Showing 117001 words to 120000 words out of 132090 words
Chapter 40 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt
k’aru saboda tsananin kama da ya yi mata da Innayo. Jikinta a sanyaye ta k’arasa ta zauna, har a lokacin shima kallon ta yake duk da dai ba abinda ta ‘dauko na Innarta amma tsananin kamar da suke da mahaifiyar su Adda ya yi yawa. Girmama girman Ubangiji yake kawai a zuciyarsa kafin ya mik’e yana sake zame rawaninsa ya kalli Ummeey da Fulani ya ce “Ga duk wanda ya san Adda ya san wannan jininta ce saboda yarda ta yi kama da ita kwabo da kwabo, ya sunan Mahaifiyarki?” Amma Talatu ta ‘dago da sauri tana kallonsa ta ce “Sunanta Hauwa Kulu, ana kiranta Danejo.” Kowa sai da ya ‘dago yana kallnta musamman Maimartaba cikin mamaki ya ce “Hasashena ya tabbata yau ga jinin Danejo a gaba na, Alhamdulillah ya Allah mahaifiyarki ciki ‘d’aya muke da ita ni na sha Nono na sakar mata, masu satar mutane ne suka raba mu da ita, rabawar da ta zamo ta har abada shikkenan har yau ban sake jin labarin ‘dan uwa na ko ‘d’aya ba sai yau da Allah ya ha’da ni da ke, Alhamdulillah ya Allah.” Shikkenan guri ya ru’de da murna, Kamilu yana gefe yana jaddada girman Ubangiji Ai kuwa zai je Shagogo ya sanar da su wacece Talatu da ake wa gorin dangin Mahaifiya ga shi nan wan Mahaifiyarta ne zai zama Sarkin fulanin Gombe, ashe dai Ayra tsatson su ‘d’aya da Turaki, shi kansa Turakin mamaki ne yasa ya tsaya cak yana duban Ayra bai tab’a zata ko a mafarki Ayra y’ar uwarsa ce ta jini ba. Talatu kam murna take sosai ta kama hannun mai martaba ta rik’e gam tana jin sa kamar Innayonta ashe zata ga wannan ranar, ashe zata ga dangin mahaifiyarta bayan ta gama fitar da rai.
Har dare murna bata bar ahalin nan ba, haka aka zauna aka dinga labarin lokutan baya, Mai martaba ya dinga bada labarin y’an uwansa da ya rasa.
Sai da suka koma sashensu Ummeey ta kalli Ayra da Tasleem da Tayseer da itama ta iso a yammacin ranar ta ce “Maza ku tafi gidan Addarku Adda petal ku kwana a can, za ku fi sakewa tunda gidan nan a cike yake damk’am. Suka mik’e suka shiga ‘d’aki don ‘Debo abinda za su buk’ata, Turaki da yake gefe ya yi kamar bai ji me suke cewa ba ya mik’e tsam yana kallon Ummeey ya ce “Sai da safe.” Sannan ya kalli Amma ya ‘dan rusuna ya ce “Amma sai da safe.” Duka suka amsa da Allah ya tashe mu lafiya.
Ya isa can inda ake ajiyar motocin fadar, ya hau kan motarsa ya zauna yana jiran ya ga ta inda za su b’ullo. Suna isowa gurin sam ba su kula da shi ba sai ji suka yi ya ce “Hey, ku shiga mu tafi.” Ba su kawo komai ba suka shiga motar. Ayra ta saka kai zata shiga ta ji ya fisgo hannunta ya ce “Shiga gaba madam, ba driver bane.” Ta ‘dan ha’de ranta tana kallonsa kafin ta bu’de k’ofar ta shiga. Ya saki murmushi yana shiga b’arin driver shima ya fisgi motar da mugun speed dama yanayin tuk’insa kenan.
Daidai gidan Adda petal ya tsaya yana kallon su Tasleem bayan ya bu’de motar ya saka hannu ‘d’aya ya damk’i hannun Ayra ya ce “Oya ku je ku ce ina gaishe ta ita zan bata sak’o yanzu zata shigo.” Suka fita shi kuma ya sake locking motar ya fisgeta da sauri, Ayra ta ‘dago tana kallonsa “Ina za mu je.” Ya gimtse fuskarsa yana sake matsa hannunta ya ce “Neman lada……..
