Showing 21001 words to 24000 words out of 159314 words
Chapter 8 - Wata Kishiya Complete writing by Sa'adatu Bint Abdullahi .txt
saude ta karashe maganar tana yatsina fuska. Hajiya kande ta amshe da "Dama mana hajiya yo Allah na tuba Ai mijinki babban mutum ne yau ko yan indian yakeso su dafa masa abinci ai ze samu, Allah na tuba kudi nefa tako ina Allah ya baku.." Saude ta yamutsa fuska tace "kundeji sharuddana kou?" Kande ta amsa "Anji ranki ya dade kuma dole abi ko ince anbi ma tini..." Hajiya saude tace "Yafi de...ynzu ku tashi kuje side din masu aiki kice larai tazo inasan ganinta dan dole wannan dund'um din seda waya sbda ta nan za a dinga mata messages din abinda zata dingama mijin nawa..." Kande ta karbe da "Dundum ma haka take wannan ai tafi dundum..." Saude ta yatsina fuska kana tace " nan zaki kwana ke kande ?'' Hajiya kande tace "Aah hajiya tafiya zanyi me napep ma na can yana jirana..." Saude tace "Okay ba dmwa ku tafi ki turomin laran de inajin yau yarinyar zata fara Aikinta mugani ya nata hannun yake..." Kande da tini suka mike tsaye ita da yarinyar ta kara amshewa da "Dama mana ta fara hajiya to meye amfaninta ai daman aikin tazoyi ba hutu ba, hutu aise ku dakukaci kuka tara..." Hajiya kande ta fadi zuciya cike da rashin imani. Saude ta tabe baki hadi da lalubar Aljihunta ta lalubo kudi yan dubu dubu kusan dubu talatin ta mikawa kande, kande ta tsugunna ta amshe jiki na rawa ta shiga antayo mata godiya ruwa ruwa, hajiya saude bata bi ta kanta ba tace "Sannan kudin aikin yarinyar nawa za a bata?'' Kande da bakinta yaki rufuwa saboda farin cikin kudin da saude ta bata tace "toh hajiya a bata abinda kikaga ya dace..." Hajiya saude tace "Okay...ya sunan yarinyar ne?" Kande tayi jim tace kai na mnta sunanta da wahala gaskiya. Saude ta daga kafada irin ko a jikintannan daman ita ko tasan sunanta ba amfani ze mata ba dan sunan duk ma'aikatanta daya ne a gunta Wato Ke\kai. Hjya Kande ta karama hjya saude godiya kana suka fice a falon, ta kai yarinyar gun sauran masu aikin nan wajen kiching sannan ta gayawa larai hajiya saude nason ganinta cikin hanzari larai ta tafi amsa kiran madam dinta. kande ta tafi cikin murnar abinda take bukata ya tafi dai-dai ko tace abinda aka sata,se hamdala takeyi a zuciyarta tana tafe tana waiwayon yarinyar , haka kawai kuma taji zuciyarta na cike da tausayin yarinyar, bata taba kawo me aiki taji tausayintaba kmr yadda taji tausayin wannan yarinyar har zuwa kasan zuciyarta, a hk ta fice a gidan zuciya cike da murna data fito tasha bazataga me napep din ba se kuma akaci sa'ah taga be tafi ba ashe yana nan yana jiranta hakuri ta bashi na barinsa datayi yanata jiranta, bakomai yace yana me jiran fitowar yarinyar danshi sbda ita ya tsaya jira da baze ma jirataba a wannan uban dadewar datayi, ganin hajiya kande ta shiga bega yarinyar ta fito ba. yasashi tambayar ina dayar dasuke tare. Hajiya kande tace " daman ai aiki na kawo ta tana cikin gidannan..." "Allah sarki..." Cewar me napep din, a zahirin gaskiya Sam me napep din ba haka yaso ba, yaso ya sake ganin yarinyar haka kawai yakejin san yarinyar na ratsashi. Wayarta dake cikin jaka ta dauko tayi dealing wata number wadda bata da suna se J kawai aka rubuta a kn sunan, hajiya kande tayi dealing number din