Showing 24001 words to 27000 words out of 159314 words

Chapter 9 - Wata Kishiya Complete writing by Sa'adatu Bint Abdullahi .txt

green ba karamin amsarta kalar yayiba, abinka da farin mutum kalarsa komi akasa mata kyau yake mata, se kamshin turarrukan da aka bata takeyi. Larai ta zubo mata ido kyar kirjinnan nata cike luntsum-luntsum da nonuwa tsayayyu wanda hatta da kan nonuwan duk ana gani kasancewar rigar taso ta dan kamata, dukda rigar taji jiki ammafa ta mata tsananin kyau. Kasancewar kanta ba dankwali hakan ya bawa larai damar ganin cukurkudadd'en sumar kanta wadda ta zubo mata har gadon bayanta zuwa duwawuknta mnya-manyannan wadanda suma suka cika rigar dake jikinta. "ya subhanallahi!'' larai ta fadi a bayyane yayin data karaso ta shafo sumar kn yarinyar matsalar gashin ba gyara, a farko larai tasha gashin doki ne seda ta taba ta tabbatar da gashin yarinyar ne, mamaki ya rufeta ta rike baki tana salallami hadi da salatuttuka "La'ilaha ilallahu ni Larai²×, oh muna ganin indian a TV yau ga Indian har gida Allah ya kawo mana ita..." Jin abinda larai tace yasa Yarinyar yin murmushi hadi da mikewa tsaye ta dukunkune sumar kan nata ta dauresa larai na tsaye tana kallonta se doko salallami takeyi hadi da hailala wasu tayisu completely wasu kuma ina, daman bata iya ba dan bashan inuwan Mkrntar allo tayi ba sbda kauyensu kauyene na karau, burin iyayensu in suka haifa yara mata sukai 10yrs su musu aure sam iyayen yara basa nemawa yaranasu cigaba dukda akwai makarantun gwabnati a garin, da isilamiyoyi amma sam su yan garin basa zuwa da Anga yarinya ma tana zuwa boko shikenan za a hau gulma ace tazama yar iska me bin maza(Allah ya rabamu da jahilci wanda yafi hauka wuyar magani) "ke yarnan ya sunanki ne dan Allah? Amma daga indian kikazo ko?'' Larai dake tsaye ta zubo ma yarinyar wadannan tambayoyin masu cike da sambatu hadi da dimauta, itafa tinda uwarta ta haifota bata taba ganin farar fata bama face to face kamar wannan yarinyar ba se yau shiyasa ta dimauce iya dimauta. Yarinyar data juyo ta kalli Larai ta sakar mata murmushi hadi da kokarin bude baki ta fara magana cikin karyewar harshe hade da bebanta, se a lokacin matar ta fuskanci ashe bebiya ce, wani irin ruwan maliyar tausayin yarinyar ne yayi tsalle ya wanke ma larai zuciyarta nan da nan se taji madarar tausayin yarinyar ya wanke mata makoshi, kawai se taji idanuwanta na cikowa da ruwan hawaye, ta girgiza kai hadi dacewa ''Oh duk wannan halittar da ubangiji ya zuba, ga baya ga tudu biyu luntsum-luntsum, ga madubi me kyau, mace iya mace, kaya iya kaya , Amma Allah ya tauyeta ta hanyar magana Allah sarki!'' Cewar larai murya cikeda tausayi, nan da nan hawayen tausayi hadi da imani suka wankewa laran fuska yarinyar takai hannu ta share mata hawayen sbda duk tanajin me laran ke cewa, hijjabin larai ta dauko ta bata black color cikin sabbin hijjabs din da aka bata, tasaka hijjabin yaxo mata har zuwa kasan kafafuwanta, sosai hijjabin ya amsheta ya mata kyau ainu. ganin time na tafiya yasasu ficewa a dakin, suka nufa kiching, da kiching din da dakin nata ba nisa ita dakinta ba kusa yake da dakunan masu Aiki ba, an wareshi ne daban kuma yafi ko wanni dakunan masu aiki kyau a ciki.


