Showing 9001 words to 12000 words out of 159314 words
Chapter 4 - Wata Kishiya Complete writing by Sa'adatu Bint Abdullahi .txt
knta goganniyar tasa seda taji hankalinta ya dunguma ya kuma mikewa Tana bala'in san jin batsarsa a hnkli yake yinta amma ya iyata sosai, daze ci gaba da mata ire-iren klmnnan nasa yana daga tsayennan tana daga kwancannan ta tabbatar seta kawo ba tare data ankare ba. Dan ciza lips dinta na sama tayi hafi da Shan murr da kar ya bata mata ayyukn data juma tana ginawa tace " Ba yanzuba ni banda ma lafiya a kwanakinnan sam.sam banjin dadih gaskiya sena warke na nemeka..." (Haka take masa wannan renin hnklin harse ta shiririntar dashi) Kallonta yayi kawai ba tare dayace komi ba ta saba masa fin hkn ma, kuma shifa a can kasan ransa badan yana sha'awarta bane ko dadinta yakeji aah ko daya kawai deshi beda yadda zeyi ne besan daliliba,shide yasan kawai so yakeyi yaci gindin mace kuma bana haramunba shiyasa yake nacewa natan dan itace halak malak dinsa,. "Allah ya kara sauki kije asibiti mna..." Ya fadi cikin daddadar muryarsa me kama da busar sabuwar wasashshiyar sarewa. Yana gama fadin hakan ya juya jiki a sanyaye ya nufa hanyar barin falon, binshi tayi da ido harya gama ficewa daga falon, ko ganinsa tayi wlhi se taji bala'in sha'awarsa ta turniketa, dande bata da yadda zatayi ne Amma wallahi tana bktr gaban mijinta tsundum a nata gaban.,... Yana barin bangarennata farfajiyar gidan ya fito ko ina tarr da hasken kwan fitilu kai kace rana ce, gidan ya tsaru iya tsaruwa ashe babban gida ne na innalillahi wa'inna ilaihirraju'un! Hasken daya haskaka gidan shiya bani damar ganin tsarin makaken dankareren tamfatsetsen gidan wanda ke dauke da packing space babba na bugawa a BBC, irin wanda A kallah ze dauki motoci hamsin ba tare daya cika ba, tako ina gidan ya tsaru ban taba ganin gida me kyaun tsari tako ina ba kmr wannan gidan na Alhaji AASARAKI, tako ina anyi shuke shuken flowers masu kawatarwa, se kamshi ke tashi tako ina a compound din gidan direct hanyar bakin get ya nufa batare dayasanma ya nufa bakin get din ba zuciyarsa bata tare dashi kwata kwata, zuciyar tasa tini tayi gabas shi kuma ya nufa yamma. Masu gadi kusan su ashirin dake bakin get din a tsaitsaye wadanda suke sanye da kayan yan sanda, Suna ganin yana tunkarosu duk suka kakkame tin be karaso ba suka fara miko masa gaisuwa. "Good evening sir!'' Suka hada baki gun miko masa gaisuwar. Gaisuwar tasuce tasashi dawowa hayyacinsa, yayinda rabin zuciyarta ta dawo garesa, ya zubo musu ido kawai se kuma ya dauke idon nasa a kansu, hadi da cusa lallausar soft hand dinsa a cikin audigar sumar knsa wadda ke cike taf da kn nasa,.''la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalumin!" Ya fadi a bayyane cikin sanyin sound, haka kawai yakejin duniyar bata masa dadih lokuta da dama yana jin hakan sometimes seya dingajin kamar ze haukace ko yadinga ganin kmr ma bashi bane, kwata-kwata bayajin dadin rayuwarsa ta duniya tinda ya mallaki hankalin kansa ya zama magidanci yadena jin dadin duniya kwata-kwata, shide gashinan ne kmr wani sifili..lum-lum eyes dinsa ya zubawa ma'aikatan dasuke a kame kyam kwana sukeyi a tsaye suna gadin gidan, sun kai su hamsin a gidan wasu nata wajen gidan wasu nata baya, wasu nata cikin gidan domin akwai hanyoyi kusan goma a gidan