Showing 51001 words to 54000 words out of 110313 words
Chapter 18 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt
taba ganin namiji ya karbarma mace jaka, ko a tarin burinta bata tsawwala da abinda ake kira 'Public affection' ba, wato nuna kulawa ko kauna a bainar jama'a. Saboda abune da bai saba faruwa a Najeriya ba, duk kuwa kalar kaunar da take tsakanin masoya, ta hasaso faruwar abu irin haka idan suna kasar waje lokacin honeymoon dinsu, inda zasu barji soyayyar su batare da fargabar sa idon al'ummar Najeriya ba. Jerewa sukayi har cikin wajen, Hindu najinta kamar wata Sarauniya, musamman yanda Hamza yake janta da hira kadan-kadan suna murmushi.
Sai ta hango hannunta sakale cikin nata, ta hango yara biyu, daya a gefen shi daya a gefenta, a lokaci daya tana hasosu yanda rayuwar auren su zata kasance, kafin taji muryar Dimples na katse ta da
'Sannu Hindatu Khan Bachaan'
Kamar yanda takan fada mata idan tana wani zancen soyayyar, ko tana fadar abinda zasuyi ita da mijinta. Dimples kance indiyawa sune karshe dai a soyayya. Kuma Hindu batajin hakan, dan Korea sun shallake indiyawa ta wannan fannin, nesa ba kusa ba, amman gaddama da Dimples babu riba, shisa bata taba kwatantawa ba. Ko da zasu zauna ma, Hamza da kanshi yadan janyo mata kujera bayan ya ajiye jakarta akan tebir din da yake gabansu, yana zama ya kama bayan kujerar yadan tura, sannan yaja tashi ya zauna yana fuskantarta kamar bai lalata mata duk wata fita da zatayi da wani namiji da bashi ba har karshen rayuwarta. Dan sosai zata dinga auna duk wani abu da zai faru da wanda ya faru a tsakanin su.
Hamza take kallo da har lokacin yaki nuna alamun yayi mata wani abu, asalima yanda yake nunawa kamar abinda ya faru ba bako bane a wajen shi, kamar abune da yakeyi yau da kullum, ga restaurant din ya kawatar da ita. Waiters din gurin tsaf-tsaf dasu, daya daga ciki yazo yana kawo musu Menu, amman sam Hindu ta rasa abinda zata ce a kawo mata, dan bama taji yunwa kwata-kwata, hakan yasa ta yanke hukuncin zabar hadin salad. Sai a zabin abin sha ta dauki cocktail. Gira Hamza ya daga mata da yasata dauka hakan sabon shine, dan yayi yafi a kirga daga haduwarsu zuwa yanzun
"Me kike nufi? Iya abinda zakici kenan?"
Kai Hindu ta jinjina mishi tana dorawa da
"Banajin yunwa"
Yanda ya tsareta da idanuwa yasata dan shagwabe mishi fuska
"Da gaske"
Kai ya girgiza mata
"Ba zaki kalleni ina cin abinci ba aikam"
Da kanshi ya kara cewa a hado mata da kaza sai spaghetti. Sannan ya zabi nashi shima, waiter din na tafiya dan ya kawo musu abubuwan da suka zaba din, gyara zama Hamza yayi
"Is not fair kina ganin gabaki daya fuskata ni bana ganin taki"
Murmushi Hindu tayi a kunyace, kafin tayi wani yunkuri Hamza ya mika hannun shi ya kama tabarau din fuskarta ya zare, yana sauke idanuwan shi cikin nata da suka firfito da alamar tsoro, tana tabbatar mishi da zaton da yakeyi a kanta. Ita din ba kamar sauran matan bace ba, Hindu dabance da duk wasu mata da ya taba cin karo da su, kan tebir din a kusa da ita ya ajiye gilashin yana fadin
"Hakan yafi"
Yasa ta sauke idanuwanta daga cikin nashi, wayarta taji tayi vibrating alamar shigowar sako, hakan yasa ta daukar jakarta tana ciro wayar. Bude sakon tayi ta whatsapp tana ganin a class group dinsune wani ya turo zanen da yakeyi dan a duba mishi ko da kuskure. Hamza ita yake kallo, bai saba yana zaune da mace hankalinta na wani waje banda kan shi ba, bama yaso kwata-kwata
"Baki san ba kyau kina tare da mutum ki dinga danna waya ba?"
