Showing 93001 words to 96000 words out of 132090 words
Chapter 32 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt
Talatu, me za’a yi da Miji irin Kabiru? Tunda nake ban tab’a ganin matsiyaci ba irinsa, ki yi hak’uri dai uban y’ay’anki ne, amma dole na fa’di gaskiya.” Talatu ta yi murmushin takaici kafin ta ce “Wallahi zage shi son ranki, ya cancanci zagin ne ai shi ya jawowa kansa.”
_________
Kashegari kuwa kamar yarda y’an uwan Hajiya suka ce haka suka zo suka sallami su Talatu ko nace suka musu kora da hali don k’arfe bakwai a gidan ta musu suka fitar da kowa har mai gadi basu bar sa ba. Cikinsu ba wanda ya damu tunda suna da mahallin zama, hatta da furniture sai da Hajiya ta zuba musu a gidajen nasu masu ‘dakuna bibbiyu da falo da kitchen da toilet a falo da kuma cikin kowane ‘dakuna. Gidan dai Ma sha Allah ‘dan madaidaici mai kyau da shi. Kuma cikin unguwa ‘d’aya a layi ‘d’aya. Gidan Talatu a jikin na Jummai yake.
Talatu har hawaye ta yi da suka zauna suna kimtsa kayansu. Ayra ma Zugum Ta yi, haka sauran da su sun zama y’an mata Majeeda na da shekaru sha takwas ita kuma Zainab na da sha bakwai tunda tazararsu shekara guda ne, Ayshatu tana da sha biyar da rabi. Deejah ce mai sha d’aya sai Auta Ayra da take da bakwai. Majeedah da Zainab ma a wannan shekarar za su gama makaranta Aysha tana SS 1 Deejah na JS 2 sai Ayra mai primary 2 a intercontinental School.
A yammacin ranar da suka dawo, sai ga Kamilu yazo. Jummai ce ta je har titi ta taro shi. Ta kuma rakasa har gidan Talatu inda Kamilu ya hau baza ido yana kallon yarda Talatun ta zama uwar mata ga yaranta mata kyawawan gaske. Ya dinga binsu da ido Suna gaisheshi cike da ladabi don yaran Talatu ba dai tarbiyya ba. Talatun ma ba yabo ba fallasa ta gaida shi, kafin ta saka Zainab ta kawo masa abincin da suka girka jallop ‘din shinkafa da bandar kifi ta kuma kawo masa zob’o a jug. Sai da ya ci ya yi hani’an sannan Jummai ta dubeshi ta ce “Kamilu ina son magana da kai, amma ka dubi girman Allah ka gaya min idan abinda zan gaya maka zuciyarka ta amince da shi.” Ya ‘daga kansa “Fa’di kan ki tsaye
hajjaju ba abinda zan b’oye miki.” “Aurenka nake son yi, ba don komai ba sai don ka zamewa Talatu da yaranta da ni kaina Garkuwa.” Wani irin washe baki Kamilu ya yi ba wani ja’inja ya ce “Na amince Hajjaju ko yau kike so a ‘daura kawai, tabbas an yi aiki da hankali a nan.” Jummai ta yi murmushi ta ce “Ai dama yau za’a ‘daura a masallacin unguwar nan don na sanar da wanda zai amsa auren nawa ma.” Kamilu cike da nisha’di ya ce “Falillahil Hamdu amma fa ba ni da sadaki.” “Sai ka bayar daga baya.” In ji Talatu ta fa’da tana ‘dan sakin murmushi. Wannan ne mafarin auren Kamilu da matarsa Jummai. Daga ranar ya tare a gidan Jummai.
Sai da sati ya zagayo, sannan ya ‘debi Jummai suka tafi Shagogo inda a can sauran matansa suke. Bata wani samu matsala da mutanen garin ba ta yi kwana biyu ta dawo.
