Showing 24001 words to 27000 words out of 110313 words
Chapter 9 - MIJIN NOVEL COMPLETE Na Maman Khalid.txt
Fulani'
Sai taji kamar fitilar Hamza nason dishewa a ranta. Akwai wani abu tattare da Sarauta da yake burgeta har cikin kasusuwan jikin ta, lokutta da dama takan ji daman ace ita din ta fito daga gidan Sarauta ne. Kasa duba shafikan telolin tayi, ta saka wayar a key tana yin addu'ar bacci, tukunna ta juya hannu tana lumshe idanuwan ta, da fatan Allah ya taimaketa ta samu bacci. Aikam baccin tayi cike da mafarkin Hamza ya zama sarki, ita kuma ta zama Sarauniya, tana gefen shi tsaye ana zuba musu kirari.
Ita kanta da safe da ta tashi sai da dariya ta kamata. Yau saboda tana cikin farin ciki kitchen ta wuce ta fara sharewa, babu ma wanke-wanke, da alama Asma tayi da dare. Doya ta fere ta dora, sannan ta fito ta share falon ta gyara ko ina. Ta koma ta tace doyar, lokacin Asma ta fito itama
"Sannu da aiki. Ni me zan tayaki?"
Kai Hindu ta girgiza mata
"Kije kiyi shirin islamiyya abunki, doya kawai zan soya mana"
Dan tsaye Asma tayi
"Ko ki kawo in soya doyar to"
Dan murmushi Hindu tayi, tana da tabbacin Asma ta gyara musu daki kafin ta fito
"Asma ki wuce ki kyaleni, kullum ba ke kikeyin aikin ba?"
Dariya kawai Asma tayi tana wucewa ta koma dakin su. Ita aiki bata dauke shi komai ba. Doyar kuwa Hindu ta fara soyawa, ta kunna karatun Qur'ani da take tabi a hankali, Zaid ya shigo kitchen din
"Me kike soyawa? Ina ci... Yunwa nake ji"
Dan juyowa tayi ta kalle shi
"Yaya... Ina kwana. Doya ce fa, amman ban dafa ruwan zafi ba tukunna, bari in duba maka a flask ko akwai saura"
Kai Zaid ya girgiza mata, tashi yayi cikin shi kamar anyi sata.
"In da miya ki saka mun, idan babu kibani a haka nikam, kyale ruwan zafin nan"
Plate ta dauka ta dibi doyar ta zuba mishi, tana karasawa ta bude tukunyar miya da take ajiye ta zuba mishi a gefe. Sannan ta mika mishi, ya karba da fadin
"Nagode sosai"
Ya fice, duk baudadden halin shi, koya kayi mishi abu sai ya nuna maka yaji dadi. Ko shara ya saka idan kayi, ko da baya kusa ya dawo yagani sai yazo ya sameka yace maka ya gode. Akan ce maza basu cika nuna jin dadin su akan al'amura ba, ita kam ta yarda maza nada banbanci halayya, kowa da yanda na shi yake, dan Zaid kawai yasa ta karyata wannan fadar da mutane kanyi. Ko Anty tana cewa matar shi zata sha wahala da halayen shi da yawa, amman idan ta fahimce su zasu dade basu sami matsala ba, dan shi mutum ne mai saukin kai. Kuma kamar yanda zai nuna maka yaji dadi in kayi mishi abu, haka zai nuna maka baiji dadi ba idan kayi mishi ba dai-dai ba.
Tana karasa soyawa, ta gyara takardar ta rufe kular, dan kar zufa ta koma cikin doyar shisa ta saka takarda a kasa. Tasu ita da Asma ta dauka tana kai musu daki, sannan ta dawo ta duba flask, akwai ruwan zafi, shayinta kawai ta hada, tunda tasan bai dami Asma ba, shisa ma ta saka musu miya a gefe. Tare suka karya yau suna dan taba hira, har suka gama cin doyar. Asma ta dauke plate din da kofin da Hindu tasha shayi ta mayar kitchen, hijabi ta dauka da jakarta tana fadin
"Ni kam na wuce"
Hindu na amsa ta da
"Kina da kudine a hannun ki?"
Dan yini sukeyi ranakun asabar da lahadi
"Ina da Naira dari"
Tsaki Hindu taja a fili, dan tasan Asma ba shiga wajen Baba zatayi ba kafin ta wuce din, tana rasa kalarta wasu lokuttan, ko kudine idan ba'a dauka an bata ba, ba zata taba bude bakinta ta tambaya ba.
