Showing 144001 words to 147000 words out of 159314 words

Chapter 49 - Wata Kishiya Complete writing by Sa'adatu Bint Abdullahi .txt

kanta tanajin wani irin ni'ima a jikinta, lafiyar datakeji a jikinta tafi ta da. Ta tsurawa dr mus'ab wato detector ido, seta kalleshi kuma ta dawo ta kalli nurse mami, a fari tsoronsu takeyi amma zuwa yanzu ta aminta dasu mutanen kirki ne. "Sannu da jiki mama..." Cewar dr mus'ab. Ammah tace "Yawwah sannunku da hidima nagode..." Dr mus'ab yace "bakomai mama..." Ammah ta kure dr mus'ab da ido ta sassauta murya tace "Dan Allah kuyi hkri zuciyata na cike da tambayoyi,zan iya muku tambaya dan Allah?..." Tayi mgnr da hausar da bata wadacetaba. dr mus'ab yace "Eh mama zaki iya mana, muma zuciyoyinmu na cike da tambaya sosai a kanku..." Ammah tace "Dan Allah su waye ku? Ku temakeni ku gayamin ina jikata Almuqri'ah,, kunce ku ba macuta bane, na yadda, zuciyarta ta aminta daku, dan Allah karku sa zuciyata tayi rawa a kanku, ku gayamin ina jikata Almuqri'ah bani da kowa a duniya se ita, dan Allah karku cutar da ita kara ku cutar dani..." Ammah tayi maganar cikin tsananin damuwa, idanuwanta sukayi rau-rau da kwallah, fargaba ya cika zuciyarta, tana tsananin bktr san ganin Almuqri'ah, idanuwanta na tsananin yunwar ganinta.




Paid book ne
39
Dr mus'ab ya cire glass din dake idanuwansa ya ajiyeshi a gefe, ya tsurawa Ammah ido, jarida tabi dr da ido. Yayi kasa da kansa kana ya fara magana cikin kwarewa"Ki kwantar da hankalinki mama Almuqri'ah na nan Lafiya lau...xan sanar dake komi daga farkon haduwarmu daku har zuwa yanzu insha Allahu, ina fatan zaki fahimceni mama..." Ammah ta gyara zamanta tace "insha Allahu, inajinka ka gayamin,....." Dr mus'ab ya gyada kai hadi da fara magana cikin nutsuwa irin ta zallar yan boko. "Ni sunana dr mus'ab,ni dan garin yola ne, amma iyayena cikakkun katsinawa ne,, inada asibiti a yola,sannan inadashi a katsina state garin iyayena da kakannina kenan,, mun hadu daku ne a katsina, kun kai 8months a asibiti na keda Almuqri'ah baki da lafiya kina fama da blood Cancer, seda nazo naga halin da kike ciki na daukeki na kawoki wannan kasar ta America, na dauki nauyin aikinki aka miki juyen jini, har kusan 3tyms...toh Alhamdulillahi ansamu nasara kin samu sauki, wannan kuma jarida nurse ce wadda take kula dake da kuna asibitin katsina, a lkcin da bakya hayyacinki,, itama jarida ta bada gudumawarta a kanki duk watannin dakukayi a asibitin ita ke biyan kudin dakin asibitin dakuke kwance a albashinta, cin Almuqri'ah da shanta da take jinyarki duk ita ce,, Bata barku a katsina ba da muka nufo nan American ma da ita muka taho domin kula da lafiyarki, tana kaunarku saboda Allah, itama jagora ce, tayi temako da dukiyarta, kuma tayi da lafiyarta, muna kara mata godiya, ubangiji ya biyata da Alkhairi Yadda ta baro yayanta a nigerian da iyayenta tazo nan ta zauna tsawon 8month muna fatan Allah yajibnceta har ta mutu..." Ammah da tini ta fashe da kuka ta amshe da amin,a zuciyarta se jinjinawa Dr mus'ab da temakon dayayi mata takeyi, bashi ba har nurse mami ma ta jinjina mata. Ammah ta kara fashewa da kuka ta kalli Dr mus'ab da mami tashiga musu godiya tana kuka hadi dasa musu Albarka mara iyaka, "ashe na Allah suna nan