——————
Kwatsam bayan zuwan su da sati guda labarin rasuwar Innar su Kabiru ya riskesu, wacce ta zamo Uwa ga Kamilun ya gigita k’warai da zancen mutuwar Innar don haka da asussuba suka hau shiri shi da Jummai don su tafi Shagogo. Jummai tana gama shiri ta fa’da gidan Talatu don ta sanar mata. Talatu ta ware ido tana kallonta “Inna ta mutu Jummai?” Jummai ta ‘d’aga kai “Kinga kuwa zuwa Shagogo ya kama ki, ni ina son ma ki je suga yarda Allah ya mayar da ke duk wanda ya gan ki yanzu ya san Naira ta zauna Hajiya kawai ki shirya mu je.” Talatu ta yi ‘dan jim tana wasi wasi a ranta, sai kuma ta tuna yarda Kamilu yake kula da al’amarinsu bai kamata ta kallesa ta ce ba zata gaisuwar Mahaifiyarsu ba, ban da wani ga jikokinta har biyar da idan aka tsaga jikinsu za’a ga Jinin Inna ya zama dole ta je. Ta ‘d’aga kai “Shikkenan bari yaran su yi sauri su shirya sai mu ranka ya ga ba ‘d’aya ko bakomai ina son ganin Kabiru dama a yi wacce za’a yi.” Haka ta shiga wanka a gaggauce su Majeedah ma suka kimtsa kayansu suka kuma shirya cikin rantsatstsun dogayen riguna bak’ake haskensu ya sake bayyana ga wani kyau da suka sake yi gwanin sha’awa Ma sha Allah, har wani sihirtaccen k’amshi suke fitarwa. Talatu ma ta fito tsaf cikin wani lace ‘dinta mara nauyi coffee colour ya sake fitar da zahirin kyanta da kwarjininta. A tasha suka samu babbar mota wagon da zata kai su k’auyen Shagogo suka biya ku’dinta gaba ‘d’aya.
Kafin su isa ma har an kai gawar Innah.
Isarsu a motar yasa su Kabiru da suke zaman makoki zubawa motar ido, suna jiran su ga wa’danda za su fito daga motar. Yawun bakin Kabiru ne ya k’afe k’af sanda ya yi arba da Talatu da zaratan y’an matanta!
To fa! Ko ya zata kasance mu ha’du ranar litinin In sha Allah, nagode sosai. Jikar Nashe Taku ce.😊
Takaicin Uba…
Nazeefah Nashe
47.
💔💔💔💔
Idanuwan Kabiru sosai suka shige cikin na Talatu, da tsananin mamaki yake kallon yarda Talatun ta canja gaba ‘dayanta. Ta yi wani irin murjewa da k’iba ga fatarta sai shek’i take tamkar dai zuwa aka yi aka saketa a engine. Bai tsinke da lamarin ba sai da ya ga yarda yaransa ma suka zama kyawawa da su gwanin sha’awa. Ta gabansu suka zo suka wuce ba tare da ko kallonsu sun yi ba, don Talatu bata basu tarbiyyar kula mutane akan hanya ba. Kabiru ya shak’i wadataccen k’amshin da haka kawai ya zauna a kayan Talatu ko bata saka kaya ba sai ka ji wannan k’amshin tun suna gidan Hajiya ya bi ya yi naso a kayansu. Sarai ta gan shi ta kuma ji kaifin idanunsa a kanta saboda yarda ya tsareta da ido ko mutanen wajen sun lura da shi. Nan hirar jama’ar wajen ya koma kanta fa’di suke Kamar Talatu ko? Hadi ‘dan kanzagin Kabiru ya ce “Wallahi itace, ai wato Alaji in dai ka ce zaka shiga harka ta karuwanci zaka aikta abinda ya fi haka ma.” Kamilu da yake gefe zuwan sa wajen kenan ya ji kalamin Hadi sai ya ja tsaki ya ce “Allah ya kyauta maka Hadi da wannan k’azafin da ka mata Ina tabbatar maka sai kun tsaya gaban shaidu ranar alk’iyama a ina kaje ka ga tana Karuwancin? Ku sam mutuwa ma ta kasa zame muku Ishara.” Ya fa’da yana kallon Kabirun da ya fa’da zuzzurfan tunanin Talatu da yarda ta koma zai iya rantsuwa kaf matansa ba wacce a yanzu ta kama k’afar Talatu wajen kyau da cikakken dirin jiki, ya zama dole ya yi wani abu kai dole ne ya mayar da aurensa da Talatu ko tana so ko bata so. Kamilu dai ya zabga tsaki ya shige cikin gidan a zuciyarsa yana nemawa Talatu add’oin shiriya da kariya daga sharrin su Kabiru da muk’arrabansa don a zamansa da Talatu ya fuskanci kyawawan halayenta da nagartattun d’abiunta sam bata ‘dau duniya da zafi ba, tana kuma da kyauta sosai da sosai abin hannunta bai rufe mata ido ba.
