Showing 33001 words to 36000 words out of 159314 words
Chapter 12 - Wata Kishiya Complete writing by Sa'adatu Bint Abdullahi .txt
karayi bayn kallon data masa na farko, shi kuma ya fada wata fadama me nisa ta kyaunta, shi da knsa yasan ya zauce. Ganinta da yayi ya gano yadda akayi ta iya ire-ire girkin ummansa sbda dagani base an fadi ba ya fahimci balarabiya ce yarinyar "To me ya kawota aiki a nigeria?'' Ya tambayi knsa da knsa, ya rasa wanda ze basa amsa, murmushin dake kan fuskarsa ya kara fad'ad'a ya kure inda ta tsugunna gaidasa da ido, yaji de ta gaidasa amma ya gaza amsawa saboda ya shagala da kallonta a gaskiya dabeda karfin imani daze iya Narkewa daganin kyaun Yarinyar. "Alhamdulillahi..." Ya fadi a bayyabe yayinda wani sanyi me tattare da AC din ni'ima suka mamaye zuciyarsa sbda ganin yarinyar da yayi yasashi yin hamdalar dabesanma yayi ba, ko ince besan dalilin daya sashi yin hamdalar ba, kawai yaji a jikinsa akwai wani sirri a tattare da yarinyar nan daya gani, wani irin murmushi ya karayi me fidda sound fuskarsa ta kara fadada murmushin Annashuwar dake tattare da ita, ya mance when last yayi nishadi da farin ciki kamar na yau, haka kawai kuma ya kara tsintar kansa dasan kara ganin kyakyawar fuskar yarinyar, sbda ganin yarinyar kwantar masa da hankali yayi, yasan inya sake ganinta ma zuciyarsa zata kara nutsuwa, fin da...yafi karfin 1h tsaye nan yana kallon inda ta tsugunna ta gaidasa farin ciki se yawaita yakeyi a zuciyarsa,...juyawa yayi ya bar dinning room din se nishad'i yakeyi, ya nufa upstairs dinsa, yana tunano yadda yarinyar ta kwashe sauran kayan dinning din ta fice a falon dagani de tsoronsa ma takeji, wani murmushi ne ya subuce masa, tuna yadda ta gansa tayi hanzarin ficewa kmr taga dodo....
Bayan ta fice a side din nasa, seda ta samu guri ta zauna a waje ta maida ajiyar zuciya hadi da sauke numfarfashi, gabaki daya ganinsa chanza mata lissafi yayi, seda ta kwashi 30mnt tana maida numfarfashi hadi da tunano kyakyawar fuskarsa a kallon data masa duk tagano kyaunsa kuma tagane shidin dogo ne (wato mijin manyan mata), murmushi ne ya subuce mata a bayyane,, da kyar ta iya daddafawa ta nufa kiching din ta kimtsa komi a kiching din, da tunanin sa a manne da kasan a ranta, ta hada abubuwan datake bukata na breakfast dinsa gobe, kana ta nufa dakinta, ta kwanta da carbi a hannunta tana lazimi tana tunanosa, so takeyi tayi bacci amma ta kasa baccin dan hk mikewa tayi ta nufa toilet ta dauro alwala ta dawo ta hau kn dadduma ta fara nafilfili sallar dare. Sallarh takeyi amma rabin tunaninta na kan mutuminnan data gani yabi ya tsaya mata a rai ta rasa dalilin hakan, kuma yaki fita daga ran nata. A bangaren goganma hakan take koma ince tafi hakan, a dadduma shima ya kwana yana nafilfili amma zuciyarsa na kn yarinyar time to time se kaga kawai yasaki murmushi, be taba ganin halittar databi ta zauna masa a kahon zuciya ba kamar yarinyar nan , ya rasa yazeyi ganinta ya kara sa masa kwad'ayin sake ganinta again, be saba da yanayin da yake ciki ba, dan haka zuciyarsa kmr ta fito fili Allah Allah ya dingayi gari ya waye ya sake ganinta ko ze kara samun sassaucin gobarar dake nemsn tashi a birnin gonar zuciyarsa..bayan yayi sallar asubah ya kasa komawa bacci ya dawo falon ya zauna sanye da kayan bacci riga da wando butter milk masu tsantsi hadi da tafshi, ba karamin amsarshi kayan baccin sukayi ba