Showing 24001 words to 27000 words out of 132090 words
Chapter 9 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt
je Abbu.” Tsaki ya ja yana k’ok’arin tsiyaya masa fresh milk a cup. Aman duk da shekarun da yake da su shekara goma cur har a lokacin baya iya yiwa kansa komai saboda shagwab’a shi da suka yi. Cup ‘din ya karb’a ya sha sosai kafin ya ce “Abbu, Please Ummeey.” Ya zuba masa ido kafin cikin b’acin rai ya ce “Aman zan zaneka fa, nace maka Ummeey na Nigeria ni kuma ban shirya zuwa Nigeria yanzu ba…” Yaron cikin takaci ya fice da sauri yana kuka sosai. Jikin Turaki ya yi sanyi saboda Sam baya son b’acin ran Aman ‘din don haka don dole ya fara nema musu ticket na tahowa Nigeria, da shirin idan ya zo dole ya ruguza auren da ake son masa, sabida har a lokacin zuciyarsa bata gama amincewa da auren ba. Zai bi duk hanyar da zai bi yaga ba’a yi auren ba.
TAKAICIN UBA…..
Last free page In sha Allah.
Na
Nazeefah Sabo Nashe.
08033748387.
Ku biya ku’din ku ‘dari biyar kacal ta wannan account ‘din 2118666253 U B A. (Labarin Ayra Gaya dai yanzu aka fara, tafiyar mai tsaho ce, wannan kamar masomi ne abubuwa da dama suna gaba)
ArewaBooks @Nazeefah Nashe
Wattpad @Nazeefah381
_______________________
Ana saura sati biki aka kai lefe, lefen da Ya amsa sunansa na lefe don kaya ne a ciki ba na wasa ba. Sai dai duk zuzuta kayan da jama’a suke bai saka Ayra koda da sau ‘daya ta dubi kayan ba, wani irin ciwo take ji zuciyarta na mata, Wanda bata raba ‘daya biyu ciwon zuciya ne yake son kamata, ji take da Allah zai ‘dauki ranta da ta huta da bak’in ciki akan a wayi gari ana fa’din Ayra matar wani k’ato. Suna nufin Alwashin da ta sha ya bi iska kenan? Har a lokacin k’iyayyar jinsin maza na nan ‘danfare cikin ranta, ta kuma k’udirce abubuwa da yawa cikin ranta akan mutumin da aka ce zata aura.. Kuka ta yi sosai kafin ta mik’e tsam ta fara zagaye cikin ‘dakin hannayenta sak’ale a baya ta isa walk-in closet’s ‘din da yake ‘dakin, cikin wani k’aramin akwati ta janyo sak’on da aka kawo mata ranar a office ta tsaya tana duban kayan tana sakin murmushi “Gwara na k’are rayuwata a prison da na amince na ha’da jiki da wani gardin da sunan aure duk da na San a duk sanda ya kusanceni sai ya yi nadamar kusantata….
Ta runtse idanunta tana girgiza kai “Oh No! God forbid na tabbata duk randa na ji namiji a jikina ranar zan tafi lahira bak’in ciki ka’dai ya isa ya tarwatsa zuciyata.
A ranar ma tun safe aka dinga fama da ita akan ta bari a yi mata gyaran jiki amma ta k’i. Ganin yarda ta hassala har tana neman zube musu ne yasa Majeederh ta ce su k’yaleta ai fatarta mai kyau ce bata buk’atar gyara tunda ko gashi babu a fatarta luwai take kwance kamar bayan k’wai, kada su suka ta shi’de musu kamar yarda take aikatawa a duk sanda ta kai k’ololuwar b’acin rai.
Babu k’awarta ko ‘d’aya da suka San da labarin bikin, ta ja bakinta ta tsuke duk da dama ta San wasu da dama idan ta gayyacesu bikin ba zuwa za su yi ba, tunda itama bata halartar na su bikin.