Sanda Matan gidan suka ga Talatu sam basu ganeta ba, tunda shekarun da dama shekaru har bakwai rugis dole komai ya canja. Ta zauna tana gaishesu kafin wata daga cikin k’annen Kabiru mata ta ce “Ikon Allah! Sai na ga kamar Talatu ko?” Talatu ta ‘dan saki murmushi ta ce “Nice Sabuwa ya hak’urin Inna?” Sabuwa ta saki salati cikin alajabi ta fara k’walawa jama’ar gidan kira tana fa’din Jama’a ku zo ga Talatu.” Kan kace me gida ya cika damk’am kowa fa’di yake “k’warai na so na shaida kamannin to gaba ‘d’aya ta canza ga zaratan y’an mata wa zai kawo ita ce. Wata kuma ta ce “Oh Talatu rai kan ga rai yanzu duk tsawon shekarun nan ina kika shige?” Sakina mara kunyar cikinsu tace “Kema dai Yaya Algaje da wani zance kike, to har a wani tambayi in da ta shige ga alamu nan sun bayyana Ai yawon karuwanci ana samun ku’di k’arshe ne dai ba zai yi kyau ba.” “Eeh, k’warai kuwa y’ar nan na ga Alama, da Idanu na ya rife to Allah ya rufa mana asiri, ai kuwa idan haka ne Kabiru dole ya karb’i y’an matan nan a aurar da su ko su Lawandi a rok’a su auresu don ba a barta da yara mata a hannunta ta saka su a
Hanyar banza ba.” A harzuk’e Majeeda ta ‘dago zata yi magana Jummai ta ‘dan harareta kafin ta ce “Yanzu ku fisabilillah wa ya ce muku Talatu yawon karuwanci ta tafi? Ku baku san girman k’azafi ba ko? To Talatu tunda ta bar gari nan muna tare kuma ban tab’a ganinta tsaye da wani Mijin ba balle ta kai ga maganar karuwanci.” Talatu ta saki murmushi mai ciwo tana mik’ewa ta ce “Jummai ki rabu da su, ba za su tab’a fuskantar kalaman Ki ba kin san akwai k’arancin ilimi kuma ni na janyowa kai na da nazo garin sai dai an yi na farko an yi na k’arshe, kuma karuwanci da kika ce Ina yi ina ce idan ma na yi ba matsalarku a ciki, kuma ba karuwanci ba ko me na saka yara na ina ce ba abinda ya shafe ku da su akwai abinda kuka tab’a basu ne tunda aka haifesu sai yanzu da suka girma ake nema ace za a gwada min k’arfi to ko shi Kabirun bai isa ya min iko da y’ay’a ba, yanzu na san mutuncin kai na na san kuma hanyar da ake bi a maka mutum a kotu don haka ku kiyayeni, yanzu na da bace bana shakkar kowa!” Tsananin mamaki da razani yasa suka kasa yi mata magana suka ja bakinsu suka yi tsit suna aikin kallonta a tsorace a hasashensu tabbas kamar yarda Talatun ta canja haka halayenta gaba ‘daya ya canja. Haka suka dinga jan jiki ‘d’aya bayan ‘daya suna ficewa daga ‘dakin don tabbas basu hango sauk’i da salama a idanun Talatun ba. Ba ‘digon sassauci a tare da ita sam.
Har azahar suna gidan mutuwar, inda gidan mutuwar ya zama gidan gulma da tsegumi don wasu dai ba don Allah suke zuwa ba sai don su ga Talatun da yaranta da suka koma tamkar ba hausawa ba, fatarsu ta goge ga hasken ilimi da tarbiyya a tattare da su.
