Showing 75001 words to 78000 words out of 110313 words
Chapter 26 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt
ya koma ma mace sau biyu. Har iskanci Fodio yake mishi, cewar yana tsoron attachment. Kuma da gaskene, duk wani abu da zai takura shi baya kaunar shi. Abdallah ne ya kula ya kasa gajiya da yi musu nasiha akan mata shi da Fodio, AbdulHafiz ya dauki idanuwa ya saka musu yanzun.
Basa dai hirar a gaban shi ne, tun ranar da yayi musu hauka sosai yafi sati hudu ko waya bata hadasu ba, sai suke taka tsantsan da yanda suke hirar mata, daman shi da Fodio ne kadai. Kusan Hamza zaice yanda matan suke yawan kawo mishi kansu ne ya fara jan ra'ayin shi, tun yana ND kuma wasu cikin abokan karatun shi da suke kwana studio tare suka koya mishi fara shaye-shaye. Tun yana mamakin yanda bacci baya kamasu har suka sanar dashi wiwi ce, a indomie suke dafawa, ko su zuba a shayi, in zaka kwana idanka kyam, ga yanda yake jin kwakwalwar shi har wani kaifin tunani take karawa.
Sai kuma ya samu Fodio ma yana dan sha, duk da shisa ce abinda yafi bulbula ma cikin shi, Arafat ma na shan shisa. Hamza zuwa club ya fara koya mishi daga kwalba, sai kuma yaga kan shi na rike wuta, bata bugar da shi kamar yanda yake ganin tana yiwa sauran mutane. AbdulHafiz kan ce
'Kana cutar da kanka Hamza, akwai kuskuren da kakeyi a cikin sallarka, shisa bata hana maka aikata wannan abubuwan... Wallahi ka gyara kafin lokaci ya kure maka'
Nasihar kanbi ta kunnen shi na dama ta wuce a ta haggu ne, abinda yasani kawai shine komai yana da lokacin shi, idan lokacin barin yayi zai bari. Kuma azumin litinin da alhamis baya wuce shi sam, in ba rashin lafiya ba, safiyar yau saboda yasan zai zo gida, bai niyyar shan wani abu ba, amman hirar Hindu da wannan 'katon banzan' kamar yanda ya fadi ta saka shi kunna wiwi, hakan kuma yasa shi yin fada da AbdulHafiz da bayason jin warin ta, shisa bayason damuwa ko kadan, haka kawai daga ganin hoton yarinya kamar jaraba ta manne mishi a kai.
Shisa har wajen sha daya tukunna yayi wanka ya fito. Yanzun ma tsintar kanshi yayi da komawa Instagram, yana duba hotonta da yake na karshe da ta saka, dan yatsa yasa yana shafa kan fuskarta, na rana daya idan ya sameta ma yayi mishi, zai cireta daga kan shi kwata-kwata. Yana da wannan yakinin, sakkonni ya shiga yana ganin sunanta a sama alamar ta mishi magana
"Sai yanzun zakiyi mun magana?"
Ya fadi a fili kamar tana jin shi, tun da ya tashi yake dubawa, baisan me zaice mata ba, shi daya fara mata magana, kuma bai saba yima mace magana ba sam, bude sakonnin yayi yana shiga hotunan, badan abinda tayi din ba dai-dai bane a zanen, akwai dai gyara da yawa, kuma layikan basuyi mishi yanda yake so ba. Sallamarta ya amsa sannan ya ce
'Akwai gyara kam, bazan iya dogon typing ba. Zan kiraki'
Sai da ya tura yai tunanin bashi da lambarta balle ya kirata din, baima san dalilin da zaisa yace mata haka din ba, kawai zuciyar shi ce ta darsa mishi son jin muryarta, ko zatayi dai-dai da kalar fuskarta. Sauka zaiyi daga Instagram din yaga alamar tana rubutu
'Da gaske? Like da gaske zaka kirani?'
