Showing 1 words to 3000 words out of 99609 words

Chapter 1 - CAPTAIN SADIQ COMPLETE BOOK BY Salma Mas'ud Nadabo.pdf

Captain sadiq complete*CAPTAIN SADIQ*
‍♂

*writing by*
*Salma mas'ud nadabo*


*Edit by*
*boold sister deeja*

*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*

1_2



Yarinya ce yar shekara 10 na hango, tana tafe tana rusa kuka kamar anmata mutuwa.Fara ce
sosai, ita ba siriri ya ba, ita ba lukuta ba, Dan kwallinta ne a hannu ta, hakan ya sa na kalli
gashin kanta, baki ne sosai amma saboda tsabar datti yayi jawur,kallo daya na mai na gane mai
laushi ne,rashin kullawa ne yasa yayi haka, Hancin ta yayi jaga-jaga da majina, gata da manyan
ido, tana tafe tana kukan, dan ba dainawa tayi ba, dai-dai wani madaidaicin gida ta tsaya chak,
gidan kasane na tallakawa sosai,dan ko kofar gidan bata samu ishashiyar kofa ba.Ihu ta Kara
saki kamar an watsa mata ruwan zafi,inna da ke kurya daki ta fito tana gyara zani, inda sabo to
ya kamata ta saba da halin fatuha,amma ba yadda ta iya dole ta fito inba fitowa tayi ba to
wallahi sai dai maqota su fito,ganin inna ta leko yasa fatuha tuna a kasa tana ihu,inna ta gyara
tsayuwa. "ohni fatuha nabani yau kuma wakika tsokana kika ci bugu? fatuha ciki mirya tsiwa irin
na yara masu wayau masu rashin ji ta ce "inna wallahi tallahi kwarankwatsi dubu bani na
tsokane shi ba inna. Ta kara rushewa da kuka,inna ta san halin ta sarai shiyasa ta ja bakin ta
tayi shuru, to fatuha waya bige ki?"wallah Inna Rabi'u ne ya bigeni har da taka min ruwan ciki,ta
Kara rushewa da saban kuka,"kuma inna billahilazi ba zan yadda ba,ta inda zancan tana katse
majina hancin ta.saboda inna ta San karya fatuha take ba yadda za'ayi rabi'u ya bige ta har ya
taka mata ruwan ciki, sai dai in laifi ta mai kuma ko bugun ta yayi bai taka mata ruwan ciki qila
ma satan mangwaro taje ya kamata, "yi hakuri fatuha ki kyale shi kin ji kuma kiga Rabi'u ba
sa'an ki bane kin ji diyar baffan ta" "kambuuuu!!! ta zaro manya idanuwan ta "qur'an inna ban
hakura haba" "fatuha yi hakuri Zan baki biyar kin ji" washe baki tayi kamar ba ita ke ihu da
koke-koke ba, "to inna na hakura kwarankwatsi" Inna ta washe baki fatuha ko ba wai har cikin
zuciyar ta, ta hakura ba, dan ta dau alwashi se ta Rama bugun da Rabi'u ya Mata haka ta bi
inna cikin uwar daka tana matse kwalla da katse majina.



Misalin karfe hudu na yamma fatuha ce zaune tsakar gida wadda take share kwal ba dani
ko daya da yake inna akwai san tsafta duk yadda ta so ta gyara fatuha da fita zata Dawo kamar

almajira ko sabuwar mahauciya, saboda tsaban rashin ji ko wanka se anyi da gaske inna ke
samu ta dirje ta, fura take sha hankali kwance daga gani fura na kai mata karo dan sai rausaya
kai take kamar kadangaruwa, inna ce ta leko daga uwar daka tace, "fatuha yi Sauri ki shirya ki
tai makaranta allo" baki ta turo gaba kamar wadda ta tunkudi birji "gaskeya yau inna ban zuwa
inna na gaji qur'an kullun Malam dalha sai ya bigeni" ta inda zancan tana matsar kwalla "to
fatuha in baki je makarantar ba inaa zaki sauke baki so na siya maki shanun a yanka ranar
sauka" washe baki tayi tace, "to inna zani wallahi ko dan ki yanka min shanuwa babba tafi tasu
fatsima kwarankwatsi" "yawa yar albarka maza ki shirya hijabin ta dake saman igiya ta janyo ta
zura ta fita da gudu inna ta girgiza kai ta dau kwana fura ta Kai madafi ta aje.


