Showing 141001 words to 144000 words out of 159314 words

Chapter 48 - Wata Kishiya Complete writing by Sa'adatu Bint Abdullahi .txt

kukan tashin hankli me tambarin matsifa da bala'in dake tattare da ita ko kwatan Abdoljalal bata kaiba. Larai de na gefe. Jin abinda jimmalo tace yasa kunnuwan Abdoljalal daukewa na wasu dakiku, idanuwansa suka lumshe da yana, yaji wani luuuu kmr ze fadi, se kuma ya rike jikinsa sbda shi namijin duniya be yayan namijim zaki ne,sam ba a ganin tashin hnklinsa duka, dan hk yanzuma rabi aka gani a zahiri. "Banji me kikace ba? Ta gudu? Ita wa ta gudu? Almuqri'ah ta gudu? Ta ina tabi ta gudu? Ina taje? Ina cikina na jikinta??'' abdoljalal yayi maganganun kamar ze haukace saboda rudu da gigita, idanuwansa se lumshewa sukeyi yana kara budesu, tashin hnklinsa baze misaltuba har abadan, kai kace cewa akayi masa Almuqri'ah din ta mutu. Jimmalo ta kasa amsa masa tambayoyinsa se faman rusar kuka takeyi. Larai tayi carab tace "ta gudu ranka ya dade, wallahi ta gudu yarinyar nan, ta bakin get tabi ta gudu, suma kansu securities basu san guduwa zatayiba suka barta ta fita , ..." "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!'' Abdoljalal ya maimaita 3ryms hadi da dafe kansa,, idanuwansa suka kara lumshewa. "Ta gudun min da ciki? Ina tajemin da cikina? Ku fada mata ta dawo ta bani cikina dan Allah...innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!''' Abdoljalal ya fadi kmr saban hauka so yakeyi yayi kuka amma ya kasa, tashin hankali mara misaltuwa ya shiga, zuciyarsa tashiga, fuskarta ta bayyana Dmwar zuciyarsa,. Larai tayi lakur, tana hango bala'in dake tattare ga Abdoljalal. Jimmalo kam se kuka takeyi. "Karya kuke min bata gudun min da ciki ba wlhi,,, se kun nemomin ita tabani cikina wlhi..." Ya fadi yana girgiza kai, ji yakeyi kmr a mafarki yake,. ya juya cikin hanzari ya nufo bakin get securities na ganinsa sukayi kasa da kansu, dmwa da tashin hankalin dake kan face dinsa basu taba ganin makamancinsa ba a tattare dashi se yau. "Da gaske ne Almuqri'ah ta gudu?'' Abdoljalal ya fadi a haukace byn ya iso inda suke kmr zararre , jijiyoyin knsa duk sun tashi . Duk suka kasa magana sede suka kara kasa da kansu. Abdoljalal ya daka musu tsawar dabe taba daka musu irintaba se yau "Nace da gaske ta gudun min da ciki?" Jikinsu na rawa suka amsa da "A, sir..tuba muke sir..." Suka hada baki gun fadar hakan. Idanuwan Abdoljalal suka kawo wasu zafafan kwallah, nan da nan suka karayin jajawur zuciyarsa kmr zata fito fili, jikinsa ya dauki rawa. kaf ma'aikatan suka karayin kasa da idanuwansu, zuciyarsu nata fatt fatt fatt, sun san karshen zamansu a gidan yazo, tini suka fara kokawa kansu. "Ku kuka barta ta fita daga bakin get?bayan ga cikina a jikinta?'' Abdoljalal ya fadi cikin kuka se yarfa hannu yakeyi sbda rad'adin da zuciyarsa keyi be tabajin irinsaba se yau.. Securities sukayi shiru suka kasa amsa wa.. "Badaku nake mgna ba dan kan babbar bura ubanku ku amsani, karku karamin shiru, in ba haka ba, wallahi zansa muku bom in kashemu baki daya nida ku, shegu tsinannu, yan iska, nace ku kuka barta ta fita a bakin get, gets hard guda uku ta fice a cikinsu ta gudunmin da cikina a jikinta, dan kutmar babbar bura ubanku?'' Abdoljalal ya fadi cikin fitar hayyaci da tsantsar tsagwaron ruwan wutar bala'i hadi da gobarar tashin hankali. Duk ma'aikatan suka kara shiga taitayinsu, sbda tashin hankalin dasuke tsammani zasu gansa a ciki se suka gansa a mafiyinsa. Duk suka amsa da yess hadi da ban hakuri. "Kuka