Showing 27001 words to 30000 words out of 132090 words
Chapter 10 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt
fakaice ta yi mata hoto ta turawa Turaki y’a ga canca’de’diyar matar da ta samo masa. “Na ga kowa ban ga daughter ta ta ba.” Amma tana murmushi ta ce “Ai Allah ya ha’daki da misklar yarinya sai kun yi hak’uri da halinta. Dijah kirata tana sama ‘dakinta.” Dijah ta tafi da sauri ta bar Ummeey tana fa’din “Ai gwara haka sau tari yawan surutun ba shi da amfani.” Amma ta ce “Kamar yarda rashin maganar ma ba shi da amfani ba. Yauwa ni kuwa mu je daga can falon akwai maganar da za mu yi da ke…” Ummeey ta mik’e ta bi bayanta suka bar su Zainab suna maganar kirkin Ummeey “Wallahi Ayra banda shak’iya ce ai ta dace da Surika ta k’warai”
A falo Amma ta ‘d’an dubi Hameeda kafin ta ce “Dama tambaya zan miki anya shi Turakin ya amince da auren nan?” Ummeey ta na murmushi ta ce “Me kika gani?” “Gani na yi har yanzu ko wata ban ce Sun tab’a yi ba.” Ummeey ta ja ajiyar zuciya “Turaki Talatu yana da taurin Kai da kafiya idan na biyewa ta son ransa ba zai yi aure ba shi yasa sam ban damu da amincewarsa ba kamar yarda na tabbatar itama Ayran ba wai ta amince ba ne don haka ki k’yalesu idan suka je su ci kansu sa daidaita kansu a can.” Amma ta ja ajiyar zuciya Sam ba amsar da ta so ji ba kenan, amma ya ta iya burinta sada Ayra da ‘dakin mijinta. “Amma Hameeda mai yake raba shi da wa’dancan matan?” Hameeda ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce “K’addara duk da dai yanzu ya gaya min wai ba masu kamun Kai ake Kai masa ba sai Sun gama gantalewa a titi. Kin ga amsar tambayar dai shine ba sa Kai budurcinsu……….”
Zuciyar Ayra da take niyyar shigowa ‘dakin ta wani irin bugawa kafin ta saki wani zazzafan murmushi ta jingina da bango “Idan kuwa haka ne Turaki wannan karan…..”
“Waye nan?”
Maganar Amma ta katse mata tunaninta hakan yasa da sauri ta fa’da falon tana furta “Ni ce fa Amma!” Amma ta saki tsaki tana jinjina maganar Hameeda ta kalli Ayra ta ce “Lab’e kuma kika koma yi?” Ayra ta girgiza Kai nik’abin da yake fuskarta ne ya sa Amman bata ga dariyar da fara’arta ba. Da k’yar ta durk’usa a gefen Ummeey tana gaisheta Ummeey ta dafa bayanta ta ce “Yau ‘din ma rowar fuskar za’a min? Ai shikkenan idan da Hotonki turo zan nunawa angonki..” da sauri ta girgiza Kai cikin takaici ta ce “Ummeey bana hoto ko a waya.” Amma ma ta sake tabbatar mata, Ummeey cike da mamaki ta gyara zama “To saboda me? Ko da yake duk ba matsala bace ki je yanzu waje wata daga y’an uwan ki ta d’aukeki sai a turo min, sannan ki bani sizes na ki.” Ayra ta dinga ha’diyar wani yawu mai ‘daci a zuciyarta tana Jin haushin Ummeey da ta bi ta shigo rayuwarta ta yamutsata. Dabara ta fa’do mata ta ce “Ummeey na rok’i alfarma please!” Ummeeyn kallonta take sosai kafin ta dafata cikin kulawa ta ce “Ba wannan tsakani na da ke Daughter just go straight to the point, ki fa’di ko me kike so zan miki.” Ayra ta ji da’din jin hakan sosai don haka murya a sanyaye ta ce “Kada ku bari mutumin da zan aura ya san zahirin kamanni na don Allah.” Ta fa’da tana ha’da hannayenta alamar rok’o. Amma