Suna isa kiching din nan yarinyar ta saki ido tana kallon ikon Allah da zallar dukiyar da aka zubawa kiching din gashi wani irin fadede dashi danse mutum talatin su tsaya a cikinsa ba tare daya cika ba, an zuba komi na bukatuwa a kiching din, duk kayan furniture din kiching din dark green ne hkn ya kara daukar hankalinta a kyaun kiching din. Larai ta shiga nunna mata komi da komi, kama daga kn kiching har zuwa kan store da dakin da kulolin da ake zubawa gogan abinci suke, dakine guda wanda ke cike da manyan kuloli na Alfarma bawai na kananun alfarma ba guys i mean alfarma wadda ta amsa sunanta alfarma ba muna Alfarma ba Alaji, kyaun kulolin ya ratsa yarinyar tin a nan ta lura komi de na mutumin nan is perfect and nice, hakan ya bata tabbacin shi din special guy ne. A gaggauce larai ta fiddo mata da macaroni da kifinsa busashe da kayayyakin vegetables da komi dazata bukata har tagama fiddo mata da komi yarinyar idanuwanta na kan wasu kwalebaninndake cike da kayayyakin spaces irin wadanda ta saba gani tin a kasar ta, sede tayi mamakin ganin larai bata bata dasu ba. "Yawwa ba asa masa gishi a abinci knji kou?'' Cewar larai yarinyar ta daga mata kai alamar Eh, daman ita de larai ba gane maganar bebaye takeyi ba shiyasa tanaso ta tambayeta abubuwa da dama amma ta hadiye, kasancewar tambayar data mata a dakima data fara mata magana gaza gane me take nufi tayi, dan haka ta hakura ta hadiye tambayoyinta ta barwa cikinta Amma fa jikinta na bata yarinyar nan special ce ba local ba. Larai na gefe tana kallon yarinyar ta fara ayyuknta cikin natsuwa hadi da sassarfa hkn ya bata damar gano yarinyar nada zafin nama, a natse take aiki amma kuma saurin aiki ne da ita. Larai na kallon yarinyar ta hada komi ta daura a kn gass hadi da kunna fan din dake saman gass din wadda ke zuke kamshin tiririn abinci ta yadda kamshin baze taba fita waje ba. Larai tayi mamakin yadda komi da yarinyar ke amfani dashi a kiching din cikin kwarewa take amfani dasu, dagani de komi ba sabo bane a gareta, larai na gani ta isa ta dakko wadannan glasses bottle din robobin spaces din daba me amfani dasu se ita da aka kawo yau-yau, har laraba ta gama ayyukanta a gidan na tsawon shekaru bata taba amfani da wadannan spaces din ba, amma duk bayan wata daya za a zubar dasu asa wasu a nan gurin, se yau rana daya taga yarinyar ta dakko duka kwale banin spaces din ta bude hadi da duba rubutun kasan ko wanne, ta diba ta zuba kala biyar a girkin guda uku kuma a cikin farfesun busashen kifin, larai na kallonta bata dakatar da ita ba, tana gani ta bude frij ta dauko wani abu a cikin ledarda ta kamfani shima duk kayan vegetables ne, amma laran bata taba ganin anyi amfani dashi ba se yau, yarinyar ta wankesa tasa a cikin farfesun kifin, azabar kamshi ya kara rikirkid'a larai, se hadiyar miyau takeyi kwat-kwat. Yarinyar ta gama girkin tsaf cikin kwarewa, larai jiki na rawa tazo ta diba kowanne taci nan ta kara jinjinawa yarinyar domin bata taba cin abinci me dadin wannanba. Larai ta nunnuna ma yarinyar kulolin daza tasa farfesun da dafadukan macaroni. Yarinyar