Showing 18001 words to 21000 words out of 132090 words

Chapter 7 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt

yana tunano irin zaman y’an Marina da za suyi da Future wife ‘din tasa.
Takaicin Uba…..

Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387


Page 10..




_____________________



Da safiyar lahadi Hameeda ta isa gidan aminiyarta don ta isar mata da kyakykyawan albishir, sannan ta tambayeta in da za’a samu Kabiru mahaifin Ayra a
Je masa da zancen neman auren.


Tsaye Ayran take a parlour sanda ta dinga jin knocking ‘din da ake daga babbar k’ofar parlourn na su, da sauri ta ‘dau Hijabinta ta zura shi tana mamakin Wanda zai zo musu gida a irin wannan time ‘din musamman ranar da ta kasance ta hutu ce ga duk ma’aikatan gwamnati wato hutun Ester Monday.

Fuskarta ba walwala sosai ta dire burner ‘din da take hannunta tana aikin turare gidan. Ta k’arasa cike da takaicin koma waye bak’on ba tayi maraba lale da zuwan sa ba. “Wanene?” Ta fa’da cikin sanyin murya sab’anin waccan muryar da take ara ta yafa mai kauri da rashin da’din amo.
Ummeey tana murmushi ta ce “Bu’de Ayra bak’i ne.” Tuni cikin Ayra Ya yamutsa don tabbas ko da magagin barci ta tashi ba zata mance muryar matar da tazo ta Dagula mata lissafi ba fargabarta ‘daya kada ace tare take da ‘dan nata, don haka da sauri ta mayar da kallonta kan CCTV camera ‘din da take parlourn don tabbatar da hasashenta. Ba taga kowa ba sai Ummeeyn da y’an matanta da suka zo rannan ta ja tsaki bayan ta jawo nik’ab ‘dinta ta k’unshe fuskarta. Sannan ta Zare lock ‘din murya a cunkushe ta ce “Barka da zuwa.” Ummeey ta shafa kanta ha’de da fa’din “Barakillah! Ma sha Allah” ta fa’da duk da ba ta ganin fuskar Ayran. Ita dai bata yi magana ba ta juya da sauri don ta basu damar shiga cikin parlourn.

Ba tarbiyyarsu bane k’in gaida bak’i musamman babban mutum don haka bisa tilas ta durk’usa ta gaida Ummeeyn ba tare da ta cire nik’ab ‘din ba. Sam Ummeey bata damu da hakan ba ta amsa mata cike da kulawa sannan ta mik’e ta hau don kiran Amma. Da sauri Tayseer ta ce “Wait Ayra tsaya mu gaisa.” Takaicin yarinyar yasa kamar ta juya ta mata duka sai dai ta mik’a mata hannu sannan ta sake mik’awa Tasleem hannu itama suka mik’e suka rungumeta don haka kawai suke son Ayran suna kuma fatan maganar da Ummeey ta gaya musu ta tabbata tabbas da Yaya Turaki ya gwangwaje da mata.



A saman sallaya ta tarar da Amma da casbaha a hannunta, da alama sallar walaha ta idar.
Babu damuwa sosai a fuskarta don ta yi alk’awarin ta daina nuna damuwar ta ce “Amma, kin yi bak’i a k’asa.” Amma ta ‘d’ago tana kallonta da son k’arin bayani ba tare da ta yi magana ba, Ayra ta saki ajiyar zuciya kafin ta ce “Bak’uwar aminiyarki ta yarinya ita ce ta zo.” Daga haka ta juya ta shige wani k’aramin falon da yake saman don bata son ma komawa k’asan balle ta sake ha’duwa da yaran can masu shegen magana kamar ana saka musu batir. Amma ta bita da kallo tana ‘dan sakin murmushi kafin ta mik’e ta nufi parlourn k’asan.

Da murna da farin ciki ta tari bak’uwarta ta ta zauna a gefenta bayan ta k’wala wa mai aikinta Inna Habi kira, tana zuwa ta saka ta kawo musu ‘dan abin motsa baki. Sai da suka gama ‘dan ciye ciyensu sannan Amma ta ce su Tayseer su hau sama wajen Ayra.

Suna tafiya Ummeey ta dubeta ta ce “sai ki ka ganni da sassafe, Yallab’ai ne Ya ce na zo na tambayeki inda za’a samu Kabiru aje masa da maganar auren tunda na ji kin ce min yanzu ba kwa tare.”

Gaba ‘daya annurin dake fuskar Amma ya ‘dauke tsaf, ta ha’de ranta sosai bayan ta zube idanunta a k’asan carpet ‘din da yake shimfid’e a wajen. Tsawon lokaci tana jin yarda zuciyarta take tuk’uk’in b’acin rai, an zo gab’ar da bata so a duk lamarin auren yaranta, gab’ar da za’a ce sai an ga ubansu sannan za’a yi maganar aure da su, ina ma zata iya da wallahi ta Mayewa Ayra gurbin Kabiru don bai cancanta ya zame mata uba ba idan su wa’dancan ta amince Ya yi wakilcin auren su Ayra fa? Shin ya cancanta ya zama waliyyinta a wurin aurenta? Ya cancanta ya amsa sunan mahaifinta? Zuciyarta ta dinga bugu tana jin kamar ta fito ta gayawa Hameeda duk abinda ake ciki, sai dai tana tsoro tana tsoron kada maganar auren ta rushe da tabbas sai ta fito ta ce da Hameeda Ayra bata da uban da Ya wuce ita kanta, itace Uwar Ayra sannan kuma ita ce ubanta.. ajiyar zuciyar da take yawan saukewa ne yasa gaban Hameeda Ya dinga fa’duwa ta fara hasasho tabbas akwai matsala shin mai aminiyarta take b’oye mata ne game da rayuwarta ta baya? Jiki a salub’e ta kama hannayen Amman ta matsa su sosai cikin sigar son kwantar mata da hankali ta ce “Me ke faruwa ne Talatu? Menene abinda kike son b’oye min ki sanar da ni komai muninsa ni mai rufa miki asiri ce.”

