Showing 72001 words to 75000 words out of 132090 words
Chapter 25 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt
kuma fa ka tsaya kamar soja, ko kallon hoton Mar’atussalihar ne har yanzu?” Basarwa ya yi ka’dan ya je ya jingine hoton don ya san magana ce mai kama da harshen samo Ummeeyn ta gwa’ba masa “Duk wata mace ba burinta bane rasa Budurcinta kafin a kaita gidan miji, ba lallai bane a yawon banza Yarinya take rasa budurcinta wata k’addara ce wasu dole aka musu wasu kuma girman shekaru ne da aiyukan yau da kullum suke kawar musu da budurci, ka daina jam’u kana tattare mata gaba ‘d’aya kana musu ku’din goro, ka ji na gaya maka.” Ummeey ta fa’da cike da basarwar duk da ta hango matsananciyar kunya a fuskar Ayran da ta yi kamar ta zunduma ihu. Shi kuwa gogan ko a jikinsa sai ma waskewa da ya yi ya zauna daga gefe yana gaida Ummeeyn, ta amsa kadaran kadahan fuskar ba yabo fallasa. “Dama sallama na zo miki, gobe zan wuce Turkey.” “Ma sha Allah visar Ayran ta fito kenan?” Da sauri ya ‘dago yana kallonta kamar ya ‘dora hannu a kai ya yi ta zunduma ihu. “Ba da ita zan tafi ba, akwai maganar ma da ta zo gaya miki.” “Ashe kaima baka shirya tafiyar ba.” Idanunsa a raunace ya ‘dago yana kallonta sai dai bata ma nuna ta san me yake ba, ta ‘dauke kanta tana kallon Ayra “K’afarki k’afar Mijinki duk inda zai je ki zame masa kamar jaka, kuskurena babba barin mijinki lulawa wata k’asar ba tare da ke na in dai yana da halin tafiya da ke ‘din.” Sannan ta mayar da kallonta wajen Turaki fuska ba wasa ta ce “A tun tashinka ka san sarai ba na barin Abbunku ya yi tafiya ba dani ba, don haka idan kana don ganin b’acin raina ka tafi ba da Ayra ba, ba gama magana.” Daga haka ta k’walawa Mai aikinta kira don su Tayseer ba sa nan sun tafi Saloon “Maza ki kawowa Ayra abinci.” Mai aikin ta juya da sauri. Turaki ya tsume a kan kujera sai zabgawa Ayra hararar k’asan ido yake. Ummeey duk abinda yake tana kallonsa kafin ta tab’e baki a ranta ta furta sai dai ka mutu. Ganin bai samu goyon baya ba, don haka ana kawo abincin ya mik’e zumbur ya ce “Ke tashi tafiya za mu yi.” Ayra ta ajiye cup ‘din Kunun ayar da yake hannunta duk da taso cin abincin ta Kuma lura da gayya ya mata haka sai dai bata damu ba ta saki murmushi kawai Ummeey ma ta lura da mugunta ya shirya don haka ta k’walawa Salame kira tana zuwa ta ce “Juyewa Ayra abincin nan a coolers ki zuba mata kunun ayar, yau na hutar da ita girki.” Turaki cikin k’unk’uni ya ce “Wallahi sai ta yi don ni tuwo zan ci.” Ummeey dariya ce taso kufce mata sai dai ta gimtse ta ce “Bakomai zata yi Ai lada zata samu, aikin miji ba abinda ya fishi samun lada, duk abinda ya saka ki ki yi kin ji littafin ki na shiga aljanna kike cikawa.” Ayra ta ‘d’aga kai tana amsar ledar da Ummeeyn ta bata na ha’daddun turarukan Humras da designers. “Idan kun shirya tafiyar ka samar mata visar sai ka yi waya ka sanar min in mata shirin tafiya, ka kuma kaita gidansu, don na san kaima baka je ba, daga nan ku wuce can direct ka yi wa mahaifiyarta godiya.” “Mahaifinta fa?” Ya fa’da yana kallon Ummeey.
