Showing 81001 words to 84000 words out of 159314 words
Chapter 28 - Wata Kishiya Complete writing by Sa'adatu Bint Abdullahi .txt
mata kira amma ina tini ta nufa dakinta. Abdoljalal ya girgiza kai kawai yaso yataba nonuwa amma taki ta masa ciki black. "Ai zamu hadu ne..." Ya fadi yana nufar part dinsa.
Tana shiga dakinta idanuwanta suka sauka a knta zaune gefen gadonta, nan da nan gabanta ya yanke ya fadi jikinta ya dauki rawar tsoro ..."yau na shiga uku..." Al-muqri'ah ta fadi a zuciyarta yayinda zuciyarta ke luguden dakan turmin dukan dubu-dubu, idanuwanta suka waro waje alamar tsoro ya bayyana gareta..... "Daga ina kike..." Itace kalmar data fito daga bakin wadda ke zaune gefen bed din, duhu-duhun dake dakin sbda ba yarwar haske , hasken lamp ne, shiya hanani gano wacece....''
*vip 1000 normal group 500.... Transfer 0542703718 Saadatu Abdullahi gt bank.... Ko m.t.n card ko VTU duk ta wannan lambar 08101626484*
SAADATU BINTU ABDULLAHI (writer of Kyautar Allah)
Paid Page21
Jikin al-muqri'ah ya kara daukar rawa,jin tambayar data fito daga bakinta,duk tabi ta daburce, se yanzu take kara nadamar biye masa datayi suka kwana biyu can, ta rasa dalilin dayasa zuwa yanzu bata iya masa musu. Tsureta larai tayi da ido, dukda ba haske Amma ita tana ganinta sosai, larai ta hango tsoro da razana hadi da firgici a kan fuskarta, mikewa tayi ta nufa makunnin ainihin light din dakin ta kunna,haske ya yawaita a dakin, Al-muqri'ah ta kureta da ido, ita fa saboda tsabar firgici da gigita tasha hajiya saude ce ashe Larai ce, kawai tunaninta da lissafin hankalinta karanto mata Hajiya saude ya dingayi, ko dan itace a ranta oho. kuma kiri kiri tana gani tasan ba ita bace larai ce, kawaide tunaninta ne ke can gun sauden. seda ta sauke ajiyar zuciya da tunsni da hankalinta ya dawo gareta a lokacin fahimci larai ce, zuciyarta ta shiga dukan uku-uku ba kamar farko ba da zuciyarta ke dubar dari hudu-hudu. Yadda larai ta hango firgici da tashin hankali a tattare da ita ya bata tabbacin bazata samu abinda takeson sani ba a kan abubuwan dake faruwa kaf a kan idanuwanta a game da yarinyar da saraki. yanzu haka kwana biyunnan datayi, bata nan duk larai na ankare, kuma tana ganin sadda tashiga motar Abdoljalal, yaja suka bar gidan, ita kadai ta barwa kanta wannan abu data gani real Aini, labewa tayi tana gani ya bude mata mota ta shiga, tana hango soyayyar yarinyar a cikin idanuwan yallabai me gida, a ranar daya bude mata motar tashiga ta hango tsantsar san yarinyar a cikin idanuwan Abdoljalal. "Tashin hankali!" Kaf notikan kan larai sun kunce, so takeyi tasan meke wakana tsakanin Al-muqri'ah da saraki, domin tana sa musu ido sosai, kawai de tama kanta alqawari baza a tabajin mutuwar sarki a bakintaba, tin bata tabbatar dameke wakana tsakaninsu ba a halin yanzu tini tausan yarinyar takeyi, dole taji tausanta saboda Saude tafi wuta azabar zafi da rad'ad'i, musammanma inde a kan mijinta ne, zata iya aikata komi a kn mijinta,,kowa ma ya san da hakan. Karasawa kusa da ita larai tayi , ta Kamo hannunta, ta zaunar da ita gefen bed, ta juyo ta fuskanceta yayinda kan al-muqri'ah ke kasa, gani takeyi dasun hada ido da larai zata fahimci abinda ya faru tsakaninta da Saraki. Larai ta fara magana idanuwanta na kan al-muqri'ah data kara kyau se sheki takeyi fatarta na glowing