𝔍𝖎𝖐𝖆𝖗 𝕹𝖆𝖘𝖍𝖊✍️
Takaicin Uba….
59.
Gaba ‘daya walwalar fuskar Ayra ta b’ace b’at ganin yarda Turaki ya kawota. Idanu ta zuba masa cike da son k’arin bayani. Shima nasa idanuwan ya zuba mata yana lumshe su “Sauka Mu je, Malama.” Ta ji furucinsa a cikin kunnenta, da sauri ta janye jikinta jin yarda ya kusantota sosai, ya ‘Dan ‘dauke kai yana dariya k’asa-k’asa “Ki sauka na ce.” “Ba zan sauka ba, ta yaya zaka kawo ni Hotel bayan ga yarda Ummeey ta ce mu je.” Ta fa’da tana kawar da tsoro da shakkar da suke ranta. “Ummeey ce ta biya min ku’din sadakin auren ki?, ki fita ta Lislama ko kuma na fitar da ke da kaina, ba kunyar kowa zan ji anan ba kowa harkar gabansa yake.” Ta sake lafewa a jikin kujerar alamar bata ji maganarsa ba. Turaki ya ji ransa ya fara b’aci kawai sai ya fita ya zaga ya bu’de k’ofar yana fincikota zai kinkimeta. Da sauri ta ture sa “Ka bari zan fita da kaina.” Ya saki hannunta yana murmushin k’asan leb’e. “Da dai kin tsaya kiga ko zan kasa ‘daukar ki.” Ta suri jakarta ta fita tana k’unk’uni da sauri Turaki ya rufe k’ofar ya fita suka shiga cikin hotel ‘din. A reception ya zaunar da ita ya k’arasa don samo musu D’aki.
Ayra ji take kamar ta rusa ihu, tana tunanin duk wani plan nata ya rushe, tana kallonsa ya taho cikin takun isa yana ‘d’aga mata gira ya ce “Ya dai y’an matan Ummeey, yau ga ni ga ki ba Ummeey mai tare miki fa’da.” Ta ‘dauke kanta a hankali ta ce “Akwai Allah, shi zai min maganinka.” Ya sunkuya daidai fuskarta yana murmushi “Yi hak’uri y’an mata, har kin karaya?” Wata jarumta ce ta zo mata ta mik’e tana kallonsa a zuciyarta tana fa’din ba dai jikina kake yi wa ba, ai kuwa yau k’walelenka. Kamar yana karanta yanayinta ta ji ya ce “Dole dai komai wayon amarya a sha manta.” Bata kulasa ba ta bi shi suka k’arasa ‘dan ku gun da zai sadaka da ‘dakunan Hotel ‘din.
Yana bu’de k’ofar ya saki murmushi yana kallon Ayra “Ma sha Allah, wajen nan zai yi da’din baje amarci.” Ayra ta ha’diye wani abu da ya tsaya mata kafin ta kai idanunta kan gadon ‘dakin da ya ji wani tattausan bedsheet. Ta ajiye jakarta a saman kujera kafin ta bi jakar ta zauna ta zame tana kwanciya a kan kujerar ha’de da fa’din “Allah ya tashemu lafiya. Turaki ya zuba mata ido kafin ya ce “Me ye haka?” “Da aka yi me fa?” Itama ta jefa masa tambayar tana kallonsa da lumsassun idanunta “Don k’azanta haka za ki kwanta ba ki wanka ba, balle uwa Uba Brush.” Ayra ta tab’e baki ha’de da fa’din “Yau dai kam na yafe wankan brush kuma na yi a gida kafin na fito.” Turaki ya tab’e baki yana ‘daukar towel ya shiga toilet yana fa’din “Za ki yi na dole yanzu.” Yana gama nasa wankan ya fito jikinsa ‘dauke da towel, sai ya tarar har ta fara barci a takure kan kujera, ya k’arasa kusa da ita yana sunkuya wa kanta cak ya ‘daga ta, Ayra da barci bai yi nisa ba sosai ta fara mutsu-mutsu na son k’wace jikinta “Bari Malama, if you don’t want me to smash your face.” Shiru ta yi tana jinsa ya shiga toilet ‘din ya ajiyeta cikin showerr da ruwanta yake zuba sosai. Ayra