Barcin safen da Ya ‘dauketa ne yasa ta wani mafarki da ta Saba yi shekarun baya, mafarki ne mai firgitar wa akan rayuwarta ta baya da ta gabata, tunda ganin abubuwan da suka farun kamar a lokacin suka farun take ta dinga wani irin ihu. Ihun da ta kara’de kafatanin gidan nasu. Kowa da yake gidan ya ji ihun. Hakan yasa Amma da y’an uwanta suka bazama ‘dakin nata. Sai suka tarar da ita cikin mafarkin take wannan ihun tana kiran Amma zai raba ni da mutuncina Amma ya cuceni……
Amma ki taimaka shikkenan sun…..
Zufa ko ta ina yanko mata ya ke. Tuni Amma ta k’arasa wajenta cikin tashin hankali ta kamata tana karanta mata duk Addu’oin da suka zo bakinta. Ta da’de bata ga y’ar tata cikin wannan halin ba, ta ma da’de ba tayi wannan mafarkin ba. Sai yanzu? Aka kunna mata a.c saboda gumin da take zubarwa ga wani irin ja da fatarta ta yi, jijiyoyin kanta suka bayyana ra’da-ra’da. Jikin Amma a sanyaye ta dinga Shafa mata ruwa a sassan jikinta kafin ta kawo ajiyar numfashi alamar ta farka daga suman nata wuncin gadi….
Ta dinga bin ‘dakin da kallo, kafin ta kafawa Majeederh ido tana sakin hawaye ta mik’awa Majeedarn hannu da itama take bulbular da nata hawayen kamar yanzu abubuwan suka wakana Sun dawo musu sabbi gar a cikin zuk’atansu. Sauran y’an uwan nata ma kukan suke. Amma bata hanasu ba don itama a b’oye take share nata hawayen. Ko da yaushe Ayra ta yi irin wannan mafarkin a halin da suke kasancewa kenan. Hatta jikokin Amma da basu San tushen abin ba sai da jikinsu ya yi sanyi suka kafawa iyayensu ido suna nazartar su, so suke su gano me iyayen nasu suke b’oye musu da har yau ba su sani ba. Sai dai ina? Yanayin fuskar tasu yasa suka kasa bu’de baki su yi musu tambayar da take cin ran su. Ayra ta yi lamo akan cinyar Amman tamkar dai wancan lokacin sanda lamarin mai gigita tunani ya wakana. Tausayi Amman take bata tafi tausayawa Amman akan ita kanta. Ta kama hannun Amman tana matsawa, tana so ta ‘dauke mata damuwar da ta gani a idanunta, ta sani duk abinda Amman take dauriya kawai take duk da tarin walwalar da take ciki, ta San zuciyar Amman a wahala take, kamar yarda ta tashi tun farkon rayuwarta Har yanzu wannan arzikin nasu bai isa ya saka zuciyar Amma ta manta da wancan bak’in al’amarin ba da sam bata son tuno shi. “Ki yi hak’uri Amma, mafarki na yi, mafarkin da kullum bana son yin sa, har murna nake da na ‘dau lokaci bai dawo min ba, sai yau har gaban abada Amma ba zan yafewa wancan mutumin ba, shi ya dasa min wannan bak’in cikin a rayuwata da sau tari wani lokacin nake jina kamar na rasa nutsuwata da hankalina har tambaya nake wa kaina me yasa tun a lokacin Allah bai ‘dauki raina na huta ba, ga wani bak’in cikin zan sake shigarsa Amma bana son auren nan wallahi zuciyata ciwo take min, Amma idan har kun dage sai an yi na amince sai dai ina rok’onku kada ku yi wani sha’ani da zai bayyanawa duniya ina murna, wallahi bana murna Amma bak’in ciki nake yi! Bak’in cikin da nake ji da dama in dai ba laifi a kaina da na kashe kaina na huta da na amsa sunan matar namiji. Na tsani Maza Amma! Na tsanesu duk duniya ba abinda bana so irin Jinsin maza, har godiya nakewa Allah da Ubangiji yasa ba ki haifi namiji ba, na tabbata da ba zan so shi ba, ba zan masa kallon tausayi da jin k’ai ba… Yaya kuke ji idan na yi aure Allah ya k’addara min na haifi namiji Am sure ba zan so shi ba… ta fa’da tana k’unshe bakinta saboda wani irin kuka da ya k’wace mata.
