Showing 54001 words to 57000 words out of 132090 words
Chapter 19 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt
tausayawa irin wannan ba, don haka dole su masa tawaye. Kabiru kuwa hankali tashe yake duban Maigari jin abinda ya ce wai dole shi zai rik’e yaransa ya ciji leb’ensa yana sakin tsaki k’asa-k’asa shi da baya son wahala don me za’a jingina masa ta y’ay’a ya zama dole ya yi abinda zai girgiza zuk’atan kowa a daren yau, ko don gujewa rik’on yaran da baya farinciki da wanzuwarsu a duniya da sunan ahalinsa.
Talatu kuwa zuciyarta ce take dukan tara-tara Sam wannan hukuncin na Uban gari bai mata ba, ya k’yaleta kawai su yi tafiyarta ita da yaranta don bata son cigaba da zama a Shagogo garin da kai tsaya ba zata k’arar da arzikin da ta samu a cikin sa ba, banda arzikin haihuwar yaranta, ta Yaya ma Mai gari zai ce zai rabata da yaranta? Bayan su ne farin cikinta, su ne danginta uwa uba don su ka’dai take zaune take dake zuciyarta take rayuwa banda haka da tuni wani labarin ake ba wannan ba, sai dai ya zama dole ta yiwa Maigari biyayya a k’ok’arin sa na kare mata mutunci da ya yi bai cancanci butulci a wajenta ba, don haka ta yi gum da bakinta tana sauraran bugun zuciyarta da take jin kamar zata wuntsilo. Mai gari ya bata umarnin ta je ta kwaso kayanta ta kawo gidansa ta kuma dank’awa Kabiru yaransa. Yana jiranta a safiyar gobe ta dawo gidansa.
Tana wucewa ana binta da maganganu k’asa-k’asa maganganu masu ciwo masu suka nauyin zuk’ata. Ta dake ta share ta dinga amabatar Allah a zuciyarta.
Har dare Kabiru yana ‘dakinsa na sashen amaryarsa yana k’ulla mai fishsheshi. Kafin ya amince da shawarar da zuciyarsa ta ba shi “Guduwa zan yi na bar garin, idan ya so sai naga uban da zai ‘dora min wahalar y’ay’a, itama wannan shak’iyiyar yarinyar sakinta zan yi in je in samu mai zak’in mu gudu Lagos abin mu, kafin na mana cuku-cuku mu haura k’asar Dubai.” Ya saki shewa shikkenan fak’at ba ni da wata matsala……
Jikar Nashe✍🏽
Takaicin Uba…
Nazeefah Nashe✍🏽
27.
💔💔💔💔
*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*NA GWADA NA GA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWAR ZAKI YI AMFANI DA ITA SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL, AKWAI RABI TA, YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*..
Hankalin Kabiru ya kwanta da shawarar da zuciyarsa ta ba shi. Don haka cikin daren ya saki amaryarsa ta hanyar rubuta mata takarda ya ajiye a kan gadon ‘d’akin inda idan ta dawo zata gani.
Babu tausayi ba tsoron Allah, ya gama kammale kayansa tsaf. Asubar Fari ya shige cikin motarsa mai k’irar Carina Toyota tun samfurin ta mutanen da. Ya jata da sauri ya bar garin yana tunanin har abada ya rabu da alak’ak’ai Talatu da shirgin y’ay’anta mata.
Ko da safe Talatu da ta game ha’de shirginta tsaf na tafiya gidan Maigari, hankalinta bai kwanta da barin yaranta ba, don haka sam zuciyarta ba sukuni ta dinga jawa Kabiru Allah ya isa a cikin ranta da ya zama silar rabuwar farin cikin su, ina yaranta za su tsoma kansu bayan babu Abba Jabiru babu ita kanta Uwarsu da ta tabbatar dai su biyun dai sune majinginar y’ay’anta a rayuwa.
Su kansu yaran ba sukuni a cikin ransu, zuwa yanzu sun tabbatar da abinda suke zargi rabuwa da mahaifiyarsu bayan Abba Jabiru shima ya tafi. Majeeda da Zainab kuka kawai suke na tashin hankali, Talatu tana bin su da kallo rashin sanin abinda Zata ce musu ya sa ta ja bakinta ta tsuke tana jin tafasar da zuciyarta take mata.