wadanda zasu fiddaka wajen gidan, wannan get din de shine babban get din gidan sauran hanyoyin ba kowama suka san dasu ba. Kallonsu yakeyi Amma sam hankalinsa baya knsu yana can kan wani tunani dabesanma wani irin tunani yakeyiba. Kaf securities din hankalinsu seda ya tashi ganin irin kallon da yake musu duk da shi din me Adalcine amma seda gabansu ya shiga dukan dari uku-uku, sbda kallon dayake musu dole ne duk wani me lissafi inya gani yasha ko wani lefin suka maka masa. Babban cikinsu mustapha wanda shine na hannun daman Abdoljalal shiya iya dauriyar matsowa ga Abdoljalal din ya kame cikin girmamawa yace "Tuba muke Sir ! Dan sarki jikan sarki! Jarumin jarumai Tuba mukeyi kanmu bisa wuyanmu" maganganun mustapha ne yasa Abdoljalal dawowa cikin hayyacinsa, ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, "Ya ilahil alameen!'' Ya ambato sunan Allah yana me dawo da dubansa kan mustapha, still lallausar hannunsa na cikin audigar sumar kansa. "Ranka ya dade yallabai ko munyi wani lefinne? Allah de yaja kwanan ka uban dakinmu...'' Mustapha yaci gaba da fadi hadi da rankwafawa cikin sigar ladabi da biyayya. Kokarin controlling zuciyarsa daga mood din datake yayi cikin isa da kasaisa da low voice dinsa wadda seka natsu iya nutsuwa kana kake iya jin me yake cewa yace "Nop,, bakuyi komi ba nazo naga yakuke ne? Ya aikin?'' Mustapha dashi kadai ne yaji me yace sbda muryarsa tayi low dayawa ya dunkule hannu daya yace "godiya muke uban dakinmu sarkin adalci lafiya lau muke Alhamdulillahi, Allah de ya baka shugabancin kasar nan dan martanar Annabi muhammadu SAW...." Duk sauran ma'aikatanta suka amsa da amin dayake yawancinsu duk bawanda bejin hausa duk sunajin hausa kmr jakan kano, se ynzu suka natsu dukda basuji me Abdoljalal kecewa ba Amma de sun san ba lefi suka masa ba. Murmushi kawai gogan yayi danshi baya san mulkin kawai jama'arh ke sansa ko ince farin jinin jama'ah ne dashi dan yayi sun gani. juyawa yayi ya bar inda suke still hannunsa na cikin audigar sumar knsa se dayan hannun nasa yana cikin aljihun wandon dake jikinsa,, a memakon ya nufa side dinsa direct kawai seya nufa inda aka tanada dan shakatawarta a wannan uban daren, Bin ko ina yakeyi da ido kmr wanda ya warke makanta, babban kayataccen guri ne wanda ya hadu ya gaji da haduwa an shirya kujeru launin brown masu kyau da laushi na shakatawa a gurin,, tako ina iska se kadawa takeyi tana dukan hancinsa hadi da wani irin daddan kamshin dake fita a kaf gidan musammanma nan gun shakatawar tasa kullum a ka'ida se ansawa kaf flowers din gidan launin kamshi wanda ya dace, nan ko gun shakatawarsa sau biyar ake gyaransa a kullum asa masa sinadaran kamshi koda kuwa bezo gun ba ka'ida ne se an gyara, danma gidan akwai yawaitar ma'aikata bayan securities sunada kusan ma'aikata fin hamsin. Karasawa yayi ya zauna bisa kujera me daukar Mutum daya ya sauke ajiyar zuciya, yana me bending a kn kujerar nan da nan naga kujerar ta bude ta kwanta ashe na'urace daka kwanta zata kwanta itama, ji yayi yaji dadin kwanciyar ya juya ya kwanta a kn gefensa na dama ya rungume hannayensa duka biyu a kirjinsa yana daga nan kwance, daka kalleshi inde kanada cikakken hnkli sekasan yanada boyeyyiyar damuwa kuma dole sekaji ya baka tausayi, kurawa gefe daya yayi ido, yayin da hasken farin wata ke kara