Showing 78001 words to 81000 words out of 110313 words

Chapter 27 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt

kamar a gajimare take yawo, itama jirin taji yana neman kwasarta, saita tsugunna tana rarrafawa ta karasa inda Hamza yake, kafin tayi wani abu harya riko hannunta


"Bakiyi mun komai ba, ina so in zauna ni kadai ne.... Hindu ki taimaka mun, ya zanyi in kwance sarkar da ta daure ni? Ya zanyi? Bana so, ban shiryaa ba, wallahi ban shiryaa ba, ki taimaka mun"


Idanuwanta cike suke taf da hawaye, hannunta dayake rike dashi ta dago tare da nashi, tana dumtsawa a cikin nata, ganin a buge yake, kamar baima san me yake ce mata ba


"Hamza....me ka sha? Me kake sha? Kar kayimun haka, dan Allah ka rufamun asiri, ka rufamun asiri"


Take fadi, wani irin gunjun kuka na kwance mata, tana saka shi zame hannunshi daga cikin nata, ya kama fuskarta yana fadin


"Shhhhh.... Ban sha da yawa ba, ban sha da yawa ba, ban sha da yawa ba"


Yake fadi yana kara maimaitawa, amman ta kasa yin shirun, batasan yanda zata fara yin shiru ba a wannan halin, so takeyi idan yau mafarkine ta farka, dan zuciyarta zata tarwatse, tasan yana neman mata, wannan abune da take da yakinin zata iya canza shi a kai, saboda tana da abinda zata bashi, amman wannan, wannan abin da take gani batasan yanda zata fara ba, yarda da abinda yake gabanta ma na mata barazana, balle tasan yanda zatayi da shi, ga wani irin wari da batasan meye ba daya cika mata hanci yana kara dagula mata lissafi.


"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"


Ta furta tana dora hannayenta kan na Hamza da yake fuskarta, wani sabon kukan na kwace mata, kafin taga ya lumshe idanuwan shi, yana yi mata wani irin nauyin dayake neman rinjayar su biyun, yana sakata sakin hannuwan shi babu shiri, faduwa taga yayi ya kwanta, yana kara mata tashin hankalin da take ciki


"Hamza..."


Ta fadi, tana girgiza shi


"Hamzaa"


Ta sake fadi, tsoro da firgici bayyane a muryarta, sosai take girgiza shi, amman ko motsi baiyi ba, kuka take har sautin shi baya fita saboda tashin hankali. Hannunta ta dora kan kirjin shi tana jin bugun zuciyar shi daya nutsar da abinda yake mata tunanin ko mutuwa yayi, kafin ta dora kanta a jikin shi tana kuka kamar ranta zai fita. Tabbas labarin tashin hankali take ji, yaune tasan yanda yake. Ko kadan ba wannan bane abinda ta shirya, a mugun mafarki bata hangoma kanta irin haka ba, yanzun lokacine daya kamata ace suna more soyayyar su, ba wannan tashin hankalin ba


"Babe ji nake kamar in janyo satika biyun nan da suka rage. Bacci ni kadai yana mun wani iri yanzun, saboda ina tunanin yanda zan fara yin shi tare dake"


Maganganun shi suka fado mata


"Da zasu mun adalci, sai suce inzo in dauke ki, bama sai sun rakomun ke ba Hindu, in zo in dauki matata mu taho gidan mu"


Wani irin numfashi takeyi, ko shima zai taimaka ya farkar da ita, taga wannan abin da yake faruwa mafarkine


"Na kagu lokaci yayi da zan farka daga bacci in ganki a kusa dani, kece mace ta farko da take gwada hakurina haka"


Dago da kanta tayi, kan daya sara mata yasa ta mayar da shi a jikin Hamza, zuwa yanzun hawayenta ma sun daina zuba, banda wani yaji-yaji da idanuwanta sukeyi mata, kokarin kirjinta take gani, batasan yana da kwari haka ba, sai da taga har yanzun bai tsage dan abinda yake cikin shi ya fado ba. Ciwo dai yake mata na ban mamaki. Batasan ya lokaci yake tafiya ba tunda na ganin shi takeyi ba, duk da yanzun bata tunanin akwai wani mamaki da rayuwa zata bata, sai da baccin wahala ya dauketa mai nauyin gaske.


