Showing 6001 words to 9000 words out of 132090 words
Chapter 3 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt
Shakka babu, tunda na taso na lura maza suna son d’aga min hankali Saboda fuska da kyawun jikina na gwammace na zama haka, ba su ganni ba ma balle su kwad’aitu da so na.” Saliman tana sakin wani irin bahagon murmushi ta ce “Sai dai idan ubangiji bai nufa ba, da ikon rabbissamawati sai alkadarinki ya karye soonest za ki aure.” Wani irin kallo Ayra take mata da idanunta da suke bayyana tsagwaron b’acin ranta ta janye hannunta daga kafad’arta cikin b’acin rai ta nuna ta da yatsa “Matuk’ar kin San irin alkaba’in da za ki dinga janyo min kenan, na rok’eki kada ki sake bayyana fuskarki a a idanuna sabida komai ma zai iya faruwa siblings d’ina ma ina samun mummunan sab’ani da su a duk lokacin da suka min irin wannan.” Hawaye ne fal idanunta ta mik’e ta shige toilet d’in da yake office d’in. Jikin Salima Sa’ad ya yi sanyi sosai har ta ji tana nadamar furucinta ita kanta hawayen ne yake son zubo mata. Fitowar Ayran daga toilet ya saka hankalin Saliman ya sake ta shi ganin yarda idanunta suka jirkita saboda tsananin tashin hankali. Sai dai da murmushi ta ke kallon Saliman da alamun son kawar da waccan damuwar daga ranta. Ko bakomai Saliman bak’uwace shekara nawa ba su had’u ba bai kamata ta bak’unceta da wannan yanayin ba. Ta dafa kafad’arta tana sake wawuro murmushin duk da k’ok’arin kufce mata da yake son yi ta saki ajiyar zuciya. Idanunta cikin na Saliman ta ce “Kada ki damu K’awata komai ya wuce raina ne ya b’aci, bana Iya controlling temper d’ina a duk lokacin da aka bijiro min da waccan maganar dafatan za ki kiyaye please.” Da sauri Saliman ta d’aga mata kai tana sakin tata ajiyar zuciyar had’e da fad’in “Alhamdulillah, wallahi na zata kina fitowa shak’eni za ki yi.” Murmushi Ayra ta saka had’e da sake mayar da nik’ab d’inta ta sakeshi ya rufe mata fuska ruf jin ana mata knocking sannan murya a kaurare kamar yarda ta saba kaurarata don bata son ko dad’in muryarta ya ja hankalin maza, balle su so sanin fuskar mamallakiyarta, ta bada izinin shigowa. sakatariya ce take sanar da ita zuwan wani bak’on costomern su da ya saba zuwa siyan kayan k’awata toilet. Tana ba shi izinin shigowa Saliman ta mik’e tana fad’in “Ayra bari na wuce Zan shigo Gida In sha Allah don ina son ki taya ni zab’an outfits da zan amfani da su lokacin biki, may be jibi tunda week end ne ki ganni ki turo min address d’in gidan.” Ayra ta zura hannu a jaka ta ciro mata compliment card da address d’in gidansu yake jiki ta mik’a mata. Saliman ta sa hannu ta amsa tana nazarin yarda take jin sunan unguwar ta railway, jin shigowar mutumin yasa cikin azama Saliman ta mata sallama ta fice. Tsawon mintuna suna k’ulla harkar kasuwanci da mutumin ba tare da ya san yarda fuskarta take ba, har mamakin yarda take k’udundune fuskarta yake don ko k’wayar idanunta baya gani, ya sha tunanin wani irin miji take aure mai matuk’ar tsanani da takura har haka da ko yatsun matarsa bai amince a gani ba. Sau tari ya kan ja ajiyar zuciya ya kuma jinjinawa mijin nata a zuciyarsa don ko bakomai ya yi maganin masu zalamar kallon mata irinsa, duk ga tunaninsa Ayran matar aure ce. Yau d’in ma siyayya mai yawa ya musu sannan ya mata sallama bayan ya tura mata takardar da take nuna shaidar ya biya kud’in. Ayra ta bi bayansa da kallo tana mamakin yarda yake kafeta da ido ta tabbata da zata bari ya ga fuskarta ba abinda zai hana shi nuna mata zalamarsa a fili, ta ja dogon tsaki had’e da jin tsanarsa a ranta ta tsani kallo ta kuma tsani duk namiji mai kallon mata irin kallon da ake kira kallon k’urilla.