Cike da sabon mamakin shi Hindu ta raba idanuwanta da wayar tana kallon shi
"Ko waye ya jira sai bama tare, karya shigar mun lokacina dake, bana so..."
Ya karashe maganar cike da ikon da kyawun da yai mata bai hanata ganin karfin halin shi ba, data dinta ta kashe tana mayar da wayar a jaka
"Nagode"
Hamza ya fadi yana sata cewa
"Kana da rigima"
Dan daga mata kafadu yayi
"Nasani, kawai bai dameni bane tunda rigimar nasani samun abinda nake so"
Siririyar dariya tayi, ko a littatafai kuwa bata tunanin ta taba ganin kalar shi, tunda yawancin mazan novel basa magana, ita ya kamata ace tanata mishi surutun da tasan ba zata iya ba, amman shi yake ta mata magana bai damu ba, ta dauka tana son namiji shiru-shiru sai yanzun da Hamza yake zaune a gabanta. Abincin su da ya saukane ya ceceta, dan batasan amsar daya kamata taba Hamza ba. Kallon abincin takeyi tana ganin kamar daga Instagram aka ciro shi aka ajiye a gabansu saboda yanda ya qawatu.
Robar ruwa Hindu ta bude tana dan kurba saboda yanda taji makoshinta ya bushe. Tana kallon Hamza ya fara cin abincin shi a nutse kamar bashi da wani abu mai muhimmanci daya wuce cin abincin, itama salad din ta faraci kadan, tana jin yanda yake dira cikinta da wani irin yanayi. Hamza na kallonta ta kasan idanuwan shi, sai dai baya surutu idan yanacin abinci, bama yaso wani yai mishi wata magana, yasan bai isa ya zabi hanyar da zai mutu ba, yana dai kokarin kaucema faruwar hakan ta hanyar shaqewa da abinci. Shi bai ga dalilin da zaisa a dinga magana ba idan anacin abinci.
Ita kuma ta saba tana cin abinci tana danna waya, yanzun sai shirun yai mata wani iri, tana ganin kamar hankalin Hamza na kanta, lokaci zuwa lokaci take dago idanuwa ta kalle shi, amman sai taga abincin shi yakeci a nutse. Dakyar taci rabin salad din da yake gabanta, dan kar yace yasa an kawo mata abinci bataci ba, shisa tadan dibi taliyar tasa a bakinta, ta kuma yi mata dadi, ba zata iyaci bane ba kawai. Kazar ma kadan ta gutsira, ta ajiye cokulan tana ci gaba da kurbar lemon gabanta. Har Hamza ya gama dan kadan ya rage a tarkacen abubuwan a aka kawo mishi, wasu ma bata taba ganin su ba balle tasan sunayen su.
Masu kudi na sha'ani da rayuwar su, ta fadi a ranta
"Karki ce mun kin koshi"
Hamza ya bukata, kai tadan daga mishi tana murmushi
"Hmm..."
Ya furta yana dorawa da
"Kin kyauta"
Ya dauki wani dan kati da take tunanin kudinsune a rubuce ya duba, hannu taga yakai aljihun shi yana fito da wallet din shi, sai dai tayi mamakin yan dubu-dubun da taga yana kirgawa yakai na dubu goma sha, ya bude dan katin ya saka a ciki, sannan yadan kalleta
"Muje?"
Ta bukata, ya jinjina mata kai, a tare suka mike, Hindu na daukar jakarta, da tabarau ta makala a fuskarta,har lokacin tana mamakin yawan kudin da kuma dan abinda sukaci. Suna shiga motar yaga wayar shi na ta haske, dauka yayi ya duba
"Dammn"
Ya furta yana mayarwa ya ajiye. Yaga Hindu bata wani ci abin kirki ba, yaso su biya ko Havilah ne. Yasan mata bakowa kecin abinci irin haka ba, sunfi jin dadin ci a gida, amman Murjanatu, Autar su tasa yasan mata akwai san kayan zaki, duk da shi baya ta'ammali da kayan zaki, amman tana son desserts sosai
"Wajen aikine..."