"Ki mikomun jakata din can, ke ba zaki taba bude baki ki tambaya a baki kudi ba, banza kawai. Uban me zaki siya da Naira dari? Salon ulcer taje ta kamaki a banza"
Asma dai batace komai ba, murmushi kawai takeyi, ita abubuwa irin haka basa bata mata rai. Jakar ta mika ma Hindu, ta bude tana bata dari biyar. Dan ita ko ranar juma'a sai da Baba ya bata kudi.
"Nagode sosai"
Asma ta fadi, tana saka Hindun sake jan wani tsakin. Dariya kawai tayi ta fice daga dakin. Hindu kuwa wayarta ta dauko ta duba taga ko Hamza yai mata magana, amman shiru. Tana tunanin ko ta tura mishi sako taji ya tashi lafiya. Ko kuma ta kyale shi, duk da Dimples kance mata
'Matan Hausawa na da matsala, sun ma jan aji mummunar fahimta. Su a ganin su jan aji shine namiji ne kawai zai dinga kiranki, idan shi bai miki magana ba ke ba zaki taba mishi magana ba, idan chatting kuke ki dinga amsa shi dai-dai. Kowa fa nasan kulawa, idan bai kira ki ba, ba wani abu bane dan ke kin kira kin duba shi, aji na cikin kama mutuncin ki, karki taba rokon shi wani abu, kisan me kikeyi. Amman ina amfanin bakiyi mishi magana ba, amman yana kira kina makale murya kina fadin sub dina ma ya kare'
Yar siririyar dariya Hindu tayi yanzun ma, babu yanda za'ayi kai mintina biyar da Dimples bakayi dariya ba. Amman a cikin abinda da yawa kan dauka rashin hankalinta, akwai maganganu masu tarin ma'ana, text tayiwa Hamza
'Ka tashi lafiya? Ya gajiyar ka?'
Sannan ta ajiye wayar tana shiga tayi wanka ta fito. Duk da babu inda zataje bai hanata yin kwalliya ba, ta feshe jikinta da turaruka masu karfi tunda tana gida. Doguwar riga ta saka ta material ja da baki daya karbi jikinta, ta sami hula kalar kayan ta saka a kanta tana dan turata baya. Tayi kyau dai-dai ita, sannan ta dauki wayarta tana dorawa kan drawing table dinta, ta dibo kayan zanenta, ta saita takarda, sai da ta saka earpiece a kunnuwanta ta hada da wayar tana sauraren wakokin Ed Sheeran, sannan ta fara zanenta. Jin alamar shigowar sako yasa ta mika hannu ta dauki wayar tana dubawa, Hamza ne
'Alhamdulillah. Ke ya kika tashi? Vid call?'
Tana karanta ta zare earpiece din daga kunnenta da sauri, ta tura kujerar da take zaune kai baya tana mikewa, mayafi ta dauka ta nade kanta dashi tana gyara mishi zama. Tukunna ta tura mishi
'Sure'
Tana komawa manhajar whatsapp, saiga kiran shi ya shigo, kunne daya na earpiece din ta makala tana daga kiran, kyakkyawar fuskar shi na cika screen din wayarta, tana saka ta tunanin yanda mutum zai kasance da kyau haka. Hannu yadan dago mata yana murmushi, a kunyace tace
"Ina kwana"
Maganar da alama ta dade bata kai mishi ba
"Lafiya lau, kin yi kyau"
Ya furta yana sakata ware idanuwa, dan tasan idan yana waje babu wanda zaice tana da kyau
"Zolaya ko?"
Hakoran shi ta fara gani kafin taji yayi dariya, sai dai kafin tace wani abu taga ya juya yana kokarin ture wani da yake son leqowa, amman sai da ya leqo din
"Hello, Fodio ne"
Tana kallo Hamza ya kauda fuskar wayar dan taga alamun kujeru, batajin me yake cewa dai, yakai mintina biyu sannan ya dago taga fuskar shi
"Kiyi hakuri, zakiyita ganin kalar abubuwan nan, abokai na sai hamdala"
Yar dariya Hindu tayi
"Bakomai. Ka gaishe da Fodio din"
Kai ya jinjina mata
"Zan fita yanzun. Amman zamuyi magana anjima. Ki kula da kanki"
Ta bude baki tace mishi shima ya kula da kan shi ya kashe kiran, kai kawai ta girgiza tana rubuta maganar ta tura mishi, sannan ta ajiye wayar tana cire mayafin ta cilla kan gado. Zanen ta cigaba da wani nishadi na daban wannan karin.