Ba Ummeey ka’daiba har Ayra sai da ta razana da jin tambayarsa, tun da take bata tab’a jin haushin tambayar ina Mahaifinta ba kamar yanzu, kafin tayi wani yunk’uri na fa’dar abinda yake bakinta ta ji furucinsa cikin dakakkiyar murya yana fa’din “Ko da yake na ji labarin ba su ‘dauke shi da daraja ba, yana can yana walagigi da rashin lafiya, ba su damu da shi ba balle su agaza masa a yanayin ciwon da yake ciki, amma ba mamaki yana gudun cin dukiyar da ta tabbata hanyar da aka sameta ba ba ta halal ba ce….” Amin!” Ummeey ta ambaci sunansa cikin tsawa hakan yasa ya ha’diye sauran zantukan da suke ransa wanda tabbas ya yi su ne don ya hassala zuciyar Ayran. K’wallar bak’in ciki ce ta fara gangara a kumatun Ayra, a yau kam ta sake dank’arawa Maza suna ‘daya duka kuma halinsu ‘daya sam bata hango banbancin da ake cewa suna da shi ba. Cikin b’acin rai Ummeey tace “Wani irin shirme ne haka Turaki, me yasa kake son tabbatar da abinda bai zama lalle bane gaskiyarsa, shin ka zauna ka tuhumi Ayra labarin rayuwarta ne, ko kuma ka fi yarda da na yamad’idin da mutane suke zuwa suke gaya maka, ka kiyaye fa! Bana son rashin hankali kana ganin yarda ka sakata kuka ka b’ata mata raina banza, shi wanda yazo ya baka labarin me yasa bai baka labarin abinda shi mahaifin nasu ya yi musu ba? Kada ka sake bana so idan kuma ya sake ki bugo waya
Ki gaya min.” Ta fa’da tana share mata hawayen da har a lokacin yake sintirin zuba daga idanunta. “Yi hak’uri kin ji daughter wata rana sai labari, kuje Allah ya yi miki albarka.” Kafin su yi aune tuni Amin ya yi gaba don haushin kukanta yake k’ara masa ji yake shima da da hali tabbas kukan zai saka.
Driving kawai yake ba tare da ya sake kallon b’angaren da take ba, duk da yana jin shashshek’ar kukanta a kai a kai, ya maze ya basar yana yak’i da tasa zuciyar. Har suka je gidansu Ayran kafin su shiga ya yi parking yana juyowa gaba ‘d’aya ha’de da zuba mata ido. Ji yake kamar ya rungumota jikinsa ya lallasheta amma hassalalliyar zuciyar sa na kwab’arsa da aikata haka. “Ki yi min shiru, kuka dai kuka sai ka ce ke ka’dai ce me idon kuka.” Ya fa’da yana kafeta da narkakkun idanunsa, kamar sake tunzirata ya yi ta sake sakin kukan wannan karan da ‘dan k’arfin gaske. “Mtsw! Wallahi idan ba ki min shiru ba
Zan miki abinda tilas na kashe miki bakin kukan, haba meye haka salon mu shiga a ce wani abu na yi miki, ni ya kamata na yi kuka ni da aka ha’dani da jangwam amma kece mai bakin kuka.” Ba tayi shirun ba duk da warning ‘din da ya yi mata, hassala zuciyarsa ta yi bai san sanda ya janyota jikinsa da k’arfin tsiya ba, ya saka bakinsa cikin nata kamar wanda ake sakawa shocking haka Ayra ta ji, ta fara k’ok’arin k’wacewa amma ta kasa sakamakon sake shigar da jikinsa cikin nata da ya yi sosai, tuni Ayra ta nemi kukan ta rasa sai tsoro da rawar jiki. “Sai da nace ki min shiru kika k’i shi yasa na biyo da ke ta hanyar da tilas ki yi shirun.” Ya fa’da yana sakinta ha’de da goge bakinsa da tissue yana harararta k’asa-k’asa “Haka kawai kin sani ha’da baki da bakin da ya ga mazan duniya.” Tsit ta yi cikin mutuwar jiki tana gyara gyalenta gaba ‘daya wani yanayi ne yake bak’untar jikinta, ga idanunsa da suke mata yawo a jiki da ta kasa samun nutsuwa da su. “Ka daina kallona bana so.” Ta yi furucin cikin matuk’ar kasala da zai lura k’warai zai gane bak’uwa ce a lamarin ya tab’e baki “Me zan kalla a