da sauri ta ce “Saboda me kenan?” Ummeey ta yi saurin dakatar da Amman tana murmushi “Ba ruwanki, ba mu sako ki cikin zancenmu ba, na amince Ayra na ‘daukar Miki wannan alk’awarin na San kina da babbar hujjar da tasa za ki aikata haka.” Ta sunkuyar da kanta sosai ta ji da’din samun Ummeey a yarda take so ta yi godiya sosai kafin ta ce “Sannan please ba zan bi shi ko ina ba zan zauna anan garin, saboda ni nake kula da companyn mu.” Ummeey ta yi jum tana tunanin yarda zata amincewa Ayran da hakan, sai dai bata son Ayran ta ‘dauketa a matsayin mace mai son kanta don haka ta ce “Shikkenan, zan duba wannan In sha Allah tunda anan ‘din ma yana da gida ai y’a tab’a zama da matarsa ta farko Amma da Abbansu Abuja Ya ce za’a kai ki.” “Abujan zata je ita zata zab’a wa kanta abinda take so.” Amma ta fa’da cikin hassala da jin haushin Ayra na wannan titsiye da ta yiwa surukarta. Ummeey ta girgiza kai “Ko ‘daya, yarda take so haka za’a yi tunda ba mu zamu yi mata zaman auren ba, yanzu ki tashi ki je ki rubuto min abubuwan da ki ke buk’ata a lefenki da sizes na komai na ki.” Da sauri ta mik’e ta cikin hijab take kallon hararar da Amma take watso mata. Ta ‘d’an saki murmushi a karo na farko shirinta ya fara tafiya yarda take so.
A bakin gado ta zauna hannayenta zube a fuskarta, takarda da biron a hannunta idanunta na zubar da k’walla takaici take ji wai ita ce zata yi aure duk da alwashin da ta sha a kan ‘da namiji, wai yau da kanta zata rubuta abinda take so na aurenta ashe kuwa ba zasu kawo mata lefen ba. Ko sunan lefen bata son ji, angon ma bata San sunansa ba kuma bata buk’atar ji, buk’atar ta shine samun hanyar da zata gujewa auren nan…
Ina ma zata iya tafiya ta bar Amma tabbas da ta tserewa auren nan ko da kuwa ta hanyar barin k’asar ne, duk da dai ta San burinta zai cika musamman sanin cewa ance shima angon baya maraba da auren?
Shigowar Dijah da dariyar da ta shigo tana yi ne ya dawo da ita cikin hayyacinta. Ta zubawa Dijahn ido da ta shigo ‘dauke da wasu kaya a hannunta tana fa’din “Bikin autarmu ai dole mu kece raini, wajen event mafi tsada za mu kama mu dagargaji Dinner, sati guda za mu yi muna cashewa abinda muka da’de muna fata Allah dai ya nuna mana, ga ankonki ma a hannuna ki turo Drivernki ya karb’a” ta fa’da tana kashe wayar idanunta cikin na Ayra da itama ta ke kallonta cikin mabayyanin b’acin rai, Da gaske ji take kamar ta tashi ta rufe Dijah da duka su tuna lokutan baya. “Idan da Wanda ya isa ya jani ya kai ni gurin bikin ai sai mu gan shi. Dijah ki fita daga harka ta abubuwanki Sun fara isata.” “Kamar yarda na ki suka fara isata ba, biki kam ai dole ki je shi Allah ya nuna mana lokaci. Yanzu ma Amma ce ta ce na gaya miki mai miki gyaran jiki ta zo zata ga yanayin fatar taki.” “Kan bala’i, au Har wani gyaran jiki kuka shirya yi min? To wallahi kada ma idan ba so kuke na fasa auren ba..” Dijah ta bita da kallo tana nazarinta ‘Tabbas akwai abinda Ayra take b’oye musu bata shirya zaman auren nan ba, ta amsa ne kawai gudun b’acin ran Amma don haka jikinta a salub’e ta fice ya zama dole ta tattauna da y’an uwanta kada a zo matsala ta faru….”