Daga wannan takaicin ta ji aikin ma ya gundureta gaba d’aya ta yi switching system d’inta had’e da mik’ewa ta fara tattara komatsanta da niyyar tafiya gida.
_____________
A harabar gidan nasu da yake railway tsaye kusa da maigadi Mal. Hadi ne yake masa magiyar a bar shi ya shiga. Mai gadin ya kafa ya tsare a kan dokar gidan da Ayra ta kafa masa na rashin amincewa duk wani namiji shiga gidan sai da sanin ta matuk’ar ba d’aya daga cikin surikan gidan ba, shima ta jaddadawa mai gadi idan da wasu suke tare ya tbbata ya sanar da ita zuwansu kafin su shiga cikin gidan, duk wannan tana yi ne a k’ok’arin killace kanta daga idanuwan duk wani namiji.
Dannowar kan motar Ayran ya bawa Baba mai gadi damar fad’in “Alhamdulillah ga Hajiyata nan ma ta zo idan ta amince ka shiga sai ka shiga.” Malam Hadi ya hau gyara babbar rigarsa da ta sha guga daga shekara sai shekara yake sakata, ranar idi Amma yau ganin gidan da zai zo yasa ya cancad’e kwalliya cikinta shine har da nad’a rawani. Gyaran murya kawai yake yana shaidawa Maigadi “Yanzu zaka ga ko wanene ni? Zaka san
Ka wulak’anta ni saboda ni da mahaifin yaran nan ba mu da wani banbanci.” Hankalin Maigadi ya d’an tashi ga zatonsa duka abinda Hadin ya fad’a da gaske ya ke. Tun da ta yi parking bata fito daga cikin motar ba illa k’urawa mutumin da yake tsaye kusa da mai gadi ido da ta yi. Ba zata mance da shi ba, ba zata manta wannan fuskar ba, fuskar makusancin aminin mutumin da ya kira kansa da sunan mahaifinsu. Ta runtse idanunta ta bud’e tana sake sauke magananta a kan mutumin, wani b’acin rai da tashin hankali yana sake ziyartarta ta tsani duk wani mutum da yake da alak’a da wancan mutumin mai amsa sunan mahaifi a wajensu. A hankali ta cigaba da dukan sitiyarin motar cikin mabayyanin b’acin rai. Ji take tamkar ta fisgi motar da gudu ta je ta take shi ta huta da ganin fuskarsa da take tuna mata da fuskar wancan mutumin.
Tsawon lokaci tana cikin motar ba tare da ta san me ya kamata ta aikata ba. Tabbas ta san idan ta bari ya shiga gidansu yau mahaifiyarta Ammaty ba zata kwana lafiya ba, sai ya tayar mata da tsohon mikin da yake zuciyarta. Dabara ce ta fad’o mata, hakan ya sa ta daddage ta sakarwa Baba Mai gadi wani irin gigitaccen horn, da ba shiri ya saka shi tahowa wajenta a sukane. Da kyar ta sauke glass d’in motar idanunta a rufe ta watsowa Baba mai gadi tambayar “Me wancan mutumin ya ke yi a gidan nan?” Baba Mai gadi da bai san dawar garin ba, cikin in ina ya ce “Wai wajen Hajiya yazo.” Ta ciji leb’enta na k’asa da k’arfin gaske kafin ta murza yatsun hannunta suka bada k’ara k’as-k’as “Ka sanar da shi kafin na irga Biyar ya bar cikin gidan nan idan ba haka ba, ko ma me ya faru da shi ba ruwana.”
Da sauri kuwa Baba Mai gadi ya koma wajensa ya sanar da shi sak’on, sai dai madadin ya tafi wata dariya ya tuntsire da ita cike da tabbatarwa ya ce “Ka koma ka sanar da ita ba inda zan je sai na ga Hajiya.”
