Showing 57001 words to 60000 words out of 132090 words

Chapter 20 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt

ji duk labarin da nake baki daga farko har k’arshe.” Hameeda ma jikinta rawa yake ta hau bubbuga Ayran sai dai kamar tana buga Dutse, don Ayran bata da alamar ta san me take yi, hankalinta tashe ta kalli Talatu tana fa’din “Dama ta tab’a irin haka?” Talatu tana hawaye sosai ta girgiza kai tana fa’din “Tana suma dai, amma bata tab’a sandarewa irin wannan ba.” “Kamata mu kaita asibiti.” Hameeda ta fa’da da sauri tana k’ok’arin ‘daga Ayran da su Dijah suka zagaye suna kuka gani suke shikkenan Ayran ta mutu ta bar su, tunda ta sha fa’da Insha Allah idan suka nufi yi mata aure kafin su sadata da gidan miji zata mutu kowa ya huta.


A guje Hameeda take jan motar, cikin wani irin mugun speed, sam ta manta a Nigeria take ba a k’asar su Lebanon ba, burinta ceton rayuwar surukartata da take jin sake son aurensu da Turaki tun bayan da ta ji wani sashe na labarinsu duk da bata gama ji ba, amma yanzu ta ‘dora ‘danbar son aurensu, za kuma ta yi yak’i da duk wanda ya bayyana k’iyayyarsa ga auren cikin kuwa har da mijinta ko da hakan yana nufin abubuwa da dama..

Mintuna k’alilan ne suka sada su da asibitin Nasarawa in da anan Babban likitan da yake ganin Ayran yake.



A tsorace yake kallon Ayran da take kamar gawa a shimfi’de a sandare, hankalinsa tashe ya shiga k’ok’arin ceto lafiyar ta sai dai hakan ya gagara dole ne sai ya gayyato wasu daga cikin manyan likitoci daga asibitin Aminu Kano saboda ya yi iya yinsa amma Ayran bata farka ba. Don haka ya ‘dan saka mata drip da wasu allurai ya fice da sauri ba tare da ya saurari su Amma da suka taso da saurin suma don son sanin ko Ayran ta farka. Sai dai ba su ci sa’ar cimma sa ba don a hanzarce yake tafiyar kamar zai tashi sama.



Tsawon awoyi biyar likitocin biyar suka ‘dauka kafin su samu Ayra ta kawo wata doguwar ajiyar zuciya, ta sake runtse idonta tana fata ta bu’de idon ta ganta a cikin Kabari bata son a ce tana raye a wannan duniyar mai cike da ru’dani, tsawon mintuna biyar idanunta a runtse tana fatan y’an maganganun da take ji a cikin ‘d’akin k’asa k’asa na likitoci ya zama maganar Mala’iku ce, da ta yi murna da farin ciki ta kuma godewa Allah da ya ‘d’auke ranta a wannan duniyar da ba abinda ta tsinta sai ba’cin rai, ashe bayan wancan gagarumin laifin da Kabiru ya mata akwai wani laifin na Sheganta ta da yasa Mutanen Shagogo suka yi. Anya kuwa a duniya akwai yaran da ba su yi sa’ar mahaifi ba kamar ita da y’an uwanta har abada ba zata yafewa Kabiru ba, kuma tana jiransa ya zo lahira a yi shari’a a tunanin Ayra fa Duk wannan zantukan da take yi a cikin Kabari take, murna take ta mutu ta huta ba za’a mata auren da bata so ba.


“Dagota.” Ta jiyo muryar Likitan da take zaton Mala’ika ne, don haka ta ‘dan kanne ido da son ganin Mala’iku da wata suffa suka zo mata, tunda ta san ance idan ka yi aiki Mai kyau suna zuwa maka a kyakykyawar suffa, idan ka yi Mummuna su zo maka a mummunar Kama.

Tsaf murnarta ta koma ciki, ganin likitan da sirinji a hannunsa ya na shirin yi mata allura, bata tantama asibiti ne, abinda yake nuna a zahire har a lokacin tana raye kenan, me yasa bata mutu duk da burinta na son Mutuwa kawai sai ta samu bakinta yana furta “Ya Allah na fi buk’atar zuwa wajenka a kan zama cikin duniyar nan, don haka kada ku sake ku min allurar nan, da za ku burge nima da nace muku na fi son ku min allurar da zata zama ajalina…” Cak likitocin suka tsaya da aikinsu cikin tausayawa suka zuba mata ido..
Ya Ilahi me ya samu yarinyar nan ne?