____________
A kitchen suke shi da yaron sa Aman, da ya samu hutu a ranar, yaron yana da rashin ji ga shi sosai y’a sangarta shi ganin shi ka’dai Hibba ta bar masa yarinyar da ta Haifa wajen haihuwa ita ma ta bita. Turo baki yaron kawai yake cike da sangarta yake furta “Ni Ummeey zan je Abbu.” Tsaki ya ja yana k’ok’arin tsiyaya masa fresh milk a cup. Aman duk da shekarun da yake da su shekara goma cur har a lokacin baya iya yiwa kansa komai saboda shagwab’a shi da suka yi. Cup ‘din ya karb’a ya sha sosai kafin ya ce “Abbu, Please Ummeey.” Ya zuba masa ido kafin cikin b’acin rai ya ce “Aman zan zaneka fa, nace maka Ummeey na Nigeria ni kuma ban shirya zuwa Nigeria yanzu ba…” Yaron cikin takaci ya fice da sauri yana kuka sosai. Jikin Turaki ya yi sanyi saboda Sam baya son b’acin ran Aman ‘din don haka don dole ya fara nema musu ticket na tahowa Nigeria, da shirin idan ya zo dole ya ruguza auren da ake son masa, sabida har a lokacin zuciyarsa bata gama amincewa da auren ba. Zai bi duk hanyar da zai bi yaga ba’a yi auren ba.
Takaicin Uba..
Alk’alamin ——-Jikar Nashe
08033748387.
Motsin yarda Aman ke turjewa ne ya ankarar da Ummeey da S.Turaki cewa tabbas akwai alamun mutum a wajen. Da sauri S.Turaki Ya mik’e don ganin wanene. Turaki ya gani a tsaye yana k’ok’arin ciccib’ar Aman da ya zama mai k’iba irin ta yara ka’dan, Aman ‘din yana turjewa alamar rashin son tafiya. Cikin tsawa S.Turaki ya ce “Turaki me ye haka? Yaushe ma kazo ban sani ba?” Turaki da takaicin Aman ya gama k’ullewa ya dire shi yana k’ok’arin shiga cikin gidan don ta window Abban ya masa magana.
Ransa a b’ace ya danna kai cikin falon idanunsa a kan Ummeey da ta yi zugum hannayenta a kan k’unci ta zabga uban tagumi. Tausayin Amma ne a ranta da kallon da mutane suke mata ba tare da ita ta sani ba. Ba ta zuwan Turaki take ba yanzu yarda zata tursasa mijinta ya amince da auren shine abinda da take buri a yanzu.
Ta sauke ganinta a kan Turaki da yake zaune idanunsa a lumshe zuciyarsa yake Jin tana shirin tarwatsewa, Jin takaicin wai Ummeey ce zata ha’da shi aure da karuwa? Yanayinsa Babansa ka’dai ya kalla ya tabbatar ya ji duk zancen da suke, shi yasa tun shigowarsa ya kasa furta musu komai sai matsa yatsunsa yake yi. Idanunsa a lumshe. “Ka daina gaisuwa ne?” S. Turaki ya watso masa tambayar yana k’ok’arin jan Aman da ya yi tsaye silently yana bin su da kallo da alama bai saba ganinsu a hakan ba. Da k’yar Turaki ya ‘dago yana kallon Uban nasa “Am Sorry Abba, ina cikin wani yanayi ne, na zo shigowa ne na ji kamar ana zancen yarinyar da za ku aura min karuwa ce.” Da sauri Ummeey ta ‘d’ago tana zuba masa kallo cikin idanunta masu rauni shikkenan kuma magana ta rushe tunda har Turaki ya ji wannan maganar ta San ko me za’a yi ba zai amince da auren ba. Ta fara Jin k’walla na son zubo mata Me zata cewa Talatu? Me zata ce mata ta fahimci ba laifin ta bane rashin auren Turaki da Ayran? Babu! Zuciyarta direct ta bata amsa Tabbas Talatu zata ‘dauke ki mayaudariya tana murna zata aurar da y’ar ta da take jiran lokacin tsawon lokaci, sai katsam ana shirin ‘daura aure taje mata da bak’in labarin an fasa anya zata iya kuwa? Abin da ciwo fa…
“Tabbas abinda kunnuwanka ya jiye maka, haka abin yake Turaki, yara ne mata da suka tashi a hannun uwarsu mace suka tara mata dukiyar da ba a San musabbabinta ba, bayan rabuwar auren su da Baban yaran, a matsayinka na mai cikakken hankali me zaka kawo yarinyar tana yi da suka tara uban ku’di haka? Sannan yarinyar shekarunta ashirin da bakwai cur babu maganar aure a tsarin rayuwarta saboda tana samun inda ake ‘debe mata kewa, Babban abin takaicin ma yarda suka banzagatar da uban su, don Baka ga muhallin da yake ba, ga shi a kwance ciwon paralysed ya kama shi saboda bak’in cikin su, ta ko ina bai kamata ka auri yarinyar nan ba, ka bari zan nema maka yarinya y’ar gidan mutunci ka aura.”