Jikinki, ba fa na son fulako idan zaki saki jiki ki saka Kina acting just like you don’t know anything.” Ya fa’da yana cize bakinsa ha’de da son sake lalubo k’wayar idanunta amma ta kasa ba shi dama, madadin haka ma da sauri ta fice daga motar tana furta Allah ya isa k’asa-k’asa sosai da murya. Kawai sai ya samu kansa da zabga murmushi yana shafa lab’bansa da har a lokacin yake
Jin taushin sussulb’an leb’enta a kansa “She has a kissable and sweetable lips.” Ya fa’da a hankali ha’de da lumshe ido yana sakin sassauk’ar ajiyar zuciya tabbas ya sake janyowa
Kansa jangwam yau. Da k’yar ya samu komai ya lafa masa ya sarrafa kansa wajen fita da azama daga motar kamar komai ma bai faru ba. Sai dai idanunsa sai da ya maka musu bak’in glass don idan ba haka ba tsaf za a faro jirginsa yarda idanun suka canja kala suke nuna zallar jarabar da yake ciki. Duk inda ya motsa kuma k’amshin mayataccen turarenta na nan a jikinsa, kamar yarda nasa ya mak’ale a nata jikin.
Amma tunda ta sauke idanunta a kan Ayra wani farin ciki ya ratsa zuciyarta, tabbas burinta ya cika yau ga Ayra ta zo gidanta a matsayin Matar wani, abinda zatonta bai tab’a bata ba. Sam bakinta ya kasa rufuwa ji take kamar sun shekara ba su ha’du duk da kwana biyu ne kacal. Rungumeta ta yi sosai a jikinta, itama Ayran ta cusa kanta jikin Amman tana sakin kuka mai tafe da shagwab’a “Amma na na yi kewarki.” “Nima na yi kewar Ayra ta.” Amman ta fa’da tana shafa bayan Ayran cike da tausayi da kulawa. Sun da’de a haka suna jin bugun zuciyoyin junansu kafin Amman ta janyeta suka zauna kan kujera tana fa’din “k’alau dai ko? Farin cikin ganinki ya makantar da ni na kasa ganin aibun fitarki a kwana biyu kacal.” Ayra ta ‘dan ‘d’aga kai da niyyar amsa mata sai suka tsinkayi muryarsa daga bakin k’ofa yana fa’din “K’arya zata miki Amma, ba wani k’alau takura ni ta yi sai na kawota da takardar sakinta…..”
Ya fa’da yana zura hannu a aljihu da niyyar zaro takardar da yake nufi ba. Ba Amma ka’dai ba hatta Ayra sai da ta ji fa’duwar gaba ta dinga bin takardar da yake mik’a mata da kallo. Shi kuwa ya kafeta da ido lokaci guda kuma yana lumshe idon ha’de da sake mik’a mata takardar. Wannan karan saura k’iris zuciyar Amma ta daina aiki…….
(A yi hak’uri cigaba zai biyo bayan sallah In sha Allah.)
Kada ku manta Alk’alamin rubuta Labarin k’addarar Ayra mai tsawo ne. Ku dai ku cigaba da bibiyar Jikar Nashe in sha Allah ba za ku yi asarar ku’din ku ba. Ayi sallah lafiya Love you all. 😊😌)
Takaicin Uba…
Nazeefah Nashe
36.
💔💔💔💔
Dafatan an Yi sallah lafiya? Allah ya maimaita mana yasa mun yi karb’ab’biyar ibada.