Kafin ya amsa yaga alamar ta sake cigaba da rubutun
'Kaifa zaka kirani, dan Allah karka ce mun wasa kake mun'
Dariya yayi mai sauti, yana fara rubutu
'Ki ajiye lambarki kafin in canza ra'ayina'
Bai taba ganin saurin rubutu kamar yanda ta turo lambar ba, kwafa yayi yana saving da Hindu. Sannan ya danna kira, ta daga yayi mata sallamar da ta amsa shi yana jin farin cikin da yake tattare da muryarta hadi da wani irin excitement da duk basu hana muryar sauka cikin kunnen shi da wani sauti na daban ba, bai tambayi ya take ba, ko ya makaranta, kawai abinda yake so ta gyara a jikin zanen ya fada mata, ko godiyarta bai jira ba ya kashe wayar shi, dan yana ganin kamar duk sakokin da yake kara magana da ita, da yanda take sake manne mishi a kai, da yanda zuciyar shi ke kara kwadaituwa da ita.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 21
Lokaci zuwa lokaci take dan juyawa tana kallon Hamza da yake tukin shi hankali a kwance, ko sau daya bai juyo ya kalleta ba tunda aka tashi daga dinner din da ta kawatu daga wajen shirin kujerun, ko hotunan da aka dinga yi musu sai dai yadan yi murmushi, wani ya rike hannunta, wani ya tsaya a bayanta. Da aka kira su filin ma, hannunta ya rike sukayi tsaye. Tasan daga shi har abokan shi suna da kudi, amman yau sun nuna mata kudin nan da suke dashi basa jin komai wajen liqasu. A cikinsu mutum dayane taga yana liqa dari bibbiyu ma. Amman daga dubu sai dari biyar, sosai sukayi ta ruwan kudi, duk da taron awa biyu akayi, daga takwas zuwa goma na dare.
Kalma ko guda daya bata hadata da Hamza ba, zuciyarta take jin tanayi mata rawa, ta dauka babu wani abu da zai shiga tsakaninta da farin cikinta a rana irin ta yau, ga dinner ta samu irin wadda take mafarki, dan tana da tabbacin zata tsinci hotunan su da Hamza a shafuka daban-daban na Instagram. Amman zuciyarta a jagule take, duk da tabbacin daya bata na cewa babu abinda tayi mishi, kowaye yai mishi wani abu yau bai kyauta mata ba sam, kuma bai mata adalci ba. Duk da fiye da rabin hankalinta akan Hamza yake, tana kula da hanyar da suke komawa bata nan suka biyo ba wajen zuwa. Kanta ta jingina da kujerar motar tana sauke wani irin numfashi mai nauyin gaske.
Idanuwanta na kafe kan titi, amman hankalinta yana can wata duniya da take bakuwa a wajenta, jin Hamza yayi parking yasa ta dago kai tana kallon shi, kafin ta kalli inda yayi parking din, Barcode Lounge, sai take ganin kamar a Barnawa suke, amman batajin ko hanya ta taba biyowa da ita ta wajen. Da matukar mamakin dalilin tsayawar su ta juya ta kalli Hamza da yake tattare babbar rigar jikin shi, kafin ya dan daga yana zarota daga jikin shi ya cireta gabaki daya, duqunquneta yayi yana jefawa bayan motar. Kafin ya fara dube-dube jikin gaban motar yana bude wani waje ya zaro ATM. Ficewa yayi daga motar, baice mata komai ba.
Ya kusan mintina sha biyar, dan tanayi tana duba wayarta data karba bayan sun fito daga wajen dinner din, tana jin Dimples nayiwa su Fodio mita
"Me kuke nufi wai? Yanzun kudin siyan bakin ne ba kwaso ku fitar shine kuke so a rabu tun nan?"
Ta kuma ji AbdulHafiz na fadin
"Dan kudin siyan baki, ku fadi ko nawane ni in biya. Amman ku taimaka mun, dare nayi..."
Da alama sauri yakeyi tunda da matar shi yazo, yanda take nunawa kuwa a takure take, duk da idanuwanta kawai ake iya gani saboda face mask din daya rufe fiye da rabin fuskarta. Tayi wani irin kyau cikin alkyabbar ta silver. Dan juyawa baya tayi jin Hamza ya bude murfin motar wajen yana saka wani abu da duhun cikin motar bai bari taga ko menene ba, amman kamar lemuka da alama, tunda harda kiret taji alamar kacafniyar kwalabe. Juyawa ta sakeyi tana gyara zamanta, harya gama saka abubuwan da zai saka ya zagayo ya shigo, yana tayar da motar suka bar wajen.
