Showing 39001 words to 42000 words out of 132090 words

Chapter 14 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt

zuba mata ido yasa ta yi k’arfin halin tartaro nutsuwa ta sakawa kanta. Tana murmushin k’arfin hali ta kalli Jabiru ta ce “Me yasa ka watsa min ruwa ina barci na mai da’di?” Jabiru ya ‘dauke k’wallar da take idonsa don baya son k’ara mata damuwa a kan wacce take ciki. “Na tashe ki kin k’i tashi, shi yasa na zuba miki ruwa.” Ta sauke kakkaurar ajiyar zuciyar tana kallon Majeedah da Zainabu da suka yi zugum, sai kuma ta mik’e tana fa’din “Kai mu je tsakar gida mu sha iska..” “Mama Baba Mugune, ba zai ga Annabi ba ko? Kema dukan ki ya yi? Dama ya mutu.” Cak ta tsaya daga shirin ficewa daga ‘dakin da ta yi ta juyo tana kallon Majeedah da take furucin kuma da alama iya gaskiyar abinda yake zuciyarta kenan. Ranta a b’ace ta dawo ta ‘daga Majeedah ta zuba mata mari “Kul na sake ji Majeedah mahaifin naki kike kira da wannan kalamin.” “Ba shi da sunan da ya zarce wannan Anty Talatu ki barta ta fa’di abinda yake ranta.” Jabiru ya fa’da fuskarsa kamar ya saka kuka. Talatu ta bi bango ta sulale ta zauna hankalinta a tashe, ta fara tunanin wace wauta Kabiru yake da har ya sanyawa y’ay’ansa tsanarsa ba tare da ya lura da cewa Kansa yake cuta ba.” Kuka ne ya kufce mata ta fara tunanin mai zai faru ranar da aka wayi gari y’ay’anta Sun k’i mahaifinsu saboda tarin laifukansa Ya subhanallah! Allah ka shiryi Kabiru ka ganar da shi gaskiya tun lokaci bai k’ure masa ba. Ta furta a hankali kafin murya a raunane ta dafa Jabiru da Majeedah ta ce “Ku yi hak’uri musamman ke Majeedah ba a tab’a canja mahaifi kuma ko me ya yi Miki har abada yana nan a sunan mahaifinki don haka ki ce Astagfirullah Akan sab’on da kika yi, idan ba so ki ke Allah ya k’ona ki ba.” Da sauri Majeedah ta ce Astagfirullah Allah na tuba sannan ta fa’da kan Cinyar Talatun tana kuka tana fa’din Mama ni bana son sa tunda kema ba ya son ki.” “Ba zaki daina ba kenan ko Majeedah?” Ta furta a tsawace kafin ta tureta daga jikinta ta mik’e ta yi tsakar gida tunawa da ta yi yaran ko abinci ba su ci ba.





__________


⭐️Haka rayuwar ta cigaba da gangarawa cikin wani irin yanayi mai wuyar fasaltuwa a wajen Talatu, Zamani ne da ba zata manta da shi ba kacokam zata iya kiran kanta Mara sa’a a rayuwa a wancan lokacin. Kabiru ya banzagatar da ita da y’ay’anta tun bayan da ya fahimci bata da mamora ya bi kuma duk wata hanya ta cusguna mata don ta gudu ta bar aurensa, Amma Talatu ta yi mursisi a gidan auren saboda ba ta da inda zata je, don haka tilas ta hak’ura da duk wani wulak’ancin Kabiru.

Idan ya saka k’afa ya bar k’auyen ma sai ya shekara bai waiwayesu ba da ita da yaranta ita take kula da su gaba ‘daya Jabiru shi yake fita ya yi hak’ilo ya samo musu tsabar abinci ita kuma ta samo musu Kayan masarufin da zasu dafa abincin.

A wannan yanayin katsaham Kabiru ya zo garin, ya kuma sanar mata za su koma cikin garin Kano kuma shawarar matarsa mai tsohon ciki ya bi, Akan ya zo ya tafi da Talatun ta dinga yi mata aikace-aikacen gidan, don Kabiru ya zo birni a sa’a duk da har a lokacin ba a San sana’arsa ba Amma fa yana da gidan Kansa da motarsa ta hawa, gida kuwa mai gate duk da dai ba tanfatsetse bane a Amma a wajen mutanen k’auye dole za su kira shi aljannar duniya.

