Showing 150001 words to 153000 words out of 159314 words
Chapter 51 - Wata Kishiya Complete writing by Sa'adatu Bint Abdullahi .txt
taji ta kamu da tsananin san yarinyar da abinda ke cikinta. Kusan 1h suna tsaye bakin kofar dakin haihuwa hajiya salma da jakadiya, amma sukaji shiru, hankalin ummusalma yaki kwanciya se zagaye kawai takeyi a kofar dakin, zuciyarta nata bugawa da tsananin karfi. Awa daya da minti goma sha biyar suka shude kana dr ya fito ya kalli hajiya ummu salma yace ta biyoshi office, ba musu ta bishi ya kalleta ya cire glass din idanuwansa kana ya fara magana cikin harshen turanci. "Hajiya bazata iya haihuwa da kanta ba sede a mata CS din gaggawa..." Nan take ummusalma tace "Inde ba damuwa a mata CS din..." Cikin harshen turanci. Nan dr ya tambayeta wacece dinta? Hajiya salma tayi jim ta rasa yazatace se kuma ta tsinci bakinta dacewa "Ni uwar mijintace..."dr yace okay..ya bata wata takadda tasa hannu,. Dr suka dukufa a kan Almuqri'ah aka mata CS ,ba bata lokaci aka ciro mata yaranta guda hudu uku maza daya mace. Dr ya fito ya samu hajiya salma inda take tsaye sam ta kasa zama jakadiya na zaune. Tana ganin dr ta nufosa kafin ya karaso inda take. "Ya ake ciki?'' Ta tambayesa cikin harshen turanci, yayinda take cikin tashin hnkli, gabaki daya tunaninta na kan yarinyar da yayan dazata haifa. Dr yayi murmushi kana ya cire face marks din fuskarsa cikin ladabi ya fara mgna cikin harshen nasara "ina tayaki murna ranki ya dade, anyi CS lafiya an samu nasarar ciro mata yara hudu uku maza se mace daya..." Hajiya salma taji wani irin sanyi da ddh sun ratsata a lokaci kankani. "Alhamdulillahi..." Ta fadi hadi da dukawa nan tayi sujjadar godiyar ubangiji, ta dago ta kalli Dr din bakinta har kunne, yayinda tini itama jakadiya ta taso ganin hajiya salma na sujjada. "Ta haihu ta haifa yara hudu uku maza daya mace..."hajiya salma ta fadima jakadiya bakinta kmr gonar audiga..haka kawai itama jakadiya seta tsinci kanta a zallar farin ciki. "Alhamdulillahi Allah ya rayasu dan Annabi SAW..." Duk suka amsa da Amin. Nan take salma tama dr din daya mata albishir dinnan gagarumar kyautar kujeru guda hudu na hajji , se guda hudu na umrah..dr ya dinga dogiya domin musulmi ne, ya dinga godiya kmr ze tsugunna mata. "Aje a siyo kayayyakin jarirai maza na Alfarma..." Ummusalma tayi mgnr da jakadiya fuskarta nata kara fadada da murna da zallar farin ciki, batasan meyasa ta tsinci kanta a farin ciki mara misaltuwa ba. Jakadiya tace angama, ta fice a asibitin domin gudanar da umarnin hajiyarta. Ummsalma ta dawo da dubanta kan dr muhammad tace "Dr a kaini inga babys dinnan dan Allah..." Da turanci tayi mgnr. Dr yace "Angama ranki ya dade
.." Suka juya zasu nufa dakin da yaran suke, ganin me martaba ya nufo inda take yasata dakatawa, ya kureta da ido yana me mamakin ganin farin ciki da Annashuwar dazece be taba ganin irinsaba a tattare da ita se yau, tsawon shekaru suna tare. "Waya gaya maka ina asibitin me martaba?'' Ta jefo masa tambayar yayinda bakinta ke a bude dan dariya. Me martaba ya karaso hadi dacewa "Ai duk abinda ya faru a kan idonane,,, matata sarkin temako, tin dazu nake jira inga kun dawo naji shiru shiyasa na kira drevanki ya gayamin inda kuke shine nasa a kawoni..."ummu salma tace "To barka da zuwa..wannan karan temakon da nayi yasani a nishadi mijina, wlhi ji nakeyi kmr anmin bushara da Aljannarh..." Me martaba ma ya shiga annashuwa