Showing 60001 words to 63000 words out of 159314 words
Chapter 21 - Wata Kishiya Complete writing by Sa'adatu Bint Abdullahi .txt
suna gama mata abinda zasu mata suka fice a dakin, sunata yabawa da kyaunta hatta dr seda ta yaba da kyaun nata.
Al-muqri'ah ta koma ta kwanta tanata Allah Allah ya dawo, dan tsoro ma takeji ya tafi ya barta ita kadai,. Dr din da nurses basu jima da fita ba ya dawo sanye da manyan kaya na Alfarma wadanda suka amshi launinin jikinsa ga kamshi yanata zubawa tako ina,. Dagowa tayi ta kalleshi shima itan yake kallo ba karamin tsananin kyau ta masa ba, hijjabin ya amsheta ainun,. Ita knta taga kyaunsa sosai, daman deshi me kyaune ta fahimci hakan tin ganinta dashi na farko. Karasowa yayi hannunsa rikeda ledoji ya ajiye yana fadin "Me kyauna knyi kyau sosai...." Murmushi ta sakar masa, hadi da masa godiya tace shima yayi kyau da bebanci... Abdoljalal ya karaso ya zauna cikin nishadi da farin ciki,, shima ya mata godiyar kyaun datace yayi.. Ya kalli hannunta yaga an maida mata wani drib din se yanzu ma ya lura saboda hankalinsa na kanta be kula ba sam "dr ya shigo ne?''Abdoljalal ya tambayeta. Al-muqri'ah ta amsa da "A..." Yace "Okay ya kikejin jikin dasauki!'' Ta daga masa kai alamar eh , yace "Allah ya kara sauki..." Ta amsa da amin, duk suka sakarwa junansu murmushi a lokaci guda. ...
Wata iriyar kulawa yake bata ta musamman a zamansu a asibitin, hadi da tattali, da zallar kimar mutumcin SO, yabi ya maidata wata narkakkiya se narke masa takeyi,. satinsu daya aka sallamesu suka koma gida, ma'aikatan gidan duk suka zuba ido, gulma ajali in ba ayi ba a mutu, amma fa wannan gulmar sede gani kawai. seda duk suka gwale ido sukaga komi.... Har dakinta ya rakata ya kwashi kayayyakin daya siyo mata danya mata sabon shopping. ya kai kayayyakin dakinta da kanshi ya hanata daukar komi ma'aikatan gidan na kallo a kan idansu akayi komi, tantiri kam ai baki da jiki tini duk suka mutu, amma shifa yasawa ranshi kawai tausayintane yasa oga keyi mata hakan, danshi yanada tausayi shiyasa yake bata kulawar nan, amma fa dukda haka kulawar tayi yawa,... " tantiri ya fadi a zuciyarsa, amma fa har yanzu yana cikin kwad'ayin yarinyar, kuma shi inde miyaunsa ya tsinke tabbas seya maida yawu.
Al-muqri'ah ta masa godiya, bayan ya gama kwaso kayayyakin suna zaune gefen bed shida ita, amma sunada dan tazara da juna, duk yadda ya kaiga jin sha'awarta har suka gama zaman asibitin ko tabata beyi ba, dukda yana azabtuwa amma haka nan yake jurewa da matsewa yake maida kwad'ayinsa, amma fa duwawu nashan kallo. Abdoljalal ya kureta da ido sam be gajiya da kallonta, har wata kiba tayi na kulawar daya dinga bata a asibitin tayi fresh wahalalhalun rayuwar dake tattare da ita suka fara gushewa tini zallar kyaunta harya fara bayyana, kasannan nata ya kara cika fam wato duwawukanta, sun kara bayyana, ta kara yin kyau da ita, takai mace ta riga ta kama kasa. Godiya ta masa na hidimar daya dingayi da ita a asibitin kanta na kasa. "Banasan kinamin godiya ai rance na baki zaki biyani nan bada jimawa ba....." Abdoljalal ya fadi yana wani karewa jikinta kallo kasa-kasa. Al-muqri'ah ta dago ta tsuresa da ido, jin yace wai zata biyashi... "Ni ai banda abinda zan biyaka..." Ta fadi hakan da bebanci. Abdoljalal yayi murmushi yace "Kinadashi mana ..." Al-muqri'ah tayi jim kana tace "ina yake?'' Da