Waje biyu suka kara tsaya, tukunna suka karasa gida, sai lokacin Hindu ta samu ta karema gidan kallo daga waje, yayi mata kyau har saida murmushi ya kwace mata duk da damuwar da take ciki. Da kanta ta bude murfin motar tana fitowa, ganin Hamza nata sauko da kaya, yasata mika hannun dan takarbi ledojin da ya tattaro
"Kibar shi zan shigo da shi"
Yayi maganar da wani irin yanayi a muryar shi
"Kayan da yawa, ka kawo in tayaka"
Mika mata ledojin yayi, saboda bayason doguwar magana, bayama son yin magana gabaki daya, ji yake kamar zai kurma ihu ko zai samu saukin takurar da yakeji rayuwar shi tayi. Idan har zai samu ya daure zuciyar shi ya kwana a gidan nan yau batare daya fito ya koma gidan Fodio ba, to yana bukatar ya sha wani abu. Yasan bashi da komai a cikin gidan, shisa ya biya ta Barcode ya siyo kalaluwan giyar daya kan sha. A hankali ya dinga dauka yana shiga dasu gidan, baiga inda Hindu tayi ba, shi dai sama ya haura yana kai kayan part din da nashi ne, dan har furnitures da komai ya zuba. Har kayan sawar shi ya dibo wasu ya kawo nan gidan.
Fridge din bangaren ya shirya komai yana cika shi taf, tunda harda coke ya siyo. Saida ya gama sannan ya balle links din rigar shi yana cire shaddar, daga shi sai singlet a jikin shi yaji kamar ana murda hannun kofar dakin da yake ciki, runtsa idanuwan shi yayi yana bude su a hankali hadi da juyawa, Hindu yagani data bude kofar tana tsayawa a bakin kofar, rigar da suka dawo da itace a jikinta, amman ta cire mayafin, sai dankwali. Bayason yanda take kallon shi idanuwanta cike da maikon hawaye.
Ita kuma tunda ta shigo, saita wuce dakin da aka fara ajiyeta nan kasa, ledojin ma duk a dakin ta ajiye, wayarta da jakarta ta jefa su akan gado, ta kwance mayafin daga wajen da yake maqale a kafadunta tana ajiye shi, ta zame takalman kafafunta, ta karasa ta zauna gefen gadon, wani irin shiru daya gauraye gidan ya saukar mata da kadaici na ban mamaki, ga kuma bakunta da zullumin sabuwar rayuwa duk suka hadar mata. Haka kawai taji idanuwanta sun cika da hawaye, suna zubo mata, musamman da taga Hamza yaki shigowa, sosai hawaye ke zubar mata, wani na ture wani, ba haka ta hango daren farkon ta ba sam.
Wani irin tsoro taji ya tsirga mata da batasan daga inda ya taso ba yana sakata mikewa babu shiri, waje ta fara lekawa ko takalma bata saka ba, sai dai ta hango motar Hamza inda ya ajiyeta, ko ina a rufe kuma, babu kowa, ko maigadi bata iya hangowa daga inda take, sai tarin shuke-shuken da suke a tsare. Dawowa tayi tana fara bin dakunan gidan na nan kasa gabaki daya tana neman Hamza, har kitchen sai da ta shiga. Tana dubawa, hawaye na sake zubo mata, dan batasan koya fita yabarta ita kadai a wannan tanqamemen gidan ba. Da kuwa bai kyauta mata ba
"Kar kaimun haka, dan Allah Hamza"
Ta tsinci kanta da furtawa, wasu hawayen na sake zubo mata, tuntuni ta yanke shawarar kiran shi da sunan shi, saboda duk wani suna da tayi tunani, taga tarin yan mata sun kira shi dashi, bataso kuma ta zama kamar su, ko sunan shi a wayarta sai daga baya ta sake zuwa 'Hilwatee'. Shima din shiya taba kiranta da hakan, ta tambaye shi ma'anar yace mata 'My sweet' da yaren Annar shi. Da yake saitama jima ko sunan nashi bata kira ba. Ganin duk ta duba dakunan kasan baya nan, ta yanke hukuncin hawa sama, shima daki biyu ta bude tana leqawa, kafin ta shiga wani dan lungu daya sadata da falon da bai kai na kasan girma ba, a hankali take kawa harta sake yin wani dan lungun tana ganin kofa, murzawa tayi ta tura a hankali.
