Showing 135001 words to 138000 words out of 159314 words

Chapter 46 - Wata Kishiya Complete writing by Sa'adatu Bint Abdullahi .txt

kinji, dukda bansan meke faruwa ba amma ki kwantarda hankalinki dan Allah, kodan cikine dake jikinki knji..." Jimmalo tayi mgnr cikin muryar kwantar da hankali. Almuqri'ah ta sauke ajiyar zuciyar dake cike da tsananin damuwa taji dadin klmn jimmalo dukda sam bata shiga kwanciyar hnklin datace ba saboda tana hango tashin hankalin dake gaba wanda tasan kanta sam baze dauka ba. Jimmalo ta dinga mata ma Almuqri'ah kalamn kwantar da hnkli,,, seda taga ta dan natsa kana ta tambayi meke faruwa..Almuqri'ah bata rage mata komi ba, seda ta sheda mata komi yadda ya wakana, harta da sex din dasukeyi da Abdoljalal bata boye mataba, da yadda sukaji ihu sukaga mutum kawai yashe a tsakiyar daki, dukda Almuqri'ah bata sani ba amma tasan saude ta gansu ne real Aini hakan ne yasata sumewa. Jimmalo ta sauke ajiyar zuciyar zallar tashin hankalinta dayaso ya zarce na Almuqri'ah. "Ya Allah..." Jimmalo ta fadi, zuciyarta kmr ta fito waje dan tsabar bugun tashin hankali, tasan akwai babbar matsala gaba,. Sam bata nunawa Almuqri'ah akwai matsala ba nan ta kara kwantar mata da hankali, Sam hankalin Almuqri'ah ya kasa kwanciya tasan saude ba mutuwa tayi ba, to tabbas in har saude bata mutu ba tasan seta kasheta ita, wannan magana tasan dole ce, abu daya take gudu d'an cikinta da acema ita kadaice seta zauna kawai ayi yadda zatayi, tanasan d'an cikinta sam batason wani abu ya sameshi, Tana alfahari da cikin jikinta ta kwammace da wani abu yasamu d'an cikinta kwara ita ya sameta. Suna nan zaune har 1:am jimmalo na kwantarma da Almuqri'ah hankli da kalamai, amma ina sam Almuqri'ah bataji kwanciyar hankalin ba a cikin zuciyarta. Mikewa tayi ta nufa bandaki tayi wankan tsarki ta dauro alwala ta fito ta tadda jimmalo batanan. Almuqri'ah ta chanza kaya, tasa hijjabinta, tada sallar nafila tayi,domin tafiso ta gayawa ubangiji damuwarta a halinnan datake ciki Allah ne ze iya kwantar mata da hankali, a zaune takeyin sallarh damn tin cikinta na 7month ta kasa tsayuwar sallarh. A haka jimmalo tadawo dakin tasameta tanata nafilfili, jimmalo ta zauna gefen bed din da waya a hannunta daman data fice a dakin, dakinta taje ta dauki waya dan kiran kande ta sheda mata meke faruwa, ta mata kiran duniyar nan amma wayarta a kashe, se tashin hankalin jimmalo ya karu saboda batasan yaza ayi ba yanzu tasan de zaman Almuqri'ah a gidan bazeci gaba da yuwwa ba in ba hk ba kuwa lamarin ze haifar da d'a mara ido. Jimmalo ta dinga kiran hajiya kande taji shiru har zuwa 3:am , gashi ita jimmalo bata iya message ba balle ta turawa hajiya kande ta yadda zata gani inta kunna wayarta ta kirata. "Innalillahi wa'innah ilaihirraju'un!” jimmalo ta fadi ita kadai tasan irin mugun tashin hankalin datake ciki itama, ta ajiye wayar ta mike ta nufa toilet din Almuqri'ah ta dauro alwala itama ta dawo ta tada sallar nafila itama nan kusa da Almuqri'ah. sallar jimmalo keyi amma sam hankalinta baya jikinta....har asubahi suna kan dadduma, se yanzu Almuqri'ah ta farajin kwanciyar hankali a zuciyarta saboda ta gana da mahalucci. "Kije ki kwanta kiyi bacci..." Cewar jummai datayi mgnr byn sun idar da Asubahi. Almuqri'ah tace toh domin tana bukatar baccin ta tashi ta haye kan gadonta tana me sauke numfashi, hankalinta Almuqri'ah ya d'an kwanta ba kamar dazu ba, ta rufe idanuwanta kmr tana bacci amma ta kasa baccin so takeyi tayi baccin amma sam ta gaza yinsa,, da jimmalo taga idanuwanta a kulle setasha ko bacci tayi dan haka ta mike ta fice a dakin hannunta rikeda wayarta se kara dealing number din hajiya kande takeyi amma shiru, har jimmalo ta isa dakinta