a ru’de ta fara kallonsa yana k’ok’arin zare rigarta “Bari zan yi da kai na.” Ya saki murmushi yana fa’din “Bar shi dai na yi miki mai kike b’oyewa ne? Wani daren ne jemage bai gani ba.” Turaki please!” Ya yi cak yana kallon yarda ta furta sunan nasa, kamar a bakinta aka ra’da ko don bai tab’a jin ta kirasa da sunan ba ne.” Ya kai hannu yana kewaye lab’b’anta ya ce “Say ita again, it sounds so good in your voice” Ta ture hannunsa tana shammatarsa zata fita da sauri ya sake janyota jikinsa yana jin yarda kowane gab’a na jikinsa yake amsa soyayyarta da tsananin sha’awarta “Ki bari madam, kada ki saka komai ya faru anan, kin san yarda na yi missing ‘dinki kuwa? Haba Ayra kada tsinuwar mala’iku ta kamaki.” Ta runtse idonta tana fa’din “To me na yi kuma?” “Komai ma, fita ba da izinin mijinki ba rashin ba ni ha’din kai, ke abubuwa da yawa, yanzu kuma ina son…..” ya fa’da yana k’ura mata ido, gaba d’aya kallon ya hargitsa kanta tana ji tana gani Turaki bai kyaleta ba sai da ta yi wankan nan na dole, sannan ya fita ya barta yana jin wani farin ciki da annashuwa da alama dai tarkonsa ya kama kurciya……😀
Da k’yar ta iya saka kaya a gabansa, kallonta kawai yake yana mamakin da mai yasa idonsa ya rufe ya amince Karuwa ce, bayan ba abinda ya yi kala da karuwanci a jikinta, shi yasa ba a son ka yi aiki da jita-jita, ya lumshe ido kafin ya mik’e ya isa in da take zaune a gaba dresser tana aikin sake k’udundune jikinta da hijabinta don kunyar ya ganta da rigar barcin take. Fuskarta sam bai hango alamar zata masa sassauci ba. Ya durk’ushe a gabanta yana kamo hannayenta masu taushi da sulb’i ya ce “Afuwa Hayateey let forget the past and look for the future.” Ta sake ‘daure fuskarta tsam kafin murya a sauk’ake ta ce “Ba zan iya ba.” What?” Ya furta a ‘dimauce yana kallonta “Me yasa ki ke da rik’o ne? Kin san tsawon rayuwata ban tab’a begging wani ‘dan Adam ba, amma dube ni durk’ushe a gabanki ina rok’on ki kina ce min you will never forget.” Ta lumshe idonta kafin k’arfin zuciya ya zo mata ta mik’e tana kallonsa cikin ido “Kana zata abinda ka min zai yi sauk’in mantawa a wajena? Karuwa fa ka ce min? Ka san tsananin b’acin ran da mutum yake ji idan aka danganta shi da abinda bai tab’a aikatawa ba? Bana jin a rayuwa akwai abinda ba zan manta ba kamar a min k’azafi a danganta ni da abinda ban aikata ba it hurts me so badly, ba zan sake yarda ka kusance ni ba na amince ka auri waccan budurwartaka ni ka bar ni kawai.” Turaki lumshe idonsa ya yi kawai yana jingina da kujera bai san kuma me Ayra take son ya mata ba. Yana ji ta zame hannunta ta juya bu’de fridge ta yi ta ‘dau robar ruwa ta sha sosai kafin ta isa gefen kujerar da yake kwance rik’e da kansa ta ce “Ka tashi ka koma kan gadon, zan kwanta a kujeran.” Bai amsata ba illa murza goshinsa kawai da yake cikin tsananin b’acin rai, yana jin da yana da iko da ya janye wancan furucin, ba ya son Shaheedah kuma bai shirya auren ta ba, duk abinda ta ga sun yi set up ne kawai. Shak’ar