Talatu ta yi Jim tana kallonsa, Sam bata son binsa birni anan ma da yake ganin idon Wanda ya sani yana wulak’anta ta ina ga an je birni, cikin k’asa da murya ta ce “Ni dai da zaka bar mu anan ‘din da yafi bana son zaman maraya.” Ya watso mata harara kafin ya ce “Ai kuwa idan kika ce ba zaki bi ni ba, ki tabbata kin yiwa igiyar aurenki. Da kika samu ma zan Kai ki birnin aikin banza banda Sahiba ce ta takura ni ban ga dalilin da zan yayabeki zuwa birni ba.” Tana Jin haka ta ja bakinta ta yi shiru ta tashi ta fara ha’da musu tsummokaransu don dai su ne kawai da su ba wani abin ba. Don ko katifa ba su da ita ta lalace gaba ‘dayanta. Sai da za su tafi sannan ta ga Ashe har da Hadi da matarsa kuma suna ‘dan ‘dasawa da mAtar Hadin, Hadin ne dai Sam ba sa shiri. Wani k’aramin gida Kabirun ya kamawa Hadin anan unguwar da yake, ba don komai ba sai don Hadin ya iya masa banba’danci.


Tunda suka sauka suka fara kalle-kalle abinka da ba sabanba kuma ba su tab’a shiga birnin ba. Sanda suka je gidan Kabirun suka shiga falon matar sa Sun yi mamakin ganin dukiyar da Kabirun ya tara Amma ya kasa tallafarta da yaranta. Ta ha’diye wani Abu mai ‘daci bayan da ya umarceta ta durk’usa ta gaida matar, dama ko bai ce ba ta yi niyya don ita dai bata ga Aibu ga hakan ba tunda dai matar ta girmeta, sai dai shi hakan da yayi ya yi ne don ya cusguna
Mata. A yatsine take amsa gaisuwarsu kafin ta watsa wa Kabirun wani kallo ta ce “Mai da’din ai sai ka kaisu can ‘dakin bakin gate ko? Don ka San dai wannan k’azantar ba a gidana ba, ka kuma sanar da ita dalilin da yasa ka dawo da ita nan ko? Don ban amince kwanciyar aure ta shiga tsakaninku ba, ba zan iya wannan jagwal ‘din ba ina zaman zamana a harba min ciwon sanyi, kai ma bak’in nacinka ka saki matar nan ka k’i sakinta, ko da yake barta ma na huta Neman y’ar aiki Amma dai zan gaya Miki ba ke ba mijina, nawa ne ni ka’dai na fi son ko da yaushe na ji shi a jikina kina ji na ko? Idan kin kiyaye komai kike so za ki samu ke da yaranki Amma idan kin k’i zaki ga wulak’anci wallahi.” Ta fa’da tana wani k’as k’as da chewingum sai kuma ta watsawa su Majeedah harara “Ku don ubanku baku iya gaisuwa bane?” Kabiru ya ce “Ina za su iya? Ai bata koya musu ba, ban da abinki kema mai zak’in me zan yi da ita yanzu matar da ta wawake kamar k’ofar gari ai ta tashi daga aiki ina zaune da ita saboda har yanzu ta k’i yi min gagarumin laifin da zan saketa almura da tuni na aikata ta tafi duk inda zata je ma.”


Wani k’ululu ne ya tokarewa Talatu k’irji sai dai ta danne kukan da take ji yana taso mata don bata San ta nunawa Kabiru karayarta da wuri, don ta fahimci don ya tuburata ya ‘daukota ya kawota nan, to zata jure zata jure duk wani k’alubale da zata fuskanta daga wajensa fatanta Allah yasa ta amsa jarrabawarta daidai.


Kabiru ya mik’e yana harararta “Sai ki mik’e mu je na raka ki, kin kwaso sangamemen ‘da kin taho min da shi to kuwa sai dai ya zama Maigadi ya dinga kwana a bakin gate.”