Suna zaune jugum a tsakargida Amaryar Kabiru ta yi sallama ta shigo gidan, dawowarta daga bikin da suka je a birnin kano kenan, ta riski wannan bak’in labarin da ta ji shi kamar saukar aradu, da gaske lamarin ya girgizata duk da ta san ko mafarki take ba za’a ce mata Talatu ta aikata hakan ba ta yarda, a ‘dan zaman da ta yi da Talatun ta tabbatar da nagartuwar halayenta da sahihancin sauk’in kanta ba zata tab’a amincewa Talatun zata aikata haka ba, ta san sharri ne irin Kabiru da ya riga ya kafawa Talatun karan tsana. Shi yasa tun daga wajen da aka gaya mata take sharar k’walla tana jin tausayin Talatun ya game zuciyarta da sassan jikinta. Yanzu ma ‘dora idanunta a kansu kenan ta ji zuciyatta ta tsinke murya a raunane da alamun kuka ta ce “Allah ya saka miki Talatu, tabbas Kabiru ya cika azzalimi nima kuma tabbas zama na da shi ya k’are don ance idan kaga gemun ‘dan uwanka ya kama da wuta ka shafawa naka ruwa, zai iya yi min abinda ya miki.” Talatu ta ‘dago da raunannun idanunta ta zube su akan Amarya. Kuka ne yake son zubo mata amma tana k’ok’arin danne su da k’arfin tsiya ta girgiza kai “Kada kice haka, ke dai nake murna zaki rik’e min y’ay’ana na san ba zaki tab’a cutar da su ba, kamar yarda zuciyata take gasgata min kina da jajurtacciyar zuciyar da zaki kula min da su.” Shiru amarya ta yi tana goge hawayenta tabbas zata iya cigaba da zama da Kabiru ko don ta rungumi y’ay’an Talatu da take jin su kamar nata y’ay’an, ba wai Zata zauna bane don Kabiru. Tsawon lokaci suna zaune Jugum, Talatu so take ta zare jiki ta fice ta bar yaran sai dai zuciyarta na mata wani irin nauyi idan ta tuna ko raba makwanci ba su tab’a yi da yaranta ba lokaci guda ace za’a raba su tabbas za su sha wahala.
Jikin Amarya a salub’e ta mik’e ta shige ‘d’aki anan idanunta suka sauka kan takardar da Kabiru ya ajiye mata a kan gado, da sauri ta zura hannu ta ‘dauka da yake ta yi karatu har makarantar k’aramar secondary don haka bata sha wahalar karantawa ba. Tsaf ta gama karance takardar sakin nata da ya yi mata har uku, madadin b’acin rai murmushi ta saki tana furta “Hakan ya fiye min, ita kanta Talatu tafiyar taka na san ta fiye mata sau dubu ko bakomai dole a bar mata yaranta da gidan ma gaba ‘d’aya, mugu azzalimi In sha Allah sai Allah ya saka mata.”
Daga haka ta fito rik’e da takardar a hannu tana murmushi ta ce “D’an akuyan
Mijin naki nima ya sakeni saki uku, don haka ba mai rabaki da yaranki ki cigaba da zama a gidan nan kina kula da su. Allah ya tayaki Talatu.” Farin ciki ne sosai ya dirga a zuciyarta, tabbas ta ji da’din jin hakan ta dinga furta Alhamdulillah cikin tarin annashuwa da farin ciki. Ta godewa Allah da hakan ya faru ta tabbata Maigari zai ce ta yi zamanta gidan Kabirun.
Ai kuwa Kamar ha’din baki Maigari yana jin labarin guduwar Kabirun ya saki murmushi kawai, ya tabbatar Kabirun ‘dan iska ne ajin farko a shai’danun mutane, ya san tabbas sai ya yi nadamar wannan abinda ya yi ko mu da’de ko mu jima. Da kansa ya yi umarnin Talatun ta cigaba da zama a gidan mijinta ta tarbiyyar da y’ay’anta wata rana zata yi alfahari da hakan.
