Showing 27001 words to 30000 words out of 159314 words
Chapter 10 - Wata Kishiya Complete writing by Sa'adatu Bint Abdullahi .txt
yayi be cinsa, inma ya huce seya dumamasa a na'urar dumama abinci to be cika son cin abinda aka dumamasa a na'ura ba. Seda ya cika plate da dafadukan macaroni din wadda rabinta duk hanta ce, jikinsa har yana rawa ya dauki spon ya fara debo abincin ya xubawa dan karamin bakinsa, Ya rasulillahi! Seda ya lumshe idanuwansa saboda dadih da gardi da zunmar ni'imar abincin, nan da nan ya hadiye ba tare daya tsaya taunawa ba kmr wani mayunwaci, wallahi ze iya rantsewa da ubangijin sammai da kassai be taba cin abinci me dadin wannan ba , sena ummihnsa. Kmr mayunwaci haka ya dingacin macaroni din yana korawa da Apple drink din, seda ya cinye plate din macaroni din tass ya kara rabin plate nanma ya cinye ba tare da abincin ya isheshi ba a baki ya hkra don dalilin cikinsa ya cika amma bakinsa na bukata dadin be isheshi ba. Dukda ya koshi amma ya zuba farfesun kifin a plate din da aka tanada dancin farfesun kifi shape din plate din shape din kifi ne, kalanshi golden kai kace gold ne. Tashi yayi ya wanke hannunsa a inda aka tanada dan wanke hannu sbda da hannu zeci farfesun kifin ya dawo ya zauna ya faracin farfesun kifin wanda ya zubasa dayawa a plate burinsa kawai ya cinyesa dan dadinsa ya riga ya gama dashi. yana ci yana lumsar idanuwa farfesun kifin yafi masa macaroni din dadih, ya tabbatar koda cikinsa ze fashe baze koshi ba sbda dadin abincin, nan da nan ya fara fuskantar duniya ni'imomi da albarkatun jikinsa suka fara kokarin dawowa garesa yayinda rabin hayyacinsa ya dawo jikinsa sbda dadihn abincin ya mantar dashi kusan kaso chasa'in na damuwarsa. Yana cikin cin kifin hajiya saude ta shigo dining room din bako sallama ta kiching ta shigo bata cikin falon ba. Dagowa yayi ya kalleta zuciya cike da mamakin ganinta a side dinsa yau, yasan akwai babban dalilin zuwan nata side dinsa, dan ze iya kirga sau nawa ta taba zuwa side dinsa a zamanshi da ita kusan 10yrs. Ganintan da yayi tini yaji duk ni'imomin dasuka zo jikinsa sun gujesa zuciyarsa ta cunkushe da wani irin kunci na bugawa a mujallah,, kallo daya ya mata ya dauke idanuwansa a knta. Tin kafin ta karaso idanuwanta ke kan dining din sbda kamshin daya cikata na abincin itama bata tabajin irin kamshin ba se yau, tini nata yawun ya tsinke amma ta hadiye tunawa datayi da kiyayyar datakewa wadda ta dafa abincin. Karasowa tayi ta zauna a dayar kujerar dining din tana facing dinsa a yadda taga yanacin kifin da kuma yadda taga dayan plate empty ya tabbatar mata da yarinyar ta iya abinci domin in abinci ba dadih be iya ci duk yunwar dayakeji tariga tasan hkn a tattare dashi.....