ganin farin cikinsa a annashuwa yace " ai naga Alama farin cikina meke faruwa?'' Ummusalma ta kara fadada murmushinta tace "Wadda na kawo asibitin CS aka mata ta haifi yan hudu uku maza daya mace,,kaji kyautar Allah ko mijina, muje muga yaran wallahi dukna kagu in gansu,,,dr yimana jagora.." Ta karashe mgnrta da dr muhammad. "Masha Allahu..." Me martaba ya fadi cikin zallar nishadin da shima besan kona menene ba. Dr ya gaidasa Cikin girmamawa domin ya ganeshi. Kana ya musu jagora zuwa dakin da yaran suke kwance a kan wani kyakyawan mayen bed. Hajiya salma da me martaba sukabi fararen yaran da ido yayinda duk yaranma suka idanuwansu a bude yake an killacesu cikin kayan yaran da asibitin kesawa yara in an haifesu, in mace zata haihu a asibitin sam bata bktr zuwa da kaya sede in ita tazo, macen sanye take da peach din kayan jarirai masu azabar kyau an lullube mata kai da hula peach abin lullubintama peach ne ta bude idanuwanta tarr ga idanuwan nata manya manya,,su kuma sauran mazan sanye suke sa kaya sky blue towel din lullubinduma sky blue ne. Me martaba da ummusalma suka tsinci kansu dajin faduwar gaba ne tsanani dasuka daura idanuwansu a kan kyawawan yaran, gani yadda yara mazan suke kama sak da Abdoljalal ya tsananin sasu a wani irin yanayi, dukkaninsu duk sunga kamannin, macen kuma sak kamanninta da hajiya salma, har wani digon baki gareta irin na jikin ummusalma. "Kinga abinda nagani kuwa?'' Me martaba ya dago ya fadi yana kallan salma wadda ko kyaftawa batayi a kallon yaran, ba tare data dago ba tace "meka gani?'' Me martaba yace "Yarannan sak kamar su daya da Abdoljalal mazan, abin mamaki, har idanuwansu da komima irin na Abdoljalal, macen kuma wallahi sak kamanninki ne da ita.." Me martaba ya karashe mgnrsa yana kallan macen yana kallan salma. "Nagani wlhi, yadda mazannan suke sak haka Abdoljalal yake da yana jariri, me martaba kamannin ya baci..." Salma ta fadi tanasa hannu ta dauki yaron namijin guda daya ji takeji kmr yaran jininta ne, tamkar zata maidasu ciki haka takeji. "Allah me iko..." Cewar me martaba shima yasa hannu ya dakko macen da maza biyun duka, ya rungumesu jikinsa, ummusalma ta tsurawa yaran data dauka a hannunta ido, haka kawai taji hawaye na zirya a kan kuncinta itade tasan bana bakin ciki bane na zallar farin cikine. "Inajin yarannan kmr jinina ne me martaba.." Salma ta fadi still tana kwallah. Me martaba ya dago ya kalleta yaga tana kwallah yace "Nima haka nakeji wlhi salma,, kinga yaran sak d'ana danafiso a duniya,,, munaso musan wacece wannan uwar yaran kuma waye uban yaran, in zeyu kawai uwar da uban su bar mana yaran ko kudi sukeso semu basu mu su bamu yaran..."cewar me martaba. Hajiya salma ta dago ta kalleshi tace "In bazasu bamu ba se in bisu gidansu wlhi ina san yarannan bani sauran in daukesu duka.." Duk dr na tsaye yana kallansu sede besan me suke cewa ba sbda bejin hausa shi ibra ne. Murna mara misaltuwa salma da Me martaba suka shigayi. Salma tayi tayi me martaba ya bata sauran yaran yaki sede ta rike dayan ta hakura shikam ya hakimce ya zauna yaki bada yara kai kace shine ubansu. Ba jimawa jakadiya ta dawo da uban kayayyaki kama daga na babys har zuwa wanda uwar baby zata bukata duk seda jakadiya ta kawo, datazo taga babys din itama seda gabanta ya yanke ya fadi, ganin yaran sak Abdoljalal, macen kuma sak hajiya salma,. Seda jakadiya ta kasa daurewa tace "yarannan se naga kmr suna kama da