haskaka ko ina a gidan, ga kuma hasken kwaye-kwayen fitilu kai ka rantse da Allah rana ce danko allura ce ta fadi zaka a hannunka tabbas daka tsugunna zaka nemota., ajiyar zuciya ya sauke a hnkli hadi da busar da iskar dake cikin cute mouth dinsa yasan yanada damuwa amma ya rasa meke damunsa gabaki daya jinsa yakeyi incomplete, jikinsa ya kara masa weak kmr wanda xaxxafan zazzabi ke shirin lullubesa, shifa ji yakeyi kamarshi ba mutum bane, kuma besan shi menene ba. "Meye matsayina pls?'' Ya tambayi kansa a bayyane wasu irin tunani tunani da dumbin kunci suka rufesa wadanda besan kona meye ba. Hannunsa na dama yakai kan saitin kirjinsa na hagu inda zuciyarsa ke masa wani irin beating ya lumshe idanuwansa na wasu yan dakiku ya kuma budewa yana sauke sassaukar ajiyar zuciya cikin sauri-sauri, shifa tinda ya hadu da saudat be kuma gane waneneshi ba wallahi har zuwa yanzu jinsa yakeyi kmr fatalwarsa ce shi ke yawo bashi bane....yafi karfin 1h a kwance yana saka da warwara a zuciyarsa ko zaka kasheshi baze iya fadar me yake sakawa ba a zuciyar tasa ba, shide kawai gashinan jinsa yakeyi kmr wani mara yanci a duniya, "akwai abinda dukiya bata siyawa me rai WATO NI'IMAR DUNIYA ba kudi bane farin ciki...." Ya fadi hkn a ransa, ya rasa ma meyasa ya fadi hakan. Tashi yayi zaune Kmr an masa allura a bom-bom, kujerar dayake kai ta koma yadda take da, ya saka takalmansa a hnkli kmr wanda kwai ya fashe masa a ciki, ya mike da kyar se yaji wani irin jiri na neman kwarsarsa ya yarb'ar dashi kasa, cikin hanzari ya rike knsa yana fadin "Hasbunallahu wani'imal wakeel, yawadudu!'' ya sakarwa gefensa na dama nauyi saboda yaji alamar na hagun ne ke gagarar daukarsa, komawa yayi kn kujerar daya tashi ya zauna yana me tsurawa yatsun hannunsa na hagu dake kan cinyarsa ido, dan daga yatsanshi na hagun yayi ya shiga dagasa yana mayar dashi yana kwantarwa kn cinyar tasa wato de wasa da yatsunsa ya dingayi na hagu a kn cinyarsa ta hagun, seda ya kara 30mnt a hkn kana ya iya mikewa ya nufa side dinsa. Tin daga wajen yanayin ginin side din nasa ya tabbatarmin daba karamin kyau cikinsa zeyi ba, domin kuwa kyaun wajen side dinsa ya taka kyaun gaba daya side din hajiya saude, an narka kudade tako ina. Yana zuwa bakin kofar dazata sadashi da babban birnin falonsa yaja ya tsaya ya daga knsa ya kalli saman falon nasa inda akayi rubutun sunansa da mnyan baki AASARAKI shine abinda aka rubuta yakai 5mnt nan tsaye yana kallon sunan nasa, kana ya karasa jikin kofar tanajin duminsa ta bude hadi da miko masa gaisuwa cikin harshen turanci dayake kofar na'ura ce wadda nasara ya kerata, shi kadai ke iya budeta, duk wanda ya biyo ta kofar bazata bude ba sede inta baya zaka shigo. Takawa yashigayi a hnkli byn ya shigo kofar ta mayar ta rufe ya zubawa kasan tiles din ido kai kace yau ya warke makanta shi knsa tiles din side din nasa ban taba Ganin irin saba , butter milk ne me tamburan heart heart kalar red da sky blue, inka tsaya tsaf zakaga knka a kn tiles din domin yafi madubi haske, wani irin kamshi se tashi yakeyi, direct falonsa ya nufa, wow! A nan kyaun yake alaji! falon ya hadu iya hadu ya kayatu harya gaji da kayatuwa sam babu hayaniya a falon, amma fa nan kyau ya tare a falon, kujerune kalar 2color a falon, 3ct da 2ct duk blue ne se 1ct butter milk dayar 1ctr dinma butter