_________________
Ayran kanta gabanta ne ya dinga fa’duwa ta zuba masa idonta da suka fara jirkita zuwa wata colour daban, me hakan yake nufi da ya yi mata wannna sharrin? So yake ya b’ata tsakaninsu da mahaifiyarta ko me? Hannu na shaking ta karb’i takardar duk da ta so samuwar takardar sai dai sam bata so fitar ta a wannan gab’ar ba. Amma ma zuciyarta zuwa lokacin tuni ta yi rauni tana jin sautin fitar numfashinta ba bisa k’aida ba. Ta dinga ware ido tana son ganin abinda yake takardar duk da har a lokacin Ayra ta kasa bu’dewa idanunta a lumshe suke kawai, hakan take so amma tana tausayin Amma bata san a yanayin da zata riski kanta. “Sak’o ne daga mai gadi wata k’awarki ce ta ce a baki ya biyo Ki zai baki ya ga har kin shige cikin gida.” Cak numfashinsu ya tsaya na wuncin gadi a lokacin suka saki ajiyar zuciya a tare Ayra ta ware idonta tana kallonsa itama Amman kallonsu take sai da ta gyara zamanta kafin ta ce “Amin me ya faru ne na ji kana min maganar Ayra ce take son ka saketa?” Ya yi k’asa da kansa sosai kafin ya tank’washe
K’afa yana gyara murya ya furta “Amma ina yini?” Sai a lokacin Amma ta tuna basu gaisa ba tana murmushin ta ce “Lafiya lau Turaki, ashe fa ba mu gaisa ba kaine duk ka ru’da min tunani tunda ba kowacce uwa bace zata so aurar da y’arta a ce an saketa a kwana biyu kacal.” Ya jinjina kai “Abinda nake ta son ta gane kenan Amma sai dai yarinyar nan taurin kai ne da ita kullum sai ta tuk’eni akan sai na saketa shi yasa na ce ta zo mu zo wajenki da kanta ta gaya miki don kada na saketa a ga laifina…” Da sauri Ayra ta ‘dago ta zuba masa ido jin sharrin da yake yi mata, suka ha’da idanun nata idon yana kawo ruwa shi kuwa da sauri ya ‘dauke kansa yana murza hannunsa. Amma kuwa tsabar takaici kasa magana ta yi illa k’asa da ta yi da kanta idanunta a runtse takaicin Ayra na neman kasheta me take son Turakin ya ‘d’auka bata da tarbiyya ko me? Jin Ayran ta fara kuka yasa Turakin da Amman suka yi saurin ‘dagowa
Suna kallonta Amma tace “Wani irin iskanci ne wannan kin yi laifi tun ba’a yi miki fa’da ba ki b’are baki kina kuka, wallahi ko ki rufe min baki ko yanzu na ba shi umarni ya zane min ke, ki bar ni da bak’in cikin ma da yake cin zuciyata, Allah ya saka maka da alheri Amin da baka aikata abinda take son ka aikata ba ka yi aikin hankali ke kuma ki je don kan ki, Ina dai gaya miki ki kiyaye tsallake umarnin Allah don wallahi aure ba abin wasa bane, ka yi hak’uri don Allah Turaki sai ka yi hak’uri da halayenta ta riga ta saka tsanar maza da aure ma gaba ‘daya ne a ranta amma wata rana sai labari In sha Allah.” Turaki yana ‘dan murmushin gefen kumatu ya ce “Bakomai Amma In sha Allah Zan cigaba da hak’uri da ita a cigaba da mana addu’a.” “Kullum ita muke yi Turaki, Allah ya ha’da kanku. Ki durk’usa ki ba shi hak’uri na ce miki.” Ayra murya na rawa tace “Ka yi hak’uri idan na maka ba daidai ba idan kuma ban maka komai ba…” “Rufe min baki anan wajen a gaban nawa ma rashin kunya za ki masa? Anya kuwa Ayra?” Ta sake ha’diyar yawu mai ‘daci kafin ta ce “Ki yi hak’uri Amma.” “Hak’uri na ‘d’aya ki bi mijinki sau da k’afa ki aikata duk abinda ya umarceki kin ji Ayra?” Ta ‘d’aga kai tana share hawayen da suka kasa tsayawa daga zuba daga idanunta “Ku tashi ku je Allah ya yi muka albarka.” Turaki ya amsa da k’arfi ita kuwa Ayra a hankali cikin dasashshiyar muryarta ta amsa abubuwa kala kala ta k’udirta a ranta da zata ‘dauki fansa a wajen mutumin da ta ra’da masa sunan mugu tabbas sai ta rama wannan alwashi ta ci. Shi kuwa Turaki cikin farin cikinsa ya fita daga gidan ya shiga motarsa ya kuma ware ki’da cikin wak’ar da yake so ko yanzu burinsa ya cika kuma ko yanzu ya saketa ya tabbata babu wanda zai ce masa don me?