Amma bayanta kawai take duka alamar rarrashi itama ji take kamar ta fasa yiwa Ayran aure kada ta je ta haukata y’arta a banza da wofi, sai dai gatan da zata mata shine auren, musamman sanin cewa ba dawwama zata yi a duniya ba, idan ta mutu Ayra ina zata kama? Don haka dole ta jajirce ta ga ta aurar da Ayran tana fatan nan gaba ka’dan abinda take ji ya zama labari.
Ta kalli sauran yaranta musamman Majeederh da take wani irin kuka kamar ranta zai fita. “Majeederh kukan nan ya isa haka, kowane bawa ba shi da ikon canja k’addarar da take bin sa, mu godewa Allah duk halin da muka tsinci kan mu.
Abu ‘d’aya da zan sanar da ku duk wata hidima da kuka shiryawa bikin nan a janyeta, a ‘daura aure kawai a yi saukar Alkur’ani a kaita ‘dakinta tunda ta ce bata so, kada zafin ya mata yawa.” Kowa ya yi na’am da haka illa Dijah da ta ji abin sam bai yi mata ba, duk k’uzun da ta sha na gwangwajewa a bikin Ayran ya bi iska kenan.. ta dinga cizar baki takaici fal fuskarta Har sai da Amman ta balbaleta da fa’da sannan ta russuna “Idan hidima kike so idan ki ka yi hak’uri ai ga ku nan da bikin y’ay’a bayan sallah sai ki je can ki k’arata, wannan dai na soketa haba ina dalili? Ta ji d abu ‘d’aya mana.” Ganin Amma ta saka fa’da yasa Dijah ta ja bakinta ta tsuke tana hararar Ayran da take sake kanainaye jiki a cinyar Amman.
Fateema ‘daya daga cikin y’an matan jikokinta ta gyara zama tana kallon Amman, tambayoyi ne fal a cikinta Amma bata San ta yarda zata b’ullo musu ba, amma a yau kam ya kamata su san menene ya wakana a rayuwar iyayen nasu da suke b’oye musu ba kuma su tab’a basu fuskar da za su fuskanta ba. Ta cire duk wani tsoro da fargaba ta dubi Amman “Amma, ya kamata yau ku bamu labarin rayuwarku da abubuwan da kuke b’oye mana, ni dai gaskiya akwai abinda nake son sani Har yau bamu tab’a ganin wani daga cikin y’an uwanki ya tako nan ba? Haka nan mun ji labarin Babansu Ammeey yana raye Amma shima bamu tab’a ganinsa ba… me kuke b’oye mana ne? Me yake faruwa ne?”
“Ubanki ne yake faruwa!” Fateema ta ji maganar Mamanta Zainab a kanta cikin zafin rai ta cigaba da cewa na ce “Fatima ubanki ne yake faruwa? Ke har kin yi girman da zaki titsiye Amma haka? Me kike so ki ce? Kina so ki ce ba ki yarda da nagartar asalinmu bane ko me?
Me ye gaminki da Uban mu? Ko Ubanki ne?” Da sauri Fateema ta girgiza kai ta runtse idanunta cikin dana sanin tambayoyinta da ya hassalo mata uwa lokaci ‘daya. “Ku tashi Ku fice ban san ma rainin da ya kawo ku cikin mu ba, kuma ko da wasa kada ku sake maimaita hakan kuna ji na?” Da sauri suka hau ‘daga kai bayan saurarar Umma sunan da suke kiran Eesha da shi kenan, jikinsu a salub’e suka tattara suka bar ‘dakin ganin fuskokin iyayensu kamar an aiko musu da mala’ikan mutuwa.
Jikin Ayran ya ‘d’auki ‘dimi da kakkarwa tilas Amman ta saka ta a gaba suka tafi asibiti ta ga likitan da ta Saba gani. Ya sake bata magunguna ya kuma ba su shawarwari akan ta rage tunanin abin da yake damunta shine yake hassala mata tashin ciwon nata. Amma ta gamsu da bayanin likitan sai dai ta San ita kanta ta yi k’arya ta ce zata kawar wa da Ayran da wannan tunanin Wanda ta girma da shi ta tashi da shi cikin ranta, sai dai Addu’a kawai zata dage da yi mata addu’a Allah ya la’d’dafa mata. Haka suka koma gida kowa zuciya ba da’di musamman Majeeda da take jin tsohon bak’in dafin yana son taso mata, don dai ita ta fi su hak’uri ne tana da hak’uri matuk’a da gaske, don haka da wuya ka gane abinda yake damunta.