9/18/20, 9:50 AM - mmn khalid: 10
Gabaki daya satin wani irin sama-sama take jinta, kamar wadda take yawo a saman gajimare, ko tafiya takeyi sai ta dinga jinta kamar reshen bishiya saboda nishadin da take ciki. Babu rana daya a cikin satin da ta wuce batare da tayi magana da Hamza ba, yana kiranta, duk da baya mata wata magana da ta shafi wani abu banda Architecture, jiyane kawai ya bukaci sanin inda take karatu. Ta kuma fada mishi, muryar shi wani irin sanyi take mata, duk yanda take a bude. Hausar shi tafi komai burgeta, bawai bai iya bane, akwai yanda yakan fitar da wasu haruffan da zasu tabbatar maka da cewa ba Hausa bace yaren da harshen shi ya fara lanqwasawa.
Har yan gidan su zuwa yanzun sun fahimci nishadin da take ciki, hatta Zaid da ba shiga harkar kowa yake yiba sai da yace mata
"Wai ke uban me yake damun ki kwana biyun nan?"
Dan tabe baki tayi tana girgiza mishi kai
"Babu komai, me kagani?"
Bai sake kallonta ba, ballantana ma tayi tunanin zai furta wata maganar. Duk yanda take son ko Khadee ce ta ba labarin Hamza wannan karin taja bakinta tayi shiru, ba zatayi jinxing din abin ba. Kuma Khadee din ma bata dameta da tambaya ba, dan hidimar bikinta da yake gabatowa, bakomai take mayar da hankali a kai ba. Garama Asma kan bita da kallon tuhuma duk idan tana waya da Hamzan, saboda yanda murmushi sam baya barin fuskarta, haka idan suna chatting dashi. Sosai take son sanin wani abu a tare dashi da ba a kafar sada zumunta ya saka ba.
Bataso tayi mishi tambayar da zata saka ya daina mata magana, dan taga har yanzun baya kula duk wani comment da zatayi a kasan posting din shi na Instagram. Ta dauka tunda suna magana ko dan liking ne zaiyi, amman bai ma nuna mata yagani ba, ta dai ga alamun yana WhatsApp ne saboda taga ya saka status kwana uku bayan ya kirata, sai tayi commenting, suka koma magana a can, maimakon Instagram. Yau kam tunda ta dawo gida wajen sha biyu da rabi, sallah ce kawai take rabata da tebirin zanenta, so take ta gama duk wani assignment da take dashi zuwa safiyar gobe asabar, dan ta samu ta fara karatun test din da take dashi ranar litinin.
Sai bayan isha'i tukunna ta samu taci abinci, ta koma kan gado ta zauna, tana dora system dinta akan cinya, taji dadin wutar da suka kawo, tana addu'ar su barta har zuwa safe. Wani American film ne take kallo, series, mai suna SUITS. Tana kuma jin dadin shi fiye da yanda tayi tunani, akwai abokinta a Instagram, Ahmad. Shi yace mata ta kalla, har makaranta yazo ya kawo mata daga farko zuwa inda aka tsaya dan ana kanyine, jininsu ya hadu da Ahmad din, yana level 3 a KASU. Shima mayen kallon fina-finai ne, shine ma abinda ya fara asassa abokantakar tasu.
Tunda tayi system ta daina damuwa da zaman falo, duk abinda take son kallo zata saka a cikin system din ta, ko kadan film baya yanke mata. Kallon taci gaba daga inda ta tsaya, da earpiece manne a kunnuwanta. Taji zir alamar shigowar sako a wayarta, batare da ta tsayar da film din ba ta dago wayar tana budewa. Hamza ne yai mata magana ta whatsapp
'Hey'
Ya fadi, amman sai da taji wani abu na yawo a kasan cikinta kafin ya gauraye zuwa ko ina na jikinta yana karasawa cikin kirjinta yai zaune. Saboda yaune karo na farko da ya fara mata magana batare da ita ta fara mishi ba, shiga WhatsApp din tayi tana amsa shi da
'Hey'
Tana fara rubuta gaisuwar da kafin ta tura yace mata
'Me kikeyi?'