face dinnan tasa tayi wani fayau da ita tayi haske irin hasken musulunci...Zaunawa yayi a falon yana kallon time 8:30am ya koma dinning room din ya zauna kawai so yakeyi yaga yarinyar daga jiya zuwa yau kansa ya juye gabaki daya ma rayuwarsa neman chanzawa takeyi, shi sam be saba da wannan mood din ba, shiyasa baze iya controlling ba, kwata-kwata yanzu ji yakeyi kawai a duniyar nan yarinyar kadai yakeso yayita gani ma a rayuwarsa yunwar cikinsa ma yadena jinta, yarinyar ce ta hanasa yin baccin yau, yasan wallahi in be ganta bama baccin baze ziyarcesa ba kwata-kwata shi kadai yasan tukikin da ransa keyi. Daura kansa yayi a kan dinning table din ya kwanta yana kallon kofa, se yaga kmr itan yake gani a jiyan, kawai se shape din bayanta ya fado masa rai ji yayi tsigar jikinsa ta tashi yarrr, a kallo daya ya gane yarinyar nada baya da cikar kirji, yana ganin mata dayawa amma be taba ganin mace kamar yarinyar ba ta zauna masa a kahon zuciya gashi dagani karama ce sosai....yana cikin tunani tunanin yarinyar bacci yayi awon gaba dashi me matukar nauyi. 9:43am ta shigo side din cikin sanda kmr munafuka zuciyarta se azabar bugu takeyi, idanuwanta suka sauka a knsa kasancewar fuskarsa na fuskantar bakin kofar shigowa, ido ta zubawa kyakyawar fuskarsa daganin yadda yake sauke numfashi tasan bacci yakeyi uwa uba kuma idanuwansa a kulle suke, karasowa tayi ta iso daf dashi ta tsura masa ido tana mejin zuciyarta na tsananta bugu, haka kawai taga ya mata kyau Ainun fin jiya data gansa...nan take ta tuna da klmn Hajiya saude a gareta a kn mijinta, saurin ajiye trea din hannunta tayi a kn dinning din kasancewar dinning din nada tsawo, ta juya zata fita ya dago yace "Ina zaki..." Daman tana shigowa yaji shigowar tata a kahon zuciyarsa kawai se yayi kamar beji ba yaji gaba da baccin karya. Duk yanajin sadda ta matso ta tsura masa ido , kasancewar ya dan bude idanuwansa kadan yana kallonta ta kasan ido, amma bata fahimta ba. Jin yace mata ina zaki yasata saurin juyowa ta zubo masa ido, itama idon taga ya zubo mata, amma ba fuskarta yake kallo ba, dan haka tabi inda yake kallo da nata narkakkun idanuwan wadanda suka fi nasa narkewa, nan take ta fahimci wato yatsun kafafuwanta yaketa kallo, sosai ya tsurawa yatsun kafafuwan nata ido, duk a harhade suke suna manne da juna yatsun kafafuwan nata sun matukar yi masa kyau, sun dauki hankalinsa, ganin yanata kallon yatsun kafafuwannata yasata dauke kafafuwan nata cikin hanzari tayi baya dasu, ya sauke ajiyar zuciya hadi da dawo da dubansa kn fuskarta suka hada ido, yayinda zuciyarsa tayi wani irin mummunar harbawa, a lokaci guda yaji wani sanyi na ratsashi daga kasa zuwa saman kwakwalwar kansa, be tabajin wannan yanayinba a rayuwarsa se a kn yarinyar nan...Al-muqri'ah kuwa tini ta dauke kwayoyin idanuwanta a kansa, sbda kwayoyin idanuwanta bazasu jure kallonsa eyes to eyes ba, shi kuma fuskarta ya tsurawa ido, dukse tabi ta rirrike jiknta sbda kallon da yake mata wani iri takeji a jikinta ta dinga wasa da hannunta a cikin hijjabin dake jikinta zumbulele sbda kada ya samu damar ganin kirjinta dan kunya takeji a dinga ganin nonuwanta, duk tafi tsanarsu a jikinta sbda mutane da dama nan sukafi kallo a jikinta kama daga jinsin mace danamiji. amma sede shi taga bema kai idanuwansa nan ba, a tunaninta batasan shidin nan din yake kallo, batare daya bari ta fahimci hakan ba, ganin tanata