saboda tasamu cream ne zallar kyau, da sabulun wanka me kyau duk saraki yasiyo mata, uwa uba kuma kulawar da sarakin ke bata na musamman ne Dole ma tayi glowing. "Kinaji yarinya magana nakeso muyi ki gayamin gaskiya kinji kou..." Cewar larai. Al-muqri'ah ta daga mata kai alamar eh, amma sede a kasan ranta ta fahimci kwanton mage Larai zata mata kuma bazata saki jiki ba, a ankare take, tin kafin tazo gidan an zana mata zance tsaf. Ba tare da larai taci gaba da magana ba ta tashi ta nufa kofar dakin ta rufe, kana ta dawo ta zauna tayi low da voice dinta ta yadda bame ji se ita al-muqri'ah din kawai, saboda larai tsoron ma daga murya takeyi, Dan wannan magana data fasu kwara larai Ajita a bakinta kwara ta mutu har lahira shi zefi mata alkhairi. "Dan Allah yarnan ina kikaje ne? Kwana biyu ina ziryar side dinnan naki naga banganki ba, ba nan kike kwana ba shin ina kikaje ne harda kwana?"' Larai ta jero mata tambayoyinnan, cikin kwarewa a jin kwakwaf da zallar munafunci. Al-muqri'ah ta dago ta kalleta jin tambayar datakeyi mata , nan da nan hantar cikinta ta kad'a da tashin hankali, tayi shiru yayinda gabanta ke dukan uku uku. Larai ta fahimci halin data shiga tini , nan take ta kara tabbatar da zarginta, ta tsure yarinyar da kallon mamaki, "kizo har gidan mace kiyitama mijinta shishigi har kuna fita da mijinta, mijin Saude bala'i saude mutsiba.. a matsayinki na yar aiki ban taba ganin inda akayi wannan karfin halin ba, barawo da sallama...miji kuma bana kowa ba miji na saude drum din yaukin ruwan mutsiba..." Larai ta fadi a ranta, ita da kanta tashiga tsananin tashin hankali, sbda tana hango ma yarinyar wulaknci nr tsanani. "Ina kike kwana ne yarnan ki bar amsata knji bakomai ki dauka tamkar ni na haifeki dan inada kamarki a gida, ni me dasa miki tarbiya ce daga inda iyayenki suka tsaya, d'a na kowa ne bawa kuma semeshi..." Cewar larai datayi mgnr cikin kwantar da kai, ita a dole se taji meke tafiya. "Kiching..." Al-muqri'ah ta fadi da bebanci batare datasanma ta fadi maganar ba, kawai ta fidda kai ce mgnr, a bazata ta fito. zamansu tare zuwa yanzu larai ta fara fahimtar maganganun al-muqri'ah dan haka tana fadin kiching ta fahimci me take nufi. Shiru larai tayi tana nazarin yarinyar, tasan karya ta mata. "Tabbas tinda ta boyemin akwai wata a kasa, kilama me afkuwa ta afku, in ba ma ta afkuba ina sukaje na tsawon kwanaki biyu....." Larai ta fadi a Zuciyarta me cike da nazari, ta riga ta fahimci akwai wata a kasa, ita kadaice kuma ta fahimci hakan a kaf gidan itama saboda tanata sa musu ido ne shiyasa ta fahimta, a ganinta kenan ita kadaice kesa musu ido. "Wannan shine matsifa..." Larai ta fadi a ranta, batare datasan maganar ta fito fili ba, al-muqri'ah ta dago ta kalleta jin abinda tace. "Matsifar me?'' Al-muqri'ah ta tambayeta da bebanci. "Matsifar dazaki sewa kanki da lafiyarki da kudinki..." Larai ta fadi a ranta amma a bayyane ta wayince tace "au zancen zuci ne ya bayyana,, kinga da mukayi waya da kanwata ne, nasamu wani mummunar labari, daya faru a kauye, wai makwabciyar knwatace ta kona kishiyarta da ranta bayan ta babbaka mata patrol ta kyasta mata ashana, nan take ta kone muruss, harta cinye kurmus ba wanda ya iya karasowa ya ceceta saboda matsifar shishiyar tata, to itace a raina shiyasa kkji nace matsifa, ina cikin jimamin