Showing 129001 words to 132000 words out of 132090 words
Chapter 44 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt
‘din JIKAR NASHE REAL FANS
JIKAR NASHE SPECIAL GROUP
(Mutane na musamman da ba zan manta da ha’din kan da kika ba ni ba alherin Allah ya kai muku a duk inda kuke.
Ina mik’a sak’on godiyata da ahalin group ‘dina na MIKIYA WRITERS ASSOCIATION Musamman
NIMCY LUV
AYUSHERCOOL
ZEE KUMURYA And all the member.
Sakon godiyata ga
ANTY SURAYYA (Halin Yau) ina muku albishir d’in zuwan littafinta Bak’ar Ta’ada nan ba da da’de wa ba In sha Allah dafatan za ku min kara ku siya.
Mutane na musamman da ba sa gajiya da comments a koda yaushe kuma ina godiya gareku Ubangiji ya fi ni yabawa. Nagode sosai.
1.Balaraba Alhassan
2.Bishira Aybo Kano
3.Abidatu Alhassan
4.Halima Sadisu Dankaka
5.Salima Abdullahi Dan Sabau
6.Mum Intisar
7.Samira Ameer
8.Ummu isma’il
9.Mami Yahya
10.A’isha Umar
11.Amina Umar Uk
12.Bintu Nouh Kd
13.A’isha Muhammad Lawal
14.Hidayah Lahmad
15.Zulaihatu Umar
16.Aisha Biochemis
17.Amira Sadik Dakin gari
18.Aisha Kawu gujirya
18.Fatima D.Isa
19.Aisha Jamilu Nashe
20.Hadiza Yahya R.lemo
21.Zainab Dankaka
22.Asma’u Dankaka
23.Habiba Muhd Nayaya
24.A’isha Mustafa Sa’id
25.Ummussalama M Makam
26.Hadiza Muhd Mahe
27.Jamila Musa
28.Maryam Abba Zanna
29.Zulaihatu
30.Habiba Bello Sarki
31.Aisha Aliyu Shanono
32.Ummi cindo
33. Saeedat Aminu Musa
34.Ummu Raymond
_____________
Yarda ta hango Amman a zaune kanta a cikin gwiwoyinta shi ya saka Ayra sakin wata ajiyar zuciyar da bata shirya fitowarta ba ko bakomai ta ji da’di da ta ga Amma she is alive sab’anin bak’in tunanin da ya zo cikin zuciyarta. K’afafunta sun yi sanyi k’alau ta k’arasa in da suke. Ummeey ce ta mik’a mata hannu da mata alamun ta iso in da take. Ba tayi nawar fa’dawa jikinta ba don haka kawai sai ta samu k’afafunta da yin rawa ga wani irin zazzafan zazza’bi da yake sake rufe mata jikinta. Ummeeey ta rungumeta a jikinta tana fa’din “Don’t cry Ayra, yanzu addu’arku ya fi buk’ata da sake nema masa gafarr Ubangiji mutuwar Uba Mahaifi akwai ciwo Amma sai an daure an cije sannan kaso mafi rinjaye daga k’unar zuciya yake raguwa.” Ayra ta ji wata fa’duwar gaba ta zo mata, kafin idanunta su cigaba da hasko mata fuskar Mahaifinta a jiya yana sakar mata murmushi, murmushin da ta kasa mayar masa a she sallama yake mata, haka kawai sai ta samu kanta da yin murmushin kamar dai ace Yana nan yana kallonta yana kuma jin ta sai dai Ina ta san yanzu ya mata nisa nisan da ta san har abada ne sai yaumul tanadi ita da ta sake ganinsa shikkenan ya tafi. Sai ta ji wani hawaye yana zirya a idanunta ga wani tashin hankali da ya risketa lokaci guda. Ta runtse idanunta tana jin yarda zuciyarta take suya da wani alhini mai sanya jin sanyi a zuk’ata da gangar jiki. Idan ta rufe idonta Mahaifinta take kallo a cikin keken gurarunsa jiya yana sakar mata murmushi.