Ko motsin Hamza ba zatace taji ba, kawai farkawa tayi cikin wani irin yanayi, kanta kamar dutse saboda nauyin da yayi mata, kafin komai ya dawo mata, zuciyarta na wata irin dokawa, hanyar bandaki tagani a bude, ta kuwa mike tana shiga, Hamza ta samu yana kwara amai kamar zai fitar da hanjin cikin shi. Shima farkawar yayi, inda sabo ya kamata ace yanzun ya saba, duk da basai wani ya fada mishi ba, yasan yasha takai mishi karo, Hindu ma da take jikin shi hankadeta yayi, da rarrafe ya fara yana samu ya mike da gudu yana shiga bandakin, da kofar a rufe take zai fara amai a waje, hakan ma ba bakon abu bane a wajen shi.


Saida ya tabbatar ya gama aman tukunna ya dago kan shi, yana tarba hannun shi a jikin fanfo ya kuskure bakin shi, kan shi kamar zai rabe biyu saboda ciwon da yakeyi. Hindu na tsaye a bandakin ta zuba mishi idanuwa cikin rashin sanin abinda ya kamata kayi, singlet din shi ya kama ya cire, ya jefar a kasa, kafin ya mike, ganin ya dora hannun shi a kugun shi, yasata fita da sauri daga bandakin tana janyo mishi kofar. Sai dai tayi tsaye a bakin kofar, tana jin ya sakarma kan shi ruwa, alamar wanka yakeyi. Daga shi sai gajeran wando ya fito yana dafe da kan shi, tana kallon shi ya fice daga dakin, nan ta zame tana zama, hawaye take nema amman sunki fito mata.


Kafin ta ga an turo kofar, Hamzan ne ya dawo, ya saka gajeran wando da riga mai dogon hannu, karasawa yayi inda take ya tsugunna, baisan me yakeji ba, baisan me zaice mata ba, ya tabbata tagan shi a halin da Fodio ne kawai ya taba ganin shi tunda yake a rayuwar shi. Bai kuma san yanda zai dauki hakan ba, abu daya yasani, bata cancanci wannan abin dayake faruwa da ita ba, kawai baisan yanda zai gyara hakan bane ba, ga kanshi da yake ciwo, hannunta ya kama, yana mikewa ya mikar da ita, janta yayi har tsakiyar dakin, yana kamata suka sake zama, kafin ya janyota ta matso sosai, yana hadata da kirjin shi ya riketa sosai.


Sai lokacin kukanta da take nema ya fito, baice mata komai ba, riketa yayi sosai, har saida yaji tayi luf a kirjin shi, alamar ta gama kukan, sannan ya mike da ita, yana jan hannunta suka shiga bandakin, ruwa ya dinga tarba da hannun shi yana zuba mata a nata ta wanke fuskarta da bakinta, sannan suka fito daga bandakin. Zaman suka sakeyi, ya mika hannu ya janyo ledojin da suke ajiye, ya siyo kaji, burger da shawarma, yana da tabbacin bata taba ko daya ba, budewa yayi duka


"Kici wani abu"


Kai take girgiza mishi, batajin zata iya cin wani abu, har yanzun sama-sama take jinta


"Kar kisani doguwar magana Hindu, kaina ciwo yake mun. Kici..."


Ya fadi muryar shi babu alamar wasa, batasan me yayi tasiri a kanta ba, burger daya ta dauka tana faraci kamar magani, dakyar taci rabi tana ajiyewa, baice mata komai ba, duk ya tattara yana fita dasu, fridge din kitchen ya bude ya saka. Ya dauko mata ruwa daya gani yana dawowa ya bude ya mika mata, sha tayi tana bashi, ya karba yasha shima sannan ya rufe robar ya ajiye a gefe, kamata yayi ya dago, suka nufi kan gadon su dukan su, saida yaga ta kwanta, ya kama mayafin da yake kai ya lullubeta. Sannan ya mika hannu ya kashe mata kwan dakin yana takawa ya fice, tana jin rufe kofar shi, ta lumshe idanuwanta, zuciyarta na wani irin ciwo.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 25


Shi kan shi wanda yake koya mata tuqin yayi mamakin yanda ta iya cikin yan kwanaki, saboda bata zaton ta taba mayar da hankalinta akan wani abu irin haka. Ko Hamza yaji dadin yanda ta iya tuqin, da yake kudi ne suke aiki, harya gama hada mata duk wani abu da take bukata, an bata lasisin tuqinta.