Yai maganar kamar yayi mata wani laifi yana dorawa da
"Nayi alkawari I will make it up to you, In shaa Allah, zamu kara samun time da aikina ba zai shigar mana ba, kina jina?"
Kai Hindu ta daga mishi tana murmushi
"Karka damu, babu komai"
Wani numfashi ya sauke yana fadin
"Nagode"
Kafin yaja motar, yanzun ma hirar sukeyi, yana bata labarai kananu da suka shafi aikin shi, yana sa tana karajin dadin kasancewa da tayi tana karantar Architecture saboda yanda take fahimtar hirar tashi. Inda ya dauketa suka karasa yasa shi cewa
"Ina zamu bi?"
Tun kafin ya karasa Hindu take girgiza mishi kai, bugun zuciyar data samu ya tafi ya dawo mata sabo, ta ina Hamza zai fara shiga lungun gidan su da ita, idan wani daga cikin gidan ya fito yaganta ta ina zata fara musu bayanin dalilin da yasa take cikin motar shi
"Karka damu, ka saukeni anan"
Kallonta yayi da yake fassara 'kice mun wasa kike'
Ganin bata da shirin ce mishi wasan takeyi yasa shi fadin
"Saboda me?"
Hadiye yawu tayi tana sauke numfashi, ta rasa abinda zatace mishi
"Kayi hakuri kai dai, kabarni zan karasa, kaga kaima ana jiran ka"
Badan yaso ba, ba kuma dan da gasken ana jiran shi ba, amman baiji dadin yanda zai ajiyeta a bakin hanya ba
"Zamuyi waya. Ki kula da kanki"
Ya karasa maganar yana dan sauka gefen titi dan suyi sallama da kyau, kai Hindu take jinjina mishi
"Nagode sosai"
Hannun shi ya mika mata, sai dai wannan karin sauka zatayi balle tayi tunanin jakarta zata bashi, ga idanuwan shi daya kafeta dasu, haka kawai yaji idan bai rike ko da hannunta bane komai zai iya faruwa, yanayinta da komai nata yasa wasu kusoshi kwancewa cikin kan shi, ganin kallon da take mishi yasa kama hannunta, yana share yanda take kallon shi kamar shine karo na farko da wani namiji ya taba rike mata hannu, dan matsa yatsunta da yaji cikin nashi yayi. Ko ba nata ba yana son yanda hannuwan mata suke, sirara, yana son jin yatsun mace a cikin na shi, balle nata da haka kawai yake ji kamar an halicci nata yatsun ne don ya rike.
Tunda take a tunaninta tasha hango lahira, amman bata taba hangota wani sashi na jikinta a wuta ba, tana neman tsari daga wuta sau bakwai da safe, bakwai da dare a rana, idan tadan kone ko yayane takan yini tana neman tsari daga azabar wutar da batasan zata iya ba, amman yanzun kam har kaurin konewar da hannunta zaiyi a wuta takeji a hancinta, ta hango shi gashi can an kama an tsoma yana babbakewa, ta kuma rasa abinda ya daskarar da ita ya hanata yin wani yunkuri wajen hana Hamza rikewa, da ya murza yatsunta har ranta taji girman zunubin.
Tana kallon shi ya kama hannun nata yana saka labban shi cikin tsakiyar tafin hannunta ya sumbata, muryar shi can kasan makoshi ya furta
"Sai munyi magana"
Hadi da sakin hannun nata kamar komai bai faru ba, kamar bai manni zunubai a labban shi ba, dakyar ta iya daga mishi kai tana bude motar ta fice. Hanya ta mike, lungun da zai kaita gida tana ta kokarin ganin hannun da Hamza ya sumbata bai taba ko ina na jikinta ba, karta goga tarin zunubin da taji yasa hannun yayi wani irin nauyi na ban mamaki
"Allah ka yafe mun... Oh Allah na... Me ya faru haka"
Take fadi ita kadai kamar sabon kamu, a gefe daya na zuciyarta tana jin inda Hamza ya samu sabon waje ya manne.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 26
Duniyar tayi mishi tsaye waje daya, kallo daya zakai mishi kasan baya cikin kwanciyar hankali, damuwar da take tare da zuciyar shi shimfide take kan fuskar shi
"Me yake damun ka?"