tana kiran lmbar kande amma shiru, ta rasa yazatayi, kota kwanta tasan de bazata iya bacci ba, dan hk seta fita danyin aikin daya zama nata, taga kaf ma'aikatan gidan mata basu fito sun fara aikinsu ba, ta nufa nata aikin zata fara kenan wata zilai me aiki tazo ta ganta tace "karkiyi aiki ki wahalar da kanki yau ai rnr hutu ce saude ta rasu..." Jimmalo ta zaro ido tace "Dan Allah ta rasu ne?” zilai tace "Insha Allahu muna fatan hakan..." "Nafiku bukatar hakan..." Cewar jimmalo datayi mgnr a zuciyarta ita da zilai tace mata saude ta rasu tasha ko ta rasun ne yanzu suka samu labari. "Wuce ki koma daki abinki ki huta..." Cewar zilai, jimmalo ta koma dakinta zilaima ta koma dakinta se shewa takeyi tana tafe tana rawa kmr karamar yarinya kuma babbar mace ce ta girmema jimmalo nesa ba kusa ba. Koda jimmalo ta dawo daki kasa bacci tayi tadinga kiran Kande amma shiru, Sam kiran baya shiga, jimmalo ta kasa dena kira dukda tanajin wayar rufe amma se aikin kira takeyi..


Har wuraren 10:am Duk yadda ta kaiga san tayi bacci sam kasawa tayi, ta daura hannunta a kan cikinta taji sam yadena harbawa ya koma gefe daya ya dunkule, ta tashi zaune a hankali hadi da dafe gurin da babyn ya koma ya zauna, tayi addu'ur'i ta tofa a gurin saboda dr Mus'ab ya gaya mata in har baby ya dena motsi akwai matsala, nan take hankalinta ya tashi abin ya zamar mata goma da ashirin, ta kai 30mnt zaune tana addu'ur'i tana tofawa cikin nata kana taji ya fara motsa mata ta sauke ajiyar zuciyar nutsuwa kadan, ta koma ta kwanta, ta rintse ido Hadi da addu'ur'i ba jimawa bacci me nauyi yayi awan gaba da ita... Ko awa daya batayi dayin baccin ba tashiga wasu mugayen mafarke-mafarke a baccin nata, saude take gani tana binta zata kasheta, har tazo zata caka mata wuka kenan a ciki, ta farka a matukar gigice kadan ya rage ta fado daga bed din datake kai, wata murya nata ce mata ki gudu a gidan! A mafarkin..... Data tashi zumbur ta mike zaune,ta jike sharkar da zufa, nishi kawai takeyi da addu'ur'i, hankalinta ya kuma tashi kan tashin hankalin datake ciki, sound din muryar mece mata ki gudu!shike yawo a cikin brain dinta,. A zabure ta mike ta dakko rigarta doguwa tasaka hankalinta a makutar tashe, tasaka takalmin slifas ta fito compound din gidan sanye take da hijjani Army green, a matukar gigice ko karfi babu a jikinta, ta nufa bakin get,.. Securities suka zubo mata ido, tana isowa inda suke duka hau miko mata gaisuwa, sbda tashin hankali ko kallansu batayi ba, ji takeyi kmr ana zuba mata wuta a jikinta, Allah-Allah kawai takeyi ta fice a gidan dukda batasan ina zataje ba. Securities na kallanta ta fice a get na daya ba halin su hanata, sede suka bita da ido, ta fice a get na biyu ma babu wanda ya hanata sede suka bita da gaisuwa, get na ukuma ta fice a cikinsa babu wanda ya iya dktr da ita ba sam, saboda basu da damar hakan,.... Tafiya tashigayi a kan line din tana tunanin ina zataje, haka kawai seta tsinci kanta da raguwa a tsananin damuwar datake ciki data fito a gidan.. Tafiya tashigayi da kafafuwanta cikin sauri kai bakace akwai tsohon ciki a jikintaba, har ta fito kan ti-ti, taga motoci na wucewa a kan babban titin unguwar sarki wanda ze kaika kawo. Kawai ta miki hanya dukda batasan ina zataje ba, ta hau tafiya a ti-ti manya manyan motocin masu kudi nata tsayawa suna mata magana sun ga jar fata, sam ko cikin jikinta basu gani, ko saurarensu Almuqri'ah batayi ba se zuba sauri takeyi sam ma ta mance da ciki a jikinta, kmr wasa ta isa kawo pack,, tana isowa cikin pack din ta samu guri ta zauna nan kasa tanata nishin uban wahalar datasha na tafiya, mararta ta kulle gu daya, se nishi takeyi, ko miyaun bakinta da kyar take hadiyeshi, tinda ta taho bata