*Vip 1k normal 500 0542703718 Saadatu Abdullahi gt bank shedar biya ta nan 08101626484 ko M.T.N card ko VTU ta waccan lambar.*
'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*WATA KISHIYA*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*Littafin ma'aurata ne*
SAADATU BINTU ABDULLAHI✍🏽(writer of Kyautar Allah)
*DEDICATED TO MALAMA ALARAMMIYA AUNTY AYSHA (MAMAN RUKAYYA)*
Free page8
"Abdoljalal Kaga me Aikin?'' Saude ta jefo masa tambayar ba tare data gaishesa ba. Dagowa yayi ya sake kallonta a karo na biyu yace "Banganta ba nadega abinci a dinning..." Saude ta lumshe idanuwanta ta budesu a Kansa Sbda yadda ya mata maganar ya haifar mata da mutuwar jiki,muryarsa kawai tada mata hankali takeyi."Okay yayi, daman ai banso ka ganta,,abinci kakeso shi zata dafa maka ni de kasanni da kishi kwata-kwata hankalina ya kasa kwanciya a kan yarinyar shiyasa nace bari in sameka nide ba ruwanka da ita, me aiki ce ta maka abinci kawai kaci shikenan, pls nide ka kula da kanka a kan kowacce mace..." Dagowa yayi ya sake kallonta daganin yadda take maganar yasan kishin nata ne na azabar ya motsa, dan ita bata da lissafi a kan kishi. Ba tare dayace komi ba ya mike byn ya gama cin Farfesun kifin ya isa ga inda aka tanada dan wanke hannu ya wanke hannayensa duka biyu da sinadarai. duk tana zaune tana kallonsa ya gama ya kwashe komi na kn dinning din ya kai kiching ya dawo ya kara wanke hannayensa duk tana zaune inda take, ya nufa hanyar dazata sadashi da falo ta taso ta biyoshi tana fadin "Bakaji abinda nace bane?'' A takaice yace "Naji..." A gaggauce ya bar falon ya nufa upstairs ta bishi da ido zuciyarsa na bata tabbacin zafin kansa baze taba bari ma ya kalli yarinyar ba, ita fa duk tunaninta kar yaci gindin wata saboda ita ba bashi gindin takeyi ba, hkn ke kara sata a halarar kishinsa, amma tasan gaskiya da wuya mijinta ya iya kunsantar gindin wata. wani irin murmushi ne ya subuce mata a kan fuskarta, ganin zuciyarta ta bata tabbacin mijinta baze taba neman wata ba da sigar ci ko ta sigar soyayya ma tasan da wuya danshi mutum ne dabesan reni, kuma babban mutum neshi dabazeso mutumcinsa ya bare a idon mutane ba,, juyawa tayi ta fice a side din nasa tana mejin kwanciyar hankali na ziyartarta tako ina, amma fa kishinsa na nan a zuciyarta ta tabbatar duk randa mijinta ya kusanci koda hannun wata ne ranar seta haukace, ko tacema faduwa zatayi ta mutu sbda tsabar azabar kishi.
Bayan ta gama sallolin nata suka nufa side din sauran masu aikin larai ta bata abincinsu na masu aiki shinkafa ce da miya da nama yanka daya, yarinyar taci sosai kasancewar tanajin yunwa, bayan ta gama ne suka nufa side din gogan suka tadda warmers din a kiching larai ta bubbude taga yaci dayawa nan take tayima yarinyar jinjina, kana suka kwashe komi suka nufa kiching suka wanke hadi da kara kimtsa komi a kiching din, larai ta rakota har dakinta kana sukayi sallahma ta gaya mata time din tashinta 8:am zata dinga tashi kullum saboda shi gogan 10:am yake breakfast. Yarinyar ta daga ma larai kai alamar toh, Sukayi sallahma tashige dakin ita kuma larai ta nufa nasu side din. Tana shiga dakin amemakon ta kwanta kawai ta fada bathroom ba jimawa ta fito daure da Alwala, ta isa ga Waldrop ta bude hadi da zuge ghana most go dinta a sama sama ta dauko wata yar bag blue ta zugeta ta fito da Alur'ani me girma hadi da askar da carbi, ta nufa daddumar hannunta rike da Alqur'anin da askar din da carbin