.." Cesar Ammah. Dr mus'ab yace "bakomai mama, ki kwantarda hankalinki....akwai wata magana kuma mama amma pls ki fahimceni wlhi ba cuta a zuciyata..." Jin yace akwai wata magana yasa Amma natsawa ta tsuresa da ido a zuciya se sa musu Albarka takeyi. Dr mus'ab ya fara magana kansa na kasa, sbda gani yakeyi kmr yayi mata lefi. "Ina me neman alfarma Daki yafemin na shiga huruminki da nayi duk da bansan ko waye kuba?na fara da neman yafiya.." Ammah tayi jim tana me tunanin meye dalilin Dr na neman yafiyarta, ta tabbatar da komi ze mata koda menene zata iya yafe mishi sbda temakon da yayi mata,. "Na yafe maka koma menene.. Amma Dan Allah ina jikata Almuqri'ah?'' Ta karashe mgnr zuciya fal rauni, se adduarh takeyi Allah yasa ba wani abu yasamu Almuqri'ah ba, mus'ab ke neman yafiyarta a kan hakan. Dr mus'ab yaci gaba da mgna knsa na kasa. "Tana nan cikin Aminci... Byn mun kawoki American,, na dawo nigeria na hada Auren jikarki da abokina Abdoljalal AASaraki..." Jin abinda dr mus'ab yace ya mummunar haifarma da Ammah faduwar gaba a fili ta maimaita "Aure!!!...Almuqri'ah akayima aure?" Ammah ta shiga tunani tunani, a zatonta ai yarinyar bata isa Aure ba saboda karama ce sosai,beci ace ta iya daukar d'ana miji ba. Dr mus'ab ya dago ya kalleta ya hango tashin hankali a kan fuskar Ammah, dan haka ya kara kwantar da murya yaci gaba da magana. "Ki kwantar da hankalinki mama wallahi bazan iya cutar daku ba, abokina ma data Aura sam ba Azzalumi bane, tare mukayi karatu nasanshi nasan gidan iyayensa,..." Ammah taji zuciyarta ta dan natsa jin klmn Dr mu'sab, ta kara aminta dasu mutanen kirki ne. Ganin ta dan natsa yasa Dr ci gaba da mgna cikin hankali. "Mun hada Auren nan ne badan mu cuceta ba wlhi, sedan temakon rayuka daga cikin hatsari, domin muna hango nasara ayin Auren, dan na fahimci ita yarinyar macece ta gari wadda duk namiji zeso samunta ga hakuri..." Dr ya dan dakata yana kallan reation din Ammah, wadda ta kara nutsuwa tana kallan dr hadi da nazarin klmnsa a cikin brain dinta na me hankali da tunani hadi da fahimta. Dr yaci gaba dacewa "Abokina Abdoljalal mutumin kirki ne sede be dace mace ba wadda tayi sanadin rabashi da iyayensa, ta rabashi da kowa nashi na duniya, nima ta rabashi dani se dan karfin kaddarar Aurensa da Almuqri'ah dake ta hannuna ya hanashi nesan tata yadda akeso...a kullum cikin dmwa da bakin cikin halin da Abdoljalal yake ciki nake kwana nake da tashi da dmwa, daga haka muka kulle da wazirin mahaifinsa kasancewar mahaifinsa sarki ne. Wazirin isma'il shima yana cikin dmwa sanadin damuwar da iyayen Abdoljalal suke ciki musammanma mahaifiyarsa da dmwar yadda aka rabata da d'anta ta tabata Ainun. A kullum cikin shawara muke nida waziri isma'il, muna nema ma iyalan na abdoljalal mafita, amma abu yaci tura har aka kwashi 10yrs yana tare da wannan muguwar mata tashi,, se daga bisani naga Almuqri'ah a asibiti na,, nasameta nace tazo office dina sukaxo ita da nurse mami, na gaya mata zan temakeki a kaiki kasar waje, amma da sharadin sede ta aure abolina Abdoljalal sannan ni kuma zan temaka muku... Ba tareda bata lokaci ba Almuqri'ah tace ta amince, sbda temakon lafiyarki da nace zanyi, danna fahimci tana tsananin kaunarki Ainun., a ranar datace ta amince nasamu ahamad ma'aikacin Abdoljalal na hannun damansa,da waziri, na gaya musu bukatata a kan hada Almuqri'ah da Abdoljalal aure,, waziri ya tambayeni meye dalilina nayin hakan,,na sanar dashi ina hango nasarar dazesa insha Allahu hankalin Abdoljalal ya dawo jikinsa, har ya koma ga iyayensa, kuma ya zama mutum tamkar ko wanni d'ana miji....na gaggayawa waxiri dalilaina masu karfi ya aminta,, a satin da aka fitar dake kasar American domin samun lafiyarki,..muka dawo gida Nigerian bayan an dauran Auren a kasa me tsarki., mukayi shawarar yadda za ayi Almuqri'ah ta tare a gidan Abdoljalal ba tare da matarsa dashi kansa sun san cewa ita din matarshi bace,,,nan