k’amshin humrar ta da yake yana sake gigita masa nutsuwa. A hankali bata yi aune ba ta ji ya fisgota jikinsa, ta fara kiciniyar k’wacewa “Bana so Turaki.” “Ni kuma ina so Ayra, Ina ji shine abinda na fi so fiye da komai a rayuwata na ji ni a jikinki ina samun wata irin nutsuwa mai wuyar fasaltawa.” Ya fa’da yana bata hot romances, Jikin Ayra har rawa yake jin abubuwan da yake mata sun fi k’arfin tunaninta, duk wata tsiwa tata ta ‘dauke. Kafin ta ji Turaki ya kinkimeta zuwa tsakiyar gadon. Sai sannan tunaninta ya dawo ganin abinda yake shirin aikatawa gaba ‘daya hankalinsa ya gushe burinsa kawai ya isa mak’ura ya ji Ayra ta ingijeshi ta sauka a guje. “Wallahi ba zan sake yarda ka kusance ni ba….” Cak ya ji ji da ganinsa suna neman ‘daukewa bakinsa na rawa cikin karyayyiyar murya ya ce “Please Ayra! Don’t kil me.” Ta runtse idonta kafin ta shige toilet tana jin duk wasu kalamai da ya dinga amfani da su wajen k’untata mata suna amsa kuwwa a dodon kunnenta. Turaki jikinsa na rawa ya mik’e ya isa bakin toilet ‘din ya mur’da ya ji sa a kulle. A hankali ya zame ya durk’ushe a k’ofar toilet ‘din don k’afafunsa ba za su iya ‘daukarsa ba, yanayin da yake abin tausayi da ace ya iya neman karuwai tabbas da ranar ya nema. Muryarsa a raunane ya shiga rok’on ta “Please ki bu’de zan miki duk abinda ki ke so.” Ayra tana jinsa tana jin kamar tausayinsa ya rinjayeta sai kuma ta runtse ido tana tuno zafafan kalamansa. “Idan ba ki bu’de ba, wallahi gobe zan saka a ‘daura min aure, ba zan zauna kina wahalar da ni ba.” “Ba matsalata bace ka auri goma ma idan ana yi.” Turaki ya saki ajiyar zuciya ganin duk irin magiyar da ya mata bata saduda ba ya koma gado yana futar da numfashin wahala, haka kawai yana zaman zamansa Ummeey ta janyo masa idan banda haka yaushe rabonsa da sha’awar wata mace balle ta ‘d’aga masa hanci. Ya kwanta yana jin kamar ya yi ihu. Da k’yar ya samu nauyayyen barci ya ‘daukesa cike da tunanin dole ne ma ya yi aure in dai Ayra ba zata canja ba.
Jin shiru ya sa Ayra a hankali ya fito daga toilet ‘din ta kwanta a saman kujera, sai sannan tsoro ya shigeta ta fara tunanin yanzu da tsinuwar mala’iku zata kwana? Ta runtse ido tana jin hawaye na zubo mata. A hankali ta mik’e ta isa bakin bed ‘din ta fara bugawa a hankali. Turaki ya bu’de idanunsa yana wara su a kanta. “Menene?” Ya furta a shak’e “Ka yi hak’uri ga ni nazo.” Tsaki ya zabga yana kallonta sama da k’asa “Kin zo me?” Ayra ta runtse idanunta tana matsa yatsun hannunta “Bana so ki je ki jik’a ki shanye, mata dai ga su nan bila adadin a gari zaki sha mamaki a gobe zan fara neman aure idan ma ba ‘a d’aura goben ba.” Ya juya yana sake sakin tsaki ya ja duvet ya rufe har kansa don da gaske haushinta yake ji sosai da sosai. Ayra jikinta a sanyaye ta shiga toilet alwala ta ‘daura ta shiga sallolin naiflfili tana jan istigfari barci ya ‘d’auketa da k’yar don komai itama dawo mata ya shiga yi daki-daki wata irin sha’awa ta dinga fusgarta ta dinga jin tamkar ta janyo sa ta dole.