abin ne kwarai da aniya..." Al-muqri'ah tatsureta da ido tana nazarin maganganun data gaya mata, dukda ita karamar yarinya ce, amma sede ta fahimci maganganun data gaya mata kmr ba gaskiya bane, akwai abinda ke kulle ga zuciyarta, al-muqri'ah ta bita da ido kawai. Larai taci gaba da magana cikin kwarewa, byn ta lura kmr yarinyar bata yaddaba, ta fahimci yarinyar nada tsananin wayau "wallahi dama seda aka gayawa matar kafin ta aureshi cewa kishiyarta bala'i ce kishiyarta matsifa ce, amma takiji gashi yanzu har abadan an karas mata da rayuwa, ina dadinta..." Al-muqri'ah tayi shiru kmr malam yaci shirwa , abinka da yarinta nan ta Yarda da labarirrikan larai, tini tunaninta ya juye ta tausaya itama. "Allah ya kyauta ya bata lafiya..." Al-muqri'ah ta fadi da bebanci, Allah ya kyauta din kawai Larai ta fahimta, ta amshe da "Amin...ai shiyasa bahaushe yace in gemun dan uwanka ya kama da wuta ka shafawa naka ruwa, Allah de ya rabamu da mummunar kaddara, dan ita ke jan wasu, ko kuwa daman ajaline yake kiran hansai oho, kinsan ajali shi kira yake...'' Al-muqri'ah tashiga jimami hadi da tausayawa ita hansai din da abin ya sameta, larai ta tabe baki hadi da mikewa bayan ta gama mata jirwaye me kama da wanka amma ita al-muqri'ah bata fahimta ba, setasha ko wanka ne tayi na soso da sabulu ta fita tass, ammafa a bayyane taga hakan a zuciyarta tana me juya wasu kalaman na larai. Har larai ta isa bakin kofar fita se kuma ta juyo ta kalli al-muqri'ah da tufafin jikinta, daman da batanan, duk seda ta bincike ko ina a dakin taga sabbin akwatuna da kayayyakin da Abdoljalal ya sayawa al-muqri'ah hakan ne ya kara sa larai a tunani tunani, hadi da nazarirrika, ba a tabayin me aikin dako kallanta me gida ya tabayi ba a kaf gidan, tsawan shekara goma larai na aiki a gidan, dan ita jurau ce, kuma tasan yadda take tafiya da saude shiyasa ta jima a gidan... Sosai fa larai tashiga tunani hadi da dasa ayar tambaya a kan yarinyar dame gida, daman tin zuwanta gidan ta fahimci gaskiya dole ne akwai wata a kasa. "Ki dinga taka tsantsan kina me tunawa da sharuddan hajiya mommy, kada ki bari ta kamaki da wani lefi koda da kwayar zarra ne, domin kuwa batada digon imani a zuciyarta...ina me baki shawarar daki kiyaye hajiya saude, domin itadin maciji ce amma fa wallahi dafinta yafi na maciji zafi..." Tana gama fadar hakan ta juya ta fice a dakin, yayin data bar al-muqri'ah da nazarirrika a kan kalamanta. "Tabbas na fahimci dafinta na iya fin na maciji..." Al-muqri'ah ta fadi a ranta, zuciyarta ta tsinke taji jikinta yayi sanyi a kan lamarin dake zaune da ita a gidan "Anya zan iya?'' Zuciyarta ta tambayi kanta, yayinda kalaman larai ke juyi a kwakwalwarta. Nan da nan damuwa ta hadu tama zuciyarta rubdugu, ta shiga tunano dalilan zuwanta gidan,,,seda tafi karfin 20mnt zaune tana nazarirrika a kan komi daya faru kama daga dalilan zuwanta gidan, har zuwa ynzu da kalaman larai ke neman rusa mata kwarin guiwa, Tasan tashiga wahala kawai, gashi bata da wanda zata gayawa damuwarta taji dadih, duk saboda kakarta tayi wannan abubuwan, amma fa zuwa yanzu bayan saboda kakarta tayi hakan gaskiya tana bautawa So amma ita bata fahimci ma meye san ba balle tasan tana bauta masa,,, kwanciya tayi hadi dayin lamo, tunaninnika dayawa na damunta a zuciyarta, kawai tana boyewa ne saboda an