Ta kuwa sauke idanuwanta kan Hamza da yake tsaye daga shi sai singlet da gajeran wando, saurin sadda kanta kasa tayi, tana kai hannu ta share kwallar da ta taru a gefen idanuwanta, kafin ta sake dagowa ta kalle shi, tana kokarin tsayar da idanuwanta a iya fuskar shi, muryarta na rawa tace
"Ban ganka ba, inata duba ka"
Idanuwan shi Hamza yadan murza, yanayin da karara yake nuna mata yanda shigowarta dakin ta takura shi, tana jin wani abu ya bude a cikin kirjinta da ba zatace ko menene ba, amman ciwon shi yasa idanuwanta sake cikowa da hawaye
"Wanka zanyi Hindu, dan Allah a gajiye nake, kije ki watsa ruwa kema. Zan zo idan na fito"
Wannan karin batayi kokarin tsayar da hawayen nata ba, barin su tayi suka zubo yagani, yana jin kan shi ya kara nauyi da kukan da tayi tsaye tana mishi kamar yai mata wani abu, ko kwana basuyi ba karkashin inuwa daya, amman a wuyan shi yake jinta ta tokare, ko iskar kirki baya iya shaka sam.
"Na tambayeka ko nayi maka wani abu, tun dazun, duk yau kanata bani attitude, idan ma bayau ba, ko wani lokaci a baya nayi maka wani abin daka rike a ranka ka zabi kabari sai yau ka horani, ka dubi girman Allah ka fadamun sai in baka hakuri....amman... Am..."
Hindu ta kasa karasa maganar saboda kukan daya kwace mata, bata baro gidansu tazo nashi dan ya dinga yi mata wannan abin ko kwana batayi ba, amare nawa ne ta karanta, ta kuma ji labarin yanda angwayen ke lallabasu a dare irin nayau, suna lallashin su yayin da suke kukan rabuwa da gida, amman yanzun ita gata a tsaye nata hawayen na zuba akan wani dalili daban, amman ko motsi Hamza baiyi ba, ballantana ya nuna alamar zai karaso inda take ya lallasheta. Kallonta kawai yakeyi, inda zai iya shima kukan zaiyi saboda abinda yake ji, kawai so ta tafi ya dan jishi shi kadai na wani lokaci.
Amman taqi tafiya, neman dalili takeyi bayan ya gaya mata babu, maganar da bayason yi take so ta saka shi dole-dole saboda rashin son zaman lafiya
"Karya kike so inyi miki? Nace miki bake bace ba, dan girman Allah ki kyaleni inji da abinda yake damuna mana, haba dan Allah"
Hamza yake fadi yanajin idan ya karasa inda take, turata waje zaiyi ya rufe kofar, bayason haka ta faru, bayason yin abinda su duka bazai musu dadi ba, tunda har ranshi yake jin babu abinda tayi mishi, abinda yakeji bashi da alaka da ita, yanzun ne take so ta hada mishi abinda yakeji da ciwon kanta, su zame mishi biyu
"Me yasa dan Allah Hindu na zaki kyaleni in shaki iska ni kadai ba?"
Hannu takai tana share hawayenta da kamar taba wasu hanyar zubowa ne, ta bude bakinta tana shakar iska, dan wadda take zarya ta hancinta da wani irin zafi take jin shigarta, ga kirjinta abinda ya bude dazun takeji yana kara budewa, batasan wanne laifi ta aikata mai girma haka da ta cancanci wannan abin ya faru da ita a darenta na farko ba.
"Wow..."
