Showing 57001 words to 60000 words out of 159314 words

Chapter 20 - Wata Kishiya Complete writing by Sa'adatu Bint Abdullahi .txt

fice yana kallanta, dukse yaji kunci ya rufe masa zuciya, wato de har yanzu fushi takeyi dashi,. Kasa cin abincin yayi, kawai ya tashi ya haye upstairs zuciya ba ddh, yayi wanka, yana ta tunani tunani,. Ya dawo kasan a nan yayi azahar , yayi la'asar, duk dan ko ze ganta amma ina taki zuwa, sede larai kawai yaketa gani, wadda tazo ta kwashe komi data ajiye yadda ta ajiyesu yaki cin komi to ko yunwa ma beji, yunwar ganinta kawai yake. Da daddare da larai tazo kwashe abincin daren data kawo ta ganshi a zaune ya dake ya tambayeta ina ita yarinyar?'' Larai datake tsugunne tace "batajin dadih ne zazzabi takeyi, girkinma a daddafe take yinsa..." Hankalinsa yayi matukar tashi jin tace wai zazzabi yarinyar keyi, "to ya jikin nata?'' Ya fadi cikin tashin hankalin daya gaza boyuwa a kn fuskarsa. Larai ta amsa da "Dasauki ranka ya dade...amma har fadawa ta danyi , ai danma yarinyar nada dauriya wallahi, ciwon kwana daya dukta zabge, inajin zazzabin cizon sauro ne, dan wannan dakin nata baze rasa sauraye ba..."cewar larai fadi ba a tambayeka ba. Ai nan hankalin Abdoljalal ya kuma tashi, kawai dannewa yayi yace "Allah ya kara sauki..." Abdoljalal ya fadi murya cikin tashin hankali. Larai ta kwashe kayan ta fice. Ya furzar da wata iska ta tashin hankali, daga bakinsa, kana ya mike ya fice, fitowa harabar gidan yayi, yana kallon larai ta gama gyara kiching din ta mayar ta kulle kiching din Ta nufa nasu bangaren. Abdoljalal bega yarinyar ba se hankalinsa ya kuma tashi, haka kawai yaji a jikinsa ciwon nata ba kadan bane. Seda ya tabbatar da larai ta kai side dinsu na masu aiki. kana ya nufa dakin nata, zuciyarsa nata tsananta bugu kmr zata fashe, ya isa kofar dakin ya taba handle yajishi a kulle jikinsa har yana rawa, ya shiga aikin knocking din dakin, al-muqri'ah dake kwance zazzabi ya Kuma lullubeta se rawar sanyi kawai takeyi, ta lulluba da bargo,, taji ana knocking, Mikewa tayi da kyar tasha ko larai ce ke buga dakin, ta karaso ta bude dakin ta koma ta zauna gefen bed din tana ganin jiri, tasan sanadin ganin jirin nata dan bata cin abinci ne, saboda kwata-kwata batajin dadin komi a duniya tasan saboda rashin ganinsa ne duk yasata a rashin jin dadin duniyarta ma baki daya,,, ga ciwo ga damuwarsa da batasanma tanayi ba..