Maganganu iri-iri suka dinga yawo a gari, akan saboda me menene hujjar da Maigari ya zab’a kyautatawa Talatu fiye da musguna mata alhali bata cancanci irin wanann abubuwan da Maigarin yake yi ba, sai zance ya fara zagaya gari a
Kan tabbas akwai abinda Maigari yake nufi da Talatun ko kuma shima kwarton tane shi yasa ya kasa ya tsare a cikin lamuranta. Bai kulasu ba duk da zantukan sun zo kunnuwansa ya ha’diye ya shanye duk wani b’acin rai da ya dinga hank’oro a zuciyarsa tunda dai shi ya san don Allah yake yi to zai cigaba da yi don Allahn yana kuma rok’on Allah ya ganar da jama’ar garinsa.
Hankalin mahaifiyar Kabiru ya tashi sosai, ta dinga jin tsanar Talatu tana sake hauhawa a zuciyarta, ta kuma yi alk’awarin tilas sai tayi sanadin da Talatun zata bar Shagogo ko da zata yi yawo tsirara, ta Yaya Mai gari zai ‘dau gida guda ya damk’a mata gida mai ginin bulo da siminti, ita kuma shine bak’in cikinta har hakan yake neman ya kassara mata zuciya wani zubin har kasa runtsawa take.
___________
Watannin da Suka biyo baya wasu irin watanni ne da Talatu ba zata mance wanzuwarsu a rayuwarta ba, saboda bak’in cikin da ta ‘dan’dana mai zafin gaske, mutane Shagogo sun tsaneta tsana mafi muni, ko me ta kasa ba’a siya akan cewa ba za su siyi kayan fasik’a ba, hakan yasa rayuwa ta sake musu tsanani ta kai ta kawo wani zubin abincin da za su ci ma gagararsu yake, sau tari Maigari ne yake mata aike a b’oye na hatsin da za su ‘dan kwana biyu suna ci, ture ta maganar hatsi idan an sameshi masarrafinsa fa? Da me zata sarrafashi su ci abinci, tunda bata da ku’din mai da na kayan ‘dan d’ano, sau tari haka suke k’amusar abincin da zallar yaji ko mai babu. Tabbas Talatu ta ga tashin hankali a wannan lokacin tashin hankalin da ko mak’iyinta bata fata ya kasance a cikin sa, rayuwa ta juya musu baya suka zama kamar almajirai har Talatu ta gwammaci barin Shagogo fiye da zaman cikinsa, amma idan ta bar Shagogo Ina zata da yara mata har hu’du, ta runtse idanunta bata son ta zama silar da yaranta za su zama karuwai, dole ne ta zauna a Shagogo tunda bata da inda ya fi nan.
________Ana Wata Ga Wata___
Murnar Talatu da take yi na gama idda ba tare da Kabiru ya sake zuwa ya mayar da ita ba, sai ya koma ciki sakamakon wayar gari da aka yi ta fara jin motsi a cikinta, motsin da ta tabbatar ciki ne, musamman yarda motsin yake sake k’arfi kamar zai fasa cikin ya fito duniya. Sanda ta fara ji gabanta ne ya shiga fa’duwa take a wajen ta fara fa’din Innalillahi Ni Talatu Naga Ta kaina! Ciki Kuma? Tabbas ta ga ta kanta tunda dai ta tabbata a sharri da makirci irin na Kabiru ba zai amshi cikin nan ba, musamman idan ta haifi mace zai iya cewa ba cikinsa bane, tunda a sanda abin ya faru da kusantar da ya yi mata bai fi sati guda ba… ta runtse idanunta tana addu’a a ranta Ya Allah ka fitar da ni daga sharri da makircin har da Tuggun Kabiru…. Wasu hawaye masu zafi suka dinga kwararo mata, sam ba ta yi farin ciki da samuwar cikin ba, kuma ba ta jin zata iya zubar da shi.