Tana daga cikin mota tana kallon yarda yake da hannunsa alamar da gaske yake abinda yake nufi ba ta yi magana ba illa ficewa da ta yi ta isa inda suke cikin tsukakkiyar fuska duk da ba ‘a ganinta kafin ta isa wajen ji take tamkar ta waska masa mari sai dai bayyanarta wajen ya canja mata tunaninta ganin yarda mutumin yake kallonta shek’ek’e kamar ya ga kashi. Ba tare da ta gaisheshi ba ta nuna masa gate cikin dakiyar murya ta ce “Cikin lumana Alhaji ka fita daga gidan nan.”
Cikin izgili ya ce “Idan na k’i fa tabbatacciya wad’anda suka d’ebe kayansu daga gaban ma’aiki, kuna nan cikin daula kun bar ubanku cikin bak’in talauci wallahi ku kiyayi ranar had’uwarku da Allah.” Cikin matuk’ar b’acin rai ta zare nik’ab d’in idanunta fuskarta ta bayyana sosai kamanninta suna nan ba su b’ace masa ba Auta ce. Ya dinga mamakin girmanta da murd’ewar halinta yarinyar da da ko hannu ba zaka saka mata a baki ta ciza ba. Ta sake nuna masa gate “Na had’a ka da Allah ka fita,ko kuma na saka fita ta dole.”
Wata dariya ya saki yana sake gyara zamansa kan kujerar robar da yake zaune a kai. “Fitar da ni ta dole” a zafafe ta juya ta nufi can baya inda Ke jin karnukansu suke na police dogs guda uku manyan gaske, da sauri ta sake su ta nuna musu gate.
TAkAICIN UBA…
Na
Nazeefah Sabo Nashe.
08033748387.
Biya ‘dari biyar kacal don a yi tafiyar Ayra Gaya da ke…
Ko ki biya special people (Mutane na musamman da ake tura musu kai tsaye cikin wayoyinsu. Akan Naira dubu kacal. Ta wannan account ‘din 2118666253 U B A)
Page 5___
Da wani irin wawan haushi suka nufi kansa, in da hakan ya saka shi wani irin rawar d’ari da firgici k’afafunsa suka shiga rawa. Ya nufi bakin gate da sauri da niyyar fita, sai dai tuni suka cim masa, bai san sanda ya saki fitsari a wandonsa yana ihu da tumami. Sai da Ayra taga suna nufin yagalgalarsa sannan ta dakatar da su ta hanyar kad’a musu harshe irin yaren da take musu kenan idan tana so su bar abu. Cak suka tsaya sai dai suna zazzalo harshensu idanunsu a Kansa da yake mutsu-mutsu ya kasa nutsuwa sam ga ni yake kamar kwanansa ya k’are. Rok’on Mai gadi yake da ya bud’e masa gate d’in ya samu ya fece amma Ayra ta k’i bada damar hakan. Cikin takun isa ta k’araso wajen idanunta cikin nasa ta tsaya a gabansa tare da nuna shi da yatsa. “Ina baka shawarar kada ka sake tunkarar gidan nan, idan ba haka ba Wallahi ka sake zuwa sai na basu damar da za su yagalgalaka. Idan ma Shine ya turoka ka d’agawa uwata hankali ka gaya masa ya shirya tafiya kotu ne? Don wallahi sai na makashi a kotu bisa tarin laififfukansa na baya don ba zan bari wani abu ya samar min mahaifiya ba matuk’ar ina raye.” Jikinsa sake b’ari yake yana tattare rigarsa ganin suna son sake nufarsa Ayra ta dakatar da su sannan ta saka Baba Maigadi ya bud’e masa gate d’in kafin kace me Hadi ya arce da gudu kamar mai gudun tsere da gaske karnukan sun firgita shi. Dariya Sosai Ayra ta yi kafin ta mayar da gate d’in ta rufe ta mayar da kallonta kan Baba Mai gadi. “Kada a sake bud’ewa Mutumin nan gate doka ce na saka.” Gyad’a kai Baban ya yi don bai hango wasa a lamarinta ba illa tsananin b’acin rai da ya hango a kan fuskarta. Ya bi bayanta da kallo tana shigewa cikin gidan. Mamaki Baba Mai gadin yake jin cewa wai mahaifinsu yana da rai har ma yana cikin wahala amma sun kasa taimaka masa, ya shiga tunanin wani irin girman laifi mahaifin nasu ya musu da har suka shafe labarinsa a duniyar su. Ya saki nauyayyiyar ajiyar zuciya yana tunanin koma menene Lamarin Mai girma ne.