Sam Kabiru ya kasa hak’urewa zuciyarsa har sai da ya mik’e bayan ya gama jin zugar da Hadi yake masa, ya nufi cikin gidan da zummar a yi wacce za’ayi. Sanda Talatu ta ji muryarsa sai da gabanta ya bada tsananin bugu ba don komai ba sai don tsanar ta gansa ‘din ba ta burin wata mu’amala ta sake ha’data da shi, da ta san kuma zasu ha’dun ba abinda zai kawota garin duk da dama burinta shine su ha’dun a yi wacce za’a yi. Ta ha’de rai ta tsuke fuskarta tamau kamar bata tab’a fara’a ba. Ta kalli su Majeeda da suke zaune a gefe a takure kamar ma a tsorace suke don rashin sabo. “Ku matso nan kusa da ni Majeedah.” Suka kuwa matsa ta na kallonsu ta ce “Ko ya shigo ban amince ku gaisa da shi ba don sarai na san kun gane shi, Deejah da Ayra ne kawai ba za su ganesa ba.” Majeeda sake ha’de rai ta yi kafin ta ce “Amma Yaushe za mu tafi?” Ta fa’da tana kallon Amman. “Yanzu In sha Allah.” Amman ta amsa mata daidai lokacin da sautin muryar Kabirun ya cigaba da k’ara kusanto su alamar nan ‘din zai shigo. Amma ta cizi bakinta tana hasashen wani irin rashin mutunci zata masa idan ya nufi yi mata magana. Sai ga shi kuwa ya ban ka’da labulan ‘dakin idanunsa a kan su Talatun da yake wa wani irin kallo mai cike al’ajabin yarda suka koma. Ya saka kansa ya shiga ‘dakin duk da yanayin fuskar Talatun ta firgita shi bai fasa himmar yi mata magana ba. “Su Talatu manyan gari, idan ke ban ci darajar da zaki gaisheni ba su kuma y’ay’ana da nake matsayin Ubansu me yasa ba za su gaisa da ni ba?” Talatu ta ‘dago cikin wani irin mabayyanin b’acin rai da Kabirun bai tab’a ganinta da shi ba ta ce “Y’ay’anka Kabiru? Y’ayanka fa kace? Yanzu ko kunyar furta hakan da bakinka ba ka ji ba, ai bai kamata a ji wannan kalmar a bakinka ba ko ka manta sanda ka ce ka bar min gayyar yara matan na je na k’arata da su har abada baka buk’atarsu? Yanzu ne kake kallon su kake kiran kanka Ubansu? Ta ina ka amsa sunan Ubansu? Ka yanka musu ragon suna? Ka ‘d’au nauyin ci da shan su? Ko ka san harkar neman iliminsu? Don haka kada ka sake duban yarana ka kira y’ay’anka, magana ta biyu shine ina son amsar takardar saki na a wajenka don na zama cikakkiyaf bazawara mai y’anci, duk da ban ‘dau gantalallen aurenka aure ba kawai dai ina son shaidar da zan kafata ko don gaba, ba zaka tare ni kace kana da aurena a kanka ba don ko mutuwa nake idan aka kai gawata gidanka ban yafe ba don haka ka bani shaidar takardar sakina ko kuma ka bani a gaban alk’ali.” Kabiru tsayawa Yayi yana kallonta cike da mamakinta, Talatu ce ta dawo haka? Talatu ce take iya tararsa tana gaya masa magana mai zafi haka, ashe kuwa za’a yi ta don aure yanzu ya fara bai ga kuma kotun da zata iya amsar takarda ta bawa Talatu ba a wajensa. Ina da sake yarda ya ga Talatun ta murje duk wata halitta ta matantaka ta sake bunk’asa a jikinta kamar ma yanzu mak’erin y’an mata yake k’erata sannan ta ce ya saketa, ta ina za’a fara tabbas za su buga wasa shi da ita don ko ana muzuru ana shaho sai ya maidata gidansa. Cikin k’arfin hali da dakewar murya ya ce “Kada ma ki fara wannan maganar Uwar gida na! Aure Ai yanzu na fara yi da ke, ni da ke mutu ka raba takalmin kaza.” “Kan uban can!” Talatu ta furta cikin muryar tashin hankali da sauri yaranta Suka kalleta suna mamakin jin zagin a bakinta “Baka so gamawa lafiya ba Kabiru dole ka sake ni, idan ka ga na koma gidanka ashe kuwa Ubana ne ya dawo duniya ya ce idan ban zauna da kai ba zai tsine min.” Kabiru ya saki murmushi yana wani kallonta k’asa-k’asa ya ce “Kin manta ko waye Kabiru ko Talatu ashe kuwa yau tuna miki, a yau zan sadu da ke na mayar da aure na cikin ‘dakin nan idan yaso na ga uban da zai raba min aurena, don yarda na kwa’daitu da ke dole ne yau na kaiwa gonarki ziyara, kai yara ku ba mu waje.”