A hankali cikin ya fara girma har ya bayyana kowa ya fara ganinsa, a lokacin ne hankalin jama’ar gari ya fara dawowa kanta, aka fara yama’di’di da zancen tun ana yinsa a b’oye har aka samu tsagerun da Suka zo har gida suka tsare Talatu cikin gatsali suka ce mata “Amma Talatu kin san ba zaki haifa mana cikin shege a garin nan ba ko? Tunda ba’a tab’a yi ba ba kuma zamu fara ta kanki ba, ba zaki haifa mana abinda zai ‘debe mana albarkar gari ba, don haka mun baki kwana biyu ki tattara dake da yaranki Ki bar garin nan, kuma a wannan karan ba Maigari ba ko waye bai isa ya ce za mu cigaba da zama da ke ba, Fasik’a Mazinaciya…” Wani irin duhu Talatu ta fara gani a idanunta sauran maganganun da suka biyo baya duk bata fahimce me suke cewa ba, ta dafe kanta da hannu biyu saboda yarda yake sara mata kamar zai rabe biyu, YA ALLAH MAFITA…” ta furta a hankali cikin wata murya mai karya zuciya ji kake yif ta sume a wajen……
Jikar Nashe✍🏽
Takaicin Uba.
Nazeefah Nashe✍🏽
28.
💔💔💔💔
Sai da suka ga ta suma sannan hankalinsu ya tashi, ba don komai ba sai don rashin sanin abinda za su cewa Maigari idan ya tambayesu yarda aka yi Talatun ta suma alhali ya garga’de su akan lamarin Talatun. Tunanin zuba mata ruwa ne ya kawo musu a kai, don haka ‘d’aya daga cikinsu ta kandamo ruwa a rijiya ta shek’awa Talatun, ai kuwa sun samu ta kawo wani dogon numfashi alamar ta farka daga suman, ta dinga bin su da ido tana jin k’ullin zuciyarta yana k’ara kananna’dewa Sharrin ya mata zafi ya kuma mata ciwo sosai fiye da nusgunawar Kabiru. Cikinta za’a sheganta mata? Cikin da ta tabbatar Kabiru ne ubansa amma mutane suna son su Sheganta mata shi? Wace irin Masifa ce wannan? Ina ma zata ga dangin Mahaifiyarta ta gudu can wajensu ta huta da wannan gararanbar da take yi a rayuwa. Kukan ma ya k’i zuwa, sai bin matan da suka cika mata gida da kallo take, tana nazarin fuskokinsu masu bayyana zahirin abinda yake zuk’atansu, da gaske Talatu ta hango tsagwaron tsanarta a idanunsu, ta lumshe ido bata ga laifinsu ba, Kabiru ne ya bada k’ofar da za su kafa mata zargi tunda shi ya mata sharrin Tarayya da Jabiru. Runtse idanunta ta yi tana sauraran furucin Matan mara da’din Ji da suke ta sakinsa a kanta. Tsawon lokaci suna abu ‘d’aya kafin su shige su tafi suna sake jaddada mata ta nemi Mafita ita da yaranta don ba za su tab’a amince mata ta zauna a garin su ba. Murmushi ta saki kawai Murmushin da yake bayyana tsananin wutar b’acin rai da take huruwa a zuciyarta, Dole na tattara na bar garin nan kafin bak’in cikin Kabiru da mazauna cikinsa ya kashe ni. Hakan ta bari a ranta, za ta yi nisa da Shagogo ta manta da labarinsa tsaf ko da hakan yana nufin komai ma a rayuwarta idan ta ce komai tana nufin komai ciki har da Mutuwa saboda wahala duk ta aminta a kan zamanta a Shagogo garin da ba zata k’arar da zaman jin da’di a cikin sa ba, sai bak’ar wahala da masifu iri-iri daga wannan sai wannan.