Goge gaisuwar tayi
'Kallo'
Emoji din alamar tambaya ya saka mata, tayi murmushi
'American film, Suits'
Ta dora da
'Kai me kakeyi?'
Ya dan dauki lokaci kafin ya amsa cikin yaren turanci
'Ba wani abu mai yawa ba'
Kallon amsar takeyi tana rasa abinda ya kamata tace, ba hirar da bata shafi Architecture suka cikayi ba, tunanin abinda zata tambayeshi takeyi
'Baka fadamun dan wanne gari bane kai'
Cewar Hindu din
'Kaduna'
Kai ta girgiza tana murmushi
'Bakayi kama da 'yan Kaduna ba'
Wannan karin shiya turo mata da Emoji din murmushi, bai amsata ba, sai ga kiran shi ya shigo. Film din ta saka a pause tana amsawa da
"Hello"
Muryar shi na dukan dodon kunnenta
"Da 'yan ina nayi kama?"
Siririyar dariya tayi
"Bansani ba, shisa nake tambayarka ai, har Hausar ka batayi kama da ta 'yan Kaduna ba"
Tana jin numfashin daya sauke ta cikin wayar
"Ann shuwace, Appa bafullatani, amman ni dan Kaduna ne tunda anan aka haifeni"
Wannan karin ita ta sauke numfashin, batayi mamaki ba sam, dan batama yi tunanin baban nashi zai kasance dan kasa ba saboda kamannin shi, duk da ba haske ya cika can ba.
"Kace kana jin yarika da yawa"
Zata rantse taji girgiza kan da yayi duk da bata ganin shi
"Guda hudu ne kawai, babu wani yawa"
Dariya tayi cikin yanayin da yake nuna alamar ya burgeta sosai. Kafin ta amsa yace
"Zan danyi abu, muyi magana anjima"
Ya kashe wayar, yana sakata sauketa daga kunnenta tana dakuna fuska, haka yake mata wannan kashe wayar, ko ba zaiyi wani abu ba, da shi ya gama maganar da yake sonyi da ita yake kashewa batare daya jira amsarta ba. Amman kuma kalar ajin shi yayi mata, saboda yayi dai-dai da kyawun shi, tana hango musu abinda batason furtawa ita da shi, addu'a kawai ta karayi, dan yanzun bata asarar gabaki daya darenta a wajen zane, tunda Hamza ya amsata, ko yayane sai tayi sallah dan tana da tarin bukatu.
Alamar shigowar sako taji, ta duba taga text ne wannan karin Hamza yayi mata, bata WhatsApp ba
'Zamu iya haduwa mu gaisa?'
Batasan ta saki wani ihun murna ba sai da taji sautin cikin kunnuwanta, zufa takeji ta wajajen da bata taba zaton suna fitar da ita ba. Yau ita Hamza Abu Abbas yake tambaya ko zai iya haduwa da ita su gaisa, ba tun yanzun tasan Allah ya amshi addu'arta ba, kawai lokacine baiyi ba sai yanzun, daman Allah yana tare da mai hakuri. Yau kuma taga ribar hakurin takaicin duk tarkacen samarin da ta dinga kwasa a baya.
'Babu wata damuwa'
Ta amsa shi, kafin ya sake tunani, kafin ya tuna cewar shine Hamza Abu Abbas, gayen da matan Instagram suke tururuwa a kanshi
'Lunch?'
Gabanta taji yayi mummunar faduwa, kafin ya gama luguden ya kara mishi gudu ta hanyar fadin
'Ki saka time ki turomun address in zo in daukeki'
Wannan karin fankar dakin bata hana gumi jiketa sharkaf ba, tabbas wannan shi Hausawa ke kira ga koshi ga kwanan yunwa. Hamza na tambayar su fita abinda turawa ke kira da 'Date' ne, yanayin shi bai nuna mata yayi kama da wanda zaizo kofar gidansu ta saka musu kujerun roba su zauna ba, batasan me yasa tayi tunanin hakan zai faru ba tun daga farko. Tasan ko mutuwa tayi ta dawo, Anty ba zata taba barinta fita da Hamza wani waje ba, kullum cikin maganar lalacewar da ta sami al'ada irin ta Malam Bahaushe take, tunda taga wani video na yawo a whatsapp na wata matashiyar budurwa da saurayinta ya hadama patin cikar shekara ashirin da uku, ya kuma tsugunna ya mika mata zobe yana tambayar ko zata aure shi kamar a kasar waje.