Fatuha da ke tafe tana yan surutai wanda ko ni salma bajin ta nake ba, chan ta tsinkayo
muryar malam dalha taja birki ta tsaya tana raba ido dan tasan kashin ta ya bushe, dan Ba
karamar makara tayi ba, Malam dalha ne ya juyo sukayi ido 4 da fatuha ya kwallo ido
"keeeeeeeee!!! fatuha dan uban ki yanzu ne lokacin zuwa makaranta? "shegiya mai Kama da
mayu duk kauyan nan kin raina uban kowa" yana huci yace, "yau zaki ci kwafar ubanki wallahi,"
fatuha dake ta raba ido ta duqa da niyar rarumar takalmin ta ta ruga, muryar Malam dalha ce ta
tsinke Mata tunani "wallahi kika ruga sai na sa basiru ya dauko min ke akai" kasancewa tasan
basiru Ba karamin kato bane yasa taja ta tsaya chaf ka daya Malam dalha ya Mata yana
muzurai kuka ta farayi tana yarfe hannu tana bashi hakuri, Allah annabi amma yayi biris ya
fisgota ya fara kila kamar an aiko shi ihu take tana jera mai Allah ya isa bugun ta yake amma
bakin yaki mutuwa, dan kan shi ya gaji da dukan ta ya hakura fatsima da ke gefe sai matsar
kwalla take tana yimai daquwa ta hijabi ta, lalabowa tayi gefe fatuha ta zauna Malam dalha be
ganta ba tace, "yi hakuri fatuha kin ji Allah sai ya saka maki" fatuha dake matsar kwalla ta turo
baki gaba "billahilazi sai na rama fatsima ba yana zuwa gidan qilu zance ba da yamma ba
kwarankwatsin dubu sai nayi maganin shi fatsima" "Kai fatuha ki kyale shi Dan wallahi ki kai mai
iskanci har gida zai biki dan Malam dalha ba wayau garashi ba ya hadaki da baffa" "yo ni ma
wayau ne ya isheni" ta karashe zancan tana washe baki fatsima taja bakin ta tayi shuru, haka
suka cigaba da karatun su dai-dai gwargwado fatuha na da kokari sai dai bata jin magana KO
kadan ba wanda bai san ta akauyan su ba.


Mayan motoci ne kira bentley guda 5 suka nufi wani katafarin gate kallo daya nayi ma
motocin na hadiye miyau dai-dai katafarin gida motocin suka kunna Kai wurin parking suka nufa
suna gama parking da sauri wasu sojoji guda 4 suka fito daga ciki motar babba at the same
time, sojojin 4 na cikin mota baya suka nufi motar tsakiya ahankali daya daga cikin sojojin ya
bude mai murfin motar tsakiya wani hadaddden kafa nagani mai sanye da booth yana cikin
kakin shi na sojoji karfafe namijine kyakyawa wow fari ne Sol idan sa sanye yake da glass fari
wadda ya fido da zala kyan shi, da qwarjinin shi dogo ni sosai jikin shi murde yana da fadandan
kirji gashin kanshi mai laushi ne duk da gashi na cikin hula shi na uniform hakan be hana
gashinshi bayyana na ba, ga sajan shi kwance da hancin shi kamar pencil dan tsini, briefcase
din shi ya amsa hannu daya daga cikin yaran sa fuskarsa murtuke Ba alamar dariya kamar an
aiko mai da wahayin mutuwa, na ce ohni Salma da guy dinan zeyi dariya da ba karamin kyau

zeyi ba, haka yaran suka bashi guri ya wuce, Kai tsaya man palour ya nufa wow fadi tsaruwar
palour bata lokaci ne saboda ba karamin haduwa yayi ba baba jummai da ke gafe cikin washe
baki ta tsugunna tana kwasar gaishuwa cikin isa kamar mai koyan magana ya amsa tare da
cewa, "mom fa? "ah mai gida tana sama" Kara daurewa yayi Dan wannan suna kona mai rai
yake a hankali yake taka matataka cikin isa Kai tsaye dakin mom ya shiga hadaddan daki mai
kyau sanyin AC sai ratsa dakin yake hajiya da ke zaune saman kujera dressing mirror tana
shafa turare Tasha hadadden leshin ta mai kyau, fara ce ba fulata na kallo daya zaka mata
kasan Hutu ya zauna mata ahankalin ya karaso yayi huging nata cikin fara'a ta juyo Dan tasan
ba mai mata haka se son, kiss ya mata yace, "mom I miss u" "miss u more son welcome back
dear, baby ka kara girma kamar ba Kai ba" turo baki yayi ya langwabe Kai alamar shagwaba
"Kai mom ni dai gaskiya ban girma ba" "ka ji da shi dai kaje kayi wanka ka dawo your food is
ready a dinning area" "ok mom" ya fice yana murmushi kamar bashine Wanda ke daurewa ba
dazu Ba.