bebanci. Abdoljalal yace "in kika kara samun sauki zan nuna miki inda yake..." Al-muqri'ah tayi shiru hadi da shiga nazari tace " aah ya gaya mata yanzu..." Abdoljalal yaki yace "Me kikeci na bakinki na zuba,, in kika kara samun sauki zan nuna miki ai zaki biyani kou? Tinda kinada kayayyakin biya sama da kasa..., gana tsakiyama duk kinadashi. ....'' Al-muqri'ah da bata fahimci me yake nufi ba tace masa ehh zata biyashi..... Tashi Abdoljalal yayi da niyar barin dakin yace ta huta kuma karta ci gaba da dafa masa abinci ta bari se ta kara samun sauki..... Yace kuma ta dinga fesa maganin sauro na fesawar daya siyo... Al-muqri'ah tace toh ta kuma masa godiya, Abdoljalal yace "Zaki biya ai...." Al-muqri'ah ta daga masa kai alamar toh... Abdoljalal ya fice a dakin zuwa side dinsa samshi ko abinci beci dukya rame inyana ganinta sam bejin yunwa. A zamansu a asibitin al-muqri'ah ta fahimci Abdoljalal mutumin kirki ne kuma shakuwa ta kara shiga tsakaninsu me tsanani , ta faraji a zuciyarta zuwa yanzu ba abinda bazata iya ma Abban nata ba, danta faranta masa, kome ma zatayi masa tasan bazata biyashi ba, dawainiyar daya dingayi da ita a asibitin har kayanta ya dinga wanke mata abinda be tabayi ba, ko kayansa be taba wankewa ba tinda yazo dunita sede boxes kadai yake wankewa kansa, amma ita kullum data cire kaya ze wanke a zamansu a asibitin.. Al-muqri'ah ta kuma fadawa kogin soyayyar Abdoljalal ba tare data sani ba, amma ita knta ta afka kogin da yake ciki tsundum ya koyar da ita sanshi kuma tini ta dauka.
8:am da talatainin safiya saude zaune a falonta, Yayinda larai ke tsugunne a kasa, fuska dauke da tsoro, hajiya saude ta zuba mata ido se faman girgiza kafafuwa takeyi, sanye take da wata buhun rigar atamfa abuja bubu, a kalla yanzu turmin atamfa biyu hajiya saude keci, ta kara tafka wata uwar rusheshiyar kiba, ta kuma dunkulewa rigijiji, ga uwar uban dukiyar kumatunan nan nata sun kara subutu subutu kamar fanje yaji yis, bakinnan nata ya kara zungurere dashi, kamar na biri gashi baki kirin kmr na yan shaye shaye,, hankalin hajiya saude kwance se kara rushewa takeyi tana tarwatsewa kamar chin-chin yaji kayan hadi. "Ina shi usman din danace ki kirawoshi ku taho tare..." Cewar gimbiya madam Hajiya saude, tana magana kumatunan nata na motsi, yayin da nonuwannan nata suka kara uban tsawo har sun wuce cikinta sun kai cibiyarta, kmr de sideden silifan, tumbinnan nata ya kuma kara uban fadi da tsawo, data zauna tumbin ze zauna shima a kn cinyoyinta rigijib. Jikin laure ya kara daukar rawa daman ita tinda akace mata wai hajiya na kira yau da sanyin safiyarnan ita da bata tashi da wuri amma yau ta tashi da sanyin safiya. larai ta gama yadda da yau akwai tashin hankali ta riga ta sadakarma kwan baya gurbi ne ze fashe, in ko ya fashe seya addabi uban kowa da wari har wadda ta fasashi. "Eh yacemin ynzu zezo saboda oga yasashi wani aiki ne shine yake dan karisawa..." Cewar larai, Hajiya saude ta bude baki zatayi magana usman ya iso yayi sallama ta masa iso ya shigo shi knsa gabansa faduwa yakeyi saboda kiran saude ba Alkhairi bane. Zubewa usman yayi ya fara koro mata gaisuwa ba tare data amsaba ta gyara xama, hadi da gyara zaman dankwalin dake knta ta turo shege gaba, ta chuno dogon bakin bakinta kana ta fara magana cikin ruwan wutar bala'i. "Kai dan bura ubanka har wuyanka yayi kaurin dani zanyi