Sai da aka masa wanka aka masa sutura sannan aka zo aka ce Iyalinsa su je su masa sallama. Jikinsu a raunane suka mik’e don isa falon da gawar take. Hawaye suke sosai suna jin da suna da dama da sun dawo da rayuwarsa sun nuna masa gatan da ba su nuna masa ba sai dai ina lokaci ya k’ure musu ba abinda za su masa ya amfaneshi a yanzu sai Sadakatul Jariya. Haka suka durk’ushe a wajen suka yiwa Mahaifinsu kallon k’arshe kallon da sun tabbatar da ga shi sai a darussalam idan suna da rabon ganin juna. Ayra hannunta na rawa ta saka ta shafi fuskar Mahaifinta tana fa’din “Mun yafe maka Baba Allah ya yafe maka Allah ya sadaka da rahmarsa.” Shikkenan ta runtse ido tana hawaye duk da ba Sabo a tsakaninsu Amma akwai wannan feeling ‘din na tsakanin zuciyar Y’ay’a da iyayensu shi su Ayra suka dinga ji har zuwa sanda suna ji suna gani aka zare hannayensu daga jikin makarar aka d’auketa Ayra ta mik’e tsaye da niyyar bin makarar sai ta ji an rik’eta an rungumeta ko ba a fa’da mata ta san Turaki ne don k’amshin turarensa ya bayyana mata haka. Sai da ya jata ya mayar da ita b’angaren Ummeey sannan ya tafi don raka gawar bayan ya tabbata ya sanyata a jikin Ummeey saboda ba ya son wani abu ya samar masa ita.
—————————
Kwana uku aka ‘dauka ana zaman makokin hakan ya janyo Turaki ya jinkirta tafiyar sa ya kuma cigaba da neman Visar Ayran don ba ya jin wannan lokacin da ta yi kakagida a zuciyarta zai iya tsallakewa ya barta A nigeria. Bayan ko nisa baya iya yi da ita wani irin so yake mata mai zafin gaske da shi kansa har mamakin kansa yake yi sau tari sai ya zauna ya dinga tunanin irin son da yake mata kamar ya shallake misali kamar aikin sihiri.
Yau ma da wuri ya dawo hannunsa ‘dauke da ledar Yalo da D’ata da Guiva da Ayra ta mayar da su abincinta tunda aka yi mutuwar su Suka zama abincinta cin su take kamar wacce ta samu abinci. Ko kallon abinci ba tayi ga wani irin fari da ta yi na masifa sai kuna saurin fushi nan da nan ta hassala duk sai ya ‘dora alhakin hakan da mutuwar mahaifinta.
Ya tsaya a parlourn Ummeeyn yana kallon Ayran da ta yi kamar bata gan sa ba don bata son ya ce tazo su tafi sashensa tunda aka yi mutuwar a wajen y’an uwanta take kwana. Murmushi kawai ya yi ya zauna yana masa gaisuwar k’annensa da suke gaishesa har da su Majeedah da yanzu itama ita take gaisheshi tunda matsayin wa yake a wajenta. Idanunsa cikin na Ayra tana zaune ta mik’e k’afa Tayseer tana kankare mata farce. Su Amma duk suna wajen shi yasa bai kulata ba.
Sai da aka gama ta mik’e don shiga bedroom ta ji ya ce “Ki kawo min abinci ina part ‘dina.” Ayra ta ‘dan turo baki alamar ranta bai so ba, ta shige kitchen ‘din tana nazarin abinda zata zuba masa don ta san bai fiye cin abinci bai nauyi ba ya fi ta’ammali da Vegetables da fruits kawai sai ta saki tsaki ta bud’e fridge ta d’ebi fruits don ta ha’da masa Fruit salad, don ba zata iya girki ba ita yanzu bata son jin k’amshin komai ma kuma komai ma haushi yake bata.
Sai da ta saka a bowl mai murfi sannan ta ‘dora a kan Tray. Kawai kuma sai ta ji kunyar ta fita Parlourn a ganta zata tafi wajensa. Da k’yar ta fito daga kitchen d’in tana sakin ajiyar zuciya ganin ba wanda ya kula ma da ita ta yi saurin shigewa b’angarensa.