Jikar Nashe✍🏽
Takaicin Uba….

Nazeefah Nashe✍🏽


29.


💔💔💔💔

*SHIN KINA DA KANNEN DA ZA'A AURAR, KO KUWA KE CE KIKE SON GYARA KANKI?*
*GUDUYO NA TALLATA MUKU INGANTATUN SAIWOWIN MUTANAN CHADI DA AKE DAHUWAR GIMBIYAR KAZAR AMARE DA WADDA TAKE SON GYARA KANTA*.
*NA GWADA NA GA INGANCINSA SHIYASA NA KE TALLATA MUKU DA K'ARFIN GUIWATA*.
*ABIN BIRGEWA DA WANNAN SAIWAR ZAKI YI AMFANI DA ITA SAMA DA SAU DAYA.*
*AKWAI FULL, AKWAI RABI TA, YADDA KOWA ZAI IYA SIYA*.
*SANNAN BABU BAURI NA TASHIN HANKALI.*
*DA KANKI ZAKI DAFA ABAR KI, KOMAI ANA SAKA WA A CIKI*.
*TUNTU'BI SURAYYA HALIN YAU*
*08032773332*
*DOMIN KARIN BAYANI, SERIOUS BUYERS ONLY PLEASE*..

—————-
Likitocin suka cigaba da zuba mata idanu cikin tarin mamaki, ganin yarda take sakin surutai barkatai kamar wacce ta ci kai. Da k’yar d’aya daga cikin likitocin ya yi azamar dakatar da ita daga yunk’urin da take na fincike abin k’arin ruwan, ya yi Saurin danne hannunta yana kallon cikin idanunta da suke jirkicewa zuwa wani yanayi na daban, kamar mai shirin rasa hankalinta da tunaninta ma gaba ‘daya. Allurar barci ya yi mata don zuwa lokacin ya hango cewa allurar barcin itace taimakon gaggawa da ya kamata a samar mata, ta saki ajiyar zuciya daidai lokacin da take lumshe manyan idanunta cinkoson hawayen da ya yiwa idanunta dafifi suka shiga rige-rigen sakkowa kamar an kunna famfo. Likitocin suka saki ajiyar zuciya a tare ha’de da yarfe gumin da yake goshinsu don ba k’aramar jigata su ta yi ba.



A zaune suka samu su Amma jigum-jigum, fuskarsu cike fal da alhini da ya bayyana a cikin idanunsu, burinsu kawai sanin Halin da Ayra take ciki zuwa lokacin Amma ta kai k’ololuwa a tashin hankali, sam bata san Ayran na nan lab’e ba da bata saki baki da jiki tana bawa Hameeda labari ba, labarin da take ta tattalinsa bata son Ayran ta sani balle ta rub’anya shi a kan wancan laifin ta sake ninka k’iyayyar maza a ranta, sai ga shi cikin sauk’i ta ji daga bakin da ta tabbata ba zai mata k’arya ba. Likitan da ya zama shine likitan Ayran tun tale-tale tun bayan afkuwar wancan lamarin da ta razana ta ‘dimauta har ya zame mata uwa zata samu matsala a kwanya, ya sauke idanunsa a kan Amma, ransa a ‘dan b’ace ya ce “Ku biyo ni Office akwai abinda zan fa’da.” Da sauri Amma da Hameeda suka mik’e suka bi bayansa, zuwa lokacin Amma bata jin akwai abinda zata b’oyewa Hameeda jin ta take kamar y’ar uwarta shak’ik’iya.