Haka dai a ka dinga shirin gudanar biki, kowane b’angaren bikin ba karkasashi har gwara b’angaren dangin ango Hameeda kam ji take kamar yanzu Turakin zai fara aure, ta zage shiri take sosai ita da autannin y’an matanta, Tasleem da Tayseer da suke ji da gayu da iyayi kamar me.. yau suke saka rai da dawowar Turakin, sai dai har dare Turakin bai dawo ba, ga shi a kashegarin ranar za’a ‘d’aura auren. Ran Hameeda kam ya b’aci don Turakin bai tab’a b’ata mata rai kamar irin ranar ba. Shiga ‘dari fita ‘dari ta danna kiransa a waya sai dai still ana sanar mata layin wayarsa na Nigeria ba’a kunne yake ba, alamar bai iso k’asar ba, takaici Ya hana Ummeey magana illa zugum da tayi hannaye a k’unci tana tunanin me zata cewa aminiyar tata? A kan rashin zuwan Turakin?
Duk wata damuwarta kawar da ita ta yi ta jingine a gefe, a sanda mijinta ya dawo fuskarsa tamkar bai tab’a dariya ba. Duk da ta San bai cika fara’a ba amma wannna karan ta san ransa a b’ace yake matuk’a. Jikinta a sanyaye ta mik’e ta shiga kitchen ta ‘dauko masa juice mai sanyi da ta ha’da masa da kanta na zallar apple da strawberry. Ta tsiyaya masa a cup tana nufar bakinsa da shi. Sai dai ga tarin mamakinta a karo na farko da ya k’i shan abin hannunta ya ture hannun nata Har lemon ya zube… kafin kace me? Gaba ‘d’aya idanunsa Sun rine saboda tsananin b’acin ran da yake ciki…..
“Waye uban yarinyar nan da Turaki zai aura? Yana raye ko ya mutu?”
Jikinta na rawa ta kalleshi gabanta yana fa’duwa ta ce “Me ya faru? Ubanta yana da rai mana bai mutu ba.”
Sai ta ga ya saki murmushi yana cizon leb’en bakinsa “Tabbas Turaki bai yi sa’ar uwa ba, da kika rasa matar da zaki aura masa sai b’aragurbi, yaran da suka mayar da ubansu bakomai ba, suka wulak’anta rayuwarsa alhali yana cikin tsananin neman taimakonsu, bayan su suna cikin daular duniya… abin da zan tambayeki shin kin san wacece yarinyar da zaki ha’da a aure tsakanin ‘dan ki da ita? Ba ki yi bincike ba ba kiyi komai ba…. Ina tabbatar miki ba zan bari Turaki ya auri yarinyar nan ba don ban ga ta inda suka ha’da hanya ba, yarda suka banzagatar da ubansu banga ta inda mu za su dubemu da idon rahma ba idan wani abu ya same mu…… Ki je ki ga muhallin da ubansu yake rayuwa a cikin tsananin ciwo.. sannan me suke yi da suka samu wannan d’aukakar lokaci guda.. matane fa.” Ya fa’da yana dallareta da idanunsa da suke bayyana b’acin ransa “Karuwa zaki aurawa Turaki… Turakin da ya saki mata har hu’du saboda ba su kai mutuncinsu gidansa ba… ta Yaya kike zaton zai zauna da Karuwa mai b’oye kamanninta don kada a shaida ita wacece kullum cikin shigar blacks Hijabs da nik’abs ita zaki aurawa Turaki?”
Turaki da yake tsaye a bayan k’ofa rik’e da hannun Aman duk ya ji zantukan Mahaifinsa.. ya damk’i hannun Aman da yake k’ok’arin fisge wa ya shige cikin gidan…..
Ina shi za’a aurawa Karuwa? Ta yaya idanun Ummmeey suka rufe? Ya ja hannun Aman da k’arfin gaske nufinsa su fice daga gidan don ko me za’a yi ba zai auri Karuwa ba……..