A zaune ta gan shi bakin gado da Laptop a gabansa yana ta aiki. Sallamar ya amsa yana ‘dagowa ya sauke idanunsa a kanta yana ‘dan murmushi ya ce “Ai na zata ba zaki zo ba?” Ta langwab’e kanta tana shirin zama bakin kujerar da take ‘dakin ta ji ya ce “Kada ki fara, matso nan na ji waye yake tab’a min ke kwana biyu na ganki ba walwala.” Kamar ba zata je ba sai kuma ta tuna da hu’du bar da Yaya Aisha da Ya.Zainab suka mata da safe na yarda ake kama miji a hannu. Don haka ta mik’e tana jin kamar k’afarta zata hard’e ta fa’di a wajen don har yanzu tana jin kunyarsa ba wai ta saba bane. Shi kuwa kallonta kawai yake yana sakin murmushi ganin yarda take komai a kunyace. Tana shirin zama ta ji ya jata jikinsa yana shinshinar wuyanta Ayra ta lumshe ido tana jin yarda yake bin duk sassan jikinta da zazzafan kiss shaidar dake nuna mata ya yi missing ‘dinta sosai in just 4 days. Don dole Ayra ta ajiye kasalarta ta biye masa mamaki ne ya kamashi sosai ganin yarda take neman zautar da shi da wasu irin hot romances da take zuba masa. Ya lumshe idanunsa kawai yana gidiya ga Allah da ya nufeshi da auren irin matar da yake so matar da zata jiyar da shi da’di daga tarin baiwar da Allah ya bata.
Towel a hannunsa ya fito daga wanka ya zuba mata narkakkun idanunsa yana fa’din “Alhamdulillah for the gifts of God. Tabbas yanzu na yi aure.” Ayra ta lumshe ido tana jin da’din zuzuta ta da yake. “Jibi za mu tafi inda muka fi wayo don haka ki fara shiri.” Ayra tana ware ido ta dubeshi “Tafiya kuma?” Ya ‘d’aga mata gira yana lumshe ido “Yes tafiya, ba zan iya barinki a nan ba ni ina can idan ba so kike na samu matsala da aikina ba, da yau ne ma to na ‘daga tafiyar ne saboda yau Aman zai dawo daga makaranta ina so na gan shi mu yi sallama don Ummeey ta ce ba zan tafi da shi ba, ni kuma bana jin zan dawo k’asar nan in the next one year ma.” Ayra ta zaro ido ya sake ‘d’aga mata girarsa “Mhmnn, na gaji da yawo a iska ina son nayi concentrating a kan k’wadagon da nake ba zan dawo ba sai kin haihu mun zo kawo musu Baby su gani tukun.” Ayra ta mirgina tana rungumar filo ha’de da lumshe idonta sam bata son tafiya ta bar Familynta Amma kuma shima bata son ta yi missing ‘dinsa musamman yanzu da ya jiyar da ita duk wani da’di da bata tab’a zaton a duniya akwaishi ba. Sai dai bata son nuna masa zulamarta a fili don haka ta ‘dan zunb’uro baki ta ce “Ni dai da ka bar ni sai mu dinga zuwa hutu da Aman.” Ya tsyaa cak yana kallonta yana jin wani abu yana bin jikinsa tsoro yake ji kada dai a ce har yanzu bai gama kame zuciyarta ba tunda har take tunanin iya zama babu shi. Jikinsa a sanyaye ya zauna a gefen gadon yana mirginota ta dawo saman cinyarsa idanu ta runtse don ba zata iya kallonsa ba a haka yarda take a jikinsa ko Riga babu. “Ayra open your eyes.” Ta sake runtse idanunta “Ki bud’e idonki ki gaya min kin fi son zama a nigeria ba kya son bi na.” Idanunta a lumshe ta ce “Bana son tafiya na bar Amma da Ummeey na.” Ya saki murmushi ka’dan ya ce “Ba kya so na har yanzu?” Bata san sanda ta ware idanunta a cikin k’wayar idanunsa ba “Wa ye yace maka bana son ka?” Ya lumshe idanunsa “Idan kina so na ba zaki ce na tafi na barki ba tunda kin san ba zaki iya barci ba idan ba kya kusa da ni, na sani ba kya so na ni nake ki’da na nake rawata.” Ya mik’e yana ajiye kanta a saman pillow. Fuskarsa ba walwala ya ce “Thank you” Da sauri Ayra ta kamo hannunsa tana mik’ewa “In dai binka ne zai saka ka gane ina son ka na amince zan bika mu zauna a can sama da shekara goma ma, ka daina cewa bana son ka.” Bai san sanda ya zube a gabanta yana jan hannayenta ba yana murzasu a hankali wani farin ciki yake ji mara misaltuwa “So You loved me Right?” Ayra ta lumshe idanunta a hankali ta furta “Surely I can do without you.” Bai san sanda ya rungumeta tsam a jikinsa ba yana fa’din Alhamdulillah!”