tazuba komi cikin tsari, kana ta hada masa Apple joice ta zuba a cikin hadadden jug dinsa me kama da danyan gold, larai de na tsaye tana kallon ikon Allah yarinyar ta gama komi ta hada a kn kayataccen trea hadi da plates da spon da de komi daza' abukata, ta hada masa, suka nufa side din nasa ta kofar baya, knocking sukayi a falon sukaji shiru dan haka suka shiga falon bakin larai dauke da sallama ba kowa a falon se azabar kamshi da sanyin dake aiki a falon, saboda tsabar sanyin dake falon kai kace inka taka kasa ruwa ne ze bulbulo. Kamshin falon daya daki yarinyar seda ta lumshe idanuwanta tana mejin wata iriyar nutsuwa na ratsata hadi da kwanciyar hnkli seda ta sauke ajiyar zuciya tana me bin falon da ido tsarin kujerun falon da shape dinsu hadi da color dinsu ya bala'in burgeta ga wasu kananun throw pillows milk a kn kujerun tsarin komi na falon is perfect ita nan yafi mata kyau a kn falon hajiya saude. Dinning room suka nufa inda aka killacesa da wani irin glass me duhun golden color, an masa zanen mnyan flowers milk color, suna isa bakin glass din ya bude se gasu a wata duniya me tsananin kyau hadi da tsari! Dinning table dinsa and chair's sun hadu iya haduwa, kalarsu milk ne masu ratsin golden , ga wani hadadden golden din carpet daya mamaye gun dinning din me tsananin kyau hadi da laushi. kujerun zaman dinning din kujeru ne guda biyu, wadanda sukaji laualshi iya laushi. ta cikin nanma akwai wani dining room din shii na zaman mutane dayawa ne sbda in case in yayi baki. tako ina a dining room din cike yake da flowers masu launika iri daban daban se uban kamshi na Alfarma flowers din ke fitarwa, ko ina de acan-acan kmr aljannarh duniya. ajiye trea din yarinyar tayi a kn kayataccen glass dining table din, larai da hannunta ke rike da trea din dake dauke da jug din Apple drink din, itama ta ajiye a kan dining daman ita shi ta riko. Basu jimaba suka fita ta wata hanya ba hanyar dasuka shigo ba wato hanyar kofar dazata kaisu ga kiching direct ba tare dasun shigo falon gidan ba.


Dawowa kiching din sukayi suka tsaftace komi na kiching din larai ta bata takaddar abincinan dame gidan keso ta rike ta shiga duddubawa, abubuwa ne dayawa wadansu ma ba a taba dafa ma gogan ba, a cikin abincinan dake jikin takaddar taga harda abincikan larabawa daman a hotonsa data gani a falon hjya saude, taga yana kama da larabawa dan haka ta kara tabbatarwa yanzu shi din balarabe ne. Seda ta gama dubawa kana suka fito zuwa side dinsu na masu aiki kafin zuwa nan da awanni su dawo su kwashe komi dasuka kai falon nasa. yarinyar taja ta tsaya larai ta juyo ta kalleta, ta mata alama da hannu da tanaso tayi sallah kasancewar ana binta la'asar magriba, isha'i tinda tayi wankan ta dauro alwala taso tayi sallarta amma setaga laran tazo ta tsaya mata hkn ya bata tabbacin sauri akeso tayi, bata taba jera salloli a knta ba kmr yau, ita kwata-kwata bata wasa da fannin ibadarta. Larai ta fahimci me take nufi dan hk suka juya zuwa dakin yarinyar ta bata daddumar dake dakin, ta nufa toilet ta kara dauro alwala ta fito ta tada ramakon sallolinta.