Bata ce masa komai ba, har zuwa sanda ya kaita wani ‘daki da yake bakin gate, wani ‘dan mitsitsi da shi, sai k’aramin Toilet da yake daga harabar gidan. Ta da’de a tsaye tana k’arewa ‘dakin kallo kafin ta saki ajiyar zuciya tana addu’ar Allah ya bt hak’uri da juriya a kan duk wani k’alubale da zata fuskanta a zaman gidan nan. Yana tsaye yana binta da kallo kafin ya saki tsaki “Ba za ma ki godewa Allah kin samu cigaba ba? Daga turb’aya kin koma ‘daki mai shimfi’de da leda?” Karo na farko ta Ware idanunta a kansa tana Jin kamar ta ce masa gwara turb’ayar akan nan inda ka kawo ni a wulak’anta ni, sai dai bakinta ya gaza furucin, bata Saba ba bata saba iya mayar masa da magana ba bata da wannan courage ‘din. Don haka ta mayar da idanunta k’asa tana ji ya zabga tsaki ya fice daga ‘dakin yana fa’din “Idan ba za ki iya ba, sai ki ja komatsan yaranki ku tafi duk gidan uwar da kika ga dama.” Zubewa kawai ta yi a k’asa sarai ta lura da take-taken Kabiru kora da hali kawai yake mata, ita kuma har yau ta kasa hak’ura ta tattara ta tafi ta bar shi, Ina ma zai bata gida ta yi zamanta da yaranta to da sai ta ce ta amince ya saketa. Su Majeedah suka matsa jikinta suka kanainayeta ga yunwa suna ji fuskarsu kamar su saka mata kuka, ta ja su ta rungume a jikinta a hankali ta ce ‘KHAIRAN IN SHA ALLAH’


Wunin ranar a tsaye cur ta yi shi saboda aikin da Karimatu ta yi ta saka ta, aiki take tuk’uru har sai da gab’banta suka dinga ciwo. Da daddare da kanta Kariman ta zuba musu wani abinci ‘dan mitsil a cikin k’aramar cooler, sanda ta bu’de abincin da suka hannu iya su uku yaran suka cinyeshi ban da ita da Jabiru, don hak’ura suka yi suka bar yaran da suke ta kukan yunwa tun yammacin ranar.


Haka rayuwa ta dinga gurgura musu ba wani haske da suka samu a rayuwar kullum a cikin duhu suke, tsawon wannan lokacin daga shi har matarsa Sun mayar da ita kamar mai aikin gidan, idan ka shigo ma gidan ba zaka tab’a tsammanin matar gida ba ce saboda yarda kamanninta ba su dace da hakan ba, yaranta ba suturar arziki duk da ta samu Karimatu ta saka Mai da’dinta ya kai yaran makarantun gwamnati a cewarta suna hanata barci, da zarar Sun dawo kuma za su tafi makarantar allo sai ka ji gidan sak’at sai b’uruntun Talatu tana aiki. Duk da tsohon cikin kullum tana kitchen tana juyo iface-ifacensu wani lokacin sai suna tsaka da saduwa da ranar Allah Kabiru zai k’wala mata kira ya ce ta kawo musu ruwa idan ta kawo kuma ya ce sai ta tsaya ta kalla ko kuma a bakacin aurenta, haka zata tsaya tana kallonsu a ranar idan ba wani ikon Allah ba ba zata yi barci ba saboda yarda zata samu kanta a Jin zafaffiyar sha’awa har kuka take da hawayenta, wani lokacin idan ta yi niyyar Jawa Kabiru Allah ya isa sai ta ji ta kasa musamman kasancewarsa Uban y’ay’anta idan ya tsiyace ya lalace dole za’a kira shi uban y’ay’anta.


A wannan mugun zaman da suke Cikin Karimatu ya isa haihuwa da ta tashi haihuwar sai Allah ya bata haihuwar ‘da namiji zo kaga murna wajen Kabiru ya dinga wage baki yana fa’din “Allah nagode maka, yanzu ne na san na haihu da na haifi ‘da namiji ba mace, Kabiru ya yi magaji.”