huta ba seda ta iso pack din batasan ma ina take ba. Nan yan union sukayi mata caaa da tambayar "ina zakije yarinya! Kano ne ko Zariya ce, ko adamawa yola, yar fara matar manya..." Almuqri'ah ta dago tana me bin ko wannensu da ido. "Ai wannan dagani garin fulani zataje, domin kuwa bafullatana ce sak wannan ma tafi fulani kyau..." Cewar daya daga yan union din dasuka rufeta a kallah sun kai mutum goma. "Kwarai kuwa..." Sauran yan union din suka hada bakin fadar hakan,. "Taso ga motar garinku nan zata tashi daman harta cika, mutum daya ya rage...." Dayan dan union din ya fadi hakan kai kace yasan inda zataje, ba musu Almuqri'ah ta tashi da kyar tabi dan union din dayace mata ga motar garinsu can,. da kyar ma take tafiya cikin jikinta yayi lakur ko motsin kirki ya denayi sede kadan-kadan, kafafuwanta sun kukkumbura sosai duk ta fice a hayyacinta. Dan union din ta mata jagora ta shiga mota ta zauna daman mutum daya ya rage motar ta tashi, wadda take ta yamma ce domin tini ta safe ta tashi yanzu ana neman 4:30pm ne. Almuqri'ah na zama me Mota yace miko kudin motarki..." Almuqri'ah ta rasa yazatayi ita de bata da kudi, ta zubawa me motan ido, ta fiddo hannayenta biyu tana kallansu ta rasama yazatayi. "Ki kawo kudi akace so mukeyi mu tashi mu samu mu fita a kaduna dawuri saboda a nan garin matsalar hanyoyi take da barayi da masu garkuwa da mutane..." Cewar dreva din dayake gajere kmr a kife. "Banda kudi ..." Ta fadi da bebanci, nan take kaf mutanen dake cikin motar suka jiyo suka kalleta, maza sunyi yawa a motar mace daya ce tal wadda Almuqri'ah ta zauna kusa da ita a kalla zata kai 36yrs. Haka kawai dreva din yaji tausanta ya rufesa saboda ganinta nakasashiya, amma beda yadda zeyi saboda motar shima ba tashi bace. "Ba a tafiya ba kudi malama,sakko to bakima shiryawa tafiyarba ashe..." Cewar daya daga dan union din, Almuqri'ah ta sakko dreva din se kallanta yakeyi da yan motar, ta zubawa motar ido matar dake cikin motar ta zubo mata ido, tin sadda ta ganta dazata shigo motar taji tausan yarinyar ya kamata domin dagani tana cikin tashin hankali, again ga ciki a jikinta. Bude jakarta tayi ta kirgo kudade yan dubu dubu ta mikawa dreva din motar tace, dreva ya kalleta yace "Kudinnan na menene?'' Matar tace "Na biyawa yarinyarnan kudin motar tashigo muyita tafiya Allah ya kaimu lafiya, d'a na kowa ne Ai..." Matar tayi maganar zuciyarta na kara cika da tausan Almuqri'ah. Dreva yace "Haka ne kam..." Ya kalli Almuqri'ah yace "Shigo yarinya wannan baiwar Allahn ta biya miki kudin motar,..." Almuqri'ah ta kalli motar dame motar ya nuna mata, ta masa godiya da bebanci, matar tace "Bakomai yarinya D'a na kowa ne,..." Almuqri'ah tashiga motar matar ta matsa mata sosai hadi dacewa "Zauna a hankali saboda larurar jikinki......." Almuqri'ah tace toh hadi da gyara zamanta. Dreva ya shiga mazauninsa ya tada motar suka fice a pack din, Almuqri'ah nata kallan bakin window ita kadai tasan me takeji a zuciyarta, Abdoljalal ne ya fado mata rai ta lumshe idanuwanta, tana mejin bugun zuciyarta na yawaita, tasan har abadan bazata kara ganinsaba a rayuwarta. "Ina zanje?'' Ta tambayi kanta a zuciyarta, motarma data shiga batasan ina zata kaisu ba, ita de kawai tashiga mota, kuma tanajin sassauci a zuciyarta data shiga motar, tasan barinta gidan shine mafi alkhairi kwara ko ina ma zataje taje kawai inhar zata tsira da d'an dake cikinta,,,,zuciyarta ta cunkushe da dumbin damuwa,. Ammah dinta kawai takeso tagani ita kadai zata gayawa dmwarta , tasanma ko ganinta tayi zuciyarta zata nutsu,, ita da knta tasan tana kan jarabawar ubangiji,,, ''Alhamdulillahi ya ilahil alameen..." ta fadi idanuwanta na cikowa da kwallar dasuka wanke fuskarta shaaaaaaa.