Kwance yake a dakinsa tinda sukayi wayar nan da hajiya saude zuciyarsa ke cike da kunci, se uban juyi kawai yakeyi a kan kayataccen gadon nasa yana sanye da riga da wando kananu masu tsantsi irin na zaman gidan yan hutu kalolin kayan blue ne sun matukar kara fito da zallar kima da mutumcin kyaunsa , sumar nan ta knsa ta kwanta luf-luf kmr gonar Audiga tayi albarka, se uban silki da shinning kawai sumar kn nasa ketayi tana dibar albarkar idanuwan me kallo, kwance yake sambal ya mikar da tsawon da Ubangiji ya hore masa, a hankali yake ta motsa zara-zaran yatsun kafarsa masu azabar kyau, farcinan kafafuwansa sun dai-daitu da yatsun kafarsa farare karr-karr dasu, kafafuwannan nasa sunyi wani irin luf-lubus-lubus Kai bakace yana taka kasa da kafafuwannasa ba, domin kuwa in akace ka lashe kafafuwan nasa tsaf ma zaka tsugunna ka tandesu tass, macen ko dakeda saurin tashi a sha'awah kafarsa kadai ta isa ta tada sha'awar diya mace, me saurin kawowa ma tana iya kawowa batare datasan ta kawo din ba inta kalli kafafuwan nasa, ga shape dinsu madai-daita shoe size dinsa 40 ne, zakasha mamakin ganinsa sambal amma beda kafa halitta ce ta Allah kawai ya tsarasa yadda yakeso cikin cikar zati...juyawa yayi daga kwanciyar dayake yana kallon saman P.O.P din dakin wanda yasha Design me matukar kyau da daukar hankalin me kallo, ya kwanta a gefensa na dama hadi da daura hannunsa na hagu a gefen hakarkarinsa na hagu, ya tsurawa tamfatsetsen TV din dake manne a bangon dakin ta yammah ido a kashe TV din yake,amma kai kace wata uwar yake kallo a TV din ganin yadda ya tsuresa da ido, lumshe idanuwansa yayi ya bude yana me gyara kwanciyarsa a kn faffadan gadon nasa, wanda ke dauke da lubus din katifa...."Alhamdulillahi..." Ya fadi a bayya ne , zuciya cike da godiya ga ubangijinsa na kaddarar daya jarabcesa dashi, yanada komi na morewa duniya, yanada kudade dabesan adadinsu ba, yanada kamfanoni wasuma ya mance dasu, yanada gidajen mai, a duk seconds din duniya kudaden account dinsa karuwa sukeyi yanada arzikin dako yau ya bar nema ze rayu cikin jin dadih haka duk wani tsatso nasa ma bazeyi talaushi ba, Uwa uba kuma ubangiji ya azurtasa da cikakkiyar lafiya sam shi bame yawan ciwace-ciwace bane sede yakanyi time zuwa time, a yanzu haka abokinsa Mus'ab nada Sugar amma shi ubangiji ya tsaresa sam ko alamar sugar babu a jikinsa, ciwonsa daya ne zuwa biyu, ciwon kai se Uban gayyar wato ciwon ciki, Wanda yake addabarsa lokuta da dama shi ma ciwon cikin yasan matsalar rashin marar daze zazzage abinda ke mararsa ne, gashi Allah yayishi a cikakken d'ana miji meji da ruwan Maniyyi a mararsa, hadi da girman Azzakari, Shi din full option ne tako ina a cike yake taf-taf, hatta da mararsa cike take taf-taf da maniyyi ze iya cewa tinda yake be taba zazzage abinda ke mararsa ba son ransa,... Duk wannan dadin da Allah ya wadacesa na duniya ga lafiya ga kudi! Ga kyau! Ga cikar zati! Ga azzakari! Ga uwa uba wadatar zuci amma sede kash ya rasa abu daya wanda seda shi rayuwa ke tafiya, dashi ne ake iya fahimtar ana cikin ni'ima a duniya, shine dadin duniyar ma baki daya, wannan abin ba komi bane illah FARIN CIKI! ya rasa FARIN CIKI! Wanda yake ganin kamar baze taba samu ba har abadan, shi de Allah ya tsara masa rayuwarsa a cikin kalubalen rashin FARIN CIKI, babu abinda ke kara dagula masa lissafi kamar inya duba dama da hagu yaga beda d'a ko y'a, inyaga yara a hanya koda a mota yake seyasa an dakata da tukin motar ya tsaya yayita kallon wadannan yaran yana mejin daman nasa ne, shi fa da ana siyan d'a da kudi ko da duk kudadensa daya mallaka ze bada kawai danya samu D'A ko Y'A,...be ankare ba yaji