*Taku har kullu Salma mas'ud nadabo**CAPTAIN SADIQ*
‍♂

*writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*blood sister deeja*

*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*

3_4


Kaitsaye bedroom nashi ya wuce komai na bedroom din golden color ne wani makeken gado ne
atsakiya daki Wanda ke kama da ba a kwanciya a saman shi, dan komai na daki very neat ne
dressing mirron din shima abin kallo ne kayan shafa ne kamar suyi magana dan yawa, perfume
kam ba'a magana da man gyara gashi tsayawa lusafa maku haduwar dakin bata lokaci ne
kayan shi ya fara cirewa,
ya shige toilet wow toilet din ma abin kallo ne dan ya hadu iya haduwa baifi 30 minutes ba ya
fito daure da towel a qugun shi daya kuma yana goge gashin kanshi da shi, dressing mirror ya
nufa ya shafe jikin shi da mayuka masu kamshi tare da gyara sumar sa da sajan shi wardrobe
nashi ya bude wow wardrobe din ma abin kallo ne saboda kaya ne a ciki kamar gurin saida
kaya, suit kala-kala da uniforms din shi na sojoji kamar suyi magana da yake shi mutun ne ba
mai yawan sa manyan kaya bane dan haka kanana kaya sunfi yawa, hannu yasa ya ciro T-shirt
din shi white mai gajeran hannu da 3qwatan shi black yasa ba karamin kyau yayi ba haka yasa
kyan shi ya bayana sosai agogo ya makala ma hannu shi mai tsada silver na azurfa, har ya kai
bakin kofa phone nashi ya fara ringing, wayar kira iPhone 7 white chak ya jaa ya tsaya hannu

ya kai saman dressing mirror nashi sweet mom ne rubuce a screem din phone din ahankali
yasa hannu ya dauka, "hello mom" "son na dauka bacci ya dauke ka? "no mom yanzu zan fito"
"ok" ta datse kiran daga dayan bangaran cikin isa yake saukowa daga sterp hannu sa daya
cikin aljihu Jidda dake dining ce ta rugu da gudu da rungume shi tace, "daddy welcome back
daga ta sama yayi yana mata wasa tana dariya har suka qarasu dining tana rike a hannu shi
mom sai murmushi take ita tayi serving din su shinkafa ce da miya wadda taji kaji da namomi
da ganyaye cikin kwanciyar hankali suke cin abincin wadda sadiq da kanshi yake feeding Jidda
itama tana feeding nashi, yarin ya ce wadda baza ta wuce 4 year ba chocolate Colo ce mai
kyau da ita gashin kanta yasha gyara sanye take da gwon pink mai dan siririn hannu yadda
sadiq ke bata kuluwa hakan zai gwada ma ba karamin ji yake da ita ba, mom dake zauna tana
Kallan su se taji tausayin Jidda ya kamata da shi kanshi dan nata Jidda ce ta katse shuru da
cewa cikin muryar ta mai tsamin, "daddy Ina tsaraba na? kallan ta yayi yana murmushi ya
lakace mata hanci "sweetheart ki bari daddy ya gama lunch mana" baki ta turo gaba "um daddy
na kosa naga tsaraba ne" "um na sani swetheat bari mu gama tukun"mom ce ta washe bakin
tace, "ke dai baki gajiya duk san da yayi tafiya fa sai ya maki tsaraba" "to ai grandma Ina so
ne" ta ida zancan tana turo baki "ke ko Allah ya shirye ki" duk hiran da suke idan sadiq nakan
little daughter din shi wadda ya ke jin ta har cikin ranshi, "oya cigaba da cin abinci sweetheart
mu gama na baki tsaraba ki sannan muje shan ice cream ko dear" "yes daddy" haka cikin
wayau ya samu yayi feeding nata.