barta ta gudun min da ciki, har tsawon 2days bata nan, ina taje? Da d'an cikina ta gudu kou? D'an cikina kou? Cikina na jikinta kou? Innalillahi wa'inna ilaihir...!!!''' Be samu dmr karasawa ba ya zube nan kasa sumamme tamkar an zare masa rai, idanuwansa suka lumshe dmn ba karfi a jikinsa. Hankalin securities din ya matukar tashi, yadda naga fuskokinsu dmwarsu suma bazata misaltuba. Gadan gadan sukayo kansa suka dagoshi, aka kawo ruwa aka yayyafa masa, amma sam be farfado ba ko ajiyar zuciya beyi ba, hankalin maza ya kara tashi wasu tini idanuwansu sun fara kawo kwallah, wadanda ba musulmai a cikinsu ba se kiran Jesus sukeyi suna ihu suna rawar diskon tashin hankali, tini suka tara kaf ma'aikata mata a gurin kukansu ya jawo hnklinsu. Tantiri kam si yafi kowa kuka da ihu harda daura hannu yayi a kai yana fadin "Wayyohhhhh mun shiga uku mun lalace !!''' Se rawar tashin hankali tumbinsa keyi.... Nan suka kwasheshi a haukace aka sashi a mota, Almustapha ya rikeshi, da salisu tantirin daketa kwallah Zuwa yanzu yayi ihun ya gaji har muryarsa ta dishe,, kaf ma'aikatan gidan sunyi nadamar barin Almuqri'ah ta fita a gidan, sbda hkn ya matukar jefasu a tashin hnkli seda kowa kowannensu yashiga tashin hankali. A guje Dreva ya shiga motar yaja suka fice a gidan, motar securities na biye dasu a baya.










Insha Allahu zaku jini da daddare. Aski yazo gaban goshi azabar zafinsa nakeji 😂


38
*na gaya muku zan dinga hutun 2days a week kuma ban fadi ranaku ba, to hutuna nayi na 2days din,, kinganni nan nasaba da zagi duk wanda ya zageni ya ragemin kayan wahala.... A barni in bi book dina a sannu pls masu sona dan Allah...wadanda basu sona adeyi hkri...*


38
Bata tsaya wata wata ba, Ta buge security din dake kofar get din wanda ya dakatar da Almuqri'ah daga karasowa cikin gidan, idanuwanta dana Almuqri'ah suka sarke cikin na juna. A lokaci guda dukkaninsu zuciyarsu ta buga da karfin, da basu san zuciyoyin nasu nada irin karfin ba. "Wacece ke?'" Hajiya ummu salma ta fadi out of control , wani abu taji a zuciyarta gami da yarinyar,.Almuqri'ah tabi Hajiya ummu salma da ido, da tayi mgna se taji zuciyarta ta buga da karfi fin a farko, voice dinta yayi kama da makusancinta amma ta rasa fahimtar wanene wannan din?" Kaf kallo ya dawo kan Hajiya ummusalma da Almuqri'ah , kama daga masu neman temako har zuwa kan securities duk suka tsuro musu ido. "Dan Allah wacece ke?'' Hajiya ummusalma ta kara tambaya hadi da dafe saitin zuciyarta sbda bugun da take mata kmr zata fashe, ta sauke idanuwanta a kan cikin jikin Almuqri'ah, hk kawai taji wani abu na fisgasta gami da cikin jikin nata. Wani irin murd'awa marar Almuqri'ah tayi ta cije, still kwayoyin idanuwanta na kan hajiya ummusalma, wadda sak kamanninta kema Almuqri'ah kama da wani data sani amma sam ta rasa tunano waneneshi wannan din. Hannu Hajiya ummusalma ta kai ta shafi cikin Almuqri'ah ba tare data sanma tayi hakan ba, Almuqri'ah ta zabura ta kalli matar, yadda ta shafar mata ciki sak haka Abdoljalal ke shafar mata ciki. "Dan Allah ki gayamin wacece ke?'' Hajiya ummusalma ta sale fadi a gigice, data shafi cikin Almuqri'ah se hankalinta ya kara gushewa, ta kasa dauke hannunta a kan cikin Almuqri'ah, ma'aikatanta da kaf da jakadiyarta suka matso kusa kusa,, mamaki ne ya rufesu musammanma jakadiyarta, nam take zuciyarta ta ayyana akwai wata a kasa. Wani irin ciwon mara ne ya turnike Almuqri'ah wanda ya wuce a daure masa nan ta durkushe kasan kafafuwanta hadi da cije lefe. Nan