kira kazo kace wai, kana karasa aikin Abdoljalal ne...” nan take usman ya shiga bata hakuri daman yasan za ayi haka, domin ya lafiyar kura balle tayi hauka, inda sabo kowa ya saba da zagin hajiya saude. Kwafa saude tayi hadi dacewa ina dai-dai da zamanin ko wani dan tsinannan me aiki a gidannan..." Duk suka hada baki gun Cewa "Allah ya huci zuciyarki..." Ta kuma yin kwafa, hadi da gyara zama irin na masu isa da duniya wadanda basu san akwai mutuwa ba. "Daman na kiraku ne in tambayeku, amma inaso duk ku gayamin gaskiya, domin in har kukamin karya na gano hakan a karshe wanda yake lahira ma seya fiku jin dadih,, kundesan wacece sauden saraki ba imani bane ya yawaita a zuciyata..." Usman da larai suka hadiye wani mugun yawu na tashin hankali suka juyo suka kalli juna, kana duk suka amsa da zasu fadi gaskiya, zuciyarsu se dukan dari uku uku takeyi, saboda basu san mezata tambayesuba. Saude taci gaba da magana, tana karkata akalarta ga usman. "Zan fara ta kanka kai usman kana jina kou...." Usman ya amsa da "A, ranki ya dade..." Har jikin usman din na rawa. Hajiya saude taci gaba da magana tana tsaresa da yan mitsilayen idanuwanta na harijai. "Kai usman kafi kusanci da bangaren mijina, ya kake ganin mu'amalarsa da wannan me dafa masa abincin, aikinta takeyi ko kuma de tana shigarmin harka mijina saraki? Dannasan de shi mijina ko kallon bnza bata isheshi ba,ni nasan mena taka a kanshi....” usman ya hadiye wani yawu kana ya saita kansa ya fara magana cikin kwarewa, "Ai ranki ya dade knsan de waye Alhaji saraki, ina .e tabbatar miki dako kallo ma wannan yarinyar bata isheshi ba, zan iya ce miki ma basu cika wani haduwa dashiba, shi yamafi zama a saman benensa, in kinga ya sakko abinci zeci, kuma daya Ci abinci shikenan seya koma sama..." Usman ya fadi ne kawai dan gaskiyar bazata fadu ba, amma shima ya fara fahimtar abubuwa, yana gani oga na shishigewa yarinyar.."wawuya jaka in banda wawanci ke kya dauko wannan dankwalin kice mijinki baze kalletaba..." Usman ya fadi hakan amma fa a can kasan ransa. hajiya saude ta sauke ajiyar zuciyar maganganun usman danta kula shi ustazi ne baze mata karyaba, nan da nan ta fara aminta da kalamansa, mummunar mafark tayi yau taga mijinta tsaye da wannan yarinya me aiki sunawa juna kallon So da kauna shine hankalinta ya tashi ta gaza komawa baccin ma yau gabaki daya, amma fa tasan kawai sherin shedan ne ke bibiyarta koda yake itama da knta tasan tafi shedan sharri. "Ka tabbata usman? Dan wallahi inna fahimci wani abu akasin abinda ka gayamin wallahi gidan nan ya mana kadan nida kai..." Cewar saude. Usman da gabansa ke dukan uku uku ya juya ya kalli larai ta daga masa kai cikin kissa alamar yace ehh ba tare da burunguzuma ta fahimtaba.. "Tabbas ranki ya dade duk cikin kalamaina babu karya, wannan magana gaskiya ce, shi yallabai fa ranki ya dade be ganin kowa a duniya seke,..." Usman ya karisa maganar hadi da zuzuta ta, danso yakeyi su gama lafiya shi da ita, dan kowa yasanta da shegen kishin bala'i. Hajiya saude tayi murmushi jin abinda usman yace kana tace "Ko ya akayi kasan haka usman?'' Usman ya tunano wata karya kana yace "Ai ranki ya dade knsan na hannun damansa, Ahamad dinnan aminina ne, shiya gayamin yacemin wallahi duk kamfanonin oga ko sakatariya beda ita mace, saboda kawai matan ma duka basa gabansa, to yanada kema mezeyi da wata mace a