"Banda kudin sai miki sabuwar mota yanzun Hindu, mu fita kiga cikin nawa ki dauki daya, banda Corolla din"


Ita kam ranta kal, bakar ta dauka kirar BMW 330i, saboda tun ranar daya fara zuwa da motar wajenta ta bala'in tafiya da ita, gata kal-kal babu inda wani abu ya sameta, shima Hamzan ita yayi niyyar bata, dan tafi sauran motocin shi haske, kuma bata koyi shekara da siye ba, bama sosai yake hawanta ba. Ya dai bari ta zabane da kanta. Ko baccin kirki bata samu ba ranar daya bata motar, ya kuma tabbatar mata da mallakinta ce, duk yanda take sonyi da ita zata iya. Ranar farko da ta koma makaranta da motarta ta koma, taji dadin yanda tayi parking ta fito, duk ga wasu cikin yan ajinsu suna ta kallonta, an ga ta zama Hajiya.


Danma Hamza bai fara mata zancen zuwa Hajji ba har yanzun, zata san yanda tayi ta sako maganar cikin hirar su, ta keta hazo itama, ta dawo manne da hakorin makkanta, inda duk zata shiga ana kiran Hajiya Hindu. Tunanin kawai na sakata nishadi na daban. Sai dai ba nan gizo ke sakar ba, cikin watanta na biyu a gidan Hamza, taje makaranta da safe, ana tsakiya da daukar darasi wani dan ajinsu da yazo a makare ya ratsa ta gefenta yana wucewa, kamshin turaren shi na cika mata kofofin hanci. Lokaci daya taji komai ya hargitse mata har jiri-jiri take ji.


Cikin tashin hankali, ko excuse bata iya dauka wajen Malamin ba, ta mike tana fita da saurin gaske, dakyar takai bakin kwalbatin da take gaban ajin, kafin ta tsugunna tana fara kelaya amai kamar zata fitar da hanjin cikinta. Hawwa ce ta fito tana taimaka mata, har ruwa ita ta siyo mata, ta kuskure bakinta, ta wanke fuskarta tana kuma samu ta sha, bata mike daga wajen ba sai da wani irin zazzabi mai zafin gaske daya lullubeta. Dole ta tarkata jakarta tana nufar gida


"Anya Hindu zaki iya tuqi kuwa? Dakin bari na sauke ki, sai in hau Napep in dawo"


Hauwa tace cike da damuwa a muryarta. Ita dince dai taqi, aikam a jigace ta shiga gida, a bandakin baki na cikin falon taci birki saboda wani sabon amai daya sake taso mata, amman kakari kawai takeyi a wahalce tunda duk wani abu da yake cikinta ta gama fito da shi, anan kan kafet ta kwanta, tana rashin lafiya. Ba zata iya kirga yawan lokutta da ta kwanta asibiti ba, amman zata rantse bata taba ciwo irin wannan daya kamata farat daya haka ba. Jinta take kamar ba'a duniyar take ba, kamar ta shiga wata irin duniya da bata taba tunanin akwai irinta a rashin lafiya ba. Ko numfashin kirki bata iyawa, ga amai da takeji yana taso mata har lokacin.


Ta kai mintina talatin anan kwance, idanuwanta a lumshe, amman sam ba bacci takeyi ba, ganin kamar mutuwa zatayi idan bata samu taimako ba, ya dan bata karfin gwiwar mikewa, taja jiki tana janyo jakarta data cillo tsakiyar dakin tun shigowarta, wayarta ta dauko daga ciki, tana samu dakyar ta kira lambar Hamza, da bugun farko ya daga da fadin


"Har kun fito ko bai zo ba yau din ma?"


Muryarta can kasa tace


"Ya zo..."


Kafin ta samu furta wani abin, daga dayan bangaren Hamza ya rigata


"Hindu? Lafiya? Me ya faru? Ya naji muryarki haka?"