farin cikinki mamanmu, ita kuma macen tana kama dake uwar dakina..."jakadiya ta fadi cikin mamaki. Salma dame martaba suka hada idon kallon junansu "e wlhi kinga ikon Allah ko.." Cewar salma. "Babban ikon Allah ma kuwa..." Cewar jakadiya da mamaki ya daskarar da ita, amma kuma seta tuna ba a mamaki da ikon Allah. Almuqri'ah ta farka cikin aminci taga yaran da ubangiji ya bata kyauta, ita kanta seda gabanta ya fadi ganin kamannin yaran da ubansu ya baci, se macen de ta rasa gane dawa take kama ita, amma tafi kaf yaran kyau da farin fata kmr a tabata jini ya fito. Seda Almuqri'ah tayi kukan farin ciki, tayima hajiya salma dame martana godiya. Se a yanzu be suka fahimci bebiya ce, se tausanta ya kara ratsasu. Salma dame martana zuciyoyinsu na cike da zallar tambaboyi ga Almuqri'ah amma sede ba halin hakan ganin halin da take ciki. Tashiga bawa yaran nata nono suka amshe kmr suna jira, nan suka zuko nonon se adduarh take musu dasa musu albarka, a zuciyarta tana ayyana inama ace Abdoljalal na nan yaga yaran nasa har hudu reras. Jefi jefi Almuqri'ah nata bin hajiya salma dame martaba da ido, se yanzu take kara ganin kamanni su da Abdoljalal. "Ikon Allah..." Shine abinda Almuqri'ah keta fadi a ranta yayinda zuciyarta ke yawan faduwa inta kallesu. Da kyar me martaba da salma suka bari yaran sukasha nonon uwarsu suka koshi suka amshesu suka rungumesu in suna rike da yaran wani irin yanayi suke shiga. Satinsu daya a asibitin Almuqri'ah tasamu sauki aka sallamesu suka koma gida da niyar nurse zata dinga zuwa duba Almuqri'ah din sbda dinkin da aka mata a ciki.. Suna komawa gidan hajiya salma tabawa Almuqri'ah part daya ita da yaranta,.wata iriyar kulawa salma ke bawa Almuqri'ah da yaranta da kullum suke gunta ta musamman. Me martaba da salma da jakadiya kullum suna part din da Almuqri'ah take, ga yara na hannunsu sallah kawai kesasu ajiye yaran a hannunsu Almuqri'ah na mamakin irin san da suke nunawa yaran nata zata iya cewa ko ita bata sansu kmr yadda su suke sansu. Byn dasowarsu da sati daya salma ta kasa daurewa , suna zaune a kayataccen dakin Almuqri'ah ta kalli Almuqri'ah ta kalli me martaba dake zaune, da kuma jakadiya dake zaune. "Baiwar Allah ki bamu labarin wacece je dan Allah? Wanene uban yarannan naki dasuke tsananin kama da d'ana dana haifa da cikina..." Cewar salma. Gaban Almuqri'ah ya yanke ya fadi jin abinda hajiya salma tace. "Suna kama da d'anki? Nima kunamin kamanni da baban yaran nawa.." Almuqri'ah ta fadi cikin zallar mamakin data jima dashi a ranta, ganin hajiya salma nasata a tsananin dmwr kewar mijinta wasu lokutan ko baccin kirki bata iyawa sbda tasan mijinta na cikin zallar tsananin dmwa da tashin hnklin rashinta a kusa dashi musammanma cikin jikinta. Dukda da bebanci tayi maganar amma duk sub fahimci me take nufi. Me martaba da salma suka kalli juna. "Dan Allah wanene ku a ina mijin naki yake?'' Cewar salma. Almuqri'ah tayi jim kana ta basu lbrin dalilin barowarta gidanta da mijinta na aure, tace ta bar gidanne kawai sbda kishiyarta zata kasheta data fahimci tanada ciki. (Almuqri'ah ta boye musu abubuwa dayawa ta basu short labarinta da Abdoljalal da saude) sukaji tausanta me tsanani, nan take duk sukaji sun kara santa soyayya me tsanani, yayin da zuciyoyinsu duk suka cika da kwad'ayin san ganin waye uban yaran nan na Almuqri'ah. "A ina yan uwanki duke?'' Cewar salma. Almuqri'ah ta basu lbrin cewa batq da kowa se kakarta kuma bata kasar tana can kasar waje gun nema mata lafiya, wani ya dauki nauyin nema mata lafiya a kasar wajen sbda su basu da komi, kuma su ba yan nigeria bane su yan sudan be.