take hajiya ummusalma ta fahimci nakuda ce,, nan take ta gigice, tasa dreva ya dakko mota, ta umurci jakadiya data tayata suka kamo Almuqri'ah zuwa cikin gidan, da kyar take daga kafafuwanta, se azabar zufa kawai take karyo mata, suka dauketa da temakon sauran ma'aikatan aka sata a bayan mota, hajiya ummu salma ta shiga bayan motar ta jawota jikinta, ta kurawa cikin jikin yarinyar data rairaye yayi kasa sosai ido, ita kadai tasan me takeji a kan cikinnan na jikin yarinyar. "Kai yi sauri kaja motar muje asibiti..." Cewar hajiya ummu salma, datayi mgnr da dreva dinta, jakadiyya ta juyo ta zubo ma Almuqri'ah ido wadda keta faman yarfe hannu tana cije baki idanuwanta a kulle suke gam,, jakadiya ta kalli ummusalma taga cikin jikin yarinyar kawai take kallo, wani irin karatune a kan fuskar hajiya ummusalmar me wuyar karantuwa, nan take jakadiya ta shiga thinking din wacece wannan yarinyar ?'' Hajiya ummusalma tasaba temakon mata da dama, tanada tsananin imani da tausayi, imanin dake kwance kan fuskarta a wannan karan dabanne. Dreva yaja motar suka nufa asibiti, hajiya ummusalma se sannu kawai taketa cewa Almuqri'ah,, haka kawai ta tsinci zuciyarta da natsawa sbda kallan dataketama cikin jikin Almuqri'ah.


*Kaduna*
Suna isa abitin da Abdoljalal ba bata lokaci doctor suka dukufa a kanshi , suka samu ya farfado daga suman da yayi, akayi masa Allurar bacci, bacci ya kwasheshi bashi ya farka ba se 12:am ,ya bude idanuwansa a saman P.O.P din dakin asibitin, tunaninsa ya dawo kansa, "da gaske be ta gudun min da ciki!!??" Ya fadi kmr zararre hadi da tashi zaune zumbur ,idanuwansa suka sauka a kan Ahamad dake zaune kan kujerar dake facing dinsa, mustapha ne ya kirashi ya sanar dashi abinda ke faruwa shine yaxo asibitin yakira larai ita kuma take asibiti gun hajiya saude wadda har yanzu bata farka daga dogon baccin tashin hankalin da takeyi ba. "Sannu sir, ya jikin naka?..."cewar Ahamad da yayi mgnr cikin tausayi da tausayawa. "Kagani ko Ahamad yarinyar nan ta gudun min da ciki? Kana gani ta gudun min da ciki kou?' Kwananta biyu kenan bata nan ta gudun min da cikina...'' Abdoljalal yayi maganar idanuwansa na cikowa da zallar kwallar tashin hankali tini ya koma kmr zararre. Ahamad ya karajin tausayinsa sosai, mustapha ya sanar dashi komi. "Ka kwantar da hankalinki sir dan Allah, zata dawo insha Allahu..." Ahamad ya fadi cikin kwantar masa da hankali. Abdoljalal ya kalli Ahamad dayayi, ya dawo ya kalli drib din hannunsa, ya girgiza kai still yana kwallar dashi kadai yasan zafinsa yace. "Bazata dawo ba...Ahamad tashi muje ka kaini in nemota, mutuwa zanyi in bangantaba..." Yayi mgnr hadi da tsige drip din hanninsa nan take jini ya balle ya fara zuba. Hankalin Ahamad ya tashi ya riko hannun nasa yana fadin " sir dakayi hkri drip din jikinka ya kare..." Abdoljalal ya mike tsaye, still jini na tsiyaya a hannunsa,ya fisge hannunsa daga rikewar da Ahamad ya masa, ya fice a dakin Ahamad ya biyoshi yana fadin "Sir bari a kira nurses su duba maka jinin nan dake zuba a hannunka..." Ina sam Abdoljalal be bi ta kansa ba ya fice a asibitin ma baki daya, ahamad ya kira nurse suka biyo shi wajen a bakin motarsa suka samesa har lokacin kuka yakeyi kmr karamin yaro yana fadin "Ta gudun min da ciki...shikenan ta tafinmin da ciki... sena kashe kaf securities din dasuka barta ta fita....a kaina gidan mahaukata, wlhi haukacewa zanyi in bangantaba..." Sune kalaman da Abdoljalal keta fadi cikin gigitar fitar lissafi. Ahamad da nurse duk sukaji tausansa