milk ce,, se wasu kujeru daga gefe na shan coffe guda biyu su kuma bakake ne masu rodi rodin golden color da dan table dinsu a tsakiyarsu golden neshi yana dauke da flowers a tsakiyarsa, gabaki daya tsarin falon tsarin tuwarawa ne ga rest chair a gefe butter milk ta hadu iya haduwa se wani kyalli takeyi na gold gold gashinan de, kaff fitilun kwan falon abin kallo ne danni ban taba ma ganin irinsu ba. Kallon falon yakeyi kmr yau Allah ya jefoshi cikinsa hk yakeyi wasu lokutan se yadinga ganinsa kmr shidin bakon duniya ne. Komi na falon is so cute and perfect komi fa ya hadu tsakiyar kujerun falon an mamayesa da wani carpet butter milk masu digo digon sky blue, ga wani dan karamin table a tsakiya wanda aka ajiye masa wata dankarereiyar flower milk color me ratsin sky blue da red red a jiki, ko wani gefe na kujerun akwai side table. Sanyin AC kawai ke tashi a falon tasama takasa na'urorin sanyi kawai ke Aiki, tamfatsetsen TV din falon se Magana yakeyi shi kadai ba dan tayi. Kyar ya tsayar da idanuwansa a kan TV na bangon daketa zubo kimtsatstsun bayanai ba kakkautawa ta cikin tashar sunnah TV ita kadai yake kallo Se BBC da tashar Aljazeera. Karasawa yayi ya daura kafarsa ta dama a kn carpet din dake tsakiyar kujerun nan da nan sekou kafarsa ta lotse luf a cikin carpet din laushi da laushi sun hadu, seya bashi wani irin lallausar laushi a tafin kafar tasa me ratsa gangar jiki da jijiyoyi, seda ya dan sauke ajiyar zuciya me fidda sarewar ni'imomi. kara daura kafarsa ta hagu kn carpet din yayi ya fara takawa a hnkli ya karasa kn kujerar 2st ya zauna seta lotsa itama tayi wani kasa dashi ta kuma ta dawo dashi sama luuuuuuuu ni'imar duniya me kwantar da hnklin bayin Allah kenan, bending din bynsa yy a kn kujerar yana me zuqo numfashinsa daddad'an kamshin dake falon ya bugesa ya kuma ya bugesa 100x, seda ya lumshe idanuwa tsawon 30second ya budesu a kan agogon bangon dake falon yaga karfe biyu ake nema zuwa yanzu,, mikewa yayi ya nufa kiching dinsa wanda kofarsa ke manne da falon. Wow! Kiching din ya hadu ya kayatu yayi wani irin luntsumemen kyau me razanarwa, color din kiching din blue ne light da butter milk, hatta da duk tiles din kiching din butter milk ne da sky blue light sosai. Se sanyin AC kawai ke aiki a kiching din kai kace kankarewa zakayi, ka koma kankara, wanda be saba da AC bama tini ze kankare ya koma kankara shikam gogan da sanyi da zafi duk be iya rayuwa seda sanyin AC sbda sabo. Komi na aiki a kiching din na'ura ce hatta da pot din girki na'ura ce,. Ma'ajin Kettle ya nufa ya latsa wasu malatsai nan da nan ruwa ya bulbulo a cikin kettle din ya kunna, ya nufa ma'ajin glasses cups dinsa dayake shan coffee dasu ya gansu jere reres a cikin glass ya danna password, nan da nan glass din ya bude, ya dauko cup din golden color da dan karamin trea din mahalin cup din ya saki famfo ya dauraye cup din da trea din, ya nufa inda kayan coffee din nasa suke ya zuzzubo komi mizanin dayakeso zuwa lokacin tini ruwan kettle din ya tafasa dan 10second yakeyi ya tafasa kara kunnawa yayi ya tafasa again kana ya zuba a cup din mizanin dayakeso ya nufo hayar dawowa falon ya zauna kan kujerar shan coffee dinsa, ya kai glass cup din bakinsa ya fara sha cikin salo a hnkli a hnkli har wani lumshe ido yakeyi dan dadin coffee din, girki ne kawai