duniya, ubangiji fa shi kadai yasan halittar daya maka miki, ai yanayinki ya wuce misali ranki ya dade, surarki ta wuce me hankali..." Larai ta kalli usman danta fahimci magana yama sauden cikin magana amma Hajiya saude bata fahimtaba sema ta shiga nishadi mara misaltuwa. "Alhamdulillahi,,, toh yanzu zan baka wani aiki na kulamin da yarinyarnan a kn mijina, insha Allahu ni nasan mezan maka..."cewar hajiya saude. Usman yace "an gama ranki ya dade..." Hajiya saude tace "yawwah jeka tokai na gana da kai, duk abinda ka gani ko ake ciki ka dinga sanar da larai tana gayamin ko kazo ka sameni...da kaga akasin abinda nakeso kazo ka gayamin..." Usman yace "toh angama ranki ya dade..." Ya mike ya bar falon yana godiya ga Allah dasuka rabu lafiya, seda yayi nisa da side din kana yace "wawuya duk wayanki kinyi ya ubangijinmu ne... Insha Allahu se munga karshenki, bi izinillahi se oga ya auro mace, danke ba mace bace, baki da maraba da botoramin film muguwa kalarki kalar zuciyarki, in ba ma kaddaraba me oga zeyi dake... Dan dagani ke bakar kaddarace a gurin oga ...." Usman ya kyakyale da dariya shifa gabaki daya halittar matarma dariya take bashi. "Burunguzuma kenan....wai!!'' Usman ya kara fadi yana tafe yana dariya.
Usman na fita hajiya saude ta dawo da dubanta da hnklinta kn larai tace "Toke ina jinki, ki gayamin gaskiya ya aikin dana saki, ya rayuwar mijina da yarinyarnan?'' Larai ta gyara zama hadi da gyaran murya tace "Yawwah hajiya knsan de gaskiya dayace kou, toh ita zan gaya miki, in kn amince..." Seda gaban hajiya saude ya fadi jin abinda larai tace. "Eh na amince ki gayamin...Ai gaskiyar nakeso ki gayamin larai...." hajiya saude ta fadi yayinda zuciyarta ke tsananta bugun da batasan na meneneba, ta kara kure larai da ido.... Har larai zata bude baki tayi magana hajiya saude ta dakatar da ita dacewa "Ki fito fili pls ki gayamin gaskiya larai dan Allah, ni knsan inde a kan mijina ne banda hankali, kawai ki gayamin gaskiyar meke faruwa da mijina da yarinyar nan..." Saude tayi maganar da kwantacciyar murya yauce rana ta farko da larai taji saude tayi magana da kwantacciyar murya batasan tanada kwantacciyar murya ba se yau.
*pls a bar fitarmin da littafi dan Allah...*
Vip 1k normal 500 0542703718 Saadatu Abdullahi gt bank shedar biya ta nan 08101626484 ko M.T.N card.
SAADATU BINTU ABDULLAHI (writer of Kyautar Allah)
Page 16
Larai tayi kasa-kasa da murya irin ta gulma da munafunci kana ta fara zayyano zance. "Yooo ranki ya dade yallabai mezeyi da wannan yarinya me siffar jinnu wal-insu, ai ranki ya dade ki tsoma ranki a ruwan sanyi kawai, ki maya wankan tsarki da ruwan kankara, kiyi bacci ki huta, yar hutu jikar hutu, babu wani abu ko makamancin abu a tsakaninsu da wannan me aikin, in takaice miki ma hajjaju ikon Allah ai shi Yallabai ma kyamar yarinyar yakeyi....." Hajiya saude tayi bending a kn kujera hadi da sauke nannauyar ajiyar zuciya, tasha wata matseefar larai zata gaya mata akasin abinda usman ya gaya mata. "Amma larai har kinsa gabana faduwa nasha akasin kalaman dasuka fito a bakinki zaki gayamin, wallahi har zazzabi ya fara rufeni..." Cewar hajiya saude da zuciyarta, ta kuma kwanciya saboda kalama larai dana usman data hada a kanta. Larai ta watsa hannu hadi dacewa "Ah'ah ranki ya dade, ai wannan magana da usman ya gaya miki kaf gaskiya ce, ko digo daya na karya