bugu daya aka dauki wayar, hajiya kande tace "wasikarnan a gayawa me aikenta ta isa inda akeso ta isa fa akwai yar matsala ..." Daga cikin wayar akayi murmushi muryar wata dattijuya wadda a kalla zata girmema hajiya kandenta fara magana. "Alhamdulillahi karki damu da matsalar tinda tasamu mazauni kawai shikenan... muna fatan wasikarnan ta isa inda akeso ta isa domin aji dadin karatunta..." Hajiya kande murmushi tayi tace "Insha Allahu damo ze isa ga harawa...ai matsalar dama ba babba bace, tinda mun kaiga ci, a fari kin amsar wasikar akayi..." Daga cikin wayar dattijuwar tace "Alhamdulillahi kice ansha gwagwarmaya?'' Kande ta amsa da "Ai kadan ya rage wasikarnan ta yage ba tare da an karan tata ba....ammafa insha Allahu zama daram, wai me nakuda tasamu katifa..." Dattijuwar dake cikin wayar ta kara sautin murmushinta hadi dacewa "Bi izinillahi...yanzu zan idda sakon zuwa inda akayi aikensa , kema kuma taki wasikar na nan tana jiranki, domin kuwa zakisha tukuicin hidima..." Hajiya kande ta washe baki zuciyarta cike da zallar farin ciki tace "Godiya nake kuma a mikamin godiya bisa godiya...fatanmu de yanzu muji iska ta dauki farar takaddar nan ta isar da ita inda mukeso..." Daga cikin wayar dattijuwar matar tace "Inde kere na yawo zabo na yawo ai dole ne wata rana a hadu mujede zuwa..." Hajiya kande tayi yar dariyar nasara kana sukayi sallama da niyar kome ake ciki in an idda sako ga wadda tayi aiken takaddar kande zataji komi.
Nafa gaya muku akwai kulalliya a kasa amma baza ku fahimta ba se nan gaba.
*Vip 1k posting kullum normal Group 500 posting bayan kwana daya-daya 0542703718 Saadatu Abdullahi gt bank shedar biya ta nan 08101626484 ko M.T.N card ta nan 08101626484.*
*LITATTAFAN MARUBUCIYAR*
KYAUTAR ALLAH
INSO CUTA NE
DA BAN SANTA BA
BOYEYYEN AL'AMARI
YAR DANDI CEH
ABD NOW WATA KISHI
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500
Dial *131*4# or *460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call *08066268951*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*WATA KISHIYA*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌸🌸🌸🌸🌸🌸
*Littafin ma'aurata ne*
SAADATU BINTU ABDULLAHI✍🏽(writer of Kyautar Allah)
*DEDICATED TO SAYYADA SIDIYA KANO*
Free page7
Larai na isa Falon hajiya Saude byn an mata iso ta shigo ta taddata hajiya sauden inda su Kande suka batta zaune tana karkada kafa cikin izzar mulki, se cin kayan marmarin dake gabanta takeyi, ita daman inkaxo gidanta ko ruwa bata cewa a bata, shiyasa kande tayi dabarar zuqe lemu kwali daya dan tasan ba bata ko ruwa za ayi ba, itama ta lashi arziki. Jiki na rawa Larai ta iso ta zube kasa ta koro ma uwar gijiyar tata gaisuwa... ko amsa gaisuwar hajiya saude batayi ba ta tsaya tana karewa laran kallo baka ce ita tanada kyau dai-dai misali a kalla zata haura 35yrs, yawancin masu aikin gidan du zawwarawa ne, sbda acewar hajiya sauden sunfi juriyar zama da ita, dan kananan yarannan bala"in musu yawa yakeyi, ga uban aiki ga matsalolinta dan hatta da bangon gidan duk se anbishi an gogesa da sinadarai kullum da kullum koda kuwa beyi datti ba Tin 5:30am ma'aimatan gidan ke fara aiki a cikin gidan side dinta kadai sbda girmanda da uban falunan data tara se a kai 12:pm ana gyaransa, dan a kallah falunanta sunkai falo shida uku a