Turo kofar dakin yayi ya shigo jikinsa har yana rawa ya kagara yasata a idanuwansa, ko ze samu kwanciyar hankali,. Kamshin turarensa ya doki hancinta yayinda tayi saurin dago idanuwansa ta zuba masa su, ji taji zuciyarta tayi mummunar harbawa, taga shi ma itan ya zubowa ido, daga jiya zuwa yau har ta rame, amma fa yafita rama,. Ganinta yasashi nan da nan yaji tausanta ya kuma lullubesa,, a bangaren al-muqri'ah kuwa ganinsa seya tunasar da ita abinda ya faru tsakaninsu na duwawuknta da yayita matsa mata su, gashinan har yanzu ciwo ma suke ta mata, saurin kauda fuskarta tayi gefe, tanajin kmr yanzu abinda ya faru tsakaninsu ya faru. "Yarinyata..." Abdoljalal ya fadi ba kunya ba tsoron Allahn duwawuknta daya gama mammatsawa amma wai yanzu yake cewa wani yarinyata. Ta dago ta sake kallonsa , seta dauke idanuwanta, Abdoljalal ya bita da kallon kewarta da yayi, yayin da the more yake kallonta the more zuciyarsa ke tsananta bugu a knta.
Karasowa yayi hadi da sosa keya danya fuskamci har yanzu fushi takeyi dashi. Ya zauna kusa da ita gefen bed din yana zama tayi zumbur ta mike, ta koma can bedside ta zauna, se kumbura fuska takeyi.. Abdoljalal de ya bita da ido. "Ya jikinki yarinyata..." Ya tambaya fuska cike da damuwa. Tajisa amma ta masa banza, ya kureta da ido kmr maye duk tabi ta zurma kmr tayi 100days tana ciwo., dawo da idanuwa sa yayi yabi dakin da kallo, har zuwa kan bed dinta, idanuwansa suka sauka a kan wayarta da hajiya saude ta bata sanda aka kawota.. Hannunsa har yana rawa ya kai ya dauki wayar, direct contact ya shiga yaga number guda biyu ne kawai, da number dinsa dana hajiya saude, ya shiga miss call yaga ba a taba kiran wayar bama, ya sauke ajiyar zuciya da har kishi ya motsa masa, yasha ko waya take tayi da maza, se Allah ya rufa mata asiri. Cewarsa. Dealing number dinsa daya gani a wayar yayi yaji akwai card, kiran na shiga ya kashe wayar yayi message ta yadda ze gane lambarta ce, kana ya ajiye wayar inda ya dauketa duk tana kallonsa, yana ajiye wayar ya dago ya zubo mata ido, tayi hanzarin dauke idonta a knsa, ya karasa ya taba jikinta, yaji wani irin zafi rau, jin ya taba mata jiki tayi hanzarin mikewa ta nufa toilet ta kulle yabi duwawuknta da kallo, mikewa yayi ya nufo toilet din danya fahimci ma kamar duk ta tsaneshi ne ne ynzu. Tsayawa yayi a kofar toilet din yayi juyin duniya ta fito suje asibiti amma taki fitowa, har wuraren 2:am yana nan yana dakin amma taki fitowa dole ya fice ya bar mata dakin, tanajin ya fice ta fito ta kulle dakin ta koma ta kwanta tanajin kanta na mata azabar ciwo, dukda tanajin haushinsa amma ganinsa ya haifar mata dajin sanyi a ranta....


Haka ya jera 1week yana ziryar dakin, wani lokaci ya sameshi a bude wani lokaci a kulle, tinda ta gane ma, yana zuwa take rufe dakinta, inyazo yayita juyin duniya ta bude amma taki budewa har yanzu fushi takeyi dashi ga zazzabi tana fama dashi, duk tabi tasashi a usumar rayuwa, sati daya be gantaba ji yakeyi kmr ze haukace, kansa ya dauki zafi yana tafiya yana layi, kmr mahaukaci haka yake jinsa a kwanakinnan, ko abincima ya dena ci. Ya shiga damuwa harya gaji da damuwa... Ko abincinma ta dena fitowa dafa masa, yasan duk sanadin matsa duwawune da yayi, gashi ansashi ababbar bala'i kwata-kwata ko bacci beyi, kwana yakeyi yana kwallar tashin hankali, be taba tabbatar da meye matsifar duniya ba se akan yarinyar nan, sam shi besanma tashin hankali ba se a knta. 10;pm yazo ya tsaya a bakin kofar dakin nata, yaci saarh yana taba handle din dakin nan take dakin ya bude, seda ya sauke ajiyar zuciya ya sako kai cikin daki da sauri kmr an jefosa, idanuwansa suka sauka a kan larai dake zaune gefen bed din ita kuma al-muqri'ah tana kwance ta lullube rub, har kanta da bargo, ganinsa a dakin yasa larai a mamaki, ta tsugunna ta gaidasa ya amsa, amma hankalinsa na kan al-muqri'ah, karasowa yayi, ya yaye mata bargon data lullube dashi, wani irin zafi da tiririn dake jikinta ya dokeshi,. "Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un!'' Ya hau salallami cikin tsananin tashin hankalin dabe taba shiga kwatan kwacinsa ba se yau,, ya zuba ma kyakyawar fuskarta ido, duk tabi ta karayin haske amma ta rame sosai, idanuwanta a kulle suke amma taji shigowarsa har zuwansa kanta duk tanaji bata bude idontaba. Jikinsa har yana rawa ya fice a dakin ya nufa side dinsa cikin gudu gudu, ya dakko car key dinsa, ya isa packing space da knsa ya dakko mota zuwa kofar dakin yarinyar, duk ma'aikatan gidan sun shiga mamakin ganin saraki da kansa yau yake driving, abinda wasu basu taba gani ba se yau, shi sam baya tukin mota sede a tukashi. Yana ajiye motar a saitin kofar dakin ya fito cikin tashin hankali, Da knshi ya tasheta zaune ya bata takalmi tasa, ba tare data masa musu ba, larai dake tsaye tana kallon munafunci da kwa-kwaf ganin gogan na niyar ya kamota yasata Saurin kamota cikin hanzari dantaji yana cewa asibiti zasuje. Laraice ta kamo masa ita har cikin motar, ta shigar da ita mazaunin gaba, duk jikinta yayi lagwa lagwa zazzabi ya karar mata da karfin jikinta. Abdoljalal ya shiga yaja motar suka fice a gidan. Nan larai ta tsaya bakin kofar dakin, tana mamakin wai Saraki ne yau da daukar me aiki a motarsa. "Tabbas da wata a kasa..." Larai ta fadi a bayyane hadi da rike haba, tin a fuskar gogan ta fuskanci abubuwa dayawa a kan yarinyar ammafa sede maganar nan bazata fito fili ba, wane mutum wane aikinsa.