______________
Kashegari Baba Waziri ya uzzirawa Maimartaba akan yana son Talatu ta tare. Mai martaba ya dinga kallonsa yana murmushi ya san a shekarun Waziri ya na buk’atar sake aure tunda ya girmeshi nesa ba kusa ba sai dai bai yi zaton zai yi rawar k’afa kamar akan Talatun ya fara aure ba ko kuma Budurwa ya aura. “Wai saurin me kake ne Waziri? Sai kace wani wanda yanzu ya fara aure? Ita Talatun nan fa ba yarinya ba ce.” Waziri yana sakin ajiyar zuciya ya ce “Ba zaka gane yarda nake jin Talatu a raina bane, soyayya nake mata fiye da soyayyar da saurayi zai wa budurwarsa ni da Talatu ta fiye min y’an mata dubu. Don Allah ta tare yau na saka an mata komai.” Maimartaba ya ‘daga kansa “Shawarar da zan baka ka nemi Hamida itace zata kai maka Talatu har ‘dakinka a yau, don idan aka bi Ta Talatu ba zata tare nan kusa ba.”
Haka kuwa aka yi Hameeda ta amsawa Baba Waziri akan zata kawota a yau ba kuma tare da ta sanar da yaranta da ita kanta Talatun ba. Don haka ana idar da Sallahr Magriba Hameeda ta shirya wasu y’an kaya a akwati ta saka aka fitar mata da shi ta k’ofar baya don bata son Talatun ta gani tunda Kabiru ya mutu yanzu ba wani Walima da za’a yi. Tana kallon Talatun ta ce “Shirya Don Allah ki raka ni dubiyar wata k’awata.” Talatu bata kawo komai a ranta ba ta mik’e ta shiga ‘d’aki ta saka zumbulelen Hijabinta sannan ta fito. Suka rankaya da Hamida da Fulani matar Sarki sai Jummai aminiyar Talatu a motarsu sai wasu Bayi guda Uku da za su taho a wata motar guda.
_______Gidan Talatu______
Tun daga bakin gate za ka san gidan ya amsa sunansa na sabon gida na zamani sai walwali yake da hasken fitilu kamar rana. Talatu tun a waje ta fara sha’awar gidan kafin su shiga ciki. Suka zube a falo Hameeda tana kallonta tana murmushi ta ce “Ma sha Allah, Allah ya kawo mu gidanki Talatu Allah ya baku zaman lafiya ke da Baba Waziri ya kawar da dukkan abin k’i.” Da hanzari Talatu ta d’ago tana kallonta Fulani da Jummai da sun Riga sun san komai suka ce “To me za’a jira Talatu ke ba yarinya ba Waziri sai suntiri yake a ba shi matarsa shi yasa muka zame muka kawo ki Allah ya baku zaman lafiya.” Daga haka suka mik’e suka bar Talatu a zaune da sakakken baki ta zama sai kace Statue. Tana k’ok’arin mik’ewa ta bi bayansu Waziri ya shigo cikin shigar Jallabiya sai ya zama kamar ba shi ba ta saba ganinsa a cikin manyan riguna. Ya sakar mata murmushi ya ce “Alhamdulillah barkanki da shigowa gidan ki Talatu Allah ya yiwa auren mu albarka.” Ya fa’da yana janta a jikinsa ya bata kyakykyawar runguma yana jin kamar ya mayar da ita ciki. A kunnenta ya dinga sauke ajiyar zuciya yana fa’din “Alhamdulillah nagode ya Rabb da ka cika min Burina.” Talatu ta lumshe idanunta tana jin wani iri a jikinta abinda bata tab’a ji ba, Waziri ya jata ya cigaba da nuna mata ‘dakunanta to Fatan Alheri BODDON WAZIRI. TALATUN KABIRU.