Tsit gidan ya yi, bayan ficewar da mutane suka yi suka bar gidan. Ta mayar da Kallonta kan yaranta mata guda hu’du da suke zaune a can gefe cikin matuk’ar tashin hankali, zuciyarta a wannan karan kasa jurewa ta yi har sai da ta zubar da k’wallar da tun ‘d’azu take kokawa da su a kan zubowarsu. Ta bu’dewa yaran nata hannu alamar su iso gareta, ai kuwa kamar jira suke suka rugo gaba ‘d’aya suka shige jikinta suna sakin nasu kukan mai matuk’ar gigita hankali. Tsawon lokaci suna kukan kafin ta bi su ‘d’aya bayan ‘d’aya ta share musu hawaye tana fa’din “To ya isa, In sha Allah ba sauran kuka yau yau za mu bar wannan garin da kullum ba abinda mu ke fuskanta a cikinsa sai bak’ar wahala. Ku tashi Majeeda ku ha’de mana y’an sauran kayan mu da suka rage masu ‘dan kyau, gwara mu je birni ko aikatau na rarrabaku a gidan mutane ni ma na samu wani gidan na dinga musu aikatau idan ya so idan muka tara abinda muka tara sai mu samu jari mu kama ko gidan haya ne.” Sosai Majeeda da Zainab suka ji da’din wannan shawarar ta ta suka kuma amince gwara kam gwara su je su yi aikatau ‘din da wannan zaman rashin madafar da suke tunda nan ‘din ko kayan sana’a suka kafa ba mai siye sai ace wai Uwarsu mazinaciya ce.
A daren ranar da suka gama kimtsa kayan su, da niyyar kashegari za su bar garin, a daren Kabiru ya sauka ya zo daga lagos afujajan da shi, kamar wanda aka cillo ya fa’da gidan Talatun. Wata irin fa’duwar gaba ce ta riski Talatun sanda ta yi arba da shi, ranta a b’ace ta dinga kallonsa, duk da wannan karan ta shirya masa ba wanda zai saka ta zauna da aurensa. Ya zauna dab’as a tsakar gida yana ‘dan kallon Talatun k’asa-k’asa ha’de da jin b’acin ran ganinta da ciki, sai kuma ya saki murmushi yana dubanta “Talatu kenan, kika wani zuba ido kina kallona ba aurenki na zo mayarwa ba, Wannan gidan nawa na zo siyarwa, saboda na je na fito da wasu kayana da Jami’ai suka rik’e min, Sai ga Shi Alhamdulillah na zo a kan gab’a don na ji labarin mutanen garin nan sun miki kashedi a kan bar musu gari sakamakon cikin shegen da kika yi.” Ya tuntsire da dariya “Kin ga cikin sauk’i sai ki wuce ki bar min gida na na siyar da shi na k’ara gaba, abin da’di har y’ay’an ma na bar miki su halak malak har duniya ta na’de bare wannan cikin da duniya ta shaida ba nawa bane, har abada ki barshi a sunan shege don ba zan amsheshi matsayin jinina ba, abu na gaba ki rik’e a ranki duk inda zaki je da igiyar aurena guda ‘daya a
Kanki don Malamina ya tabbatar min idan na sake ki ni da arziki har abada don haka tun bayan tafiyata na isa wajensa ina jin abinda ya ce kuma a take a wajen na mayar da igiyar aurena dake kan ki don haka duk inda za ki shiga kina nan a matar Kabiru ba shegen da zai aure ki, yara dai na bar miki da wannan cikin da Duk garin Shagogo sun shaida Shegantakarsa….. ya tuntsire da dariya……………”
Tsit Talatu ta yi da bada labarin sakamakon wata irin gigitarciyar k’ara da Ayra ta saki a daidai k’ofar ‘dakin. Daga ita har Hameeda suka k’arasa bakin k’ofar da sauri don sanin me ya faru. Cikin fa’duwar gaba Amma ta kai kallonta kan Ayra da ke zube kamar gawa idanunta a kakkafe ba alamar numfashi a tattare da ita. Talatu a gigice ta ratsa sauran jama’ar ta yi kan Ayra tana fa’din “Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna! Na shiga Uku Hameeda! Na kashe y’ata da kaina, sam Ayra bata san duk wannan labarin ba, ban tab’a bata ba, sabida yarda zuciyarta ta taso da tsanar mahaifinta sakamakon Tata k’addarar da ta faru tsakaninsu k’addarar da ta haddasa mata tsanar aure, na tabbata tunda ta yi wannan zubewar ta