kasa uku a sama, bedrooms dinta kuwa sun kai goma bakwai a sama uku a kasa, wasu bedrooms dinma bata Taba shigarsuba, amma dolen dole a gyarasu koda bata shiga ba, ga gida ba karamin gida ba, shiyasa takeda yawaitar ma'aikata, da ace tana sassauci da aikin yazo musu da sauki amma sam bata da sauki a duniyarta ko misqala zarratin, ba rahama a lamarinta. Hade rai hajiya saude tayi still tana karewa laran kallo kai kace yau ta fara ganinta, larai ko tini tayi kasa da knta tasan dalilin dayasa hjya saude take binta da kallon tako ina. "Ke baki da hijjabine kike yawo haka kasake-kasake dake koso kikeyi mijina ya shinshinokine dan yarannan ba haline daku ba shegu kunzo aiki kuna karewa mazan mutane kallo, mayun maza yan iska kawai..." Larai tayi shiru inda sabo ta saba da rashin mutuncin saude wanda yafi haka ma, dan haka ta toshe kunnenta kawai, sam ma batasan ba hijjabi a jikinta ba ta iso falon nata, jin ance tana kiranta yasata gigicewa batasanma ba hijjabi jikinta seda ta fara binta da kallon ta fahimci hakan.
"Bari ki sake in kara ganinki haka nan ba hijjabi zaki ci durun uwar uban kakan ubanki!, bake ba duk sauranma ki kara jadda da musu , yan iskan banza kawai shegu yayan karuwai mayun maza mabukatan maza kawai!'' Larai ta kara kasa da knta bata da katafus cikin kasa da murya tace "Ayi hakuri mommy..." Hajiya saude ta watsa wata uwar harara hadi dacewa a hasale "hakurin kanin ubanki ne daza kice inyishi shegiya da ido kmr na agolar nufawa..." Larai taja baki tayi gum hajiya saude tayi kwafa hadi da mikewa da kyar ragadadan cikinnan nata se up and down yakeyi, ga uban nonuwa rigija-rigija dasuka iso ga tumbin nata, sunbi sun kara kwanciya, kwara slifas din zuwa toilet a kansu, duk sun lakume kwata kwata nonuwan nata basu da lasisi. Cikin takunta me firgita muminai ta fara tafiya a falon ta nufa hanyar upstairs tana fadin "ke taso ki biyoni ...." Larai ta tashi jiki na rawa ta biyota a baya har suka haye upstairs din, suka isa bakin bedroom din hajiya sauden ta shige ita kuma larai ta tsaya a wajen ta tsugunna a kasa, domin ba a shigar ma hajiya saude daki mutum daya ke shigar mata daki shine me gyara mata dakin wato Samuel me dafa mata abinci Igalah ne shima daga can garinsu ta taho dashi. Bata fi 10mnt data shiga dakin ba ta fito hannunta rike da waya kirar infinix sabuwa dal hot8, a ka ida duk me aikin daxa a kawo gidan daman akwai saffin wayoyi android duk after 6months se an kawosu dayawa saboda bawa masu aiki amma ita saude bata bayarwa sam, yauma abinda yasa ta bada saboda ganin yarinyar bebiya ce bata san komi ba dole seda waya, kuma a ka'idar gogan duk me dafa masa abinci dole a bata waya. Mikawa larai tayi kwalin wayar, jiki na rawa laran ta amsa, hajiya saude tace "Wayar nan ki kaiwa yarinyar nan da aka kawo yau nasa sim a wayar.." Larai tace toh ranki ya dade..." Hajiya saude taci gaba da magana "Ki dauki key din dakinnan na waje ki dakko hijjabai guda goma zumbula zumbula ki bawa yarinyar sannan ki kara da gaya mata sharud'ana, ki kaita dakin daya zamana mallakinta ne n kwana...'' Larai ta amsa da Toh....saude taci gaba da magana " ki nuna mata kiching din da ake dafawa Saraki abinci itace zata dinga dafa masa abinci ke knyi aiki dame dafa masa abinci tada, ki nuna mata komi da