Ummeey tana komawa gida yara suka dinga kallonta kafin Ayra ta ce “Ina Amman?” Ummeey ta saki murmushi ta ce “Amma tana gidan Mijinta” duk sai suka bu’de baki suna kallonta cikin mamaki Ayra ta ce “Ko sallama babu? Gobe fa mu ma zamu tafi” Ummeey ta ce “Sai ku je goben ku mata sallama ke da Turakin ku ga gidan Aurenta daga nan.” Suka saki murmushi duk da jikinsu ya yi sanyi amma burinsu samun farin cikin Ammansu, don haka suka ja baki suka yi shiru bayan sun ce Allah ya sanya alheri. Ummeey tace “Ina Tasleem?” Ayra na murmushi ta ce “Tana wajen Abba Jabiru Ai da alama da shi za’ayi don naga ya kafa gwamnatinsa.” Amma ta saki murmushi tace “Allahu yasha, ai Jabiru mutumin arziki ne da kowa zai so ha’da zuri’a da shi.”
Kashegari kafin su Ayra su wuce suka je gidan Amman dukkansu hankalinsu ya kwanta ganin yarda Amma take walwala da farin ciki da alama komai ya tafi mata yarda take so. Baba wazirin ma ba inda ya je yana nan gidan Amman tunda ba gidansu ‘d’aya da matansa ba ya dinga jan su a jiki musamman Ayra da aka ce zata tafi yau ita da Mijinta. Suna kallon yarda yake kallon Amman cike da soyayya, sai hankalinsu ya kwanta sun san Amma ta fa’da hannu na gari a yanzu ne zata san Maza suna suka tara! A daren ranar Kuma Su Ayra suka tashi ta airport ‘din Abuja Ayra ta dinga jin kamar ta yi Kuka Amma da ta tuna tare da wa take masoyinta na gaske sai ta ji hankalinta ya kwanta ta sake kwanciya a jikinsa a cikin jirgin shi kuma ya saka hannu ya rungumeta yana sakin ajiyar zuciya.
Haka rayuwa ta cigaba da gara musu cikin farin ciki da kwanciyar hankali. Har cikin Ayra ya isa haihuwa wani dare ta tashi da nak’uda suka nufi asibiti sai Ga Ayra ta haifo y’an biyunta Maza zar masu kama da Turaki kwabo da kwabo. Sanda aka mik’o mata yaran sakar baki ta yi tana kallonsu duk da an gaya mata Twins ne bata tab’a kawowa a ranta zata haifi twins ‘din ba. Turaki yana kallonta yana murmushi ya ce “Shikkenan Ayra ta zama Maman Boys ko ya za’a yi da k’iyayyar Mazan?” Ta ‘dago tana kallonsa tana murmushi ta ce “Ai na tuba na daina tunda Allah ya cusa min soyayyar Babansu.” Ya had’asu da yaran yana murmushi ya ce “Y’an Nigeria suna hanya.” Ayra ta ware ido ta ce “Serious?” Ya ‘d’aga mata gira yana cewa “Ban gaya maka ba ne dama Just to surprise you.” Ayra ta lumshe ido.
Sai yamma aka sallamesu suna zuwa gidansu ta ga gidan a cike ta tsyaa tana kallonsu cike da farin ciki ba wanda bai zo ba a cikin ahalinta y’ay’an gidansu da jikokinsu har da K’annensu Maza da suke Uba ‘daya don tuni suka ya da makaman yak’insu suka shiga cikin y’anuwansu su kuma suka nema musu aiyukan yi da sana’a. Ayra da sauri ta rungume Ummmeeey da Amma cikin tsananin farin cikin ganinsu har da hawayenta. Aman kuwa ‘dauke yaran ya yi ya hana kowa ‘daukarsu yana ta kallonsu. Tasleem Ayra ta kalla tana murmushi tace “Ina Abba Jabiru yaushe ne Bikin?” Tayseer ta ce “Saura 2Months In sha Allah.” Ayra ta ji da’di don ko bakomai zata samu damar halarta bikin.
Deejah ta tashi tana kallon Ayra tana murmushi kafin ta kunna T.v ta yi connecting da wayarta sai ga vedion Ayra lokacin tana budurwa a gidansu gwiwarta zube gaban Amma tana hawaye “Amma kada ki bi tata tasu, ni ba zan tab’a aure ba na tsani namiji kuma duk randa ku ka min aure wallahi sai na kashe kai na.” Ayra ta lumshe ido tana murmushi kafin ta bu’de idon ta wara su akan Turaki ta ce “The Winner!” Aka saka tafi da dariya gaba ‘d’aya. Turaki yana kallonta ya ce “Ga