ta ajiyesu a gefen daddumar ta tada sallar dare dan zuwa lokacin ana neman After 1:am ne, tinda ta tada sallar nafilar bata tsagaita ba se 3:30am kana ta tsaya ta dauko carbi tayi istigfari hadi da hailala da salatin Annabi SAW, ta kara da Ya zaljalalu wal-ikram, bayan ta gama tasbihin ta ajiye carbin ta bude Alqur'ani me girma ta fara karantawa a zuciya, daga Ankabut ta fara bata tsagaitaba seda tayi izu daya, kana ta ajiye alqur'anin ta dauko askar tashiga karanto Addu'ur'in dake cikin askar din, har seda aka fara kiran asubahi kana ta ajiye askar din tayi addu'ur'inta ta shafa, ta mike ta nufa toilet ta kara dauro alwala kasancewar zuwa lokacin anata kiraye kirayen sallar asubahi ne, masallacin dake gidan tabi jam'i suka idar ta zauna tayi lazimi hadi da kara krnta arzkar har alfijir ya fara bayyana, kana ta mike ta ajiye alqu'anin da askar da carbin a kan bedside drower ta isa kn bed din da hijjabi a jikinta ta kwanta, baccin awa daya da rabi tayi, ta tashi 7:30am a gaggauce tayi wanka ta fito ta shirya cikin riga da zanin atamfa, suma duk sun kode yawancin kayayyakinta duk kodaddune, tasa kayan data cire a kwandon da aka tanada dan zuba kayan dattin. Ta zumbula hijjabi maroon ko mai bata tsaya shafawa ba, sede ta fesa perfume, ta fito ta nufa kiching din nasa, ta dauko yar takaddar da larai ta bata jiya, ta dudduba abubuwan dayakeso da safe na bangaren abincin larabawa, duba tayi taga akwai komi tashiga hada masa zallar abincin larabawa har kala hudu, 9;30am ta gama komi ta dauka ta nufa side din nasa dashi ta kofar dazata kaita direct dining room ba tare data shigo falon gidan ba tashigo, tana shigowa taga ko ina tsaf tsaf se azabar kamshi kawai ke tashi tin 6:am aka gama gyaran side din nasa. Ajiye trea din hannunta tayi a kan dinning table din ta fice ta koma ta kwaso sauran kayan ta dawo ta ajiyesu a kn dinning din tana tuna warning din hajiya saude gareta cikin hanzari ta fice a side din ta dawo kiching din wanda beda nisa da side din ta wanke komi data bata, ta gama gyara kiching din kenan larai tazo taga ta gama komi mamaki ya rufeta, ita da tazo nunnuna mata ne se kuma taga ta gama,. "Sannu da aiki..." Cewar larai. Yarinyar ta amsa mata da kai, larai tace "to tinda kin gama komi kije ki kwanta abinki zuwa 12;am seki tazo ki daura masa abincin rana..." Yarinyar ta amsa mata da kai da toh, ta juya ta kulle kiching din ta nufa dakinta larai kuma ta koma bakin aikinta, daman idanuwanta cike suke da bacci tana isa dakin ta kwanta ba jimawa bacci me azabar nauyi ya dauketa.
9:40am ya tashi yau yasamu baccin daya jima beyi irinsa ba, yasan saboda abincin dayacine ya koshi, Allah-Allah yadingayi yayi wanka shap-shap ya fito ya shirya se sauri yakeyi saboda kawai so yakeyi ya isa ga Dinning room yaci wannan daddad'an abincin, wanda da dadinsa ya kwana a ransa har mafarkin dadin abincin yadingayi. Bayan ya gama shiryawa cikin manyan kaya danyan boil dinsa light brown yasaka, se zuba mahaukacin sheki boil din keyi, ya tashi yau dajin kwanciyar hankalin dayakejin ze iya zuwa office. Ya dauko dankareren watch dinsa na zallar diamond ya mannawa tsintsiyar hannunsa, ya feshe jikinsa da turarruknsa danshi din ma'abocin kamshi ne. Ya zira hadadden bakin takalminsa wanda ya amshe lallausar kafarsa, takalmin ba karamin fito da martabar kyaun kafarsa yayiba. Ya fito dass dashi se taku kawai yakeyi cike da izza tamkar rikakken gawurtaccen namijin