________
K’arfe 9:00 su Tasleem da Adda petal suka isa ainahin main house ‘din nasu, gida har ya fara cika don taro aka shirya ba na wasa ba. Ummeey ta dinga kallonsu kafin ta ce “Ya na gan ku ku ka’dai Ina Ayran?” Kallon juna suka fara suna murmushi kafin Adda Petal ta ce “Wace Ayran? Ai ni su ka’dai suka je min.” Ummeey ta bu’de baki tana kallon ta “Ban gane ba? Matar fa ‘dan ki Turaki nake nufi.” Ta girgiza kai “Ba su je da ita ba, ba su ce min ma tare suke ba.” Ummeey ta mayar da kallonta kan su. Tasleem tana sinne kai ta ce “Wallahi Ya. Turaki ne ya mana wayo ya tafi da ita, daga cewa bari ya bata sak’o.” Ummeey ta girgiza kai tana cizar leb’enta kafin murmushi ya sub’uce mata ta ce “Ai kuwa zai zo ya same ni.” Adda petal ta ce “Wani irin zai sameki kuma shi da matarsa?” Amma ta ce “Gane min y’ar uwa.” Ummeey shiru ta yi tana murmushi don bata son su san menene ya faru. Nan aka zauna y’an uwa da abokan arziki suna ta shigowa ana gaida su Amma Talatu, farin ciki gaba ‘d’aya ya cika zuciyarta ta san tabbas y’an uwa rahma ne. Jummai kanta mamakin yarda y’an Uwan Talatun wanda duk zuri’ar Jauro ce da ya hayayyafa y’ay’a da jikoki tunda matansa hu’du y’ay’ansa talatin da biyar biyu daga cikinsu ne kawai ba su yi aure ba. Don haka suke da yawa sosai.
_________
Tun bayan sallahr asuba da suka sake komawa ba su farka ba sai da agogo ya buga k’arfe 11:30. Da sauri Ayra ta mik’e tana kallon yarda hasken rana ya b’ullo ta wibdown da sauri ta kai idanunta kan wayarta da taga missed call rututu ta mik’e da sauri tana shiga toilet. Wanka ta yi sosai sannan ta goge jikinta ta shirya a cikin toilet ‘din tana fitowa mai kawai ta shafa sai ta yi makeup sama-sama ta shafa body mist na royal oud sai humrar ta, kayannata sai k’amshin turaren wuta da aka musu gabbasa yake. Tana d’aure gashin kanta ta ‘dan bugi pillownsa. Da k’yar ya bu’de ido Saboda yarda kansa yake sara masa zazzab’i ne ma a jikinsa sosai. “Kada mu yi late a wajen taro, ga shi a gida ma ba a san muna tare ba.” “And so what? Shi ya ba ki damar ki tashe ni ina barci, idan ba za ki iya jira ba ki tafi bana son damu.” Jikinta a sanyaye take duban yarda yake mata masifa kafin ya sake lumshe idonsa ya juya mata baya. Ayra ta ja ajiyar zuciya tana zama a hankali gefen gadon ta ha’de hannayenta ta zuba kumatunta a kai tana jin kamar ta saka kuka, sam bata son b’acin ransa , sai ta ji ta damu da damuwarsa. Ta koma kan kujerar tana kallon yarda kiran Ummeey yake shigowa wayar akai a kai. A kunya ce ta d’aga wayar tana gaisheta Ummeey ta amsa tana cewa “Ba zaku zo na’din sarautar bane ko kun wuce Moscow.” Kunya ce ta ratsa Ayra cikin rawar murya ta ce “Zamu zo Ummeey ba ya jin da’di ne.” “Ayya, me ya same sa? Maza ki basa wayar na san sa idan ba shi da lafiya sai a hankali.” Ta k’arasa wajensa ganin ya ‘dan motsa ta kara masa wayar a kunne muryar Ummeey da ya ji ya saka shi mik’ewa da k’yar yana amsa wayar “Me ya sameka?” A hankali ya ce “Headache, amma yanzu za mu taho In sha Allah.” “To sai kun zo, Drive carefully don Allah, ko ka bawa Ayran motar ta tuk’a idan inda ku ke ‘din ba nisa.” Daga haka ta kashe wayar. Turaki ya lumshe idanunsa kafin ya mik’e ya shige a hankali ko kallon Ayran bai yi ba. Wayarsa ce ta dinga k’arar shigowar messages ganin sunan Shaheedah yasa Ayra ta ji kawai tana son jin mai message ‘din ya k’unsa da sauri ta ja wayar ta kai dubanta kan messages d’in “Alhamdulillah! Buri na ya cika, after long years sai yanzu ka amince da aure na, yau za ku tura gidan namu na fa’da musu?” Wata irin zufa