Dole a lokacin Talatu ta sakawa kunnenta auduga ta rufe idanunta ruf, ta daina ji ta daina gani duk don kada ta ‘dorawa kanta ciwon zuciyar Rashin mutuncin da Kabirun yake mata. Sa aka yanka a haihuwar aka yi kuma gagarimin suna, abinda bai tab’a ha’da shi da sauran y’ay’ansa ba, ko Majeeda da take y’ar fari bai mata yanka ba. Su dai nasu idanu Talatu kuma ta kwab’esu da koda wasa kada su sake su yi abinda Ubansu zai harzuk’a da su, komai lokaci ne wata rana sai labari.



Satin Karima biyu da haihuwa cikin dare matsuwa ta saka Kabiru ya nufi ‘d’akin Talatu ba tare da sanin matarsa ba. Talatu sai jinsa kawai ta yi a jikinsa tana shirin kwa’da ihu ya fella mata mari ha’de da cewa kina magana ta ji wallahi a bakin aurenki, haka ya gurji Talatu ba ruwansa da su Majeeda da suke kwance Wanda Talatu bata tantama Majeedah ta farka kuma ta gan su don bata da nauyin barci. Ba laifi ya ‘dan ji ta ha’de ka’dan sai dai ba kamar lokacin farkon aurensu ba. Haka ya mik’e yana gyara wandonsa “Saura kuma ki bari ta fuskanci wani abin ya shiga tsakaninmu wallahi a bakin aurenki.” Ya fice yana sakin tsaki bayan ya tsallake Jabiru da duk abinda yake yi a cikin kunnensa.

Daga wannan kusantar da ya yi mata cikin ikon Allah sai cikin Deejah ya shiga, ba tare da ita kanta Talatun ta sani ba don tuni Karima ta gyare jikinta suka koma suna gurzar amarci ya manta da wata Talatu. Sai da ciki ya yi wata biyar sannan Karima ta ankare ranar Talatun na mata gyaran falo ta tsaya tana dubanta kafin ta ce “Zo nan Talatu? Me ye wannan nake gani a jikin ki kamar ciki?” Talatu a daburce ta dinga ja da baya tana shafa cikin da tun watan jiya da ya fara motsi ta San da shi. Karima ta k’unduma wani uban zagi kafin ta ce “Kan Uba? Wato haintata ku ke? Ke da wancan bak’in munafukin?” Da sauri Talatu ta zube a wajen don ta tabbatar yau zamanta a gidan Kabiru ya k’are…..
Takaicin Uba…

Pg 20

Nazeefah Nashe

💔💔💔💔



Jikin Talatu sosai ya fara rawa, gwuiwoyinta da take durk’ushe a kai suka gagara ‘daukarta bata San sanda ta zube turus akan mazaunanta ba. Gumi ko ta ina ya shiga zubo mata.. Kariman na shirin sake magana shigowar Kabiru ya katseta ta dallareshi da manyan idanunta, kallon da yake nuni da zallar tuhuma.
Gabansa ne ya fa’di dalilin bai San me ya faru ba. Ya mayar da kallonsa kan Talatu da take zaune dab’as ya zabga tsaki don da alama mai zak’in ta tab’a “Kada ki damu kan ki da wannan gaya min me ta miki ba mamaki zamanta ne ya zo k’arshe a gidan nan…..” “Yi min shiru Kabiru.” Ta fa’da a tsawace “Yau k’aryar ka ta k’are me ye wannan nake gani a cikin Talatu?” Cikin mamaki ya kai dubansa kan cikin Talatun da ya fara tasawa ka’dan sai kuma ya girgiza kai yana jin fa’duwar gaba ya ce “Menene kuwa mai zak’in? Ai ni ban ga komai ba banda Tumbi da alama ta fara ci tana k’oshi zata ajiye zuguda…” Karima ta mik’e ranta a b’ace ta k’arasa wajen Talatun da ta yi k’asa da idonta tana ambaton sunan Allah a ranta, ta San dai tabbas yau aurenta da Kabiru yazo k’arshe dama abinda yake so kenan. Kallon sama da k’asa ta yi mata kafin ta ce “Ke me ye a cikin ki? Fa’da masa da bakinki saboda in ga k’arshen mak’aryaci yau.” Bakin Talatu na rawa ta ce “Ki yi hak’uri Hajiya komai ya faru ne bisa kuskure… shi… ma bai san da cikin ba?” Wani irin waro ido Kabiru ya yi ina zunduma uban ashar “Ciki? Ciki kuma? To uban wa ya miki cikin?” Karima ta fa’da idanunta cikin na Talatun. D’aga kai ta yi tana kallon Kabiru da yake k’ik’kifta ido ta nuna shi.. “Shine wallahi tun bayan haihuwarki da sati biyu ya je ya haik’e min, daga nan ne ciki ya shiga.” Karima ta saki salati tana kallon yanda Kabirun ya yi tsilli-tsilli kamar bawan da ya yiwa Uban gidansa laifi, sai zuba gumi yake yana jin kamar ya shak’o Talatun Ya mak’ureta Ya shek’ata barzahu.