wasa da hannayenta a blue din hijjabin jikinta ya bashi yar dariya amma ya shanye yasan kirjinta ne bataso yagani shiyasa taketa tutture hijjabin daga kwanciya a jikinta, dariya ce taso subce masa amma ya daure, ya komar da idanuwansa kan hips dinta masu azabar kyau, nan take mood dinsa ya kara chanzawa jikinsa ya wani bi ya narke, , dago idanuwanta daza tayi taga yana kallon hips dinta, sauri tayi ta ture hijjabin daga kwanciyar da yakeyi a hips dinta, abinda ke bata haushi komin yaya tayi se anga hips dinnan nata daya zamar mata kaddara, lumshe idanuwansa yayi, ya dago ya kalli fuskarta duk tabi tayi wani tsuru tsuru kmr wadda tayi karya. Wani irin shu'umin murmushi Ya saki ciki ciki ta yadda bame fahimta se shi, ya rasa dalilin dayasa daga jiya zuwa yanzu zuciyarsa ke cike da nishadi. "Yasunanki?'' Tambayar ta fito daga bakinsa ba tare dayasanma yayi taba, wato fitar bazata tambayar tayi masa. Dagowa tayi ta kalleshi yayinda dadin muryarsa ya doki har kasan karkashin bishiyar zuciyarta, da hannu ta shiga nuna masa Alphabet din sunanta. Yabita da ido ta zana masa A da hannun duk yana kallonta kuma yana fahimtar yadda take masa kwatancen sbda kaf hankalinsa ita ya bamawa a lokacin, har takai karshe, kana ya hada farko da karshen a bayyane yace "Almuqri'ah?" Yadda ya kira sunan yasata zuba masa ido fuska cike da mamaki, duk duniya bata taba jin wanda ya iya kiran sunanta ba kmr shi, mamaki ya mamayeta na yadda ya gane me take rubi dukda kwatance ta masa ba a rubuce ta basa ba, sunanta nada tsananin wahala ga mutane ko a rubuce ta badashi ba kowa ke iya fadi dai-dai ba amma shi dai-dai ya fadi bako gargada, abin ya burgeta ainun kuma yasata A halwar nishadin daya mamaye kaf jikinta. "Me karatu sunanki?'' Ya kara fadi idanuwansa na knta, ya rasa dalilin dayasa yakejin dadin kasancewarsa da yarinyar, dadin dabe tabajin irinsa ba a duniya. Daga masa kai tayi alamar Eh "yasan fassarar sunana..." Ta fadi a zuciyarta yayinda mamaki ya kasheta tako ina. A bayyane ya lumshe ido ya bude hadi da maimaita sunan a zuciyarsa nan take zuciyarsa ta haddace sunan nata tsaf bako gargada. "Nice name,..." Ya fadi a bayyane yana me sake kureta da ido, kyaunta na kwantar da hankalin mumini tako ina ita din kyakyawa ce,. Jin yace "nace name..." yasata yin murmushin da batasan tayishi ba. Kara tsureta da ido yayi ganin tana murmushi seta kara kyau sbda dimples dinta uku dasuka lotsa a lokaci daya, na gefe da gefen kumatu dana kuma a kasan gemunta yake,. "Kinada Dimple's har uku?wow! You are very very beautiful...'' Ya fadi a bayyane ba tare daya sanma ya fadi ba cikin zazzakar muryarsa yayinda muryar tasama ta kara dadih a lokacin da yayi maganar sbda nishadin dayake ciki. Mgnr tasa ta doketa kuma taji dadin jinta daga garesa, dukda bashi kadai ya fara cewa tanada kyau ba amma kalmar a bakinsa setayi matukar yi masa dadin saurare a zuciyarta direct taji kalmomin sun afka kokin zuciyarta. "How old are you?''yayi mata tambayar ba control. Da hannu ta kara nuna masa 1 ta dawo ta nuna masa 6, ya fahimci me take nufi yace "16yrs?'' Ta daga mishi kai alamar Eh. A zatonsa ko hajiya saude ce ta hanata magana dashi danyasan zata iya han haka be matsa mata kn seta masa magana ba, ya tsura mata ido yana mamakin ashe karamar yarinya ce amma ta tare kaya haka uwa uba kuma ga iya girki tayi sosai tafi ma wata babbar macen me 60yrs. "Nagode