Paid book ne.




36
jimmalo ta dan samu bacci kadan amma sam mara nutsuwa, se azahar ta tashi tayi wanka tayi sallah tunaninta na kan Almuqri'ah da halin da take ciki,, tana idar da sallarh ta fito ta nufo dakin Almuqri'ah, tana shigowa dakin taganshi a bude, tasa kai hadi da kiran sunan Almuqri'ah cikin sanyin murya. Amma taji shiru tashigo dakin taga bata nan , kuma taga toilet a bude, jimmalo ta leka taga bata nan, ta fito waje hadin da kwalo mata kira taji shiru, ta duba duk inda zata ganta bata ganta ba, a nan nefa hankalin jimmalo ya matukar tashi gashi tayima kande kiran duniyarnan amma waya bata shiga tini d'an kande ya dauki wayar ya siyar yaje yayi shaye-shayensa shida Abokanayensa da kudaden. Bakin get jimmalo ta isa ta tambayi securities ko sunga inda yarinyar tayi? Nan suka tabbatar mata data fita tin dazu, fuskokinsu cike da nadamar barintan dasukayi ta fitan ,sbda sunga ta jima taki dawowa. Hankalin jimmalo ya matukar tashi hantar cikinta ta kad'a nan take zazzabi ya rufeta. A matukae gigice ta tambayesu ko tagaya musu inda taje. Alnustapha Yace "bata gaya mana ba..." "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' Jimmalo ta fadi yayinda kanta ya buga,, ta fice a gets din gidan cikin hanzari take tafiya ko zata ganta. "Allah yasa ba guduwa tayi ba..."jimmalo ta fadi hankalinta a tsananin tashe, tinda Almuqri'ah tazo gidan tanada tabbacin bata taba fita ba se yau, to tabbas yau din data fito tasan da wuya in ba guduwa tayi a gidan ba. "To ina taje? Gunwa zataje da tsohon cikin jikinta na megida?'' Jimmalo ke fadi a bayyane kmr zararriya, tazama kamar mahaukaciya, tunanin Abdoljalal kawai ya fado mata rai. Har wuraren 6:pm jimmalo nata yawo a gari a kafa, tafi gabas, ta dawo tabi yamma, tabi kudu, tabi arewa Amma sam bataga Almuqri'ah ba ko me kama da ita ma bata gani ba..se bayan isha'i jimmalo ta dawo gidan securities suka bita da ido. Direct jimmalo dakin Almuqri'ah ta nufa dan ganin kota dawo amma taga bata dawo ba. Cikin tashin hnklim dabaze misaltuba jimmalo takoma dakinta taci gaba da kiran kande amma shiru waya bata shiga. Jimmalo ta fashe da kuka me kunar da zuciya, yau ko ruwa batasa a cikintaba , batajin zata iyashan ko ruwan ne a cikinta,. Ranar sam kasa bacci jimmalo tayi, ta rasa waxata kira ta gayawa damuwarta, lmbr kande bata har zuwa yanzu, ta kirata yafi 1m amma shiru.