umarceta data boye din dole,. "Inaso insan a wani hali kakata take ciki..." Al-muqri'ah ta fadi a ranta, wannan damuwar na ya kakarta take ciki yafi komi daga mata hankali , kuma wannan shine dalilin silar yawaitar yin sallar dare,, domin adduarhta kenan daya tak a kan kakarta, tinda ta taso batasan kowa da komi ba se ita, Soyayyarta ce kadai take iya fahimta a matsayin soyayya. "Allah yasa kina cikin yanayinki me kyau Kakata..." Ta fadi hakan a ranta yayinda kwallah ya cika mata idanuwa nan da nan se kuka, ta dinga kuka da shashsheka....ta kai awa biyu tana kuka kana ta iya mikewa tama dakinta key, ta fada toilet ta dauro alwala, ta dawo dakin ta hau dadduma ta fara nafilfili, zuwa yanzu harta saba bata da abokin kai kukanta ko wanda take gayawa damuwarta se ubangijin sammai da kasai, saboda yafita sanin damuwarta, dama can ita bata gayawa kowa danuwarta se mahaliccinta, shike amsar kukanta kuma shike share mata, ko zuwanta gidannan tasan karfin adduarh ne da ubangijinta ya amsa a kn kakarta, bayan tayi kuka iya kuka, harta fawwalawa ubangiji hakuri da ran datafi kauna wato kakarta, se ubangiji ya kawo musu mafita rana daya tal, tana fatan zuwa yanzu insha Allahu ran abinda takeso ya kubuta daga wahala me tsanani bayan wadda abinda takeso din tashiga a baya, kawai so takeyi taga kakarta ko taji labarin a wani hali take ciki zuwa yanzu. "Nurse lubna..." Ita ta fado mata rai, nan tasakata a adduarhta , domin itama mutumce garesu, kuma baxata mantuba a zuciyar Al-muqri'ah.
** ** ** ** ** ** ** ** ** ** **
Garin Adamawa yola.
Yau ta kasance ranar juma'ah ce, bayan an sakko daga sallarh juma'ah. Dandazon mutane na hango a bakin babban get din gidan sarki kama daga jinsin mata zuwa jinsin maza,a kalla yawan mutanen yafi a kirga, yawan mutanen ya wuce tunanin duk wani mahaluki me lissafi da tunani a duniya, dukkaninsu nakasassu ne da marasa galihu, suke taruwa a duk ranakun juma'arh domin amsar temako me tsoka daga matar Sarkin Yola hajiya ummusalma, wanda ta jima tana bayarwa shekara da shekaru. ita da kanta ne tsaye a bakin kofar gidan yayin da take kallon komi dake wakana, tako ina an kakkareta da masu tsaro(securities). Sanye takeda hijjabi nevy blue har kasa. kallo daya zakama fuskarta ka tabbatar da tana cikin matsananciyar damuwa, fuskarta na dauke da damuwa me yalwa. Ma'aikatantanta dake dawainiyar raba taimakon a kalla zasukai dari biyu, maza dari mata dari, suke mikawa kowa daki daki lullubabbiyar takadda wadda ke dauke da kudade kimanin dubu hamsin hamsin, duk ranakun juma'arh setayi wannan sadakar, tana zama sikar yayewa mutane da dama damuwarsu, tana tawassali da wannan ayyukan nata datakewa mutane da damuwar da takeyi itama tana fatan ubangiji ya yaye mata damuwarta a kan danta tilo kwara daya tal, wanda zata iya sadaukar da komi nata data mallaka ta hnyar iyayenta a kn danta tilo., iyayenta sunfi mijin datake aure kudi na fitar hankali ma kuwa. Ma'aikata keta aikin wannan raban na zallar dukiya ba tareda gajiyasaba. wasu in sukazo su kawo matsalolinsu na ciwuwwuka da de sauran jarabawar rayuwa, in aka isar da kukansu ga hajiya ummusalma, tace a basu kudade da dama dazeyi musu maganin damuwarsu, a kullum da kanta take tsayuwa a gaban idanta akeyin komi saboda gudun kada ayi zalinci,tafison sako ya isa ga mabukata direct.