Se hakuri da typing error ba editing.


Vip 1k normal 500 0542703718 Saadatu Abdullahi gt bank shedar biya ta nan 08101626484 ko M.T.N card.




SAADATU BINTU ABDULLAHI (writer of Kyautar Allah)


Page15
Tirkashi! Nan fa Ma'aikatan gidan suka rikece da gulma ammafa gulma ta zuciya domin wannan magana bazata faso fili ba, kowa sede yasawa bakinsa linzami, laf ma'aikatan gidan na cike da alhini amma ga iya wada'da suka gani, ko labari kowa ya kasa bawa dan uwansa saboda kada kace kai nace, ammafa alhini be barsu ba, dan a tsawon shekarun aikinsu a gidan basu taba ganin saraki ya dauki me aiki ba a motarsa, sun kula asibiti ze kaita, domin tin bata da lafiya larai tazo ta shafa musu labarin bata da lafiyar, amma fa yanzu bataso tace dasu komi ba, sede tayi wucewarta ta koma bakin aikinta a zuciya kadai taketa juya lamarin amma harshenta baze iya tattauna maganar da kowa ba,. "Wace ni bakina kanin kafata..." Larai ta fadi a zuciyarta tana meci gaba da aikin gabanta.




Yana driving yana kallonta cike da tausayawa, yayinda hankalinsa kwata-kwata Be jikinsa, zuciyarsa na kanta, se rawar sanyi takeyi har zuwa lokacin. Karatun alqur'ani yasa a cikin motar, saboda duk zafin ciwo inde za asa karatun alqur'ani me girma a kusa dame ciwon insha Allahi ze samu sassaucin ubangiji. Da temakon Allah kawai ya isa wani dankareren private hospital wanda yafi kusa dashi, ko kusa be tinkari zuwa asibitin dr mus'ab ba saboda yaanada nisa.. Packing kawai yayi ya fito ,ya bude mazaunin datake, yana niyar daukanta cik ta sakko da knta, cikin dakiya ya kamo mata hannu, ta kwace hannunta, asibitinma dabadan ciwo ya addabetaba da bazata zoba wallahi kawai bata da choice ne. Kaf mutane suka zubowa Al-muqri'ah ido dukda tana cikin ciwo amma se kallonta akeyi saboda tsananin kyaunta Abdoljalal se hade girar sama data kasa yakeyi, bakin ciki ya cikasa,. A jere suke tafiya shida ita Abdoljalal se kallonta yakeyi, yanata wani kakkareta, dukda darene amma asibitin nada yalwar haske kai kace rana ce, hakan ne ya bawa masu kallonta damar kallonta. "Sannu Allah baki lafiya..." Ya fadi kmr zeyi kuka yayin da yakeji kamar ya ciro ciwon yasa a jikinsa, jinyarta tafi masa zafi a zuciya a kan tasa jinyar, da ana cirewa daya ciro ya hada da nasa ciwon.. Ba bata lokaci sukaga dr a asibitin, Abdoljalal yace dr mace suke bukatar gani, dole kuwa dr macen al-muqri'ah tagani, ba wani lalata lokaci aka mata gwaje-gwaje nan ana gano maleria ce, da ulcer. Nan take aka basu gado, aka shiga bata temakon gaggawa, aka mata allurori ba jimawa bacci yayi awon gaba da ita akasa mata drib. Abdoljalal dake zaune kn kujera yana facing dinta, tausanta dukya rufesa, ansha gwagwarmaya da ita kafin ta tsaya aka mata allura besan matsoraciya bace se yau, da kyar ya riketa ta yadda aka mata allurorin, ance fararen mata basu da kwari, ita de kyakyau take tanada karfi danshi kansa dabadan yanada karfinfa da yau baze iya riketaba. Sosai ya kurewa kyakyawar fuskarta da ido, yayin da santa ke yawaita a birnin zuciyarsa, se numfashi take saukewa na