wadansu hawaye masu azabar zafi hadi hadi da tiririn dake tasowa daga zuciyarsa suna yawo a gefe da gefen idanuwansa, wani irin tukiki me azabar zafi yazo ya tokare masa zuciya na zallar bakin cikin daya jima yana kunsa a zuciyar tasa, lumshe idanuwansa yayi hadi da kai hannunsa saitin zuciyarsa ya rige gam, yana me ambato sunan ubangiji mafi girma a garesa "YA ZALJALALU WAL-IKRAM!" (Wannan shine sunan ubangiji wanda ubangjin kejin dadih in aka kirasa dashi) yafi karfin 1h a kwancen yana ambaton sunayen ubangijin kana yafarajin sassaucin abinda ya tazo masa a zuciya. Wuraren 11:30am ya iya yunkurawa hadi da mikewa kawai seyaji jiri na neman kwasheshi sbda dalilin musababbin yunwar dake zuqulqular yayan hancin marainan cikinsa, dadin dadawa kuma ga zuciya ba dadih danma da karfin Zuciyar irin ta musulunci, da tini ya jima da kamuwa da heart attacking. Komawa yayi ya zauna hadi da lumshe idanuwansa ya rike hansa da hannayensa duka biyu na kusan mintuna ashirin kana ya iya mikewa a daddafe yake takowa da kafafuwansa harya fice a dakin ya sakko down stairs, yar karamar system din dake saman kofar shiga dinning room dinsace yaga tana haske alamar de an ajiye masa abinci room din. hkn ne alamar dayake ganewa in an ajiye masa abincinsa. Ba bata lokaci ya nufa kofar ta bude ya shiga cikin takunsa na manyan maza masuji da cikakkiyar lafiya da izza, idanuwansa suka sauka a kn dinning table yaga food warmers hadi da jug haka kawai ya tsinci zuciyarsa da nishadin dabe taba shiga irin saba kamar yau, ya mnta when last yayi nishadi ma a rayuwarsa wallahi. Cikin sassarfa ya karasa yaja kujera daya ya zauna daman shi be saba da lalaci ba shike serving knsa da kansa, be saba da mutuwar jiki ba, shi din namijine na gaske beda sassanyar laka a jikinsa. Jug din Apple juice din ya bude kamshinsa ya dokesa ya dauko cup ya tsiyaya yasha wani dadih hadi da sanyi kadan ya rashashi, ya mnta when last yasha juice aka hada a gida sede na kwali kawai yaketasha kuma besansu kawai yana shane bisa larura. hannu ya kai ya Bude warmer ta farko nan da nan wani irin kamshi me bala'in dadih ya dakesa nan take kamshin ya haifar masa da faduwar gaba hadi da tunawa da mahaifiyarsa, sak kamshin abincinnan irin kamshin abincin ummansa ne wanda take dafa masa, da kyar ya iya cin wani abinci a rayuwarsa sbda sabo da yayi da abincin Ummihnsa, koda scul yaje inya dawo hutu burinsa kawai yaci abincin ummihnsa. ''Ummih!'' Ya ambata a fili hadi da zubawa dafadukan macaroni din ido wadda taji kayan lambu masu bada vitamin din kuzari a jiki, ganin launin abincinma seda ya fadar masa da gaba sak kalan abincin kalan na ummihnsa sannan kamshin launikan spaces din duk irin na ummansa ne,.. ajiyar zuciya yaja hadi da saukewa a lokaci guda mamaki da alhini suka rufesa "Wacece me irin abincin ummih na?'' Ya tambayi knsa da knsa fuska fal mamaki, be kara karaya ba seda ya bude warmer ta biyu me dauke da farfesun kifin dayakeso, kamshin kifin ya dukesa, tini wani miyau ya tarun masa kafin yayi aune tsinkakken miyaun bakinsa ya cika masa bakin nasa taf ganin yawun na kokarin zubowa yasashi saurin hadiyesa ya wuce a makogaronsa ji kake kut! Sak farfesunma irin na ummihnsa ne, tafi kowa iya dafa masa abinci a duk duniyarnan ita tasamishi soyayyar busashen kifi saboda itama akwai SO me karfi tsakaninta da farfesun busashen kifin. Zuciya cike da zallar mamaki ya zuba macaroni din a plate wanda har lokacin se kamshi takeyi tana turirin zafi, shi din becin abinci me sanyi shiyasa duk wani abu daza a dafa masa a warmer akesa masa, shi abinci ko fara hucewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login