Dan gyara kwanciyar tayi


"Bani da lafiya, na dawo gida ne ma"


Tana jin yai magana cikin yaren da bata fahimta ba kafin yace


"Ina zuwa kinji, yanzun zan zo"


Bai jira amsarta ba ya kashe wayar. Mai musu aiki sau daya take zuwa, da tayi share-share sai dan wanke-wanke da bama kullum suke da shi ba, sai in Hindun tayi girki, sauran tarkacen da sukaci, Hamza kance in tazo a fito mata dashi ko ansa a fridge ta tafi dashi, kuma Hindu ta dinga bata kudin mota, ko dubu dayane. Yanayin kyautar shi na mata dadi, ko yau da zata fita dubu goma ya bata, a cewar shi ko zata bukaci siyan wani abu a makaranta, ko takardu ba saita kira shi ba, kuma akwai kudi a account dinta. Baba ma satin daya fita taga ya tura mata dubu goma, tasan kuma na makaranta. Shisa Baba yake daban a duniyar ta. Sanin tana karkashin kulawar Hamza yanxun bai hana shi sauke nauyin da yake tunanin har yanzun yana kan shi na hidimar makarantarta ba.


Bata san iya lokacin da ta dauka ba, dan bacci ya fara daukarta taki muryar Hamza daya dago ta yana tana fuskarta, wuyanta da duk wani waje da hannun shi zai iya sauka a jikinta da zaiji yanayin zazzabin daya rufeta.


"Wanne irin zazzabi ne wannan?"


Ya fadi cikin tashin hankali, shi sam bayason yaga wani bashi da lafiya. Hankalin shi yakan tashi, musamman yanda yaga duk ta langabe mishi, zuciyar shi banda dokawa cike da tsoro babu abinda takeyi


"Hindu... Hindu"


Yake kira yana mikar da ita zaune, shi ya mike tsaye ya kamata, tana tashi dakyar saboda wani irin jiri da taji yana shirin dibarta, ga amai daya taho mata, da sauri ta kwace hannunta daga rikon da yayi mata tana rugawa bandakin, amman babu abinda ya fito sai wahala, Hamza yayi tsaye a kanta yana mata sannu, shiya taimaka mata ta mike, suna fitowa ya zaunar da ita, da kan shi ya zame mata abayar da take jikinta, ya shiga dakinta ya dauko mata hijab, yana kamawa ya saka mata.


"Ta shi muje asibiti"


Yanda take jinta motsin kirki ma dakyar takeyin shi


"Dan Allah kabari in kara hutawa"


Ta fadi kamar zata fashe miki da kuka, kan shi yake girgiza mata


"Kalli yanda kike fa, kina cemun in tsaya ki huta. Ki tashi wallahi mu tafi asibiti..."


Hamza ya karasa yana kamo hannuwanta duka biyun ya mikar da ita tsaye, amman gani yake kamar zata bata mishi lokaci, sakin hannuwan nata yayi yana dan rankwafawa ya sungumeta ya sabata a kafadar shi kamar bai dauki komai ba, bata da lafiya amman bai hanata jin wani abu ya motsa a zuciyarta ba. Da tasan rashin lafiya ce zata sa Hamza ya dauketa haka, da ko ta karyace tayi tuntuni, luf tayi a kafadar shi har suka karasa bakin motar shi daya samu ya ajiyeta, yana amfani da hannun shi daya ya riketa gam, kamar yana tsoron inya saketa zata iya faduwa, gaban motar ya bude mata, sai daya taimaka mata ta shiga, ya rufe, tukunna ya zagaya ya shiga. 44 Nigerian Reference Hospital da akafi sani da 44 NARHK ya nufa kan shi tsaye, Anna da duka yan gidan nasu nan suke zuwa yanzun in dai basu da lafiya.


Ya yarda da aikin su da kuma yanayin kulawar su, duk da tsadar da mutane suke kira asibitin na da shi. Amman yana da halin, kuma wani kyale-kyale ma yake kashe kudin shi a kai, ballantana neman lafiya. Suna shiga kuwa ana zuwa aka taimaka ma Hindun, sannan ya fara maganar bude mata nata katin, sosai aka shiga bata taimakon gaggawa, dan yanda suka ga ta galabaita har sun bata daki ma, an daura mata ruwa ko zata samu karfi a jikinta, ruwan da takeji kamar yana sake takalo mata ciwon da take jine. Hamza ya zauna tare da ita, da yake an dibi su jini ayi gwaji, har fitsari suka sa tayi a wata yar roba, bayan jerin tambayoyin da sukayi ta mata.