AbdulHafiz ya tambaye shi, kai kawai ya iya girgiza mishi yana fadin
"Babu komai"
Ya kuma ji dadin yanda bai matsa mishi da tambaya ba, saboda bashi da wata amsa tsayayya da zai iya baiwa AbdulHafiz din. A watanni biyun nan cikin Hindu ba karamin wahala yake bata ba, bata kwana biyu ba'a kara mata ruwa ba. Gara cikin satin nan yaga ta fara warware wa, watannin nan sune masu tsayi a rayuwar shi tunda ya mallaki hankalin shi da yayi su batare da mace ba. Shisa a satin nan har cikin idanuwan Hindu yake ganin yanda ko kusa da ita ya zauna a tsorace take da shi. Wuni yake bulbulawa cikin shi giyar da yakejin tana dakushe mishi abinda yake ji.
Abu daya Hindu ta kula da shi yanzun, in har yana gida, yana manne da wayar shi, ita kanta ba dadin take ji ba, sati daya kenan da take samu taci abinci ya zauna, duk tayi wata irin rama. Duk abin Anty sai da suka zo suka duba ta, Baba kuwa zuwan shi hudu, duk idan ya dawo aiki yakan biyo ya dubata, duk da sau daya ta samu ya shigo cikin gidan harya zauna ya sha ruwa. Sauran a tsaitsaye suke gaisawa, ya bata tarin siyayyar kayan ciye-ciyen da take lodawa a fridge, wanda zasu lalace ta baiwa mai aikinta, tunda ita ba iyaci takeyi ba.
Yau ta rasa abinda zatayi, da Dimples tace zata shigo ta saka mata films, saboda zataje gidan su Biebee da bikinta sauran satika uku, suna kan hidimar da ake ta faman yi babu Hindun saboda laulayin da take fama da shi, ta kuma kira cewar ba zata sami shigowa ba, dan wajen aiki basu barta tashi da wuri kamar yanda tayi tsammani ba. Tata wayar ta dauka, yanzun ta zama yar kallo a twitter saboda bakin kishi irin na Hamza, da tayi tweet ma idan yahau yaga maza sun yi magana baya ce mata komai, sai dai ta nemi tweet din ta rasa, ya goge.
Tasan duk inda yake yana gab da dawowa yanzun tunda har anyi sallar magriba. A nan inda ta idar da tata sallar take zaune tana danna wayar. Fita tayi daga nata account din tana shiga na Hamza da taga tarin Notification, ga kuma sakonni da yawa ta DM. Shiga tayi duk yanda zuciyarta take fada mata karta yi hakan, karta jama kanta abinda zai daga mata hankali, amman kuma wani bangare na zuciyar yana fada mata ta duba, tasan Mansy na nan tana bi mata miji, tana kuwa shiga, sakon farko nata ne
"Shegiya mai tallar taba"
Ta furta a fili, wani tuquqin bakin ciki na danne ta, shiga tayi tana ja ta koma daga farkon hirar da tayi mishi magana, tana duba lokaci, jiyane ma, karfe biyu na dare, saboda ita batasan darajar 'ya mace ba. Karfe biyu zata fara yi mata magana da miji, amsar Hamzan tagani, farko hira ce sukeyi mai tsafta, kafin Mansy din ta fara mishi wata magana da ta canza gabaki daya akalar hirar tasu, jikin Hindu babu inda baya bari saboda munin abinda ta kasa daina karantawa
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"
Ta furta ganin yanda Mansy take cewa Hamzan ya duba whatsapp din shi ta tura mishi hotunan da video din da ko ita da yake mijinta batajin zata taba iya tura mishi su, ko dan tsoron kar wayar tashi ta fadi, ko a sace da irin wannan abubuwan a ciki da ya kamata ace idanuwan shine kawai zasu gani. Kife wayar tayi, ko ina jikinta bari yake saboda tashin hankali. Ga hawayen da suke cike da idanuwanta sunma ki zubowa saboda zafin da zuciyarta takeyi, daukar wayar tayi tana fara rubutu
"Dan uban babanki duk hotunan da kika tura mishi suna wayata, da screenshot din wannan hirar gabaki daya. Idan bakiyi blocking din shi, kin daina mishi magana ba sainayi posting hirar nan da duka hotunan har da videos din a TL kowa yaga karuwancin da kike bin mazan mutane kina yi. Wawiya, jaka, ballagaza da batasan inda yake mata ciwo ba, tsohuwar banza kawai"
Sai taji zuciyarta tayi mata dan sanyi, da ace zata ga Mansy din ido da ido ta kamata ta jibga kamar ganga sai tafi hucewa, sau biyu tana sake sallar isha'i saboda ta farkon bata da tabbacin ga abinda ta karanta a ciki saboda tashin hankali, tana sallar tana kukan wannan jarabtar da take ciki, batasan ranar da Hamza zai bar zuciyarta ta samu hutun kirki ba. Ta dauka yanzun cikin jikinta yasa shi ya nutsu, duk tunanin da takeyi ya daina shan koma meye taga yasha a daren ta na farko a gidan, saboda bata kara ganin shi cikin maye irin wannan ba. Addu'ar da ta duqufa tana mishi ta karbu ta wannan fannin.