(tade boye musu Ainifin dalilin zuwanta gidan Abdoljalal tade bayyana musu abinds ze bayyanu sauran ta barwa ranta.) Me martaba da salma duk suka karajin tausanta sosai. "Ki zauna damu pls har Allah yayi ikonsa, kakarki ta dawo Nigeria se itama tadawo nan gidan da zama, harde ubangiji yasa ki koma gidan mijinki knji..." Cewar salma. Ba musu Almuqri'ah tace "Toh...ngde Allah ya biya da Alkhairi ." duk suka amsa da Amin, komi tace suna fahimta dukda da bebanci take magana. Hk kawai Almuqri'ah taji ta aminta dasu 100% kuma tana kaunarsu 100%.. "Wani suna za asawa yaran naki?'' Me martana ya tambayi Almuqri'ah ganib time nata tafiya bawa yaran wuduba da sunansu ba... Almuqri'ah ta rasa mezatace kawai seta tsinci kanta dacewa "Asa ma macen sunan mamana,(shine sunan data bawa salma mamanta take ce mata...) Mazan kuma asa musu sunan daya dace kawai..." Ta fadi da bebanci. Me martaba da salma sukaji dadin karamcin da yarinyar ta musu, ba bata lokaci me martaba yama yarinyar huduba da sunan salma, mazan daya yasa sunansa, se daya yasa sunan abdoljalal, dayan kuma yasa sunan isma'il wato yarimansa. Seda ya gama musu hudubar kana ya shaidawa salma sunan dayawa yaran, taji ddh sosai kaf kowa yaji dadin hakan musamman Almuqri'ah dataji ansa sunan Abdoljalal kuma yace sunan dansu ne, ita kuma sunan masoyinta ne wanda ya iya cin gindinta. Almuqri'ah taga ikon Allah sosai , ga sunan dansu da sunan mijinta duk daya, haka kawai itama taji tanaso taga d'an nasu. Byn kwana hudu aka shirya bikin suna na gani na fadi, kowanni yaro aka yanka mishi sah, wato sah hudu aka yanka ma yaran.ansha hidima ywar jego tasha sutura ta arziki, dan akwati dozin biyu tama mejegon me martaba yamata dozin biyar, sukam jariran ai dozinan kayayyakin da aka musu baze misaltuba. Anci ansha a suna an raba kayayyaki na Alfarma, harda kudi aka raba na fitar hankali dukde abinda Allah ya ciyar dakai a sunan shi zaka samu.
Paid book ne. Allah yasa mu gama lafiya.
42
Ammah tasamu sauki sosai, dan haka suka tattaro suka dawo kasar nigeria, Dr mus'ab ya siyama Ammah gida ta zauna cikin aminci se godiya take masa mara iyaka, nurse mami takoma ga yaranta domin bata da miji tini ya jima da rasuwa, . har gidan mami Ammah tasa dr mus'ab ya kaita ta mata godiya mara iyaka, harda kuka, a zamaninnan ammah bata tunanin za a samu mutane irin Dr mus'ab da nurse mami. Dr yayima mami goma sha tara na dumbin Arziki arziki. Satinsu daya da dawowa kasar Ammah taji dadin jikinta sosai, tanata ci gaba dashan sauran magungunan da likitoci suka daurata a kai, a halin yanzu jikarta Almuqri'ah kawai takeson gani, tanasan taga a wani hali take ciku zuwa yanzu. Dan haka ta fara tambayar Dr kan yaushe Almuqri'ah zatazo, ko ita zataje ta ganta... Dr ya fuskanci tana da bktr ganinta sosai, dan haka yace zeyi kokarin hakan. Tinda ya dawo kasar beje gidansu ba, shima yanada bktr san ganin Almuqri'ah da Abdoljalal, dan haka ya shirya yau after la'asar ya nufa gidan Abdoljalal,. Tin daga bakin get mus'ab yaga gidan ya chanza masa sosai, securities duk sun chanza masa, dabadan Ahamad dake bakin get din ba, da sam Dr mus'ab baze samu shiga gidan ba, sbda su securities din dake aikin ynzu basu sanshi ba. Yanayin packing Ahamad yazo ya