Anty bataga komai ba, saka mata zoben kawai yayi, sai abokanan shi da nata da suke tafa musu, matan na fitar da wasu sautika da Anty ta kira da kukan mage, cikin nuna alamar yanda abin ya kayatar dasu, amman kwana tayi tana fada kamar zata ari baki, ita Hindu taga cikakken video din, har rungume juna sukayi, suka kuma sumbaci junansu, sosai ita kanta abin yayi mata wani iri, duk da bangaren da aka bada zoben da yanda wajen ya kawatu ya matukar burgeta.
Balle kuma yanzun ita Hindu ta dauki kafafuwanta ta fadama Anty cewa Saurayi zaizo ya dauketa su fita cin abinci. Tasan magana ce da ko shaye-shaye tayi ba zata taba fara kwatantawa ba, ballantana kuma cikin hankalin ta, amman kuma ba zata bari wannan damar da ta samu ta wuce ta ba. Batare da sanin ya zatayi ba ta turama Hamza address dinta tana dorawa da
'Bayan azahar yayi?'
Emoji da yake nuna 'ok' ya turo mata. Ta saka hannu tana goge zufar da take tsatssafo mata, kafin ta lalubo Dimples, dan tasan Biebee tsaf zata sami Anty ta gaya mata ga abinda yake faruwa idan ta hanata bataji ba, inma fada zasuyi suyi, sun shirya daga baya. Amman zatace da wani abu ya sameta gara sun daina magana.
'Dee saurayi nayi haka. Ya hadu da komai dai, so yanzun yana tambayata zamu fita cin abinci, kinsan Anty ba zata taba bari ba, bansan karyar da zan ba wallahi'
Tana ganin kawunan hararar da Dimples din ta turo mata
'Babu shinkafa a gidanku ne halan?'
Yar dariya Hindu tayi duk da batajin nishadi
'Kefa banza ce matsalar, me zance mishi?'
Harar dai ta sake turowa
'Ki fada mishi gaskiya, yazo kofar gidan ubanki ya sameki, kuna da shinkafa a gidanku, idan ita yake marmari ki zuba mai a plate ki fitar mishi da ita. Amman karki fara bin saurayi yawon cin abinci, ba kowacce wayewa bace abin kwaikwayo'
Sauka Hindu tayi daga whatsapp din, Dimples ba zata taba ganewa ba, Hauwa ta kira tana fada mata abinda ta fada ma Dimples din
"Babe... Yazo gida zaifi fa"
Kai Hindu take jinjinawa
"Nasani wallahi, amman banason blowing wannan chance din, Hauwa yamun, irin yamun ba kadan ba. Dan Allah ki taimaka mun"
Tana jin Hauwa ta sauke numfashi, kafin su tsayar da magana akan dabarar da zasuyi Hindu din ta fita ko da na awa dayane. Ta sauke wayar da murmushin nutsuwa a fuskarta, tana tsintar kanta da kashe system din gabaki daya, bata da wata natsuwar da zata cigaba da kallo, gara suyi hira da Hauwa ta tayata zaben abinda ya kamata ta saka, tsikar jikinta sai mikewa take saboda excitement, ta kasa yarda da cewar itace zata ga Hamza Abu Abbas gobe.
*
"Wai murmushin me kakeyi?"
Fodio ya tambaya da mamaki bayyane a fuskar shi, sai da Hamza ya gyara zaman shi akan doguwar kujerar da yake zaune ya mike kafafuwan shi, hannun shi da kofin da ya zuba giyar da turawa kema laqabi da beer. Saboda bayaso ya rike kwalbar, a samu akasi AbdulHafiz ya shigo. Tun randa yasha wiwi a cikin gidan yana nan, har yanzun baya sakar mishi fuska. Wata magana mai tsayi ma bata hadasu ba, gara jiya da suka hadu wajen aiki sunyi magana kan project din da suke kanyi na zanen Estate a jahar Kano da ya samo musu daga gwamnatin tarayya.
"Ba zaka gane ba"
Cewar Hamza yana cigaba da danna wayar shi, hira yake da Hindu, abinda a sati daya ya fara zame mishi