Showing 48001 words to 51000 words out of 132090 words

Chapter 17 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt

dama, wannan karan ko ba ya so sai ya sake ki, yana daga cikin dalilin da yasa na k’i amsar scholarship na tafi malaysia saboda bana son na tafi na barku a wahala..” “Na sani Jabiru, ina rok’on Ubangiji Ya maka mafiyin abinda ka min ni da yara na, a yanzu na fi buk’atar ka tafi karatun ko bakomai ba ma zama masu haihuwar guzuma ba, Y’a kwance uwa kwance ka je ka yi karatunka kawai tunda Allah ya baka kwanyar yi.” Jabiru ya girgiza kansa “Ba zan iya ba Yaya Talatu, Har sai na kawar da wannan mutumin daga rayuwarku na kuma sama Miki gwagwgwab’ar sana’a.” Daga haka ya saka kai ya fice da sauri don hayaniyar y’an kawo amaryar ma sake bak’anta masa zuciya suke.

Haka y’an kai amarya suka shige suka fice, Babu Wanda Ya bi ta kan Talatu balle a bata hak’kinta na uwargida a kai amaryar wajenta su gaisa, To ta ina za su girmamata? Bayan mijinta ya k’ask’antata duk Wanda Ya shigo gidan ma zata zai yi Talatun y’ar aiki ce ba matar gida ba. Yarda Ya dank’arawa amarya gini na bulo da sumunti ga fenti da babu mai irinsa a garin sai gidan ‘dan mai gari marigayi babansu Hameedah. Haka gidan ya ‘da’de tsit sai saurarar shigowar ango da tawagarsa.


Da kirari aka rako shi gidan, Ya zubawa Talatu da yaranta harara ganin yarda suke zaune abin su suna cin tuwo miyar kuka, ya saki tsaki ganin yarda abokan nasa suke kallon Talatun da yaranta da kuma bak’in tuwon da suke ci.. shi Talatu zata tonawa asiri? Ai
Kuwa zai yi maganinta. Da yake abokan y’an a bi Yarima a
Sha ki’da ne, su ma halinsu ‘daya ba Wanda ya damu da cimar su Talatun balle sutturun da suke jikinsu Wanda tazararsu da almajirai ka’dan ne duk da wadata irin ta Kabirun.

Yana dashe baki ya burma kai cikin ‘dakin amaryar abokansa suka raka sa Har cikin ‘dakin suna zolayarsa da Alaji ka yi babban kamu fa! Ya sosa k’eya yana fa’din “Kaya iya kaya ba, mhmn harkar ai ta manyan mata ce gaba bum bum baya tum tum.” Suka saka shewa gaba ‘d’aya kaf a kunnen Talatu, ta ‘dan mele baki jira take abokan su tafi a yi wacce za’a yi tsakaninta da Kabiru da duk wani rashin mutuncinsa, saki kam kamar Ya saketa ya gama a daren yau.