Ya fa’da yana mik’ewa tsaye yana k’ok’arin zage tazugensa bayan ya ga fitar yaran da sauri illa Ayra da ta ja ta tsaya ta k’i fita don gani take wani mugun abin zai aikatawa Ammanta.
To fa! Amma Kabiru an yi tantiri.
Ku yi hak’uri yau ciwon kai na yi shi yasa za ku ga typing ‘din ka’dan.
Takaicin Uba.
48.
💔💔💔💔
Sosai Talatu suka fara kokawa da Kabiru kafin ta ciri hannunta ta zabga masa mari ta sauke hannun tana fitar da hucin b’acin rai “Ni kika mara Talatu?” “An mareka ‘din kuma ka sake kusanto k’azamin jikinka zuwa wajena ka ga idan ban maka abinda ya fi mari ba, Ka zata ni ‘din Talatun da ce? Talatun da ka mayar dabba ka haik’e mata duk sanda ka so a kuma lokacin da kaga dama, wannan karan a wanke idanuna su ke kuma na san abinda duniya take ciki, sam ba zan yarda ka take min hakkina ba da sunan wai igiyar aurenka ce a kaina, kuma da ka sake ni da kada ka sakeni uwarsu ‘daya uban su ‘d’aya na tabbata akwai inda zan kaika a saka kuma ka sakeni ta dole, bak’in mugu azzalimi Ai jikina yanzu yafi k’arfinka Kabiru ko kai idanunka basu nuna maka haka ba?” Ta sake zabga masa tsaki Daga haka ta ja hannun Ayra da take tsaye a gefe tana kallon Kabirun cike da tsana da jin haushin yarda ya mak’ure mata mahaifiya. Ba wanda ta yiwa sallama sai Jummai da ita ba zata koma a lokacin ba sai an yi sadakar bakwai ta saka kai ta fice.
Shi kuwa Kabiru gaba ‘daya gwiwarsa ce ta sare ya kasa katab’us kafin ya ji sallamarta da Jummai da sauri ya ‘dau wayarsa ya kira Hadi yana ‘dagawa ya ce “Hadi maza ka bi min Talatu har can gidan da take kada ka dawo sai ka ga inda ta shiga tunda bata san motata ba mukullin motar yana hannunka ko?” Hadi ya ce “k’warai yana hannuna” “To maza kada ka yi wasa ka tabbatar ka bi motar da ta shiga kada ka bari wannan damar ta wuce mu, akwai alheri mai yawa tattare da zama na da Talatu da nake jin yanzu ina mata son da ba nawa mata macece shi.” “Hadi ya ce In sha Allah ranka ya da’de ga tanan ma ta fito bari na yi sauri na bi ta.” Ya katse wayar yana mik’ewa ya nufi can inda motar Kabirun take.
Sam ba su san Hadin yana bin su ba har suka je gida, Hadi ya saki ajiyar zuciya bayan ya ga har unguwar da gidan ya kuma haddace ra’dam a kansa. Wannan shine mafarin sanin Kabiru inda Talatu take har ya bisu bin da ya zama mummuna kuma bak’ar k’addara a wajensu da su da duk wani mai son su. Hadi ya komawa Kabiru da dadda’dan labarin da ya samu kyauta mai tsoka saboda shi. Duniya kenan mai juyin waina yau dai ga Kabiru da ku’din sa yake biya don a gano masa mahallin Talatu da inda take zaune. Ga kuma soyayyarta da ta d’inke masa zuciya abinda bai