Cikin tsananin Kishi Kariman ta dinga zabga musu harara dukkanninsu kamar wa’danda suka aikata zina, sai kuma ta ciji leb’e ta shige ‘dakinta tana fa’din bari na tattara na bar muku gidan tunda ka samu wacce ta fini a wajenka wallahi ka bani mamaki yaushe zan iya wannan kwamacalar?” Da sauri Kabiru ya bi bayanta bayan Ya kaiwa Talatu hauri da k’afa yana fa’din “Wallahi ba abinda zai hana ni sakin ki a yau ‘din nan, mara mutunci kawai.”

Koda ya bita ‘dakin tana tattara kayan k’arya da niyyar harzuk’a masa tunani bata yi aune ba ta ji mutum a jikinta, ya san yarda take mabuk’aciya ba zata iya tsallake abinda take masa ba, dama tarko ya ‘dana mata, tuni suka yi luf suka fara aikata abinda suke so, tun Talatun na jin iface-ifacensu har ta ji tsit. Jikinta a salub’e ta mik’e ta nufi ‘dakinta ta fara tattara musu kayansu kafin su dawo daga makaranta su yi gaba, don dai ta tabbata yau zamanta a gidan Kabiru ya k’are. Wani irin k’unci da zafi game da ra’dadin zuci da na gangar jiki take ji, hawayen ma ya k’i zuwa tana mamakin hali irin na Karima da Kabirun ma gaba ‘d’aya kamar ba su San tana da hak’kin aurensa a kanta ba?


Komai ya lafa a tsakaninsu, Kabiru ya yi mata bajintar da kaso mafi yawa daga b’acin ranta ya zagwanye, illa zallar kishin da yake neman ya kassara mata zuciyarta. Yana matsa kumatunta ya ce “Dafatan dai kin hak’ura mai zak’i kamar zuma.” Ta lumshe idanunta tana fa’din “Dole na na hak’ura Amma iya laifinka ka’dai na hak’ura banda na waccen matar, a yau nake so ka saketa ka mayar da ita can k’auyen inda ka ‘daukota idan ya so ko gidan ka bar mata ni dai bana son tana shigarta yarda kake shigata kishi nake ji sosai.” Yana dariya ya ce “An gama yau nima ai ta kai ni bango, a dole fa naje na kusanceta…” da sauri ta ‘daga masa hannu “Bana son jin kalmar nan Mai da’din tana bak’anta min rai.” Ya kai mata sumba ha’de da fa’din “An gama my madara.” Ya fice yana y’ar wak’a jin sa yake a sama yarda Karima ta tarbeshi yau abin ya yi santi ne, kai Karima ta ko ina kin kai mace canca’di ni da k’orama.. Ya fa’da daidai lokacin da yake saka kai ‘dakin Talatu Ya San kuma ta ji shi sarai kuma daman don ta ji shin ya fa’da. Ta ha’de y’an suturunsu kaf a buhu tana zaune ta zuba uban tagumi. Ya ja tsaki “Maganinki ai, ba bakinki ya iya magana ba ai yanzu kya tattara ki koma k’auye ke da yaran ku cigaba da cin gabzar tuwo kuma ko haihuwa kika yi kada ki nemeni in dai ba namiji kika haifa ba ki ra’da sunanki da kanki Amma ni na sake ki saki ‘daya…..” Da sauri a kuma razane ta ‘d’ago tana kallonsa kafin ta zube a gabansa “Don Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login