rashin lafiya.... Har wuraren 12:2am yana zaune yana kallonta, kana daga bisani ya mike yaje ya kira wata nurse yace ta kular masa da ita, zeje ya dawo...." nurse Munirat tace toh sir..." se wani kwarkwasa take masa tana jujjuya rigiza rigiza din nonuwa kmr jarkoki, da uban duwawuka abin de ba tsari, kmr a kifeta da kwano, ko kallo bata isa Abdoljalal ba, shi besanma tanayi ba, a duniya mace daya ya taba gani yaji sha'awarta ta fitar hankali itace al-muqri'ah, kuma yasan itace last...




Bayan ya fito harabar asibitin ya shiga Motarsa yaja ya fice a asibitin, yana tafe yana mamakin wai yau shine Ya fita shi kadai ba tsaro, kuma da motarsa, shi da kansa yasan yana cikin hatsari amma fa se yanzu ya fahimci hakan, dazu be fahimta ba, saboda be cikin nutsuwa amma yanzu nutsuwa ta fara kusantoshi, adduarh yashigayi na neman kariyar ubangiji.... Direct babban kayataccen restaurant ya nufa ya siya abinci kala hudi, da farfesu kala biyar, akasa mishi a mota,,,, yaja motar ya karasa super market ya Shiga yayi mata siye-siyen abubuwa Da dama na makulashe,, ya koma bangaren kayayyakin sawa, ya siya mata abaya kusan kaloli asirin, se hijjabs masu kyau na kamfani, kala ashirin duma, da breziya danya kula kullum yawo takeyi ziryarta ba breziya, bata killace wadannan nonuwan shiyasa ya siyo kata bra danta dinga killacesu. Yase musu duk wani abu dazasu bukata. Bayan ya biya Aka kwashe masa kayayyakin akasa masa a mota, yayima wadanda suka kawo masa kayan motar ihsani kana yaja motar ya bar harabar mall din ya nufa asibitin duk yabi ya kosa ya isa yasata a idanuwansa ko zeji kuma jin dadih, hatta numfashinta datake saukewa ji yakeyi kamar a zuciyarsa take sauke numfashin, ta riga ta jima da zama jijiyoyi masu amfani a jikinsa. "Ina sanki...." Ya fadi yana driving amma ji yakeyi kmr yana gabanta, seda ya saki murmushin nishadi. Yana isa asibitin ya fito ya fara kwaso kayayyakin motar ya fiddosu waje, a guje securities din dake gadin asibitin suka iso suka kwashe kayan daya firfito dasu , ya musu jagora zuwa dakin da aka kwantar da ita, suka shigo suka ajiye kayayyakin suma ya nusu ihsani, suka amsa suka masa godiya suka juya abinsu, daman basu shigo ba a bakin kofar dakin suka tsaya, shi ya karaso da kayan cikin dakin. Karasowa yayi bakin gadon idanuwansa na kanta, har zuwa wannan lokacin bacci takeyi sosai se sauke numfarfashi kawai takeyi na bacci. Munirat dake zaune kn kujerar dake fuskartar Al-muqri'ah , se kallon al-muqri'ah takeyi tana yabawa da halittar da Allah yama yarinyar. Tana ganin Abdoljalal ya dawo ta wani fara kwarkwasa, ta zubo masa ido tin shigowarsa. "Ya jikin nata bata farka ba kou?'' Abdoljalal ya tambayi munirat idanuwansa na kn al-muqri'ah. "A, bata farka ba sir ,,,jikin nata da sauki a hankali zata warware duka insha Allahu. ..." Munirat ta fadi tana ta wani sanabe. Abdoljalal ya mata godiya, ya sallameta ya bata kudade 30k ta amshe se godiya takeyi ta fita zuciyarta fal farin ciki nan ta kara fadawa san guy din, dan dagani yanada danshi a hannunsa, ita danshinne ke janta.