Turaki ya saki ajiyar zuciya ya kuma yarda da duk abinda Abban ya ce masa, aure ne dai ake so ya yi to su bari da Kansa zai nemo matar aure ba sai Sun masa wannan auren na walagigi ba. “Ka bar shi Abba da kaina zan nemi mata na aura.” Abba ya girgiza Kai “Shikkenan sai ka k’ok’arin samowa kafin ka koma tunda uwar ka ta dage sai ka yi auren.” Turaki ya ‘daga Kai yana mayar da kallonsa kan mahaifiyarsa da ta fara yiwa Abban magana cikin raunin murya “Amma kafin ta Kai ga haka ka bari na je wajen Talatu na ji gaskiyar zance mana.. ni dai gani nake kamar sharri ake musu wallahi Talatu ba zata yi irin wannan rayuwar ba, akwai dai wani Abu a k’asa, akwai kuma dalilin da yasa suka banzagatar da uban nasu idan ma haka ‘din ne, ba zai yiyu haka kawai ‘da ya wulak’anta uban sa ba.” “Ke kin ga ko me ma za ki je ki jiyo ni ‘dana ba zai auri wannan yarinyar ba, don haka Kai Turaki idan yarinya mai tarbiyya kake so maza ka je gidan Alaramma akwai y’ay’a mata masu tarbiyya kuma kyawawa da su, a mayar da auren kanta.” “Ai kuwa sai dai ta ha’da mata biyu wallahi, don kamar yarda ka ke da hak’ki a kansa nima ina da hak’ki, kuma ban tab’a kawo masa kowacce mace ya aura ba sai wannan don haka ko karuwar ce haka zai aureta ai jihadi zai yi, ba ku san irin shak’uwar da muka yi da Talatu bane muna yara jin Talatu nake kamar y’ar uwata don haka ko karuwar ce wallahi in dai ni na haifeka sai ka aureta…” Hameeda ta fa’da cikin matsanancin b’acin rai. Da gaske ta tunzira sosai don tana ji ko sama da k’asa zata ha’de Babu mai canja mata ra’ayi. Turaki da mahaifinsa kallonta kawai suke. Kafin S.Turakin ya yi k’wafa ya ce “Ni kike gayawa haka? To za mu gani idan mace tana walicciin auren d’anta shashasha da baki san ciwon kan ki ba, kawai ki janyo mana jangwam cikin gida.” B’ata masa magana ba illa mik’ewa da ta yi a zafafe ta shige sashenta ta sha alwashin sai Turaki ya auri yarinyar nan ko da nata auren zai yi girgi’di da soyayyar Talatu Allah ya halicceta. Gobe asubanci zata yi ta je ta samu Talatu ta ji ainahin labarinta da dalilin da yasa suka rabu da Kabiru ka dama labarin bayan rabuwarsu..
Turaki kuwa bin mahaifiyarsa Ya yi da kallo yana mamakin yarda ta kafe a kan sai ya auri y’ar nan, sai kace wacce aka sammace, ta ina zai iya aurar yarinyar da aka ce k’iri-k’iri karuwa ce?
______________
Da sassafe Hameedah ta yi parking a harabar gidan Talatu. Ta fito jikinta a sanyaye idanunta Sun kumbura ainun kana ganinta ka San bata Samu isashshen barci ba, sam bata da kwanciyar hankali har sai ta dangana ga Talatu ta ji zahirin magana akan wancan zancen da mai gidanta yazo mata da shi. Gobe ne ‘d’aurin auren ya zama dole ta samu mafita a yau kafin duk wani shirinsu y’a ruguje.