Cikin daren ta dinga tsimayin fitowarsa daga ‘daki, saboda bata son ta je b’angaren amaryar inda za’a ga laifinta. Suna shirin kwanciya Allah ya taimaketa ta ji ya fito daga ‘dakin da sauri ta zame Dijah da take jikinta ta fita, Yana shirin saka kai a zaure ta cimmasa cikin dakakkiyar murya ta ce “Ina da magana Kabiru.” Mamaki k’arara a fuskarsa na ambatar sunansa kai tsaye da ta yi gatsal ba risunawa bakomai ya juyo yana dallareta da torch light ‘din da yake haske engine generator da ita “Lallai Talatu wuyanki ya isa yanka, ko ba sunana na ji kin ambata ba, gatsal ba alamar rusinawa.” Madadin ta shiga firgici da ganin b’acin ransa kamar yarda ta Saba a lokutan baya wani k’warin gwiwa ne ya sameta ta sake dallareshi da idanunta kafin ta ce “Ina zaton dai ainahin sunanka kenan Kabiru ba wani na canja maka ba.” Wannan karan fitilar sai da ta kusa zamewa daga hannunsa don al’ajabi. Bai farka daga wancan mafarkin ba ta sake kashe shi da wani. “Magana ta ba ta arziki bace, shi yasa babu dalilin sakaya sunanka, Sakina nake son ka yi kuma a yanzu ba sai anjima ba.” Kabiru ya saki dariya ha’de da fa’din idan na k’i fa? Zan ji duka ne? Rasa kunya.” “Dole ma za ka yi Kabiru, don kuwa na gama zama da kai, don babu amfani a cikin zaman aurenka gwara na yi zaman kaina na San zaman kaina nake, me auren naka yake tsinana min me kake ba ni da zan mararin son zaman gidanka, banda bak’ar izaya da cin mutunci, to komai Ya zo k’arshe na kai iya matsaya saki nake buk’ata.” “Ai kuwa ba za ki same shi ba, tunda har ke ki ke son sakin, ban gama buk’atar aurenki ba, idan lokaci ya yi ba sai kin buk’ata ba zan sake ki, Amma Wallahi yanzu babu mai saka ni na sake ki. Kaf garin Kano ba ma nan k’auyen Gaya ba.” Daga haka ya tada engine zuciyarsa tana jin b’acin ran titsiyen da Talatu ta yi masa, ai kuwa zai shayar da ita mamaki.


Jabiru da kaf yake jin su daga ‘d’akin da yake kwance ya yi k’wafa kafin ya mik’e ya fito a zafafe kamar an Jeho shi, daga sama Kabirun ya ji Jabirun yana cewa “Kawai tunda dai yanzu sakin take so, ai sai ka saketa fisabilillah cuta iya cuta ai ka yi mata, wace izayar kuma kake son mata bayan wannan da take ciki…” Cak Kabirun ya yi yana dallare Jabirun da yake masa magana da tsananin mamaki ya ce “Au ko zuwa ka yi ka saka ni dole na saketa? Na ga alama akwai wani sirri a tsakaninku da ku ke b’oyewa, to ba zan saketa ba har sai na cimma manufata ta aurenta idan ya so idan na saketa sai ka ji da’din Maye gurbina don da alama kai ‘din dadironta ne yarda kake hak’ilo a kanta ba banza ba…” cak Jabiru da Talatun suka yi cikin tashin hankalin jin maganarsa Jabiru a zabure ya ce “Wal’iyazubillahi, an gaya maka kowa ma macece a gabansa kamar yarda kai ka saka lamarin mata a gabanka. Kai ne ba zaka iya rayuwa sai da mace ba, Amma ni ko na rasa matar aure ba zan auri Yaya Talatun da nake mata kallon uwa ba. Kai dai da ka Saba bin matanka ka ji da kanka kada ka sake sakawa da ni. Kuma saki dole ka saketa tunda bata son Auren.” Kabiru ya ciji leb’e ba tare da ya yi magana ba, kawai ya tada engine ya yi gaba amma ya yi alk’awarin maganin Jabiru ko mu da’de ko mu jima sai ya cusawa Jabirun irin bak’in cikin kalamansa da ya cusa masa. Jabiru ya bi shi da harara kafin Ya kalli Talatun da jikinta duk ya Mutu saboda takaicin Kabiru. Bil hak’ki maganar tasa ta girgizata. “Ki share hawayenki Yaya, kada wannan ya ‘daga Miki hankali Amma dai gobe ki je wajen mai gari ki rok’eshi yasa Kabiru ya sahhale Miki auensa kafin takaicinsa ya bugar Miki da zuciya.” Hawayen idon nata kasa ‘daukewa suka yi saboda ta firgita da jin kalaman Kabiru ta tabbata shirun da ya yi yana nufin abubuwa da yawa ta kuma San ya iya sharri ko wane iri ne, sai dai fatan Allah ya kiyaye Jabiru daga sharrinsa, da Jabirun ma zai gane ya tattara Ya bar garin kafin Kabirun Ya k’ulla musu k’ullaliyya.