dawisu, tako ina ya shiga gashi dogo Sambal ba karkace. Down stairs ya sakko hannunsa rike da wayoyinsa yana tafe kamshinsa na bayyana a duk inda ya taka, daga kai yayi ya kalli saman kofar dining room dinsa yaga ta kyallaro farar wuta alamar an ajiye masa breakfast dinsa. Haka kawai ya tsinci kansa dasakin murmushin daya bayyana siririyar wushiryarsa sama da kasa, direct daga zuciyarsa murmushin ya fito, be taba murmushi a kn komi na duniya ba se yau. BA bata lokaci ya isa dinning room din batare daya ko zauna ba yashiga bubbude warmers din, kamshi abincin ya dokesa yayinda mutuwar tsaye ta sameshi, ganin abincin larabawa wanda Ummihnsa ke dafa masa. A bayyane yace "Again irin abincin ummih..." Ya bude dayar Warmer din zuciya fal mamaki nanma yaga duk abincin larabawa ne, duka warmers din seda ya budesu yaga duk irin abincin da ummih ke dafa musu ne, zaunawa yayi hadi dayin serving din kansa ya fara ci dadih ya kara kashesa nan take yaji zuciyarsa na bukatar ganin wacece wannan me irin girkin Ummih kuma har yafi na Ummihn tasama dadih. Seda ya cika tumbinsa taf kana ya tashi ya dauki warmer daya, wadda be taba komi dake ciki ba, ya isa kiching ya hada warmers din a basket da plate ya dawo dasu falon, kana ya koma ya kwashe komi na kan dinning din ya kai kiching ya zauna a falon hadi da kiran driva dinsa a waya ya sanar,dashi a shirya mota zeje office yanzu...." Ba bata lokaci aka shirya motarsa kirar Benz se motar security daya, ya hau suka fice a gidan zuwa office dinsa,...ranar wuni yayi zuciyarsa cike da tunani tunanin dadin abincin daya fara ci daga jiya zuwa yau, har ya canza kumatunansa sun fara ciccikowa, abincin daya tafi dashi office din ya Karaci da rana after azahar ya dawo gidan,,,wanka kawai yayi ya isa dinning din yaga an cikasa da abinci iri daban daban, be bata lokaci ba ya shiga bubbudewa duk abinda yakeso shi yagani kwata-kwata bega akasin abinda beso va, kuma harda kari a kn abinda yakeso dinma. Zaunawa yayi yaci ya koshi yayi nak daga jiyan zuwa yau harya koyi mugun ci saboda dadin abincin. yana cin abincin ne Kuma zuciyarsa na kara kwadaituwa dason ganin wacece ke masa wannan hadadden abincin har haka kawai yanaso ya ganta...yana gama cin abincin yaji wani irin bacci ya lullube kwayoyin idanuwansa, a daddafe ya iya kai kwanukan kn dining din duka kiching ya nufa upstairs dinsa direct ya fada bedroom dinsa ya kwanta a lallausar gadonsa be jima ba bacci me dadih wanda ke tattare da rabin kwanciyar hankalinsa ya rufesa, Alhamdulillahi daga jiya zuwa yau ni'imomi sun fara masa dirar mikiya a duk sassan jikinsa.
After 6days,...
6:pm zaune suke a kayataccen falon hajiya Saude wanda ke sama, hajiya Abulle data zubawa hajiya saude ido suna fuskantar juya tin dazu sunfi karfin 10mnt a hkn. "Kawata kin kirani kuma kin tasani a gaba knyi shiru se kallona kkyi kmr kn samu TV?'' Cewar hajiya Abulle wadda hajiya sauden tayi kiranta da yammacinnan. Hajiya saude dake fuskantar hajiya Abulle tace "Wallahi hajiya hankalinane yaki kwanciya a kan yarinyarnan me aikinnan, yau kimanin satinta daya a gidannan, wallahi dana ganta se gabana yayi ta faduwa, kinga nifa hajiya har banso tazo gaidani inna ganta hankalina tashi yakeyi gabaki daya se raina ya chanza wallahi...." Hajiya Abulle tayi wata yar dariya kana tace "Haba hajjaju bansanki da mutuwar zuciya ba a kan abu kankani, abubuwa nawa muka tunkara mukaga bayansu, se wannan abin dabeda tushe balle