ya kuma ratsasu, nurse ta karaso domin temaka masa jinin hannunsa ya dena zubowa, amma fir yaki yarda, ahamad yayi-yayi ya tsaya amma yaki tsayawa nurse ta dktr masa da jinin dake zubowa a hannun nasa. "Ka barni in mutu Ahamad,yarinyarnan ta gudunmin da ciki..." Ya kara fadi kmr ze mutum kokawa kawai yakeyi da numfashinsa. Idanuwan ahamad suka cicciko da kwallah ya zaro waya a aljihunsa yayi dealing number din dr mus'ab amma kiran be shiga ba tin jiya yake kiransa amma number taki shiga. Ahamad ya maida wayar tasa aljihu yayinda kwalla suka wanke masa fuska,yana me kallan Abdoljalal ita kanta nurse ta tausaya Ainun. "Dan Allah sir ka bari a duba maka jinin nan dake zuba a hannunka dan Allah sir, zamu nemota kuma zamu ganta insha Allahu..." Cewar ahamad da yy mgnr yana kuka Abdoljalal dinma na kuka, da kyar ya yadda suka koma ciki nurse aka bashi temakon gaggawa jinin ya dena zubowa a hannun nasa. Suka fito ahamad ya bude masa mota ya shiga, shima ya shiga yaja motar suka fice a asibitin. Abdoljalal ya kwanta a kan kujerar motar ya lumshe idanuwansa se kuka yakeyi kmr karamin yaro. Ahamad nata kallanshi shima se hawaye yakeyi tausayin Abdoljalal ya kuma cika masa zuciya be tabbatar da yanasan yarinyar ba se yau. "Sir in kaika gida ka huta? Tinda kaki yadda ka zauna a asibitin kasamu sauki ranka ya dade..." Cewar ahamad. Abdoljalal ya dago ya bude idanuwa sa ya kalli ahamad yace "aah karka kaini gida, ni ai bnda hutu yanzu senaga yarinyar nan, ka kaini inda zan nemeta in ganta dan Allah..." Ya karashe mgnr yana meci gaba dayin kuka, duk ya fice hayyacinsa, kmr zararre. Ahamad ya kalli agogon motar yace "Sir karfe dayan dare ake nema yanzu..." Abdoljalal daketa ci gaba da kuka yace "inkai zaka tafi gida ne,ni ka saukeni ko ka bani motata inje nemanta, wlhi bazan iya bacci ba sena ganta..." Tausanta ya kara cika Ahamad, ya sakejin sabon kwallah ya wanke masa fuska. "Ina zamuje to sir..." Cewar Ahamad. "Ko ina...gudunmin fa tayi da ciki...wlhi sena nemota ta bani cikina ita se tayi tafiyarta, a kan me zata gudunmin da ciki, cikina nefa, ni na mata, amma ta gudunmin da ciki..." Abdoljalal ya fadi hadi da dagowa ya kifa kansa a kan cinyoyinsa hadi da fashewa da wani irin kuka me sauti, brain dinsa har wani dil-dil yakeyi kmr ze haukace.. Ahamad shima ya kara fashewa da kuka, driving yakeyi amma hnklinsa na kan Abdoljalal. Nan suka shiga zagaye garin kaduna a daren,suna fita suna haska lungu da sakon anguwanni, amma sam basu ganta ba,,sunata zagen har akayi asubahi ko rintsawa kaf basuyi ba, seda Abdoljalal yaji kiran sallar aaubahi Kana ya tuna ana binshi bashin salloli. Tsayawa sukayi, a wani masallaci ya biya bashin sallolin da ake binsa, sukayi Asubahin, ya dinga Addu'ur'i Allah yasa yaga Almuqri'ah, ji yakeyi ze iya bada komi na rayuwarsa inde zega yarinyar. 6:am suka ci gaba da zagaye kaduna suna neman Almuqri'ah har wuraren 6:pm suna yawo sallarh kawai ke tsayar dasu, dasukayi magriba da kyar Abdoljalal ya yadda suka nufo gida , ko packing ahamad be gama yiba Abdoljalal ya fito daga motar ranshi a matukar baci zuciyarsa ji yakeyi kmr zata fashe, gabaki daya babu laka a jikinta ya karaso bakin get inda securities suke, kaf suka mike tsaye, hadi da gaishesa, da tambayarsa ya jiki...ai bebi ta kan gaisuwat dasuke masa ba ya shiga sirfafo musu wasu mahaukatan manyan zagi cikin bacin rai, ji yakeyi kmr a bashi bindiga ya harbesu. Ahamad ya karaso inda Abdoljalal yake bakin get yanata sirfafawa securities zagi sukan