________________________
Ko da ta shiga Amman tasu tana d’aki hakan ya sa bata damu sosai ba don ta san bata ji duk abinda ke faruwa ba barcin k’ailula take na bayan azahar zuwa la’asar. Zubewa ta yi kan kujera barcin take son yi amma bata son shiga d’aki tunanin da ta saba ya mata rufdugu musamman mutumin nan da yazo ya sake dawo mata da abinda ya wuce take ganin kamar a lokacin abubuwan suke faruwa. Ta runtse ido wani irin zafi take ji k’irjinta yake yi bata san Waye ya nuna masa gidan ba…..
Da sauri ta rarumi wayarta a hasalance ta shiga kiran Dijah Yayarta da take bi, tana zaune a unguwar shara’da. Sai da ta yi ringing sosai kafin Dijahn ta ‘daga. Ayra ta sauke ajiyar zuciya kafin ta gyara zamanta ta ce “Mutumin can da Yake amsa sunan mahaifinmu kin san yau ya turo Mak’ocinsa Hadi Gidan nan?” Da sauri Dijah ta zaro ido kafin ta ce “kan Uban can again? Har yanzu bai hak’ura da nacin mu yafe masa ba kenan tsawon shekara uku idan ban mance ba rabon da ya sake aikowa.” Ayra ta ja ajiyar zuciya kafin ta ce “To yau ya aiko ni kuma na rakaka Hadi da kare a yarda ya tsorata na san kuma ba zai sake waiwayo gidan nan ba.” Dijah ta yi dariya sosai kafin Ta ce “Amma Ayra kin kyauta min, sai dai Kada ki sake ki gayawa Yaya Zainab don kin san har gobe ita burinta mu manta abinda ya wuce mu yafewa Baba..” Ayra ta ja tsaki ta ce “Abinda ba zai tab’a faruwa a rayuwa ba kenan ba yafiya tsakanina da Baba wallahi.” Dijah ta ja ajiyar numfashi ita kanta zuciyarta ta fara cunkushewa da b’acin rai balle Ayra da lamarin Uban nasu ya fi shafarta murya a sanyaye ta ce “Relax Ayra ba wanda zai ce ki yafe masa ba ke ba ko ni babu yafiya tsakanina da wannan mutumin da yake kiran kansa da sunan mahaifinmu.” Ayra tana sakin wata irin ajiyar zuciya ta kashe wayar ha’de da kishingi’da ta runtse idanunta da k’arfi Ko sunan mahaifinta bata son tunawa balle ta jingina shi da sunanta shi yasa a makaranta ma kowa da AYRA GAYA ya santa kai da dama zata iya mayar da sunanta AYRA TALATU. Don shine Sunan ka’dai da ya kamata ta jingina sunanta da shi.. cikin tsananin zuzzurfan tunani wani irin barci mai nauyi ya ‘dauketa.
(Cikin barcin ta yi mafarkin da y’a gigita tunaninta, mafarkin da shine ya zamo somin tab’i na rugujewar duk wani shirinta, mafarkin da kai tsaye zata iya danganta shi da abubuwa da dama a rayuwarta…. Bata son tabbatuwar mafarkin Amma ta San abu ne me wuya bai tabbata ba, dalili ta Saba mafarki su zama zahiri a rayuwa.)
______________
Sai da ya isa bakin titi sannan ya dakata daga gudun fanfalak’in da yake. Bakin wata bishiya ya tsaya yana haki gaba d’aya ya gama tsorata, tsinuwa kuwa Ayra ta sha ta ta fi cikin kwando.
Sai da ya samu nutsuwa sosai sannan ya lura da cewa ko takalma babu a k’afarsa ya ja tsakin takaici yana da tabbacin a can gidan ya bar takalman nasa. Ya shafa kansa hular ma babu sai babbar rigarsa da take rik’e a hannunsa bai ma san sanda ya cireta ba. Ya shiga laluban aljihunsa ya ci sa’a yana da Naira d’ari biyu kacal da ta rage masa hakan ya sa ya shiga neman abin hawa.