bude masa, murfin motar ya fito ya zubawa Ahamad din ido nan take yaga duk yayi wani zyru-zuru, to duk hankali ba kwance ba, abinci wannan ma se yayi da gaske yake ci, hakan yake ga gogan shi san yadena cin abinci ma sede ruwa kadai dr ke zuwa yana kara masa, shima ruwan se yaga ze mutu ake kara masa shi, duk yabi ya fice a hayyacinsa wanda ya sanshi ada inya ganshi yanzu se yayi da gaske yake iya ganeshi. Saude kam ai tinima ita wannan ta dena ci itama tadena sha se aikin yawan bin malamai kawai takeyi, dukda malaminta ya tabbatar mata da Almuqri'ah ta mutu ita da cikin jikknta amma bata hakura ba se bin wasu malaman takeyi saboda hankalin mijinta yaki dawowa gareta, tini duk tabi ta sabe tayi wata uwar ramar daba kowa itama yake ganeta ba, sbda mulkin datakeyi yanzu sam bata isa tayishi ba, asirin takeyi amma sam gani ma takeyi asirin baya Aiki,Hajiya Abulle ta dawo da ita suke yawon bin bokayen amma sam ba nasara Saude tazama kmr zautacciya, ta nemi lambar kande domin taci ubanta amma shiru lamba bata shiga, kaf maaikatan gidan mata da maza banda securities duktasa an musu duka jina jina, ta musu cin mutumci na fitar lissafi, kana ta koresu a gidan har jimmalo, gida de ya koma daga saude seme dafa mata Abinci, to yanzu bata ma da kwanciyar hankalin dazata ci abincin dan haka ba abincinma take ci ba, aikin me dafa abinci yakoma gyaran gidanta kawai. "Ahamad meke faruwa ne duk kabi ka zabge kayi duhu? Gidanma dukya chanza min.." Cewar dr mus'ab da yy mgnr cikin dmwa yayinda jikinsa ke bashi babu lafiya. Ahamad ya fara hawaye, hkn ya kara tadawa dr hankali. "Meke faeuwa? Dan Allah ka gayamin..." Ahamad ya fara mgna yana kwallah "Ranka ya dade duk mun nemi numbers dinka shiru..." Dr yace "Wlhi bana kasar ne, Dana bar kasar duk se nasa wayoyina a yadda ni zan iya kiranka kawai...kuma na kira Abdoljalal lokuta da dama a kashe ka gayamin meke faruwa, jikina na bani akwai babbar matsala, ka gayamin meke faruwa dan Allah?..." Nan ahamad ya kwashe labarin komi dake gudana ya gayawa dr mus'ab kama daga kama Abdoljalal A kan Almuqri'ah da saude tayi har zuwa gudun Almuqri'ah a gidan, har de zuwa yanzu da halin da Abdoljalal yake ciki. Ahamad yaji kansa ya tsananin sara masa jin Ahamad yace masa wai Almuqri'ah ta gudu , seda dr ya koma ya jingina bayansa da bayan motarsa nan take yaji jiri na neman kwasarsa
"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' Itace kalmar data fito daga bakin dr, nan take idanuwamsa suka shiga kokarin daukewa daga gani na wasu yan dakiku. "Ina ta shiga?'' Cewar Dr da yayi mgnr fuska da murya dauke da zallar tashin hankali. "Bamu sani ba, an kai cigiya kaf gidajen TV da gidajen redio duk bamu samu tadawo ba, duk inda nake inada tabbacin yanzu ta haihu gaskiya,,, wlhi Oga na cikin tsananin dmwa muje kaga halin da yaje ciki..." Cewar Ahamad. Ba bata lokaci dr yabi ahamad a baya zuwa dakin Almuqri'ah inda nan Abdoljalal ya koma rayuwa tinda ta bar gidan be leka ko kofar dakinsa ba, yazama kmr mahaukaci. dr nashigowa dakin idanuwansa suka sauka a kan Abdoljalal dake kwance kasan tiles din dakin duk yabi yayi karo-karo dashi se kasusuwa kawai a jikinsa, yayi bala'in baki, tako ina jikinsa gashine buzu buzu. Tsabar tsananin tausansa ya rufe dr nan da nan se hawaye ya fara zirya a kan kuncinsa, "mutum ba komi bane..." Dr ya fadi a bayyabe ganin yadda jalalu dan gayu kyakyawa ya koma bashi da maraba da kwarangwal.