da Abincin da kike dafamin me dadih..." Ya fadi idanuwansa na knta be taba maganganu haka ba, ba control kmr yau da yarinyar ta tsaya a gabansa, ji yakeyi gabaki daya kamar bashi ba. ta dago ta kalleshi Tana mamakin babban mutum kamar wannan yake mata godiya, a lokaci kankani ta fahinci shi mutumin kirki ne, murmushi ta sakar masa hadi da tsugunnawama ta masa godiya itama kana ta juya ta fice yana kallonta se murmushi yakeyi ji yakeyi daman karta fita ta zauna ya dawwama yana kallonta. "Yarinyar nada kyau...." Ya fadi yana ciza gefen lips dinsa na sama, bayan fitarta ta juya masa wadannan manyan mazaunan, be taba ganin kyaun mace ba a duniya kmr yadda yake ganin na yarinyar, be tabajin abubuwa a kan wata mace ba kmr yadda yakeji a kn wannan yarinyar daga jiya zuwa yau, tinda ya Auri saude be kara ganin kyaun wata mace ba se wannan yarinyar..... Breakfast yayi yana ci yana nishadi yana farin ciki yaci ya koshi sosai seya karajin dadin abincin sosai har brain dinsa. Nan ya zauna yaki tashi har ta dawo kwasar kwanukan, ta tsugunna ta masa alamar gaisuwa ya amsa fuskarsa kmr gonar audiga, yana ta kallonta harta kwashe kwanonin ta fice, kana ya tashi ya nufa upstairs da tunanin yarinyar a ransa yayi wanka ya kwanta yabi lafiyar gadonsa , yajima kafin bacci me nauyi yayi awon gaba dashi zuciyarsa cike da tsananin tunanin yarinyar, hadi da sabon yanayi...3tyms dinta na kawo abincin dana zuwa kwashewa warmers duk seda suka hadu dan kasawa yayi ya tsare, yau ji yakeyi kamar Allah ya masa bushara da shiga Aljannarh a jinin jikinsa yakejin wata kaddara na tunkarosa gadan gadan, yasan wallahi be isa ya tsallakewa kaddarar ba, amma fa besan ko wacce kaddara bace haka kawai zuciyarsa ta sanar dashi wata kaddara zata samesa, amma kuma zuciyar tasa na bashi tabbacin kaddarar alkhairi ce garesa sede fa yana yawanjin faduwar gaba wanda besan dalinsa ba.
** ** ** ** ** **
*Adamawa state (Yola)*
Misalin karfe goma shaabiyun daren ranar yau Litini. hajiya Ummusalma Zaune take a kayataccen bedroom dinta tana sanye da lallausar doguwar riga ta bacci wadda ta amshi launin fatarta jikinta, knta sanye da huta ta bacci milk color, kyakyawa ce ita ta ajin farko, dukda age dinta sun tafi amma hakan be hana kyaunta bayyana ba, tanada matsifar kyau hadi da azabar kyau, uwa uba kuma tanada dirin jiki, sosai farace sol, fatar nan tata kamar a taba jini ya fito ga kyau ga hutu ga kudi ga ni'imar musulunci. Zaune take a gefen hadadden bed dinta wanda ya hadu harya gaji da haduwa, gabaki daya furnitures din bedroom dinnata peach ne light. gadonta irin Italian bed dinnan ne ya hadu harya gaji da haduwa se azabar kamshi da sanyin AC kawai ke aiki a bedroom din nata, hasken lamp light ne kadai ke working bedroom dinnata. Kwata-kwata ta kasa bacci tsawon 3days kenan bacci ya gagari idanuwanta, wani irin azabar tiriri takeji yana taso mata daga kasan zuciyarta, yayin da hakan ya haifar mata dajin zafi a jikinta dukda sanyin AC dake aiki a dakin amma ita zufa tashiga yi, tin dazu takeso tayi kuka amma ta kasa yi, ita kadai tasan irin damuwar dake dawainiya da ziciyarta tsawon shekara da shekaru... A hankali ya turo kofar bedroom din nata ya shigo sanye da kayan bacci ligt Blue me haske, riga da wando ne masu kyau ba karamin kyau suka masa ba, dogo neshi sosai dukda shekarunsa sunja ga shugabanci amma hakan be hana tsananin kyaunsa bayyana ba. babu