Fatsima da fatuha ne tafe antaso daga makarantar allo suna tafe suna tsokana dan wannan
ya zamar masu jazaman in antashi daga makaranta se sunyi tsokana san ransu suke komawa
gida wata Rana da kuka wata rana da gudu suke kuma wa gida yau kam a guje suka koma gida
fatsima ta shige gida fatuha ta shige gidan su baffa ne zaune bisa tabar ma Inna na gefe tana
zuba mai ruwa abuta saboda magrib ya kusa fatuha ta kunna kai tare da sallama ta yadda
hijabin ta kasa baffa ya bita da kallo washe baki tayi ta ce baffa sannu da gida yauwa yar
albarka an dawo daga makaranta kenan eh baffa yauwa ya karatun lahiya lau baffa taje ta
amshi buta da ke hannu inna ta kawo ma baffa yayi alwala ya wuce masallaci bashi ya dawo ba
sai bayan isha'i inna da fatuha na zaune suna cin tuwan dawa ta miyar kubewa wadda tasha
man shanu baffa ya shigo da sallama fatuha ta ruga da guda ta rungume shi ah ah zaki karya ni
fatuha wai ke baki san kin girma ba baki ta turo gaskiya baffa ban girma ba to naji ya ja hannu
ta suka zauna bisa tabarmar da Inna ke zaune murmushi inna tayi ta tatashi ta shige madafi ta
dauko kwana abinci Malam ta aje mai yana samata albarka bayan sun kamala cin abinci fatuha
ta kwashe kwanin ta dawo ta zauna kusa baffa baffa na'am fatuha baffa Ina so gobe na bika
gona dan Allah makaranta fa fatuha baki turo gaba ai gobe litinin baffa ba ta sahe inna da ke
gefe ta ce toh fatuha kin san sai 5:00 Malam ke dawowa ki bari sai ranar alhamis ki bishi kin ji
kwalla ta Fara matsewa baffa ya ce yi hakuri ki shirya goban se muje ko washe baki tayi dan ita
akwai abinda take san daukowa a gona shiyasa zata bishi inna ce ta katse mata tunanin da
cewa haba Malam wai me yasa kake biyewa fatuha dan Allah taita sangarcewa kinga ladingo
bana san haka haba dan Allah Allah ya bamu yarin ya sai baza mu faranta mata ba mun dade
muna san yara Allah be bamu ba sai yanzu yanzu kuma ya bamu sai muki faran ta mata

gaskiya bazaiyu ba ladingo ke ma kin fara daukar magana mutanan waje toh yayi ni dai ba
maimatsa ma diyata akauyanan kyale shi ladingo tayi ya ida zan can tare da daukar fatuha
wadda tuni bacci ya kwashe ta inna ta bishi da ido tare da kwashe tabarmar tsakar gida


After dinner mom da sadiq ne zaune a palour suna kallan news Jidda na kwance jikin shi
da alama tana wasa bacci ya dauke ta Teddy's din ta a baje cikin palour baba jinmai ce ta leko
daga dakin ta ta zo ta fara kwashe kayan wasan tana kaiwa dakin jidda dakine mai kyau fadi
tsaruwa dakin bata lokaci ne sai da ta gama kwashewa ta zo daukar jidda dake makale da
baban ta sadiq ne ya ce ah baba barta yau tare zamu kwana to shikenan maigida bari na mata
kwanka nasamata kayan bacci to shikenan ya miqa Jidda mom ta juyu ta kalle shi tana sanyi
magana amma ba tasan bacin ran son shiyasa taja bakin ta tayi shuru can ta ce ni ko baby aikin
da baba jinmai take be mata yawa ba gashi ba yarin ya ba ce haka ne mom tunda Mary ta tafi
Ba a kawo wata ba ni wallahi mom tsoran daukowa sweetheart wata yar aikin nake wallahi ya
ida zan can yana bata fuska ya zamuyi dole a samo wata saboda aikin ya Mata yawa to
shikenan duk yadda kukayi ki fada min to kun koyi waya da abban ka yes munyi jiya lokacin
yana airport yace sai yayi 2weeks zai dawo eh haka kasan har yanzu suna magana kan
kwangillannan ne eyya Allah ya taimaka mom ta ce ameen gobe Kai da Jidda in ka dawo daga
wajan aiki ka kaita gidan sister ka ya kamata ka leka ka bama su hanan tsaraba su ko tam bari
mu gani inna dawo da wuri sai muje sai ga baba jinmai dauke da Jidda ya amshe yayi mom
sai da safe



*Taku har kullu salma mas'ud nadabo*

*Alheri hausa novel group love u fan's*❤
*CAPTAIN SADIQ*
‍♂

*writing by*
*Salma mas'ud nadabo*

*Edit by*
*blood sister deeja*

*REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM*

5_6

Asuba ta gari fatuha ce ta tashi tunda safe ta fitu daga dan akurkin dakin ta wanda ko lafiyaya
katifa bai samu ba inna dake gefe ta na hura wuta ta gaishe ta tare da daukar tulun da ke kusa
ta inna ta fice zuwa di ban ruwa rafi gidan su fatsima ta wuce kai tsaye dai dai bakin kofa suka

ci karo ah ta washe baki kai fatsima qur'an na dauka baki tashi ba da billahilazi na higo ruwa
zan heqamaki aiko da anyi heqa heqa suna tafe suna tsokana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login