Duk da ta fara dora laifin wannan abin da taga sunyi da Mansy a kanta, watakila da ace bata nuna mishi gazawarta a satin nan bayan hakurin da yayi da ita na watanni biyu ba da bai komawa Mansy ba, da abinda ya faru bai faru ba. Tana sallame sallama sallah yana bankado dakin kamar zai karya kofar hadi da fadin
"Hindu!"
Yana hanyar dawowa, kan shi yayi bala'in nauyi saboda abinda yasha mai karfine, kuma babu wani abincin kirki a cikin shi, so yake yana shigowa gida ya watsa ruwa ya kwanta tunda yayi isha'i. Ya kusa gidan ma yaga kiran Mansy, harya yanke bai daga ba, sake kira tayi bai daga ba. Ganin tayi mishi kira na ukku yasa shi dagawa, dan ya tabbata akwai dalili me karfi da yasa take kiran shi, kukan da yaji tanayi ne yasa shi sauka daga titi yana yin parking gefe, yanda kan shi yayi nauyi ba zai samu nutsuwar yin tuqi da amsa wayar a lokaci daya ba
"Ki natsu kimun magana Mansy, bana gane me kike fadi, me ya faru? Me akai miki?"
Ya karasa tambayar da fulatanci, itama da shi take mishi magana
"Matar ka, matar ka taga hirar mu jiya, ka duba whatsapp kaga me tace mun. Hamzy ka rufamun asiri ka bata hakuri karta doramun hotuna a tl, in dai kaine na hakura wallahi..."
Cike da rashin fahimtar abinda take fadi yace
"Bangane ba..."
Amman kuka takeyi sosai, abinda bai taba gani ko jin tayi ba tunda yasan ta da shi
"Kai kasan a duniya kai kadai kake da wannan hotunan, ko na taba kasadar turawa duk iskancina saboda na yarda da kai. Wallahi ba zan yafe maka ba idan suka bazu, kayi mata magana"
Mansy ta karasa cike da kashedi tana kashe wayar, hakan yasa shi duba whatsapp din shi ko zai fahimci abinda take fadin, screenshot ne na sakon da Hindu ta tura mata
"What the fuck!"
Ya furta a harzuqe yana sauka daga whatsapp din ya kira lambar Mansy
"Bata da hotunanki ko daya, chats dinne kawai da ta gani. Ki kwantar da hankalin ki babu abinda zai faru"
Yana jin ajiyar zuciyar da take saukewa
"Dan Allah Hamza..."
Kai yake girgizawa
"Na fada miki karki damu, babu abinda zai faru, akwai dalilin da yasa kika yarda dani tun daga farko, ki sake yarda da nace miki babu abinda zai faru"
Ya fadi, kafin tace wani abu ya kashe wayar, Allah ne kawai ya karasa kawo shi gidan lafiya saboda yanda yake fisgar motar. Bai aiki Hindu duba mishi chats ba, baiga dalilin da zaisa tayi abinda tayi ba, saboda bata da wata alaqa da Mansy, da shi take da, shikuma shine yake da alaqa da Mansy, shi ya kamata ta zaga ba ita ba. Idan mutuncin shi yake bukatar