ahamad ma'aikacin Abdoljalal ya kawo shawarar taje a matsayin me Aiki? Nace ta yaya? Ahamad yace ta hannun me kawo musu me Aiki gidan mesuna hajiya kande,, ba bata lokaci ahamad ya bani lambar kande, na hadata da nurse mami, nace ta gaya mata kaf gaskiyar lamarinmu a kn zuwan Almuqri'ah gidan Abdoljalal amma ta boye mata cewa dasa hannuna a ciki, ta nuna mata cewa itama wata takema aiki,, nurse mami batasha wahala ba a kan hajiya kande kasancewarta mayyar kudi, aka shirya mata komi taje ta kai yarinyar gidan Abdoljalal mukayi nasara kuma matarshi ta dauketa a matsayin me Aikin gidan,,bamu bari haka ba muka sa kande tasamu C.I.D a gidan sbda ta dinga fadin komi dake gudana. alhamdulillahi aka kaita Almuqri'ah cikin natsarar ubangiji komi ya fara settling ga Abdoljalal domin nutsuwarsa ta dawo garesa, sede har zuwa yanzu abdoljalal besan aure ne tsakaninsa da Almuqri'ah ba, Har yanzu akwai asiri me karfi a kansa wanda baze barshi ya Auri Almuqri'ah ba, sede yayita cewa beda yadda zeyi, amma kuma yanasan yarinyar, san da yayi mata ma be tabawa wata halitta a duniya irin saba Wallahi tallahi,, sannan ya kusanceta, harma yasamu ciki na farko da ita ya zube yanzu haka akwai ciki na biyu a jikinta wanda nake da tabbacin ta kusa haifarsa ma zuwa yanzu....ina neman yafiya a karo na biyu mama..." Dr ya fadi cikin sanyin murya byn ya karasa bata labarin, ya nisa. Ammah ma nisawa tayi, ta matukar tausawa a labarin da dr mus'ab ya bata na Abdoljalal, idanuwanta suka ciko da kwallah, tasan da zafi ka haifi d'a da cikinka amma a rabaku dashi wata can mace data tsincesa a sama,,,nan tashiga tunanin a wani hali kuma ita Almuqri'ah take ciki a zamanta da wannan kishiyar tata Azzaluma da dr ya gaya mata. "Bakumin komi ba wallahi,godiya ya dace na muku...,, ni musulma ce ta gaske na yadda da kaddara, duk abubuwannan dasuka faru rubutaccen ubangiji ne, sanadin hakan ne yasa kaddara da rabo suka baro mu daga kasarmu muka dawo wannan kasar muma..." Dr mus'ab da mami wato jarida suka hada baki gun cewa "Haka ne ...." Ammah ta sauke numfashi tace "yanzu ya ita jikar tawa? Kuma shi d'an ya koma ga iyayensa?"' Dr mus'ab yace "Alhamdulillahi take, tana cikin Aminci insha Allahu,,,, be koma ga iyayen nasa ba gaskiya, amma ko a haka ma Alhamdulillahi Mama, tinda yanzu shi Abokin nawa yadawo hayyacinsa ba kmr a farko ba, sannan ga haihuwa yasamu a tare da Almuqri'ah abinda basu taba samu ba da ita saude,... mungode mungode, dole mune zamuyi godiya baku ba mama..." Ammah ta jinjina kai hadi dacewa "aah muma dole muyi godiya, kuma ni Alhamdulillahi da warakar wannan bawan Allah tazamo a garemu, Allah ya karo dumbin nasara..." Duk suka amsa da Amin. Dr yaci gaba da magana "Mama ki kara kwantar da hankalinki insha Allahu in kika gama warwarewa zamu koma nigeria zansan dabarar dazanyi Ku hadu da Almuqri'ah insha Allahu, domin har yanzu Shi Abdoljalal besan ni na tsara komi ba, shiyasa bazeyu ko mun koma nigeria ba ku hadu farad da garaje, Amma insha Allahu zanyi kokarin hakan saboda itama nasan tunaninta da hankalinta na kanki, danma tin kafin taje gidan na kwantar mata da hankali tare dace mata zaki samu sauki insha Allahu, shiyasa nasamu hankalinta ya kwanta,,," Ammah tace "Bakomai wlhi, Allah de ya kareta, ya kuma basu zmn lafiya ita da mijinta, ya karya mulkin zalinci dan Alfarmar Annabi SAW,,," duk suka amshe da Amin.nurse mami ta kalli dr ta kalli Ammah yayin da dakin ya dauki shiru kowa da abinda yake sakawa da warwarewa a zuciyarsa. "Mama ki bamu labarinku munasan musan kuma su waye?'' Cewar nurse mami.