Sai dai abin takaici duk wanda ya gan shi k’in tsayawa yake ganin k’afafunsa ko takalmi babu ga wando a yage haka yasa suke masa kallon mahaukaci sabon kamu. Haka ya dinga jan k’afafunsa ya san tabbas sai ya kusan kai magriba kafin ya isa gida. Ba Ayra ba a ranar har aminin nasa sai da ya tsinewa.
________
Ko gidansa bai isa ba ya zarce wajen da suke zama da Alhaji Kabirun duk yammacin duniya. Ya ci sa’a ya tarar abokan zaman nasu ba wanda ya dawo da kasuwa balle su zauna dama su ne ko da rana ka zo zaka same su a wajen dalilin rashin aikin yi.
Alh.Kabirun ma a zaune yake yana tsimayin jiran aminin nasa yana addu’ar Allah yasa a dace a wannan karan idan ya je. Duk abin duniya ya isheshi nadama yake sosai da sosai a cikin ransa. Yana ganin Mal. Hadi gabansa ya fad’i don ko bakomai ya tabbata ba’a yi nasara ba musamman yarda ya ganshi kamar an Jefo shi ba nutsuwa sam a tattare da shi. Zuciyarsa ce ta buga da k’arfin gaske, baya fatan jin mummunan sak’on da Hadi zai ba shi don ya tabbatar ba abin alheri ba ne, ba sai ya fad’a ba ya san hak’ansa bai cimma ruwa ba, ya sani ba su yafe masa ba kamar yarda dama yake hasashen hakan, kafiya da nacin Hadi ne yasa ya ce ya je. Sosai zuciyarsa ta yi nauyi ya sake jingina sosai da jikin bango yana lumshe idanunsa da suka jirkata suka bayyana tsananin tashin hankalin da yake ciki. Hadi ya Galla masa hararar gefen ido da takaicin rashin tamabayarsa duk da ya san baya buk’atar ji ne amma dole ya gaya masa tilas su raba b’acin ran da zuri’arsa ta k’unso masa da shi.
Ya gyara zamansa Fuskarsa a d’aure ya ce “Kabiru ka haifi bala’i, ka haifi yaran da suka d’ebe kayansu daga gaban Annabi. Auta ce fa ta so ganin bayana ba ma yayyanta ba, yarinyar nan har ta yi girman da zata kasa ganin martabata ina ce sanda abin nan ya faru bata da wayon da zata gane komai amma idan ka ga abinda yarinyar nan ta min zaka yi mamaki.” Wani irin duka k’irjinsa yake musamman da ya ji ya ambaci sunan Auta hankalinsa ya matuk’ar tashi ya fi jin shakkar ta fiye da y’an uwanta ya fi jin shakkar had’uwa da ita fiye da ta mahaifiyarta ya san girman laifin da ya aikata mata ya fi na sauran. Cikin takaici Hadi ya ce “Ina tabbatar maka idan ba gidan radio ka shiga ka tabbatar musu da zaka tsine musu ba ba za su yafe maka ba, matsiyata kawai kai yanzu ma baka da amfani a wajensu tunda ko aurensu za’a yi basa nemanka. Da kyar fa na sha ina gaya maka kare suka sakar min, jikina duka fitsari ne.” Duk da abin ya kai a yi dariya hakan bai sa ko murmusawa Alh. Kabiru ya yi ba don shi kad’ai ya san halin da zuciyarsa take ciki, ta masa nauyi sosai sai k’ok’ari yake da numfashinsa amma ya gagara samuwa, tuni idanunsa suka fara k’akkafewa Malam.Hadi bai yi auneba sai ganinsa ya yi ya zube a wajen. Da sauri ya d’aga shi ya hau jijjiga shi sai dai ba alamar numfashi a tare da shi. Mal. Hadi hankalinsa a tashe ya shiga neman taimako kasancewar gidan Alh.Kabirun da y’ar tazara daga inda suke zama. Mutane suka afu a kansa ana neman yarda za’a