sunyi kasa da kai, sunyi shiru kmr ruwa yacisu. Abdoljalal na ganin ahamad ya karaso ya kalleshi a matukar bacin rai. Yace "Kirawomin shugaban sojojin nigeria, azo a kwashemin tsinannun nan aje a ajesu a dinga dukansu,, har se dun fadi inda yarinyar nan ta tafin min da ciki, da hadin bakinsu, in ba da hadin bakinsu ba ta yaya zasu barta ta gudunmin da ciki,,,wallahi nine ajalinsu a gidannan..." Cewar Abdoljalal dake mgnr kmr ze rufesu da duka, shi kadai yasan yadda yakeji a zuciyarsa. Jin abinda Abdoljalal yace yasa securities zubewa kasa suka shiga bashi hakuri, amma fir yaki ko saurarensu, ya kara dakawa ahamad tsawa yace maza ya kira shugaban sojoji ya hadasgi dashi a waya..." Ba yadda ahamad zeyi dole ya kirashi bugu biyu ya daga sbda ta nan dmn yake mgna da Abdoljalal din in yanada bukatar sanyin waya dashi. Abdoljalal ya amshi wayar ya sanar da shugaban sojoji yasa a kawo motocin sojoji gidansa a kwashe kaf securities din gidansa aje a horasu..." Shugan sojoji yace "Subhanallahi meke faruwa saraki?'' Yayi mgnr zuciya fal mamaki sbda yasan waye Abdoljalal da tausayi da imani, yayi mamakin dayaji yace azo a kwashe kaf masu hadin gidansa. Sam abdoljalal be bashi amsar tambayarsa ba, yace "kawai azo a kwahesu yanzu, in ba hk ba wlhi zansa bom in kashesu da kaina..." Yana gama fadar hkn ya katse wayar, ya juya ya nufa dakin Almuqri'ah, da kyar yake tafiya kmr bashi da laka yakejin jikinsa. Securities sukayi tsuru tsuru wasu nata kuka, se yanzu suke kara nadamar barin Almuqri'ah dasukayi ta fita a gidan...ko 10mnt ba ayiba da wayan Abdoljalal da shugaban sojoji motoci goma suka iso gidan, suka kwashe kaf securities din suka tafi dasu tantiri se zare ido yakeyi, yayi zawo a wando yafi sau goma. Aka bar wasu sojoji kusan su hamsin a masu gadin gidan nasa.


Yana shiga dakin nata ya zauna kasa zaman dirshen kmr karamin yaro kawai ya fashe da kuka, me tsanani, ya dafe kansa ji yakeyi kmr ransa ze fita. "Why? Why? Why pls? Meyasa kika gudunmin da cikina? Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!!''' Yaketa fadi yana fusgar gashin kansa kamar mahaukaci, ya koma ya kwanta kasan tiles din dakin, yana me karajin zuciyarsa kmr zata tsage sbda tsabar tashin hankali tunanikansa cak duk duj tsaya, tunaninta kadai zuciyarsa ke iya yi. "Bansan ina take ba...bansan meyasa kika gudunmin da cikina....wayyohhh Allah na zan haukace...zan mutu....!!!! Ya ilahi!!''' Yaketa kara fadi yana male-male a kasan tiles, ya rasa yazeyi, tinda uwarsa ta kawosa duniya be taba tsintar kansa a matasfa irin wannan da yake cikiba,yau kawai har ya fara tunanin mahaifiyarsa da mahaifinsa, tashin hankalin da yake ciki,ya fara tunanin anya ba bakin iyaye ne dashiba,, sbda bala'in ya shahara ya masa yawa,be saba daukar tension ba, amma tinda ya hadu da ita ya saba daukar bala'i, tinda ya dauki matsifar santa, gashi kuma ynzu ta kara masa matsifa wato mataifar rashinta.....




USA.
Dr mus'ab yazo kasar cikin aminci, tinda ya kawota asibitin rabonshi da ita se yau, yaga jikin nata Alhamdulillahi, tasamu sauki Sosai, har ta dan fara magana sosai, a kullum maganarta a kan Almuqri'ah ne,. Satin dr mus'ab uku a kasar, Ammah tasamu sauki sosai. 10:pm suna zaune a dakin asibitin da dr mus'ab da jarida nurse mami. Ammah na zaune kan gadonta na marasa lafiya, Allah ya rabata da wannan mugun ciwon na jikinta, wato blood cancer din datake dashi ada amma yanzu da aka mata juyen jinin shikenan ita da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login