K’arshen free pages idan kana son cigaban labarin ka hanzarta biyan ku’dinka a tsunduma ka cikin paid group a kan Naira ‘Dari Biyar Kacal.. labarin Ayra dai yanzu aka soma.. shin ko kun san me Uban Ayra ya mata? Me ya haddasa mata k’iyayyar maza a zuciyarta? Shin Auren Ayra da Turaki zai yi yu? Idan ma ya yiyu ya kuke ganin zaman nasu zai kasance yarda Turaki ya tsani matansa na baya har ya sake su saboda ba su kai budurcinsu ba… ta Yaya zai so Ayra da ake mata kallon Karuwa wacce ubanta………
Ku dai biyo tafiyar y’ar mutan makwarari cikin labarin Takaicin Uba…… tafiyar mai nisan zango ce… wacece Amma? Wace irin gwagwarmayar rayuwa ta sha? Duka yana nan tafe.
Y’an gayun nan y’an k’walisa wa’danda ba sa son hayaniyar group ku biya dubu ‘d’aya kacal. Labarin zai sameki direct cikin wayarki ba ruwanki da an tsere min an wuceki abin ki yana killace kan wayarki sai sanda kika ga damar karantawa. Ku taho mu tafi garin su Ayra Gaya tare da ku.
Ki saka ku’din ku a wannan account ‘din. 2118666253 U B A.
Da ku nake alfahari..
Nazeefah Nashe…
Takaicin Uba…
Na Jikar *_Nashe*_
Paid pages. 13
Hameeda ganin S.Turaki har a lokacin bai yi niyyar tursasa ‘dan nasa ya dawo ba, da kanta ta kira shi a waya murya ba alamun wasa ta ce “Turaki wannan ce magana ta ta k’arshe da Kai a kan maganar auren nan, na gaya maka dole ne ka dawo a yi auren nan da Kai sannan kuma ka turo da sadaki da ku’din Kayan lefe kafin isowar taka.” Turaki cikin hukuncin takaici da gajiya da Jin maganar auren nan ya ce “Toh Ummeey, Amma me yasa dole sai nazo? Ku yi abinda ya dace kawai?” “Ba zamu yi abinda ya dace ba Turaki saboda aurenka ne Kai zaka zauna da matarka ya zama dole ka zo ku fahimci juna, in banda haka wane irin aure ne wannan ko ce maka aka yi sadaka suka Baka y’ar?” Turaki kamar ya amsa ta da “Eeh mana ai kamar sadakar ne yarinyar da ban Santa ba ban tab’a ganin ta ba ace an bani ita ai sadaka kawai aka bani.” A fili kuwa sai ya ja ajiyar zuciya kafin ya ce “Shikkenan Ummeey zan turo duk abinda ya dace, then I will try my best naga na zo don kawai farin cikinki.” “Yauwa ko kai fa? ‘D’an Albarka, da har kasa na fara tunanin ko an canja min Turaki ne a can k’asashen masu jajayen kunnuwa.” “Mhnn” kawai ya ce murya a shak’e alamu k’arara Sun nuna Ummeey ta gama tik’e shi. “Yauwa sai na jika.” Hameeda ta fa’da tana katsewa wayar cikin murmushin samun nasara.
Gidan Talatu take son zuwa ta ji menene abinda Ayran ta fi buk’ata ta tambayo colours da sizes ‘din takalmin Ayran da ubder wears ‘din ta. Burinta a yi auren nan duk a zatonta Matsalar Turaki ta zo k’arshe gani take Turakin ya sake dacewa da mata kamar matarsa ta farko. Bata San abinda Ayra take shukawa ‘d’an nata ba da ta sani tabbas da farin cikinta ta tak’aita.
Gaba ‘daya ahalin Amma suna baje a parlourn Ma sha Allah y’ay’a da jikoki birjik a zube Ayra ce kawai take bedroom ‘dinta saboda hayaniyarsu da ta fara damunta.
Ummeey ta yi sallama ta shiga falon da fara’arta take fa’din “Aa A’a, yau bataliyace a gidan namu haka.” Kasancewar sun je har gida Sun gaisheta hakan yasa suka ganeta da sauri suka baje suna gaisheta. Ummeey ta dinga amsa musu tana rarraba idanun yarda zata ga surikarta ta so take yau ko a