komi sannan ki bata takaddar abubuwan dayakeso dasafe da daddare da rana a jere, ki gaya mata komi de dayake bukata, sannan ki dauko komi komi da ake bawa me aiki na bukatuwa ki bata, ta farayin wanka kafin ki fara nuna mata komi knji ni kou?'' Cikin hanzari larai ta amsa da "Eh naji ranki ya dade..." Hajiya saude taci gaba da magana "Yau nakeso ta fara aikinta ta masa abinci mara nauyi macaroni dinsa da farfesun kifinsa, ai akwai komi nasa a store dinsa kou?'' Cikin ladabi Larai dake durkushe a gaban hajiya saude tace "Akwai naga jiya ma an sauke komi nasa na amfanin abincinsa..." ( Dayake duk ending month se an kawo komi na bukatuwa gidan kama daga kn abincin hajiya saude har abincin masu aiki zuwa kan abincin shi gogan danshi ba komi yakeci ba na nigeria hatta da ashanar kiching din da ake dafa masa abinci duk daga waje ake kawosu saboda ya riga ya saba da abincin can tin scul da yayi a kasar fararen fata) Hajiya saude taci gaba da magana "toh ta fara komi yau a dafa masa macaroni da farfesun busashen kifin dayakeso da Allah ayi sauri, tashi kiyi hanzari ke!...." Ta karashe maganar hadi da daka mata tsawa cikin hanzari larai dake rike da wayar ta tashi a guje ta sauko daga benen. Hajiya saude ta tsaya bakin kofar tata nan tayi tsaye tana wasu tunanunnuka tayi kuri da idanuwanta a guri daya, tafi karfin 20mnt a tsaye a bakin kofar tata kana ta juya ta shige dakin nata zuciyarta duk a dagule ta rasa dalilin dayasa ganin yarinyar nan ya daga mata hankulanta hadi da dagula mata lissafe-lissafenta.
Larai ta samu Yarinyar inda ta batta nan cikin sauran masu aikin tajawo mata hannu tana rike da jakarta, yarinyar tabi larai da ido itama laran ita take kallo a zuciyar ta tace "Kai Allah yayi halitta a nan...kwankwatsi!" Direct larai dakin daze zama na kwananta ta fara kaita, yarinyar ta tsaya se bin dakin takeyi da kallo dakine me kyau wanda ke dauke da madaidaicin gado na kwanan mutum daya da bedside dinsa guda biyu, se Waldrop me murfi biyu, akwai dan karamin TV amma dagani ba a kunna sa ko ada can dan hk da wuya ma in yanayi, komi na furniture din dakin dark purple ne haka labukayen dakin ma light purple ne. Larai ta gyara mata dakin shap-shap sbda kurar da yayi. kana laran tasa mata yar ghana most go dinta a cikin Waldrop din, yarinyar ta zauna gefen bed din tana me karema dakin kallo akwai komi na bukatuwa a dakin. Larai ta mika mata wayar da Sauden tace a bata yarinyar ta amsa tana me zubowa larai ido alamar tana neman karin bayani a kn wayar, dukda taji hajiya tace daman za a bata waya . "Hajiya ce tace a baki wayar ai kin iya waya kou?'' Yarinyar ta daga mata kai alamar Eh, larai ta bita da ido tana mamakin ganin har yanzu yarinyar bata mata magana ba, ita kadai ke rawarta da kidinta, mikewa tayi ta fice a dakin hadi dacewa ina zuwa....'' Yarinyar ta daga mata kai alamar toh...hadi da duba wayar da laran ta bata taga wayar a kunne take, contact ta Shiga taga numbers guda biyu daya an rubuta Alhaji AAsaraki dayan an rubuta Hajiya saude, duk sauden ce tasa numbers din a wayar. Daman a ka'idar AAsaraki duk me dafa masa abinci se an bata waya wannan dole ne, kuma seya zamana yanada number dinta, ta yadda ze dinga gaya mata abinda yakeso da abinda bayaso, rayuwar dasukeyi shida saude kmr rayuwar