hamza"


Daga mata gira yayi cike da masifa, kan shi ciwo yake kamar zai rabe biyu. Tana kuma kara mishi ciwon kai kan abinda ita taga zata iya karantawa, shima haka ya jure bin chats dinta da garadan duk da suke mata magana, harda Jalil, baiyi kuka ba duk yanda zuciyar shi tayi mishi ciwo, sai ita da take da hawaye a kusa zatayi amfani da su ta cuce shi, haka mata sukeyi daman ya sani, abu kadan sai su fara kuka, idan wani yagani zai baka rashin gaskiya kamar kayi musu wani babban abu.


"Na karanta hirar ku da Jalil tun daga farko har karshe, saboda bani da hawaye shine zaki fini fada"


Kai Hindu take girgiza mishi


"Karka hada wannan da Mansy, ni banbi Jalil ba, bakama san ya muka kare da shi ba"


Cikin idanuwa Hamza yake kallonta


"Zunubina ne, me yasa zai dameki?"


Mikewa tayi, ba zata iya ba, zuciyarta fadowa zatai idan taci gaba da sauraren Hamza, taci gaba da ganin yanda yake nuna zina a wajen shi ba wani babban abu bane ba. Hannunta ta kama yana janta ta koma ta zauna babu shiri, hannunta ta fisge


"Karka sake tabani, abinda ya kawoka kenan daman. Wallahi ba zaka taba samu ba, saboda ni ba Mansy bace ba, kasani dai ka cutar dani....Allah kuma ba zai barka ba"


Hindu ta karasa wasu irin hawaye masu zafi na zubo mata, zuciyarta ciwo take har cikin makoshin ta, ga wani tsoro marar misaltuwa daya lullubeta na ma'anar kalamanta, ba ta shirya ba, bata san ya zatayi idan suka rabu ba, amman ba zatayi ma kanta karya ba wannan karin, ba zata iya ba Hamza abinda yazo nema ba.


"Ni zaki hada da Allah Hindatu?"


Hamza ya tambaya yanajin tashi zuciyar na tafasa shima, duk abinda zaiyi a rayuwar shi bayaso yaji an hada shi da Allah, yana kokarin ganin zunuban shi tsakanin shi da Ubangiji ne, bai hada da hakkin mutane ba


"Me ma kike so kice mun? Bari na zakiyi?"


Ya karasa maganar muryar shi na wani irin sauka, kan shi naci gaba da sarawa, a karo na farko a tsayin lokaci a rayuwar shi da yaji tsoro ya dabai-baye shi da tunanin cewa zata bar shi.


"Ya kake so inyi? Ba zan iya ba, wallahi ba zan iya baka abinda ka zo nema ba"


Ta karasa maganar tana rufe fuskarta da hannuwanta saboda kukan da takeyi, baisan lokacin daya kama hannuwan yana rabasu da fuskarta ba, ya dumtse su cikin nata, kai yake girgiza mata


"Baki isa ba, wallahi baki isa ki rabani dake ba, Hindu baki isa kisa in fara sonki ba kibarni, ni ban tsara soyayya a rayuwata ba koda aure zanyi, saboda bana so in wahala, ba zaki barni ba, kina jina"


A hankali ta zame hannuwanta daga rikon da yayi mata, dan ya fara karya mata zuciya fiye da yanda take a karye. Mikewa tayi, ta goge fuskarta sosai tana tashi, dai-dai lokacin da aka kira sallar isha'i, muryarta a dishe tace


"Kaga an kira sallah"


Kai Hamza ya girgiza mata, shima yana mikewa


"Dan Allah ka barni, zuciyata ciwo takeyi, in ba kasheni zakayi ba yau, kabarni haka"


Numfashi ya sauke


"Karki barni to, kice ba zamu rabu ba"


Kai Hindu ta iya daga mishi, gida kawai take so ta shiga, ko zatayi kuka har sai zuciyarta ta rage mata ciwo


"Okay.... Koma menene karki barni, ina son ki"


Ya furta kalaman na sauka kunnuwan shi da tabbaci kan abinda yakeji a kanta. Kafin tayi wani abu taji ya riketa a kirjin shi, sosai wannan karin ta ture shi


"Kagani ko? Abinda kake so kenan bani ba"


Kai Hamza ya girgiza mata, ya riketa ne dan ya rage jin tsoron da yakeji, yau ko abinda take tunanin ma bayaji sam, tashin hankalin da yake ciki ya girmi wannan


"Nasan abinda nake so, kuma duka biyun ne"


Numfashi Hindu ta sauke, ta mika hannu taja kujerar daya tashi daga kai, ta dagota tana hadata da dayar. A wajen tabarsu tana wucewa ta shige gida, tsaye Hamza yayi a wajen, gabaki daya gwiwoyin shi sunyi sanyi. Dakyar ya iya zagayawa da nufin ya bude motar shi ya shiga, yaji an mishi sallama, juyowa yayi yana mika mishi hannu suka gaisa, ya gane hoton shi, Hindu tana yawan saka shi a status dinta, Zaid tace mishi, Yayanta ne, tace likita ne. Kare mishi kallo Zaid yakeyi, akwai inda ya taba ganin Hamzan, ya rasa ko ina ne, amman haka kawai yaji baiyi mishi ba.