Zaunawa yayi inda munirat ta tashi, ya kara kureta da ido, numfashinta nata fita a hankali a hankali dagani yasan tana jin jiki,. Muaahhh!! Ya karasa ya manna mata kiss a kumatunta saboda ji yayi kawai wani abu na fusgarsa a zuciyarsa game da ita. Bata farkaba se 1:30am ,ta farka da salati a bakinta, ta bude idanuwanta a kansa, taga shima itan yake kallo, haka kawai taji wani abu na ratsata me wuyar misaltuwa, in har taganshi se zuciyarta ta amshi wani irin sako da batasan wanne neba. "Sannu ya jikin naki ?'' Ta amsa da "Dasauki..." Da bebanci,,, yayi mamakin yadda ta amsa wato de yaga alamar ta fara sakkowa, daga uban fushin da akeyi dashi. Tashi yayi ya nufa toilet ya dakko wata roba sabuwa dal domin komi na asibitin tsaf yake, ya dakko ruwa a cikin kayayykin daya siyo, ya bata ta kuskure bakinta, ta zuba a robar yaje ya zubar kana ya dawo ya dakko abinci ya bata taci kadan, danma yanata lallabata kmr kwai. ya dakko maganungunan dasuka bada sukace a bata inta farka taci abinci, ya bata maganin ta kauda kai, nan ma ya fahimci har maganin ma bataso kenan. Lallabata yayi da kyar ta amsa tasha, se binsa takeyi da ido, yanata dawainiya da ita, wani abu ta dingaji a game dashi a zuciyarta, saboda dawainiyar dayakeyi da ita se taji ma ya bata tausayin da batasan dalilinsaba. "Kin yafemin pls?'' Ya fadi hadi da marairaicewa yayinda yake zaune yana kallonta. Daga masa kai tayi alamar Eh.... Ajiyar zuciya ya sauke na zallar farin cikin ya fara shawo knta tinda harta yafe masa... 2:30am ta koma bacci, shikam gogan be rintsa ba, se aikin kallonta kawai yakeyi har asubahi yayi sallah, bayan drib dinta ya kare ya cire mata. Itama tashi tayi tana mejin karfi a jikinta, ba kamar jiya ba, ta kalleshi yana kn dadduma ta nufa toilet, Tana shiga toilet din ta ganshi tsaf tsaf da sababbin brush. brush din tayi, taga komi sabo ne na bukatuwar toilet din, ga ruwan zafi, dan haka wanka tayi ta maida kayan jikinta ta dauro alwala ta fito taga benan, a dakin, taga ya ajiye mata kaya a kn gadon asibitin ta duba taga abaya ce da hijjabi, dauka tayi tasa ba karamin amsarta kayan sukayi ba musammanma hijjabin ya matukar mata kyau, ya amsheta ainun kalar abayar maroon ce, se hijjabin milk color ne, ita knta kayan sun mata kyau, se godiya take masa a zuciya. Ta nufa dadduma tayi sallah ta taso ta zauna gefen bed din kenan,dr da nurses suka shigo har zuwa lokacin be dawo ba yaje gida ne dan yayi wanka ya dakko wayoyinsa, jiya rudu be barshi ya dakko wayoyin nasa ba, kuma yasan dole ne za a nemeshi a wayoyinnasa. Dr ta dubata sosai ta mayar mata da wani drib din da allurori a ciki dan tin jiya gogan yace kawai kar a sake mata allura a jiki sede a zuba mata a drip in zeyu dr tace bakomai,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login