Tsawon lokaci yana rubutu a file ‘din Ayra ya bar su Amma da suka k’agara su ji halin da Ayran take ciki zaune sun zuba uban tagumi idanunsu a kansa, suna hango tsagwaron b’acin ran da yake ciki. Sai da ya mula don kansa sannan ya ‘dago idanunsa cikin na Amma ya ce “Idan ba kya son lafiyar yarinyarki me zai hana ni ki bar min ita kafin ki haddasa mata ciwon hauka?” Amma gabanta ya buga, bugawar da in dai kai mai k’arfin ji ne kana zaune kusa da ita sai ka jiyo. “Ta shiga condition ‘din da k’iris take jira ta kai ga limit ‘din rasa tunani, inma saboda b’acin ran da kuke haddasa mata ko kuma kuna tuno mata wancan mugun abin da na yi garga’di a kan kada a dinga tuno mata, ban da Allah ya kiyaye a yau zuciyar yarinyarki daf take da bugawa don gaba ‘d’aya sai da komai na jikinta ya tafi hutun yajin aiki saboda wani abu da ya gigita mata tunani, mun sha wahala sosai kafin daidaituwar komai a jikinta, and for My last warning kada ku sake ‘d’aga mata hankali idan ba haka ba komai zai iya faruwa idan na ce komai ina nufin komai, dafatan za ku kiyaye Allah yasa mu dace. Yanzu za ku barta a nan zuwa gobe mu ga Abinda Allah zai yi, amma dai a kiyaye, kiyayewar shine abinda muka fi buk’ata.”


Shiru ya bak’unci office ‘din, duk wani farin ciki da son auren Turaki da Ayra da Hameeda take yi sai murnarta ta koma ciki, bata son abinda zai haddasawa Ayra ciwon hauka don haka kafin aiwatar da Auren ya kyautu k’warai ta tambayi Likitan ba matsala idan aka aurar da ita? Don haka ta gyara zamanta cikin sakin nauyayyiyar ajiyar zuciya idanunta cikin na likitan da ya mayar da kallonsa kanta jin ajiyar zuciyar da take. “Ba matsala likita idan aka mata aure?” Jim ya ‘dan yi yana juya biron a hannunsa “Ba zai zama matsala ba, idan aka dace mijin na mata bahagon so wanda zai iya shanye duk wasu Matsalolin da zata zo masa da su, amma zai iya zama matsala idan aka samu miji mara kula ko kuma aka yi rashin dace ita bata son sa, amma tabbas Auren shi ya dace da ita, shine abinda zai ‘debeta mata kewa ya kuma kawar mata da wancan tunanin, duk hakan kuma zai faru ne idan aka samu dacen Mijin ya zama mai kulawa sab’anin haka kuma komai zai iya faruwa, kuma ina da yak’inin ba namijin da zai samu dalleliya kamar Ayra ya kasa kulawa da lamarinta ta kai mace duk yarda ake son Mace ta kai koma fiye da.” Likitan ya fa’da yana lumshe ido k’ok’ari yake sosai wajen danne abinda yake taso masa dangane da Ayran saboda ba tun yau ba yake jin masifar son ta sai dai ta k’i ba shi dama, ga shi Allah ya ha’da shi da wata iriyar mata mai masifaffen kishi da idan ba’a yi wasa ba haka zai k’are rayuwarsa da Mace ‘d’aya jal.

Amma ta saki ajiyar zuciya idanunta cikin na Hameeda da itama ta saki ajiyar zuciyar suka mik’e duk a tare hankalinsu a tashe da tunanin ta yarda za su b’ullowa lamarin.



Tsawon lokaci Hameeda tana tare da Amma, kafin tunanin zuwa gida ta taso Turaki a gaba ya duba Ayra yazo mata, dole ne kuma ta ja kunnensa a kan aikata duk wani kuskure da zai zamo sanadin b’acin ran Ayran, bata jin zata iya hak’ura da ha’da auren Ayra da Turaki, mafarkinta ne kuma shine burinta da take jin zata iya rasa nata auren matuk’ar Turaki zai auri Ayra, wannan karan zata bijirewa Mijinta har sai ya amince da auren ko da haka yana nufin komai ma.”

Ta mik’e hannunta rik’e da jakarta ta isa inda Ayran take barcinta cike da alamar gajiya da wahalallen numfashi da take fitarwa a nauyaye kamar ana fisgosa. Ta saka hannu ta tattare gashin Kan Ayran ta mayar da shi baya ha’de da tofa mata adduo’i a kan fuskarta. Amma ta dinga jin da’din kulawar da take bata “Bari na je gida Talatu zan dawo zuwa da Yamma na san har na dawo ma bata farka ba tunda Doctor ya ce sai zuwa Magrib Zata iya farkawa, kada ki saka komai a ran ki, ki kuma k’addara aurensu alheri ne da za mu yi tutiya da shi nan gaba.” Amma ta ‘d’aga kai tana sakin murmushi “Allah yasa Hameeda, Allah yasa mu yi Alfahari da hakan.” Gaba ‘d’aya ’d’akin suka amsa da “Ameen” Hameeda ta saka kai ta fita da ‘dan azama.