yawaitar haske a dakin amma hakan be hanashi hango ta ba can karshen bed ta rakube kmr wata marainiya, ajiyar zuciya ya sauke ya mayar da kofar bedroom din ya rufe harya karaso inda take ya zauna gefenta batasan ya shigo dakin ba, seda ya daura hannunsa a kan kafadarta sannan ta dawo daga rijiyar zurfin tunanin data fada, ta dago ta zuba masa ido shima idon ya zuba mata. "Yaushe ka shigo ranka ya dade?'' Ta fadi cikin muryarta da har yanzu bata rikede zuwa hausa ba, ji takeyi kmr ta fashe da kuka. ''Na shigo a sadda kika fada duniyar tunani.." Ya fadi hkn hadi da sakar mata murmushi me kwantar da hankali, amma sam murmushin nssa beyi tasiri gareta ba saboda bataji kwanciyar hankalin ba kwata-kwata. Jawo knta yayi ya daura a kan kafad'arsa yana me buga mata baya cikin sigar kwantar da hankali ya fara magana. "Bazaki sawa ranki hakuri ba ko uwar gidana?'' Kmr tana jiran yayi maganar kawai ta fashe da kuka tare da shashsheka kmr zuciyarta zata tarwatse haka takeji. Kara rungumeta yayi a jikinsa sosai yasa bakinsa a cikin kunnenta yana furta mata kalamai masu dadih, da kyar yasamu ta tsagaita da kukan amma still tana hawaye sbda batayi kukan daya wadaceta ba, ta dago knta dake jikinsa ta zuba masa ido kana ta fara magana "Zuciyata ta gaji da hkri....dan Allah Yallabainah yaushe saraki zezo gareni kmr yadda ko wacce uwa d'anta ke zuwa gareta? Zuciyata na cike da karaya a kan jalaluna dan Allah ka kirasa a waya kace yazo ya ganni inaso insa kansa a kirjina yaji dumin zuciyar uwa kmr yadda ko wanni d'a keji shima yasan shi d'a ne ba maraya ba..." Yadda take mgnr tini me martaba ya fahimci kmr tana neman fita a hayyacinta ne, Cikin muryar kwantarda hankali me martaba ya fara magana ta yadda knta ze dauka yasan abinda takeji a zuciyarta tanada dauriya a matsayinta na uwa kuma mace me rauni. "Zezo gareki insha Allahu salma, ki kwantardamin da hankalinki dan Allah kinga shekaran jiya dr ya duba jininki yaga ya hau..dan Allah salma kiji tausayina kisawa ranku dauriya kici gaba da Adduarh kmr yadda kk saba karki sabauta min rayuwarki dan Allah zan kirashi ince yazo ya ganki..." Ya fadi mgnr karshe ne dan hankalinta ya kwanta amma yasan koya kira dannasu da wuya ma ya daga, inma ya daga ba lallai yazo ba, gabaki daya tamkar basu suka haifesa ba haka yake rayuwarsa. Ajiyar zuciya ta sauke tasan mgnr daya fadi kawai danya kwantar mata da hankali ne, hawaye keci gaba da zirya a idanuwanta ta fara magana. "Nasan baze zoba me martaba,,," ta fadi hkn tana jinjina kai. Daura hannunsa yayi a kn cinyarta yace "muci gaba da Adduarh insha Allahu komi ze zama labari..." Girgiza masa kai tayi tana fadin "Kullum kullum inatayi Nagaji Wallahi, kasan zuciyata na cike da son yaronnan shi kadai Allah ya bani duk duniya wallahi me martaba ba wanda yasan me nakeji a zuciyata ko yau na fadi na mutu da yaronnan a zuciyata na mutu, San duniya da Allah yasamin duk ya tabbata ne a kan yaronnan, inaji a jikina kamar ba ranar da yaronnan zuciyarsa zata dawo garemu, .." Rufe mata baki me martaba yayi da hannunsa yace "karkiyi sabo knji iyalina, karki mnta da babu abinda yafi karfin ubangiji dan Allah kici gaba da hakurin danasanki dashi pls..." Daura kanta tayi a fuskar gadonta, ita kadai tasan wani hali zuciyarta ke ciki, gani takeyi abinda takeji ma a kan Abdoljalal koshi dayake ubansa bejin rabin abinda takeji, (wani abin se uwa kan uba