Ta furta tana sake kai hannu ta goge fuskarta. Kafin ta juya, ko kofar bata rufe mishi ba, tana da tabbacin tsoron da takeji bazai mata komai ba, amman yanayin Hamza da maganganun da yake fada mata na barazana da numfashinta, kafar benen bibbiyu take hadawa wajen sauka, da gudu ta koma dakin da ta fito, tana doko kofar, jikinta ko ina bari yakeyi, dankwalin kanta ta fisge tana jefa shi kasa, kafin ta fara kiciniya tana samu ta zuge zif din rigarta, ta zameta tana tsallaketa a wajen, bandaki ta shiga, da sauran kayan da suke jikinta ta bude ma kanta shawa din da ko a film bata taba ganin irin ta ba, ruwan yadan fara zubo mata, tana fita babu shiri jin ruwan zafi ne sosai, anan bandakin ta tsugunna, tana kokawa da numfashinta.
Kuka takeyi kamar ranta zai fita, kafin ta samu dakyar ta mike, dubawa tayi sosai tana samu ta dai-daita zafin ruwan ta watsa. Ta cire sauran kayan tabarsu anan bandakin, tana dauro towel ta fito. Tanajin yanda fuskarta ta kumbura har idanuwanta, dakin sake kayan data gani dazun ta shiga, ta kuwa samu kayanta a shirye a cikin wardrobes din, na cikin ta fara sakawa, ta tsaya tunani kafin ta sami wata rigar bacci mai yanayi da kimono ta saka a jikinta tana daure madaurin akan cikinta, duddubawa tayi ta samu wata farar hula, sai da ta saka towel din ta goge kanta, tana jin dadin shawarar Aina'u data dauka, tayi kitso. Sannan ta saka hular, saboda yasa tadan turata baya, dakin ta fito ta karasa kan gadon ta kwanta daga can karshe.
Kanta kamar zai bude saboda ciwon da yakeyi, ga cikinta ya daure waje daya saboda rashin abinci. Tunda ba wani abin kirki bane a ciki, banda ajiyar zuciya babu abinda take saukewa, zuciyarta kanta tayi wata irin natsuwa a cikin kirjinta, su dukansu biyun a gajiye suke da rayuwa gabaki dayanta.
*
Kwalbar hannun shi ya daga yana sake kafawa a bakin shi, sai da yaji baya iya numfashin kirki tukunna ya sauke kwalbar, a zaune yake dirshen kasa kan kafet, tunda Hindu ta fita daga dakin, yafi mintina goma a tsaye. Yasan wanka ya kamata yayi, amman kanshi ya cunkushe, gabaki daya lissafin shi ya kwance. Ya kasa tsayar da tunanin shi waje daya sam, shisa ya dauko abu daya dayake da tabbacin zai batar mishi da komai, kwalbar ya ajiye yana dafa gado ya mike, ji yayi lum, kan shi yayi wani irin juyawa, wasu taurari na giftawa ta cikin idanuwan shi. Dakyar ya samu ya dai-daita tsayuwar shi, kafin ya fara takawa yana dan tangadi ya fita daga dakin.
Baisan ya bugu ba saida ya fara gwada taka benen yaga yana rabe mishi biyu, kama karfen gefe yayi, amman ya gwada faduwa Allah na tsayar dashi yafi sau biyar, kafin ya samu ya karasa sauke, komai bibbiyu yake ganin shi, saiya runtsa idanuwan shi ya sake budewa yake dan ganin dai-dai. Dakin da Hindu take ya karasa yana tura kofar, ya hangota a kwance, bata koyi motsi ba, ballantana ta dago, dakyar ya karasa cikin dakin sosai, ya kuwa yi tuntube da ledojin da suke ajiye da sam bai kula dasu ba, kafin jiri ya dibe shi yana katantanwa cikin dakin, karar faduwar shi Hindu taji saboda hankalinta sam baya tare da ita.
A firgice da wani irin matsanancin tsoro ta mike gabaki daya, tana sauke idanuwanta kan Hamza cikin tashin hankali, tana kallon yanda yake kokarin tashi, dakyar ya mike zaune, tsaye yake so ya tashi amman saiya kara zamewa ya koma ya zauna, da wani irin tashin hankali da bata taba sanin akwai shiba a duniya take kallon Hamza, kafin ta sauke daga kan gadon tana jinta