Dan lokacin da results din suka fito bacci takeyi, Hamza ne zaune yana danna wayar shi. Har ofishin likitan ya bishi, inda aka tabbatar mishi da Hindu na da shigar cikine. Tashin farko ba zai ce ga asalin yanda yaji saukar maganar ba, dan daga ofishin yana fitowa, Hindu ya fara leqawa, yaga baccin takeyi. Tukunna ya fita yana shiga motar shi, masallacin farko daya samu ya tsaya ya gabatar da sallar azahar da yaji ana kira, sannan ya sami wani karamin restaurant, ya zauna. Dankali da kwai sai kaza yace a kawo mishi, su hado mishi da coke. Abincin yakeci ba dan yana gane kan shi ba, bama yunwa yakeji ba, jikin shine ya bashi cewar lokacin da zaici abinci yayi.


Wani irin sama-sama yake jin shi, kan shi kamar an dora dutse saboda nauyin da yayi mishi. Aure gare shi, matar shi ce dauke da cikin shi. Yau shine mace take dauke da cikin shi, baisan me ya kamata yaji ba, amman tsoro na daya daga cikin abinda yakeji, tsoron da bai tabaji ba tunda yake a rayuwar shi.


"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un"


Ya furta yana ajiye cokalin cikin plate din shi, fuskar shi ya dafe da hannuwan shi biyu yana sauke numfashi, kafin ya budeta yanajin yanda zuciyar shi take bugawa har cikin kunnuwan shi. Ko da yake hango kan shi da mata, ba zaice ya hango shi da yaro ba, bai hango wannan dawainiyar ba dan baisan ta inda zai fara ba


"Kana zaman ka lafiya ka janyowa kan ka wannan bala'in Hamza, kana zaman ka"


Shine abinda zuciyar shi take furtawa tana kara maimaita mishi. Mikewa yayi yana ajiye dubu biyu akan tebirin duk da abinda yaci dubu dayane da dari biyu. Sannan ya fice, motar shi ya shiga yana komawa asibitin, amman inda yayi parking nan yayi zaune cikin motar, yana kasa fitowa, ko ina jikin shi kyarma yakeyi saboda tashin hankali. Wayar shi ya zaro daga aljihun shaddar da yake sanye da ita, yana lalubo wayar Fodio ya kira, AbdulHafiz zai janyo mishi wasu ayoyi na yanda cikin jikin Hindu kyauta ce da Allah yake zabar bayinsa wanda zai ba, da sauran wa'azikan da basu yake bukata ba a halin yanzun. Wanda zai fahimci tsoro da firgicin shi yake so


"Hey..."


Fodio ya fadi ta dayan bangaren


"Ciki take da Fodio. Bansan me zanyi ba wallahi, I'm fucking terrified"


Hamza ya karasa muryar shi na rawa


"Shit.... Da gaske?"


Fodio ya tambaya, Hamza najin tsoron da yake muryar shi shima


"Abinda nake fadi kenan, kaima ka tsorata ballantana ni, muna asibiti tun dazun. Ina cikin mota a zaune. Fodio ban shirya ba, wallahi ban shirya ba"


Wani irin zagi Fodio yayi mishi da yasa shi fadin


"Fodio"


Cike da mamaki


"Ka jini ai, dan ubanka me kake nufi da baka shirya ba? Kana da hankali kuwa Hamza? Ita ka dai kabari a cikin asibitin bayan an fada muku? Ita kadai kabari ka fito?"


Kai Hamza yake girgiza mishi


"Bacci takeyi sanda na fito"


Ya furta a raunane, yanajin Fodio ya sauke numfashi


"Kasan me yasa ban taba tunanin aure ba? Saboda ba zan dauko yarinyar mutane ban shirya daukar nauyin ta ba. Ka jini Hamza, sai da na fada maka karkayi, nace maka wahala ce a cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login