Dr mus'ab ya dago ya kalli mami shima yanada bukatar hakan Amma beso ya takura mata danma ya fahimci tanada fahimta sosai, sannan da gani tanada ilmin Addini ga hankali wadatacce (danko da ilmi seda hankali). Ammah ta sauke ajiyar zuciya sam batasan tunano rayuwarsu kwata-kwata. Dr mus'ab ya kureta da ido, yadda tayi shiru ya bashi tabbacin akwai mummunar kaddara a cikin labarin nasu. "Mama munaso musan waye ku, saboda yanzu an zama daya, ki daure ki bamu labarinku..." Ammah taja ajiyar zuciya hadi dayin jim tace "Hakane....mu cikakkun haifaffun yan sudan ne, iyayenmu da kakanninmu duk yan sudan ne," se kuma Ammah tayi shiru. dr mus'ab ya amshe da "yawwah Almuqri'ah ta sanar damu haka nida nurse tace mana ku yan sudan be, sede bamusan ya akayi kukazo nigeria ba bata sanar damu haka ba, sannan haka aka haifa Almuqri'ah da bebanci?'' Ammah ta daga masa kai alamar eh hadi daci gaba da basu labari "Mahaifanmu ,mu uku suka haifa a duniya, nice babba, se kanwata Fad'ima, se kanina Aliyu haidar,,, kuna fahimtar hausana sosai kou?'' Ammah ta dakata da lbrin da tambayarsu sbda hausarta kwata-kwata bata fita yadda su suke hausa. Dr mus'ab da mami suka amsa da A,,," a lokaci guda.. Ammah tayi ajiyar zuciya kana taci gaba da labari. "Mu uku iyayenmu suka haifa suka rasu, tin muna kanana, suka barni da kanne na, ni na rikesu, kasancewar iyayenmu nada tsananin arziki sam bamu nemi komi mun rasa ba, munyi karatun Arabiq dana boko. Kana nazo nayi Auri wani balarabe dan makka, na haifi d'ana miji mesuna khalid, daganan ban kara haihuwa ba, har d'ana yayi 8yrs, kana kanwata tayi Aure , haihuwar farko ta haifa diya mace Ummukhaltum, gun haihuwar ummukhaltum yar uwata ta rasu, ya kasance ni na rike ummukhaltum,bamu da kowa kaf kakanni da iyaye duk dun rasu. Da ummukhaltum ta girma na hadasu aure da khalid wanda ya tashi da kwazon neman na kanshi, yayi arziki na fitar hankali,, kanina haydar ya zamana shi karatun da yayi ya tashi a banza ya fad'a halakar shaye-shaye, duk sati seya cemin beda kudi na bashi, to dayazo yaga d'ana Allah ya dagashi yayi kudi na fitar hankali, shikenan kullum seyazo yace in bashi kudi se in bashi, wata rana dayazo gidana a buge yace na bashi kudi, naki bashi nasa masu gadi suka fita dashi se zagina yakeyi saboda naki bashi kudi, daga haka ya kullaceni ya dena ko zuwa ya tambayeni kudi, abinka da jini sede ni nake aika masa da kudi time to time, sam baya amsa sena kyaleshi,, , kafin mu Ankare ya zama babban d'an ta adda wanda Kaf sudan suka sani, amma ni sam ban damu ba se rayuwata nakeyi cikin iyalina ina ma hydar adduarh da kaddarar data samesa domin komi rubutacce ne daga sarkin da baya kuskure, koda na damu ban isa in chanzawa hydar khaddararsa ba...munata rayuwa da iyalina har Allah yabawa ummukhaltum ciki ta tashi haihuwa ta haifi Almuqri'ah yarinya me tsananin kyau, ana haihuwarta nasa mata Almuqri'ah,,, data kai 7month muka fahimci akwai matsala a harshenta domin ko gwaranci batayi, har takai 9month bata uhum ba um-um, sede kullum baki gum tana kallan kowa da ido kawai,,muka neme mgni tin a wancan lokacin amma sam ba a dace ba, wani malami ya taba shedamin iskokai ne suka shigeta tin tana ciki, kuma yace duk maganin daza muyi whlr banza zamuyi