dabe iya ba da dakansa ze dinga yi shi mutum ne dabe jira a masa kwata kwata beda son jiki dan ko sadda Baba ladidi ke kawo masa abinci side dinsa daya gama ci ze kwashe komi yakai kiching ya gyara inda ya bata intazo kawai kiching take nufa ta kwashe ta fice dasu, shi be sakin jiki yace komi se an masa aah sam beda lalaci. yanashan coffee din yana kallon agogon bangon dake manne a bangon falon, 2:30am dai dai ya gamashan coffee din ya kai cup din kiching ya wanke da knsa ya mayar inda ya daukesa, ya juya ya fice daga kiching din direct matattakala ya nufa ya haye yana danjin dadin jikinsa daman dayaji bejin dadih dayasha coffee se yadanji sanyi sanyi bakomi bane sabo ne da yayi dashan coffee din, yanzu de shine ma abinsa ya manta When last yasawa cikinsa abincin kwarai. Direct bedroom dinsa ya nufa ya bude kofar bedroom din ya shigo bakinsa dauke da sallahma. Wow! So so cute ashe nan bedroom dinsa kyau yayi Aure ya tare.! Komi na bedroom din milk ne and golden light hatta furniture din kaf milk ne da cotton din dakin duk milk and light golden ne, ko ina tsaf tsaf danshi beson kazanta da tarkace shiyasa hatta bedroom din nasama beda wani uban tarkace beson haya-haya , shi sam ma baya bata wuri, bathroom dinsa ya fada, wayyoh kyau! Kyaun bathroom din ya fita yadda yafi tunanin me lissafi, duk na'urorine a toilet din, an killace gefen wanka daban, da toilet seat, duk an wawwaresu daban daban ansa musu wani irin kayataccen labule a tsakiya, komi na bathroom din butter milk ne hatta da tiles din dake bango dako ina duk butter milk ne, se uban kamshi ke tashi a bandakin ko ina tal tal kmr a lashe. Kama ruwa yayi dan already yayi wanka dazu ya dauro alwala ya fito yadawo dakin nasa ya nufa ya nufa gaban mirror dinsa wanda Yake cike taf da turarruka kmr gaban mirro din mace, ya dauki hadadden perfume dinsa wanda ko kwalbarma abin kallo ce ya feshe jikinsa dashi, ya mayar ya ajiye ya nufa inda aka tanada dan ibada a dakin ya tada sallar kmr yadda ya saba duk daren duniya...bashi ya idar ba seda aka fara kiraye kirayen sallar asubahi! Kana ya dakata yayi addu'ur'insa ya mike ya Nufa bathroom dinsa ya cire kayansa ya shiga na'urarsa tayin wanka , yana daga tsaye nan ya danna wani malatsali sega ruwa me dumi yadda yakeso ya zubo batare dayayi komi ba na'ura ta masa wanka tas da nau'ikan sabulai iri iri na kamshi, ya fito hadi da jawo towel ya goge jikinsa ya dawo dakin a gaggauce ya shirya cikin jallabiya butter milk ya feshe jikinsa da turare, ya fice zuwa masallacin dake cikin gidan, bashi ya dawo cikin gidan ba se 6:30am. Ya nufa kiching ya hada mutumin nasa wato coffee yasha 7:am yabi lafiyar gadonsa yana mejin ni'imomi na sakkowa ga jikinsa, dabadan karfin ibada ba shi knsa yasan dabesanma a yaya yake ba.
3:am a bakin get din gidan AASARAKi ta bugawa hajiya kande da wata yarinya fara Sol kmr Aljana wadda a kalla shekarunta bazasu yawai taba, yarinyar sanye take da hijjabi blue black dark sosai dukda hijjabin ya kode iya kodewa musammanma daga saman kai Amma ya amsheta Ainun ya fito da kyakyawar fuskarta zuwaiiitt doguwace fuskar tata me cikar kumatu kubul-kubul lugub-lugub, dukda akwai alamun wahala a jikinta amma hkn be hana kyaunta bayyana ba, tanada dara daran idanuwa kmr zasu fado kasa dan girmansu ta cikin idanuwan nata dan tsakan