wasu daga yawancin mutane da dama, na zargin tana hakan ne saboda danta yaci shugaban kasa a nigeria, nan ko Allah kadai yasan zuciyarta, ita dazata rasa komi a batta da d'anta dase tafi farin cikin hkn a kan wannan yalwar arzikin da Allah ya mata....jiri taji yana neman kwasarta, dan haka ta koma ta zauna daga tsayuwar datake, nan take taji kanta yayi wani dum-dum kawai kamar an saukar mata da ruwan azabar ciwon kai, nan da nan kawai taji idanuwanta sun lumshe, cikin hanzari ta mike a daddafe kmr makauniya, hajiya Binta, wato wadda tafi kusanci da ita, jakadiyarta,, na ganin ta mike ta biyota a baya sauran masu taka mata baya sukayi kokarin biyosu hajiya binta ta dakatar dasu domin tini ta fahimci chanjin yanayin uwar gijiyarta. Karasowa hajiya binta tayi ta dafeta ganin tana niyar faduwa saboda ko gabanta bata gani, sosai. "Ki kaini part din baban jalalu..." Itace kalmar data fito daga bakin hajiya salma da kyar. "An gama ranki ya dade..." Cewar hajiya binta, ita ta kamota, suka nufo part din me martaba Sarki, tin kafin su karaso ya fito daga part din nasa cikin hanzari sanye da jallabiya. ya tarbeta domin yana daga window tin sadda take tsaye baking get tana kallon masu raba sadaka, yana kallanta har zuwa yanzu. Karasowa yayi ya amsheta daga rikon da hajiya binta ta mata wadda a kalla zata kai 60yrs. Dukawa tayi har kasa ta korowa me martaba gaisuwa, ina be samu damar ansawa ba, hankalinsa na kan iyalinsa farin cikinsa. "Salmanah ya akayi? Ko jikinne?'' Ya jefowa hajiya salma tambayar, saboda yau daman ta tashi batajin dadih, dama seda yace mata ma yau ta dakatar da bada sadakarnan ta bari se next friday amma taki. "Kaina ke ciwo..." Ta fadi idanuwanta na ciccikowa da kwallah, cikin hanzari ya nufa babban falonshi da ita, yanata mata sannu, ya tabbatar ciwonne ya matsa mata sosai, da bazata taba gaya masaba, tafi karfin 2weeks tana rashin lafiya a tsaitsaye ya tambayeta meke damunta tace masa bakomai, yayi-yayi a kira dr amma taki amincewa, to tabbas yanzu data bayyana ciwon yacita sosai ne. binta ta juya ta koma bakin get tana me jimamin halin da hajiya salma ke ciki, binta tasan komi, kuma kullum cikin adduarh suke a kan Allah ya karkato da ran Farin cikin uwar gijiyarsu gareta wato JALALUDDEN.
A kan kujerar 3st suka yada zango, yayinda hajiya salma ta kwanta ta daura knta bisa cinyoyinsa, kwance take kn cinyoyinsa amma yana jiyo heart beat dinta, dan haka hnklinsa ya kuma tashi, ya dauki wayarsa ya lalubo lambar Dr, bugu daya dr rabi'u ya dauka zuciya fal mamakin yau Sarki ne da knsa ke kiransa, be taba kiransa da knsa ba, sede yasa na hannun damansa wazo Zakinsa wanda shine aminin sarki kuma me masa hidima Umar sunansa,. Yana daga kiran Me martaba yace "kazo gida ynzu,.." Yana fadar hkn ya katse wayar. Yadda yayi maganar ya kara tabbatarwa da rabi'u ba lafiya. Ba bata lokaci ya iso gidan, direct part din me martaba ya iso, ya nemi iso aka masa iso, ya shigo bakinsa dauke da sallahma yana me karewa aljannarh duniyar falon kallo, an narka dukiya ainun a falon. Karasowa dr rabi'u yayi cikin hanzari ganin hajiya salma kwance kan cinyar me martaba kallo daya ya mata ya fahimci itace ba lafiya. Ba bata lokaci dr ya dubata kasancewar akwai kebantancen asibiti da komi na bukatuwa a cikin gidan, dr yayi mata allurori nan da nan tasamu bacci. Dr ya juyo ya kalli Me martaba wanda ke zaune gadon da hajiya salma ke kwance, yayinda dr ke zaune bisa kujera. "Dr meke damunta?'' Itace Kalmar data fito daga bakin Me martaba zuwa ga dr, cikin tsananin tashin hankali me martaban yayi tambayar. Dr ya fara da kwantar masa da hankali, dukda be fahimci meke damuntaba saboda ba fanninsa bane amma ya tabbayarda akwai matsala. Me martaba yace