turawa ce ba ruwan miji da mata ammafa ita matar tanada ruwa da mijin dan duk abinda yakeyi zuciya da kwanjinta na knsa itade babban tashin hankalinta taji labarin ya kalli wata wayyo shine babban tashin hankalinta, amma bata taba ko jin labarin ya kalli watan ba itama da kanta tasan shi mata basa gabansa hidimar gabansa kawai yakeyi, ita kuma tana Aikin hidimar kishinsa..... Kyar yarinyar ta tsayar da idanuwanta a kan number din dataga An rubuta AAsaraki, se maimaita sunan takeyi a ranta. A hk larai tazo ta sameta hannunta duka biyu rike da ledoji. Larai ta karaso yarinyar ta ajiye wayar a bedside hadi da zubowa laran ido, duka ledojin larai ta ajiye a kn gadon, ta cicciro hijjaban ledar farko, ta nuna mata manya manyan hijjabai ne masu azabar kyau kuma se laran ta zabo mata colors masu kyau, maron, pink, ash dark, sky blue, golden, pusher pink, black, dark blue, Army green, brown, sune kalolin hijjaban. Yarinyar tabi Army green din da kallo shine best color dinta army green, dark green, blue light, and dark butter milk, sune favorite color dinta. "Wannan naki ne su zaki dinga sawa kullum da kullum ki kasance da hijjabi sede in a kiching in kina aiki tinda baza kiyita fama da hijjabi ba ga aiki ga hijjabi seki cire hijjabin naki in kika gama aiki seki dauko kisa knji?'' Yarinyar ta daga mata kai alamar eh. Larai ta dauki hijjabs din tasa mata a Waldrop din, kana ta bude leda ta biyu wadda ke dauke da soso, da sabulun wanka na Detol dozing biyu mnya, se brush da Colgate, da Man shafawa me gurguwa guda shida manyan kwalbar, se man kitson soulmate rabin dozing, se turaren hammata guda shida, sannan se turaren jiki dozing daya, se panties dozing daya da pad din always itama dozing daya, se takalmi slifas irin na yan hudu guda biyu. A ka'ida abubuwan da AAsaraki yace a bawa ko wacce me aiki yafi haka amma ita Sauden ce ke bada san ranta sauran abubuwan tayita ajiyarasu saboda mugun hali da bakar zuciya kuma babu abinda zatayi dasu, har atamfofi guda ashirin ashirin ya dace a dinga bawa ko wacce me aiki in aka kawota gidan amma ina ita gimbiyar yan wadannan abubuwan kadai take bada izinin a bayar. Bayan larai ta gama nunawa yarinyar komi ta bata sabulu daya a cikin dozing biyun sabulun da aka bata da soson wanka tace taje tayi wanka, sauran kayayyakin ta kwashe tasa mata a Waldrop din. Yarinyar ta isa bakin kofar bathroom din se kuma ta dawo ta bude Waldrop dim da Larai ta ajiye kayayyakin ta dauki brush da Colgate din, ta zuge jakarta ta dauki dan zanin dazata daura in tayi wankan, kana ta nufa bandakin larai na kallonta a zuciyarta tace "Dagani yarinyarnan zatayi tsafta..." Mikewa laran tayi ta isa bakin kofar toilet din tace "Kiyi hanzari ki gama..." Yarinyar ta taba kofar alamar taji, larai ta fice a dakin tana mamakin yadda har zuwa lokacin yarinyar bata mata magana ba. Zama larai tayi a bakin kofar dakin tana me jirn fitowar yarinyar daman ta fito daga dakinne danta bata guri intayi wankan ta samu dmr kimtsawa....seda larai ta farajin motsi alamar yarinyar ta fito harma ze isa ta shirya kana ta shigo dakin, tasameta tsaf tana sanye da doguwar rigar material A-shape material din ya amsheta kwarai da Aniya, kasancewar color dinsa,Army green ne irin dark dinnan sosai me adon flowers light