*A asibiti*
Kwana doctors sukayi da wuni a kan hajiya saude amma sam taki dawowa hayyacinsa,, likitoci ma sun fara cire rai dazata dawo hayyacin nata, Abdoljalal ya shiga tashin hankalin dabe taba shigarsa ba,babban tashin hankalinsa besan a wani hali Almuqri'ah take ciki ba, taci ko tasha, besani ba, shifa dmwar ciwon saude kadan ne a ransa, yanaso yabar asibitin yaje yaga Almuqri'ah dinsa da babyn cikinta dayayi kewarsu amma ba hali saboda baze yu ya bar asibitin ba dole se an tabbatar daya sauden ta kasance, ko tunanin shan ruwa Abdoljalal bayayi dukda yanajin kishi amma sam be damu da hakan ba, gashi ko waya bezo da ita ba balle ya kira yarinyar yaji dadih,. tin a daren ranar dasukaxo asibitin yayi wankan tsarki a toilet din dr umar Abokinsa ne tare sukayi scul, sanadin kawo saude asibitin yaga dr umar din, Ahamad ya dakko masa jallabiya blue a motar Abdoljalal din ya cansa, dmn baya rasa kayayyaki a motarsa.


Abdoljalal ya gaji da kewar Almuqri'ah ya amshi wayar ahamad ya kirata amma bata daga ba, seda ya mata kira goma amma bata dauka ba, nan hankalinsa ya kara karkata zuwa gida, amma dole ya jure aga abinda hali zeyi a kan Saude, kaf 2days din da Abdoljalal da yayi a asibitin ko ruwa besha wa cikinsa ba yana tafiya iska na neman daukarsa, ahamad yayi-yayi yasha ko ruwan ne amma sam Abdoljalal besha ba, dmwarsa dayace Almuqri'ah, zuciyarsa na yawan bugawa a kanta,ji yakeyi santa na karuwa a zuciyarsa, yayi kewarta tmkar yayi 10yrs begantaba. Da kyar doctors suka samu kan hajiya saude bayan sunyi 3days a kanta, se cikin dare 2:am suka samu tadawo hayyacinta, suka mata Allurori aka bata daki, tare dasa mata drib. Da Asubahi Abdoljalal nayin sallar asubahi yayi lazimi a daddafe 6;am ya nufo gidansa ya bar Ahamad nan asibitin. se Allah-Allah Abdoljalal yakeyi ya isa gidansa domin ya ga Almuqri'ah d'an cikinsa, zuciyarsa na yawan bugu a kanta. Yana isa gidan yayi packing a tsakiyar gidan ko packing space bayajin ze iya isa saboda ya kagara yaganta. Ya fito ma'aikatan gidan se miko masa gaisuwa sukeyi ko amsasu beyi ba hankali da duk tunaninsa yana kan Almuqri'ah da bebynsa. Direct ya nufa dakin Almuqri'ah, securities dasuke kallanshi ko wannensu seda hankalinsa ya kara tashi, saboda sun san yau zasuci bura ubarsu daman tin tini suke cikin fargaba mara misaltuwa, su basusha cewa Almuqri'ah bazata dawo ba sunsha zataje ta dawo ne, shiyasa suka barta ta fita ba musu,suna tsoron dktr da ita sbda suna bata girma,, gabako daya de a lokacin basusan meya shiga kansu Ba suka barta ta fita.


Da sallama ya shiga dakin. , idanuwansa suka sauka a kan gadonsu, yaganshi kace kace ba gyara,, nan take yaji jikinsa ya masa wani iri,zuciyarta tayi ba ddh, dayaga bata dakin seyasha tana toilet ne dan haka ya nufa toilet din ya Ganshi a rufe yashiga toilet din hadi da
kwalo mata kira amma shiru, se yasha ko tana farfajiyarsa tashan iska, dan haka ya nufa can , yana kwalo mata kira, securities na kallansa duk suka sha jinin jikinsu dacewar yau zasuci durin uwarsu, tin tini basu shiga damuwa ba se yanzu. Jikin Abdoljalal har yana rawa ya isa farfajiyarsa tashan iska be gantaba. "To ko tana dakin wannan yarinyar .." Wato jimmalo yake nufi. dan haka ya juyo ya nufa part din ma'aikatan mata. da larai yaci karo, be taba zuwa part din masu aiki ba se yau,. sam larai batayi mamakin ganinsa a part dinsu ba, domin zuwa yanzu kaf ma'aikatan gidan mata sun san Almuqri'ah ta gudu a gidan,sun san komi dake gudana a gidan, amma suna nuna kmr basu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login