"Idan kana son ta da gaske, ka turo ayi magana kafin ka sake zuwa"


Zaid ya fadi, ko bai tuna ina ya taba ganin Hamza ba, bayason irin su a kusa da kanwar shi, sam bayaso. Idan da wata niyya yazo Zaid nada tabbacin daga yau ba zai sake dawowa ba, hakan ma zaifi mishi, dan ko turowa yayi har unguwar su zaije da kan shi yayi bincike a kan shi, ba kullum yake yankewa mutane hukunci batare da yasan labarin su ba, amman kuma zuciyar shi kanyi gaskiya akan mutane da yawa, in har yaji kamar baka da hali me kyau sai hakan ya kasance gaskiya. Wucewa yayi kafin Hamzan yace wani abu, dan karma ya samu fuskar ganin wasa yake da shi.


Motar shi Hamza ya shiga, yau dai kowa so yake ya raba shi da Hindu, harda ita da kanta, kuma zai nuna musu basu isa ba, kamar yanda yace ne, yana son ta, da a rabashi da ita gara yayi abinda bai shirya ba, duk sai su sama mishi lafiya su daina kokarin ganin sun rabasu. Hanyar da zata kai shi Tudun Wada ya nufa, gara yayi magana da Appa.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 2


Hamza na daya daga cikin mutanen da ba karamin sha zaiwa giya kafin ta bugar dashi, yasan ba ita bace ta saka shi bacci, duk da ya kwankwada daren jiya saboda yanda ranshi yake a bace, dan haka da wani irin ciwon kai ya tashi, kan na shi ya kara sarawa saboda aman da yayi na giyar. Shisa baya so yasha ta da wannan yawan, ran shi a bala'in bace yake jin shi har lokacin. Dan bayan ciwon kan da yake har wani dumi yaji ya dauka na bacin rai, dan karamin kitchen din da turawa sukafi yiwa lakabi da kitchenette ya shiga, dan wajen girkine da zaka iya dafa abin kari ko wani abu dai marar nauyi.


Jikin shi sanye da gajeran wando, amman ya saka riga mai dogon hannu hadi da hula ya saki hular a bayan shi, ya riga yayi wani irin sabo da riguna masu dogon hannu, komin zafin da akeyi kuwa, sai yaji iska na shigar mishi hannuwa duk idan ya saka riga mai gajeran hannu, ko a gida baya zama da ita, da daddare ma ba kullum yake kwanciya da singlet ba, dan ma zai lullube jikin shi tunda da AC. Coffee ya hada ya zuba a kofin tangaran da yake rubuce da Arc Hamzy a jiki, da yake bayason zaki ko da can, ballantana da yasan illar da yake da ita a jikin dan adam idan yayi yawa, haka ya fito da Mug din a hannun shi.


Kurba yayi yana hadiye shi dakyar saboda zafi


"Oh shit..."


Ya furta yana furzo iska ta bakin shi, babu shiri ya koma kitchenette din ya dauko cokali ya saka a ciki yana jujjuyawa cikin son yadan sha iska ko yayane, kan mudubin dakin baccin ya ajiye kofin yana duba agogon dakin yaga karfe takwas da kusan kwata, yana da dan sauran lokaci, dan karfe tara zai fita, kuma yayi wanka. Wajen drawer din gado ya karasa yana zama tukunna ya janyo, paracetamol ya dauko ya balli guda biyu yana daukar robar ruwa da take ajiye a gefe ya jefa maganin a bakin shi tukunna yabi da ruwa. Ya sake mikewa ya dauko Mug din ya kurba yaji zafin ya mishi dai-dai. Bai dauki wani lokaci ba ya shanye yana zuwa ya wanke kofin tukunna ya mayar da shi inda ya dauka.


Gyara gadon yayi tsaf, dan a rayuwar shi bayason ganin waje a hargitse, bakuma ya son kazanta koya take. Ko wajen ajiye kayan shi ka bude a tsare yake sai abin ya burgeka, kowanne kalar kaya wajen su daban, boxers din shi da singlet kan su a tsari suke. Shisa ya tsani wani ya shigar mishi daki, idan akwai abinda yafi saurin bata mishi rai shine wani ya shigo mishi daki ya taba wani abin, dan koya akai kokarin mayar dashi yanda aka gani yana shigowa saiya gane. Saida ya gama tukunna ya taka wajen wardrobe din da take cike da bango daya na dakin saboda girmanta. Wani farin yadi ya dauko da babu aiki a jiki, sai maballan ne kawai da aka saka mishi blue, links ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login