Kashegari ba ta yi k’asa a gwiwa ba ta nufi wajen Mai gari ta zayyane masa duk rashin mutuncin da Kabirun yake mata, Babu abinda ya canja tun daga zuwa wajen mai gari shekarun baya Har kawo lokacin da take bawa mai garin labari. Hankalin Mai gari ya tashi matuk’a da gaske ya kuma aika ‘dan aike Ya taho masa da Kabiru ko da a kaine. Kabiru yana jin sak’on Mai garin Ya saki murmushi a ransa Ya ce “Talatu kenan, idan kin san wata ai ba ki San wata ba mu je zuwa.” Ya bi bayan ‘d’an Aiken suka tafi wajen Maigarin.

Ran Maigarin a b’ace Ya wankeshi tas ba tare da ya tsaya Ya ji ta bakinsa ba, Kabiru ransa ya b’aci da tijarar da Talatu ta janyo masa a wajen Mai garin, sai dai bai ce komai ba ya bada hak’uri ha’de da yin nadama kamar yarda ya aikata a wancan zaman nasu na farko. An kai ruwa rana kafin mai gari ya yarda ya amshi tayin hak’urinsa sai da ya saka shi Ya bawa Talatu hak’uri ha’de da tabbatar masa dole ne ya ‘d’auke duk wani nauyi na Talatu da yaranta, kuma wajensa zai dinga kawo komai duk k’arshen wata. Kabiru ya amsa ba tare da ja in ja ba. Tun a wajen Mai gari ya ciri ku’din da aka yanka masa ya dank’awa Talatu da yake zuba mata harara ta k’asan ido ba tare da kowa ya sani ba. Talatu ta amshi ku’din tana zubawa Mai gari godiya “Bakomai Talatu, ki je kuma duk abinda ya sake miki ki zo ki gaya min, ni ba azzalumin shugaba bane kuma ba zan yarda wani ya zalunci wani a yankinaba matuk’ar ni ne shugaba a wannan garin.” Kabiru dai hak’uri yake bayarwa kawai “Kuma ka tabbatar itama ka gyara mata mahallinta kamar na waccan matar da ka ajiye, da da wuri ma na samu labari ba zan bari ita matar taka ta tare ba sai dai Talatun ta tare ko baka so. Na gaya maka umarni ne na baka ba shawara ba.” Kabiru dai hak’uri ya sake bayarwa yana k’ok’arin danne fushinsa kada abinda ya b’oye Ya fallasu, Amma shi ka’dai ya san abinda yake zuciyarsa na daga tanadin rashin arzikin da zai yiwa Talatu da ma Jabirun da ya zugata. Ya ci alwashin sai Mai gari ya yi tur da su sai kuma yasa a koresu daga garin gaba ‘d’aya.



Abin mamaki ko a fuska bai nunawa Talatu b’acin ransa ba, ya dai raya a zuciyarsa aurensa da Talatun ya zo k’arshe.



A lokacin da yake hidimar shirin aikata tuggunsa a lokacin Allah ya k’addara shigar cikin Ayra. Tsawon shekaru biyu cur bai yi kwanciyar aure da Talatun ba, tun bayan wancan lamari da ya faru, kwatsam wani dare ya je ya Sha kalar maganin da ya tab’a sha a kwanaki saboda yana son koyawa yarinyar da ya aura hankali musamman rashin kunyar da take masa a kan yarda yake gallazawa Talatu, Sau tari tana bawa yaran Talatu abubuwa a b’oye su k’wai madara da bread, da suke karyawa da su, wani lokacin Har da ragowar nama, don haka kawai sai Allah ya kintsawa amarya son Talatun da jin tausayin halin da take ciki. Ya sha kamata idan ya ce ta daina sai ta yi masa rashin kunya ta ce ba zata daina ba. Yana gayawa Hadi sai Hadi ya zuga shi da cewa ba mamaki Amaryar ta raina k’ok’arin sa a gado ne shi yasa ba ta masa biyayya, duk da Kabiru ya ji shakkun hakan don ya san raki irin na Suwaiba sau tari guduwa take ta bar shi idan ta ji wahala, sai ya kasa k’aryata Hadin, Hadin ya kawo masa maganin maza mai k’arfin gaske.