babu, shiyasa nima na kara tabbatar miki da gaskiyarnan bisa gaskiya,,, ranki ya dade kmr fa cewar usman ne ke kadaice a gidannan, kuma har abadan ni banga alamar oga ma nada lokacin wasu banzayen mataba... Yooo Allah ya temakeki ta ina ma oga ze jajibowa kansa wahala, shifa ba ruwansa kwata-kwata ko mu nan masu aiki in muka gaidasa bema kallonmu...." Nan take Hajiya saude ta karajin zuciya da hankakinta ya kwanta luf a kan mijinta ta kuma sauke ajiyar zuciya, ta furzar da iskar nishadi. "Naji dadin kalamanki larai,, ni daman nasani mijina mezeyi da wata bayan duk na kulle ko ina a birnin zuciyarsa dazega wata mace, kawai shedanne ke dorani a kan wasu tunani tunani..." Larai ta amshe da "Ranki ya dade ki kori tunani tunanin, ki kwanta kiyi bacci, ki kara hutu bisa hutu, wannan maganganu nawa babu na karya a ciki, ai yadda kikasan bola haka mijinki ke kallan me dafa masa abincinnan, yoo hajiya meze kallah a jikinta wanda be kallah Ba a jikinki..." A wannan karan seda Hajiya saude tayi murmushi, yauce rana ta farko da larai taga nurmushinta a duniya, larai ta fuskanci daman tini karya tafi mata dadih a kan gaskiya. "Aiko karyar zamuyita shirga miki bakar daga...." Larai ta fadi hakan a zuciyarta. "Allah larai kice nima kyakyawa ce ta last class..." Hajiya saude ta fadi tana karewa knta kallo ita a dole ga kyakyawa. Larai ta dago ta kalleta dariya ta tarun mata a wuya amma dole ta hadiyeta tace "Tsananin kyaune dake ranki ya dade, ai kyaun naki ne da SO ya hana Alhajinki gigin kallon wata, haba ranki ya dade ai ko kusa ma karki kara kawo tunanin Daddy ze iya kallon wata ko wacece ita, ki kwantar da hankalinki...." Hajiya saude ta kara shiga nishadi da farin ciki zuciyarta ta kuma nutsuwa tsam a guri daya a kan mijinta.."toh shikenan larai, amma fa kici gaba dasamin ido de a kansu ko za a samu wata jaridar akasin wannan da kika fayyacemin yanzu...." "Aiko an samu bazata saiduba domin wannan jaridar ko me saidata ma se kiyi ajalinsa...jaridar bakin jini ne da ita..." Larai ta fadi a can bedroom din zuciyarta. , amma a fili tace "Ai ranki ya dade baza a taba samun ma wata jaridar akasin wannan ba, kin de sanni dasa ido hajjaju to tsawan lokacinnan banga komi ba, wannan jarida dana sauke miki ita yanzu ita nagani kuma ita kowa yagani..." Hajiya saude ta kara sakankancewa zuciyarta ta fita a wasi wasi. "Toh shikenan larai tashi ki tafi abinki anjima kizo zan baku babban tukuici keda usman, maganganunku sun sani a ni'imar nishadi, saboda ni mijina shine duniyata...." Larai tace "Toh ranki ya dade, mungode Allah ya saka da Alkhairi Allah y kara arziki, Allah yasa daga ke ba kari..." Saude ta amshe da fadin "Ai dagani din ba kari ne na har abadan..."tayi maganar cikin tabbatarwa. "Jahili jahili ne...." Larai ta fadi a ranta domin duk jahilcinta tafi saude ilmi yaza ayi ace Allah ki kawo wani zancen bnza kuma. "Insha Allahu kuwa hajiya, ai kin kulle ko ina da ko ina Ni'imar da Allah ya miki dabance..." Larai ta fadi hakan a bayyane. Saude ta kara shiga nishadi, ita da knta tana tabbatarwa da kanta, mijinta be isa ya kalli koda wata mace ba balle yasota da Aure. "To ta ina..." Saude ta fadi a ranta, yayinda nishadinta ya yawaita, larai ta mike ta bar side din nata Ita fa larai tama fara tunanin hajiya saude bata da hankali, in ba rashin hankali ba, ke ba zuwa bangaren mijinki kikeyi ba, ke