❤️❤️❤️❤️

Daidai lokacin yana tsaye a ‘dakinsa, hannayensa saye cikin dogon wandon da yake jikinsa a bakin babban windown yake tsaye idanunsa a kan harabar gidan kamar mai nazarin wani abu, sai dai tunani ne cunkushe a zuciyarsa, tunanin macen da ta tsaya masa a rai bayan Mutuwar Hibba, da zai ganta ita ka’dai yake jin zai iya aura ya kuma zauna da ita cike da soyayyarta kamar yarda ya so Hibba. Sau ‘d’aya ya tab’a ganinta a kuma kallo ‘daya wanda ya sa shi azamar snapping ‘dinta a wayarsa ba tare da ta sani ba, kallon da ya mata yasa ta zabga masa harara ha’de da ‘d’auke kanta tana cije leb’e har yau abin ya k’i b’ace masa, kamar bita haka yake hango fuskarta da take nunawa Yayarta shi ta mata nuni su tashi su bar wajen. Turaki ya lumshe ido ya saki murmushi ha’de da ware idon ya sauke a kan wayarsa ma’adanar inda yake ajiye hoton ya shiga, kullum yana cikin wayarsa kuma ko ya canja waya hoton yana nan ba ya saka in rabuwa da shi. Murya a d’ashe cikin sautin da yake bayyana tsananin buk’atuwarsa da son ganin yarinyar ya furta “When? And Where? Ya fa’da yana ‘dan taune harshen sa, sai kuma direct ya shige ‘d’akin da yake zane-zanensa da yake shi mutum ne ma’abocin zane-zane, kaca-kaca ‘d’akin yake da shirgin hotunanta da na matarsa mai rasuwa, ya dinga bin hotunan da kallo tamkar su ne za su sada shi da inda yarinyar take. A hankali ya ja ajiyar zuciya jin wayarsa na k’ara yana dubawa ya ga sunan Ummeeey Hayateey’ d’an murmushin da bai shirya yinsa bane ya sub’uce masa a hankali ya ce “Dangerteey kuma ba, ke ka’dai ce a rayuwa zaki min auren dole na yarda, amma wannan karan am sorry to say idan yarinyar nan ta sake ta shigo hannuna Zata wahala.’ Shi ka’dai yake magana kafin ya kai wayar kunnensa “Turaki kana ji na?” Sai da ya lumshe ya bu’de a kan hoton yarinyar da ta k’ura masa ido sannan yace “Yes Ummeey.” Yauwa ka zo gida yanzu ina son ganinka.” Daga haka ta katse wayar ta bar Turaki da waya a hannu yana kallonta, kafin ya mayar da kallonsa kan aljannar sa ta airport da ta huda masa zuciya. Ya ‘dan shafi gefen k’uncinta kamar wani zararre ya hau zagaye kyakykyawan kissable lips d’inta. “Kin gani ko? Kin ga abinda ki ke shirin jawo mana kin k’i ki bayyana min kan ki ga Hayateey nan zata min auren dole, ba ruwana kin jawowa kan ki zama da kishiya It’s your fault Angel.” Ya fa’da yana lumshe ido kafin da azama ya fice yana tunanin ko hotunanta zai baza cigiya.

Sai da ya sake wanka, sannan ya saka wata arniyar shaddarsa bak’a wuluk mai masifar k’yalli, sai ta sake fito da ainahin kalarsa da ta kasance fara mai fatsifatsi, don shi ba fari bane dau tsaka-tsaki yake kalarsa ta caku’da data larabawa da kuma ta Ubansa da ya kasance usulin bak’in bafulatani. Ba gwanin saka hula bane don haka ya yi combing kansa ya shafa masa mai da Hair spray. Ya fito yana baza k’amshin turaren Miyaki ‘dan usulin mai tsadar gaske.