Cikin Dare Amarya da taga tashin hankali kwatankwacin Wanda Talatu ta gani a wancan daren, sai ta bawa wandonta iska ta fice a guje sai gidan iyayenta don ta lura sosai Kabiru ya fi k’arfinta ba zata iya da shi ba. Hankalin Kabiru a tashe ya zura jallabiya ya isa ‘dakin Talatun, cikin barci Talatu ta ji yana jan hannunta yana fa’din “Ke Talatu tashi ki bani hak’kina.” Talatu ta Ware idonta jin zancen banbarakwai “Ki tashi Malama, idan kuma kin k’i wallahi sakin ki zan yi, kuma ba za ki tafi min da yaro ko ‘d’aya ba.” Tilas Talatu ta bi shi ‘dakin amarya in da ta ga ya nufa, a tsorace take kallonsa “Ina matar gidan?” “Ba wannan na tambayekiba gyara kawai Malama.” Shikkenan ya afka mata.

Sai da komai ya nutsa, Ya yi tsaki yana zuba mata ido. “Ke wai Talatu ba za ki je ki nemi maganin da zai mayar da ke mace ba ko? Kina zaune mace ba ‘dan’dano ba komai abu kamar k’ofar gari, wallahi dole ma na rabu da ke don ba zai yiwu na dinga ciyar da ke a banza ba, dole ma na San hanyar da zan bi na rabu da ke ba tare da kowa ya ga laifina ba.” Talatu ta saki nurmushin takaici kafin ta ce “Ka ba ni ku’din ka ga ban je bane?” Ya saki tsaki yana fa’din “Tashi don Allah ki tafi wajen yaranki, ai ke kin tashi daga aiki ba wani garanbawul da za ki yiwa kanki.”


An kai ruwa rana kafin amarya ta dawo, da zummar a ja masa komai ya daina shan abubuwan da za su k’ara masa k’arfi don ba zata jura ba. Kabiru murmushi kawai ya yi don itama tabbas rabuwa zai yi da ita Karima ce mai iya ‘d’aukan lalurarsa to itama ta ‘d’an fara sanyi dalilin ciwon bayan da sakota a gaba.



Wata ‘daya da faruwar wannan abin abubuwan marasa da’di suka faru, domin dai kamar yarda Kabirun ya ci alwashin ramuwar gayya hakan ce ta wakana da taimakon Hadi da ya sake ba shi gurguwar shawara “Wallahi hakan kawai za ka yi ka rabu da ita salin alin, kuma Har yaran ka ce baka so, tunda ba ka tabbatar da zamantowarsu naka ba.” Kabiru ya ji da’din ba shi k’warin gwiwa da Hadi ya yi don da gaske yana jin haushin ciyar da Talatun da yaranta da yake yi. Don haka suka shirya mai fishshesu.


Ranar da abin ya faru sai da ya daidaici amarya ta tafi gidansu kwana sannan ya fakaici idon Jabiru da Ya dawo daga wajen abokansa zaman hira ya shigo da ‘y’ar wak’arsa a bakinsa kawai sai Kabiru da Hadin suka shak’eshi a zauren gidan suka saka masa yanki a hanci take ya sandare musu, Hadi ne ha rik’eshi shi kuma Kabiru ya je ya shak’awa Talatu a fuska dama barci take sai ta cigaba da nauyayyan barcinta, ya Zare yaranta Ya mayar da su ‘dakin da Jabiru yake kwana ita kuma ya zare mata Riga suka zo suka ‘dora Hadin a jikinta bayan Sun cire masa tasa rigar daga haka suka fice suna dariyar cimma burinsu Kabiru ya tafa da Hadin ha’de da cewa Shikkenan na huta da k’aya haba ka yi ta wahala da mace a iska sai a bi wani yariman a sha ki’da…


Waje suka fita suna ihu ha’de da kiran mak’ota “Ku zo ku zama shaida Innalillahi kwarto a gidana a kan shimfi’dar mata ta suna nan haihuwar turmi da tab’arya……..” Kabiru ya fa’da a wata majalisa da ba su tashi ba, cikin kuka da gigitar tashin hankali kamar gaske………