Da mamaki Ayra da take tsaye a falo tana k’ok’arin fifita ruwan sha don zata sha ta fice aiki take kallonta. Da sauri ta dire cup ‘din a kan console ‘din da yake bayan k’ofar da ta bud’ewa Ummeey. Ta matsa gefe tana ce mata “Barka da zuwa.” A sanyaye Ummeeyn ta amsa tana bin falon da kallo kafin ta mayar da kallonta kan Ayra da take kallonta tana nazarin yarda Ummeeyn ta canja gaba ‘d’aya bata da walwala kamar yarda ta Saba shigowa da fara’a a lokutan baya. “Talatu ta tashi?” Ayra ta ‘daga kai “Bari na kira ta.” Ummeey ta girgiza kai tana ‘d’an sakin murmushi a hankali “Kyaleta bari na k’arasa ‘dakin.” Ta haye saman ta bar Ayran tana ‘d’an tab’e baki addu’a take a ranta Allah yasa auren aka fasa da don zallar murna sai ta zuba ruwa a k’asa ta sha ta kuma jero azimi na wata guda cur.
Amma da ta idar da Sallahr walaha tana ganin Hameeda ta mik’e da sauri tana k’arasawa wajenta ha’de da Zare hijab ‘din da yake jikinta. Idanunwanta sun bawa Amma tsoro don daga ganin su basa cikin kwanciyar hankali. Ta saka hannu ta ja hannunta suka zauna bakin gado. “Ko baki fa’da ba na san akwai abinda ya tayar miki da hankali..” Amma ta ce murya a sanyaye don yarda zuciyarta take bugu ta tabbatar maganar auren ce suka fasa, ba mamaki Sun juyo mummunan abu akan Ayran, shi yasa ta dinga fargabar auren.
Hameeda ta ja ajiyar zuciya “Ki kwantar da hankalinki Talatu, ko da na ji mugun abu babu abinda zai hana na ha’da Aure Turaki da Ayra ki k’addara Sun auri juna Sun gama..” Ta dafa kafa’dar Talatun “Akwai wani abu Talatu, akwai wani abu da kike b’oye min ko kuma ba kya son tuna shi, shine dalilin da yasa ba ki gaya min ba, Ina son ji Talatu, Ina son jin tarihin ki da bayan rabuwarmu, me ya faru a rayuwar aurenki da Kabiru duk da ina ji lamari ne mai girma, amma ki k’addara ni y’ar uwarki ce ta jini da zan iya b’oye Miki sirrinki kada ki ji shayin gaya min…” Ko kafin ta gama idanun Talatu Sun fara tsiyayar da hawaye, kuka take sosai tana tuno waccen rayuwar da ko mak’iyi ta bata fatan ta shiga irinta… Ta runtse idanunta tana ganin hotunan abin kamar yanzu lokacin abubuwan suka faru…… majigin abubuwan ta dinga gani a idanunta. Murya a shak’e idanunta a kulle ta ce
A wani lokaci a can zamanin baya….
Amma ta dinga cizar bakinta tana k’ok’arin fa’da da zuciyar da take son hana ta bawa Hameeda labari, duk da wasu abubuwan ta sani amma wasu fa? Anya idan Hameeda ta ji gaskiyar zance zata yarda ‘danta ya auri Ayra?
Kanta a k’asa cikin raunanniyar murya ta cigaba da k’ok’arin bada labarin nata…
Takaicin Uba….
Na Jikar Nashe
08033748387
Paid pages (Ki kiyaye hak’kin wani kada ki karanta abinda baki biya ku’dinsa ba, 500 ne kacal ga mai buk’ata.)
Cikin wani irin Yanayi Amman ta fara
Shekaru ne bila adadin da suka gabata, Iyayen mahaifiyarta irin fulanin nan ne na tashi, ba sa wannan daji basa wancan.
A wannan karan ma suka yada zango a dajin Mambila da take jihar TARABA STATE. Ba su ‘dau kwanaki da kafa bukkokinsu ba ayarin y’an fashi masu tafiya da mutane su siyar a matsayin bayi suka shigo rigar suka dinga sara da suka don kawai su yi gaba da