madafa zaki daga hankalinki a kansa a hofi...'' Hajiya saude da duk jikinta yayi sanyi tace "Hajiya kamar baki fuskanci me nake nufi ba dan Allah ki fahimceni, ni gabaki daya zuciyata bata kwantamin ba da yarinyar nan gaskiya..." Hajiya Abulle dake fuskantarta hadi da nazartarta tace "Na fahimceki mana hajiya..kinsawa ranki yarinyar ne shiyasa zakiga zuciyarki taki kwanciya a knta, ki cireta a ranki kwata-kwata ki tuna duk duniya babu me iya ja da kadarinki kema knsani boka ma ya fadi da kankin kansa, sannan uwa uba mijinki fa ba irin nawa bane, ni knga nawa dabadan ina tsaye ba a knsa da Allah kadai yasan kwashe-kwashen daze dinga min dukda ma burar tasa bata aiki amma a haka se uban kwashe kwashe,,,to kinga akasin shi AASARAKI ko ada can shi ba ruwansa da wata mace hidimar gabansa kadai yakeyi, ko wannan ya isa ace zuciyarki ta nutsu guri daya saude, haba da Allah kawata karki bani kunya mana tsawon 10yrs kina mulkin mijinki ba abinda ke daga miki hankali a gidanki se yanzu a kan abu qalilan wanda ko sauron dakinki yarinyar bata kaishi daraja ba, kuma wai bebiya, karki taba daga hankalinki a kan komi na duniya mufa keda boka na gaba da bakin dutse boka dan sokoto, to aiko knga mu keda komi na duniya, kefa ynzu in kikaso a kashe rai yau dinnan za a kasheshi to meye ne dazaki addabi kanki babu dalili...." Ajiyar zuciya hajiya saude ta sauke zuciyarta na nazarin kalaman hajiya Abulle amma kuma sede zuciyar tata ta kasa nutsuwa. "Hajiya gaskiya ina ganin kawai in kira kande tazo ta dauki yarinyar nan ta kawomin wata kawai ni zuciyata har yanzu bata nutsuba..." Hajiya saude ta fadi hadi da daukar wayarta da niyar ta kira hajiya kande. Abulle ta dakatar da ita ta hanyar cewa "dan Allah hajiya karkiyi gudun gara ki fada gidan zago pls..." Hajiya saude data dakata daga kiran kande ta tsurowa abulle ido cike da rashin fahimtar me take nufi tace "Kamarya hajiya?'' Hajiya abulle ta watsa hannu biyu irin na yan duniya tace "eh mana hajiya, yanzu in aka tafi da wannan knsan wa za a kawo miki? bakincemin a waya wannan bakauyiya bace ? " hajiya saude tace "eh gaskiya kmr bakauyiya take hakanan de bata magana ai na gaya miki gata nan ni se inganta ma kmr bata da wayau..dan tinda nace karta kuskura ta hadu da mijina data kai masa abinci ta bar side dinsa, to wallahi har yanzu basu hadu ba, akwai larai me aikina danasata tasama yarinyar ido sosai a kn ta da mijina nace dataga wata baraka ta gayamin..." Abulle tace "To kngani angaya miki a yaran yanzu yan aikinnan masu budedden ido zaki samu wadda zatayi abinda yarinyarnan tayi ne, wlhi in wata ce kina nuna bakiso taga mijinki duk yadda kika kaiga tsaranki seta gansa sema kiji labari ya sauya, sede kiji har an bude an lulluma bura, amma wannan kince fa bagidajiya ce .." Hajiya saude taji maganganun Abulle sun shigeta sun haifar mata da kwanciyar hankaki tace "Eh bari in kira larai ta kirata ki ganta..." Ta lalubo wayarta ta kira lmbar larai bugu daya ta cafke ta gaidata ba tare data amsa ba ta mata izini dasuzo da yarinyrnan sabuwar me aikin da kande ta kawo falonta na sama... Ba jimawa suka iso falon duk suka zube a kasa tin shiguwarsu falon hajiya abulle ke kallon yarinyar wadda ke sanye da hijjabi brown har kasa amma dukda hijjabin datasa be boye albarkatun jikinta ba, se yanzu Abulle taga dalilin dayasa hankalin qawar tata yaki kwanciya a kan yarinyar ashe fitinannen kyau ne da yarinyar... nan take hajiya