(CAB, Kai Kabiru ta nan kuma ka b’ullo tashin hankali dole yaranka su k’i yafe maka, Anya Kabiru za ka gama da duniya lafiya, to ko wannan ne laifin da Ayra ta rik’e ko kuma akwai wani gagarumin laifin a gaba? Mhmnn Tabbas yara ko daga haka aka tsaya kun ga Takaicin Uba….. sai dai fa akwai wata a gaba ku dai ku cigaba da saurare don jin wata sabuwar k’addarar da ta afku tsakanin Ayra Gaya da Babanta…🤔 a yi hak’uri gobe ba na typing sai sunday In sha Allah, nagode da jumirin karatu. Love you all.”
Takaicin Uba…..

Nazeefah Nashe.

25

💔💔💔💔

*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*NA GWADA NA GA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWAR ZAKI YI AMFANI DA ITA SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL, AKWAI RABI TA, YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*..
________


Mutanen Majalisar ba su gama yarda da abubuwan da Kabirun yake fa’di ba, saboda shiga ru’dani da tashin hankali, abu ne da za su kira shi sabon abu don hakan bata tab’a kasancewa a garin su ba, garin da suke girmamashi suke kuma ganinsa a gari mafi k’ololuwar daraja. Ganin ba su yarda ‘din ba, Ya sa Kabiru k’ara sakar musu kuka “Na san za ku yi mamaki, Amma ina son ku zo idanuwanku su nuna muku abinda na fa’da ‘din da gaske nake ba kuskure sharri ko k’age a cikinsa.” Firgitgit kamar an tsikaresu suka mik’e don zuwa su tabbatar da abinda ya fa’da musu, idan kuwa ta tabbata tabbas sai sun ‘dau hukunci irin na Shari’a akan Matar Kabiru da kwarton da aka kamata da shi, ba za su yarda ba, ba za su amince su bar yankinsu kara zube ba, a dinga aikata duk ba’dalar da aka so dole su ‘dau mataki irin Wanda addinin musulunci ya tanadar.


Zuwansu tsakar gidan ya saka Kabiru saurin shammatarsu ya kamfato ruwa a bokiti don ba ya son su San ba sa hankalinsu balle a ‘d’ago shi. Yana shiga ‘dakin kafin su Farga ya shek’a musu ruwa a fuskarsu, tuni suka kawo doguwar ajiyar zuciya da yake maganin k’arfinsa bai kai har yarda za su ‘dau tsawon lokaci suna barci ba. Da sauri mutanen wajen suka fara jan salati da salallami suna ficewa daga ‘dakin cikin tashin hankali.

Sai a lokacin Jabiru da Talatu suka farga da halin da suke ciki, Jabiru ya runtse idanunsa da yake jin sun masa nauyi, zuciyarsa kamar ta fito don tsananin harbawar da take, Shikkenan Kabiru yaci riba a kansa ya nuna masa ya fi shi sanin duniya kamar yarda ya sha jan kunnensa, Ya zai yi dole ya amsa laifinsa, laifin da baya tunanin ko giyar wake ya sha zai iya aikata shi da wanin Talatu ma da ta masa rik’on ‘da balle ita Talatun da kanta. Tabbas Kabiru ya cucesu musamman Talatun da abin sai ya fi tab’a mutunci da k’imarta ba mamaki ya shafi har zuri’arta. Hawaye ne Ya ji yana zubo masa, hawayen da Kabirun Ya da’de yana son ganinsu a idanunsa yau ga shi suna zuba kamar famfo.

Talatu kuwa tsabar bak’in ciki tun bayan da ta Ankara da halin da take ciki ta ji zuciyarta kamar an danneta da bulo, numfashinta ma da k’yar yake fita sai ta fisge shi da k’arfi, Bata tab’a sanin Kabiru ya mata tsana Har irin haka ba, da za ta kai ya b’ata mata sunan ta ya b’ata mata sunan zuri’arta ya shafa mata bak’in fenti Mara gogewa. Me ta yiwa Kabiru ne? Me ta yi masa har haka da ta cancanci wannan bak’ar cutarwa daga garesa. Ashe bata cancanta Ya gode mata ba, bisa ‘dawainiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login