Jikinta a sanyaye ta bu’de marufin k’ofar don shiga, daga cikin yake k’arewa idanunta kallo abinka da mai girman idanu tuni sun tashi sun yi luhu-luhu sabida kukan da ta fara. Maganar Baba Maigadi ce ta tsayar da ita daga shiga motar. “Hajiya kin ga sak’o ko?” Ta ‘dan mayar da mayafinta ya rufe mata fuska don bata son yaga alamun ta yi kuka kafin ta ‘d’aga kai murya a dashe ta ce “Na gani Baba, daga ina ne?” “K’awarki ce ta ce a baki, da nace ga numberrki ta kira ki sai ta ce ba zata kira ba itama tana da numberrki amma yanzu ta goge tunda kin nuna bata da muhimmanci an yi bikin ki bata sani ba.” Ayra ta ‘dan saki murmushi ka’dan don ta san Besty ce zata mata haka “Bakomai Baba zan nemeta nagode.” Ta zuge jaka ta ‘Debo ku’din da bata san adadinsu ba ta ba shi.
Godiya sosai ya yi mata tare da jaddada addu’ar neman zaman lafiya a aurensu da zuri’a ‘dayyiba. Bata san me yasa ba kawai sai ta samu bakinta da amsa addu’ar tana shiga motar. Amin ya zube mata idanunsa kafin ya ‘dauke yana tab’e baki ka’dan ya ce “Kika amsa kuma? Kin manta sunan auren namu?” Bata amsa shi ba, don ba k’aramin haushi yake bata ba ji take kamar ta shak’o shi ta yi ta dukansa har sai ta gaji. Ya cigaba da jan motarsa yana bin wak’arsa cikin nisha’di.
Tsawon kwana uku ya ‘d’auka yana nemar mata visa duk da bai so haka ba ya zama dole ya bi umarnin Ummeey idan yana son gamawa da duniya lafiya. Da k’yar aka gama mata visar don haka yau a gajiye lik’is ya dawo gidan da kuma neman fa’dansa kamar yarda ya saba. Sai dai bai sameta a falon ba, da alama tana ‘daki ba mamaki ta gaji da rigimar yau ta shige ‘dakinta da wuri. Shi kuma yana son janta da rigimar don sau tari ta haka ne ka’dai yake samu ya ha’da jikinsa da nata ya samu sauk’i a wasu lamarin, don shi ka’dai ya san a yanayin da yake kwana. Ya san kansa ya san shi ‘din ma buk’aci ne yana mamakin yarda ya ‘d’au tsawon shekaru har hu’du bai kusanci mace ba, duk da magunguna yake sha da y’an dabaru amma yana wahala, yanzu kuwa da yaga mace kusa da shi kuma macen da ya da’de yana mafarkin samuwarta a matsayin matarsa tazo masa a matsayin matarsa sai lamarin yake da’da k’amari yake kuma nema yafi k’arfinsa. Sau tari ji yake kamar yaje ya kusanceta ko da ta k’arfin tsiya ne, da ya tuna wasu banza sun Riga sun bu’de hanyar sai ya ji ransa ya b’aci.
Sai da ya yi wanka ya saka pyjamas na barci ya feshe jikinsa da turaruka sannan ya nufi ‘dakinta don ya sanar da ita ta shirya goben flight ‘din 4:30 za su bi zuwa Moscow, don ya fasa turkey ‘din sai ya je Moscow tukun na zai dawo ya je Turkey. Don a Moscow ne yake da gida nasa na kansa kuma a can zai barta ya nufi Turkey ‘din.
Daga ita sai b’ingilin towel take zaune gaban mudubi shima ta zameshi zuwa k’ugunta don ta ji da’din shafawa jikinta mai sosai. Bata san yana gidan ba bata san kuma zai shigo ba da bata zauna a haka ba. Kuma k’ofarta ma a bu’de ta barta don ta saba ko a gida haka take fitowa daga wanka ta zame kuma towel ‘din ta shafe jikinta da Oil ko moisturizer. Idanunsa ne suka masa kyakykyawan