Ya da’de a falon gidan su yana ‘dan waige-waige da jiran ta inda Ummeey zata fito, kafin Tayseer ta fito tana niyyar shiga kitchen ta hangoshi a zaune ya jingina a kujera idanunsa a lumshe kamar mai barci. “Ya Turaki Barka da zuwa.” Idanun a lumshe ya amsa “kice ma Ummeey na zo.” Bata wani damu da rashin kallon ta da bai yi ba, don ba tun yanzu suka saba da yanayinsa da ya jirkice haka ba tun bayan mutuwar matarsa, da Kam Turaki mutum ne mai barkwanci da yake tasa su a gaba da wasa da dariya banda yanzu da ya rikid’e musu ya koma SINGHAM, sunan da suke kiransa kenan ita da Tasleem.

Tana sanar da Ummeey ta ce “Ki ce masa ya shigo nan.” Tayseer ta juya da sauri don isar da sak’on Ummeeyn.


Tana gaya masa ya mik’e, don ya san tunda Ummeey ta ce ya shiga ‘d’aki magana ce mai muhimmanci za su yi, Allah yasa dai ba a kan auren Karuwar nan bane.


Hannayenta zube bisa k’uncinta ya same ta, da alamar yanayin damuwa da yake shimfi’de bisa fuskarta, ya gama karantar halayen mahaifiyarsa zai kuma iya rubuta littafi guda akan halayenta abu ‘d’aya ya kasa sabawa da shi, rigimarta da kafewa a kan ra’ayinta sama da na kowa ko da kuwa ba itace da gaskiya ba.

Idanunta da suka taru da k’walla ta zuba masa, hakan ya sanya shi mutuwar jiki har bai san sanda ya isa gabanta ba ya durk’ushe sosai yana kamo tattausassun hannayenta cikin nasa yana matsawa a hankali cike da ladabi da alamar rarrashi. “Menene Hayateey?” Shiru ta masa tsawon lokaci tana nazartar k’wayar idanunsa kafin ta saka hannayenta cikin tarin sumar gashin kansa murya a k’asa ta fara magana “Ku biyar Allah ya ba ni, a cikinsu kuma kai ka’dai ne namiji, wanda nake jin ina da iko da shi fiye sa sauran matan tunda su da zarar sun yi aure sun koma k’ark’ashin ikon mijinsu, wanda suka yi auren kuma dama
Suna can k’ark’ashin iko da umarnin Mijinsu, me yasa Turaki? Me yasa kake son karyan gwiwa ta hanyar bijirewa umarnina, yau ko yarinyar nan da gaske karuwa ce ashe ba zaka iya sacrificing farin cikin ka ba don samar da nawa, ka aureta?” Ta sake murza hannunta cikin nasa tana son ganin yanayinsa da sanin shin maganarta ta tana huda zuciya da kwanyarsa. “Burina samar da farin ciki a rayuwar Ahalin Talatu, ta sha wahala sosai a
Rayuwa, wahalar da ko da karuwancin ta shiga ba za’a ga laifinta ba, ko y’ay’anta karuwancin suka yi sun yi a kan gab’ar da ta dace, balle bai zama lallai ace hakan ta faru da su ba, Ka min alfarma a wannan karan ko da hakan shine alfarmar da zaka min ta k’arshe a rayuwa ka auri yarinyar nan.” Ta fa’da tana sakin wasu irin hawaye, hawayen da take son su k’arya masa zuciya har ya amince da buk’atarta. Hak’anta kuwa ya cimma ruwa don yarda jikinsa ya dinga rayuwa zuciyarsa ta dinga bugawa sakamakon jin hawayen yana ‘diga masa ya dinga furzar da ajiyar zuciya har bai san sanda cikin tashin hankali da rawar murya ya damk’i hannunta ba yana furta “Na amince Na amince Ummeey ko da hakan yana nufin k’arshen rayuwata!” Murmushin da bata shirya yinsa bane ya sub’uce mata a kan kyakykyawar dattijuwar fuskarta, ta dinga murza hannunta tana fa’din “Thankyou Turaki, Shukran Al’amin Allah ya yi maka albarka Aminullahi.”

Yayinda take farin ciki shi kuma bak’in ciki ne yake nuk’urk’usar zuciyarsa, ya dinga jin sautin bugunta da k’arfin gaske, ga wani ‘daci da ya yi masa dabaibayi a mak’ogaransa, tabbas ko wacece yarinyar nan ta zame masa bak’ar k’addara a rayuwarsa kuma zai wahalar da ita ta cikin ruwan sanyi ba tare da ya bar kowacce irin kafa da Ummeey ko mutane za su gane ba, shi da auren Karuwa? Ya dinga murza

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login