baza muci nasara ba, amma ya shaida mna akwai ranar da bakinta ze bude tass ranar da daya daga iskokan dake kanta ta fita wato ita wadda take bebiyar kenan...da mukaji hkn muka fawwalawa Allah, muka ci gaba da rayuwa cikin yadda da khaddara me kyau ko mara kyau,, da Almuqri'ah tayi 1yrs , iyayenta suka rasu duka ta hanyar hatsarin jirgin sama, zasuje ibada kasa me tsarki, da Almuqri'ah sukayi hatsarin amma sam ita ba abinda ya sameta a gefe ma aka sameta kwance ko kurjewa batayi ba...aka kawomin gawawwakin yarana aka musu wanka aka kaisu makwancinsu, na dauki kaddara nayi musu fatan samun kwanciyar hankali a makwancinsu na gaskiya. ..muka ci gaba da rayuwa a katafaren gidan mu, har Almuqri'ah ta kai 8yrs duk tanata zuwa makarantar isilamiyya da boko, tin a 8yrs tayi saukar Alqur'ani me girma kasancewarta me tsananin hazakha, tanada 9yrs ta gama primary scul sbda kwazonta da hazakarta. A lokacin duk muna cikin daula saboda mahaifinta ya bar dukiya da gidaje da har mu mutu baza muyi talauci ba insha Allahu,, a haka har Almuqri'ah ta kai 12yrs zuwa lokacin ta gama JJSS, tana shiga SS1 na fara fuskantar barazana a gurin kanina hydar wanda zuwa yanzu ya kara shahara ya zama babban dan daban da kaf kasarmu ke kara tsoronsa ko hukuma bata ja dashi. Ya dingamin barazana kan in ban kawo masa kaf dukiyar da mahaifin Almuqri'ah ya bari ba ze kashemu nida Almuqri'ah duka,,senaji tsoro na kwashi rabi na kai masa, muka samu ya shafa mana lafiya, Almuqri'ah taci gaba da karatunta cikin gata a jirgin sama ma ake kaita scul saboda tsanar dukiya da ubanta keda shi...tin tana 12yrs ta iya komi na girki, saboda na koya mata, ta iya komi kwarai, ga ilmi ga komari, tana SS2 ta zana Jarabawar fita zuwa makarantar gaba,, kwatsam muna zaune a gidanmu sega hydar da mukarrabansu, ya nunamin wuka ze kasheni, ya dinga zagina wai na masa karya na bashi dukiya kadan, dan haka yanzu ze kwace komi da Khalid ya bari a doron duniya...aiko hkm yayi ya kwace komi yasa aka jefomu a jirgi aka kawomu nigeria garin Abuja, to bamusan kowa ba a abuja, dan haka muka fara bara,,daman tin tini inada blood cancer amma abin beyi kamari ba seda mukazo nigeria saboda bani da yadda zanyi insha maganin ciwon, yazamana abinci ma da kyar muke samu muci, Se munyi bara, kayan jikinmu ma se munyi bara muke samu,, muna barar na fara matsanancin ciwo, gashi bamu dako daki a titi muke kwana a bakin hanya,, tin ina iya tashi har nazo ban iya tashi, kaf jigilata Almuqri'ah keyi wadda maza keta kawo mata hari da iskanci amma inata kafa-kafa itama tanata kafa-kafa da mutuncinta. tin ina sanin inda kaina yake har yazamana ban gane mutane sosai sbda ciwo daya fara cin karfina,, ana haka wani bawan Allah yazo bamu bara yaga halinnda muke ciki, ya daukemu a motarsa ya kawomin asibitinka aka dubani akaga abinda ke damuna, yace ze biya kudin komi amma se Almuqri'ah ta yadda ya tare da ita, ni kuma nace inta amince wani yayi amfani da ita ba mijin Aurentaba Allah ya isa ban yafe mata ba... Fir taki yadda da mutumin ganin hakan yasashi kin temakonmu sbda besamu abinda yakeso ya samu ba a jikin Almuqri'ah...kunji yadda labarina ya kasance, munyi rayuwar kankaci a kasar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login