Amma ta zuba idanunta cikin na Ummeey tana jin kamar ta gaya mata wata zuciyar na kwab’arta don haka ta yi saurin sakin yak’en dole kafin ta ce “Rabuwar mu da Kabiru ba ‘a yi rabuwar da’di ba, mun rabu ne tsiya-tsiya kuma tsahon lokacin nan gaskiya ba zan ce ga inda za’a same shi ba, don haka ina ga kawai ba sai an kai maganar wajensa ba kin san ni, na sanki kuma kin san asalina kuma da aure na haifi Shu’aira ba da zina ba na amince Shu’aira ta auri Turaki na bashi auren ta halak malak.”

Ummeey ta saki ajiyar zuciya jin ba wata matsala bace gagaruma sai dai ta San ko giyar wake ta sha bata isa ta je ta ce da Abban Turaki a cire maganar uban Ayra a ‘d’aura aure kawai ta San lamari ne da ba zai yiwu ba musamman sanin sa a mutum mai kafaffen ra’ayi Wanda ba ya jin bari dole ne a nemo Kabiru ko kuma a samo wani mutum daga cikin danginsa ya maye gurbinsa, don haka ta mayar da kallonta kan Amma kafin ta ce “Samun Kabiru ba zai yi wuya ba, kamar yarda neman inda kike bai min wuya ba Talatu don haka zan koma can unguwarmu inda a can aka min kwatancen nan na tambayesu ko Sun San inda Kabiru yake..” Da sauri Amma ta girgiza Kai “Kada ki fara Hameeda, don har Abada ba zan amince Kabiru ya yi waliccin Ayra ba balle ya amsa sunansa a matsayin mahaifi da na yi haka gwara na hak’ura da aurar da Ayra na sakata a gaba na yi ta kallo, Abu ‘daya zan iya amincewa da shi, shima ba bisa son raina ba sai don bin dokar shari’a a je a samu wani daga dangin Kabiru ya ‘daura mata aure kamar yarda na yiwa sauran y’an Uwanta a can k’auyensu akwai Kamilu k’anin ubansu shi ya aurar da sauran y’an uwanta to itama Ayran bisa dole na amince ya zama waliyyinta.” Shiru Ummeey ta yi bayan gama Jin Amman, tana da abin cewa sai dai bata son ta tilastawa Amman wajen bata labarin da ta tabbata Jin sa ba mai da’di bane. Gaba ‘daya walwalar da ta tarar da aminiyarta ta a cikinta tuni ta yi k’aura daga fuskarta don haka ta fara k’ok’arin gajarta musu zaman. “Shikkenan, ba damuwa zan samu Mai gidan da wannan maganar na gaya masa suje can k’auyen Gayan a nemi Kamilun, Amma idan Sun je ta yaya za su gane kwatancen gidan da za su je?” Amma ta yi tsam da ranta don bata da numberr kowa daga dangin mijinta da sai ta ba su don haka ta saki ajiyar zuciya “Idan Sun je Garin Gaya a k’auyen Shagogo su tambayi gidan Sarkin K’ira Kamilu ba za su sha wahala ba za’a kai su.” Ta fa’da tana kawar da kai da jin takaicin ambata sunan garin da ta yi, don shi kansa garin bata buk’atar tuna shi balle ahalin cikinsa. Ummeey ta rubuta a waya ta yi saving don gudun mantuwa sannan ta mik’e tana k’walawa su Tayseer kira. Amma da bata son su cigaba da zama bata hana su tafiya ba, saboda yarda zuciyarta take a tunzire duk wasu abubuwa da suka shu’de suna k’ok’arin sabunta a zuciyarta. Har bakin k’ofa ta raka su kafin ta dawo ta zauna ta shiga zuzzurfan tunani, tsoronta ‘d’aya kada aje garin neman aure a binciko wancan abin takaicin da take dakon b’oyansa shekara da shekaru.. ta hau jijjiga kai cikin muryar kuka a hankali yarda ba za’a jita ba, duk da dama a cikin ‘daki take ta ce “Kaiconka Kabiru Allah Ya isa ba zan tab’a yafe maka ba, Har gaban abada kuwa..” zuwa lokacin bugun zuciyarta ya k’ara tsananta tana jin zuciyar na mata wani irin ciwo da nauyi sosai.





______________________

Tunda ya dawo daga Office Ya zube a kujerar da take balcony ‘din gidan. A hankali yake jin b’acin ran nasa na yawaita tun bayan da Abbansa Ya kira shi ya sanar da shi za’a nema masa auren da bai San da zamansa ba. Wato dai da gaske suke sai sun masa auren dole haka mana zai kira shi? Gaba ‘d’aya jijiyoyin kansa suka ‘d’aure ya dinga jin tunanin matarsa yana dawo masa cikin zuciya. Ita ka’dai ce macen da ya samu a budurwa duka sauran da ya aura fanko suke It means duka matan yanzu sai sun yi watsewarsu a titi suke aure a
Nasa tunanin fa kenan. “Ba abinda zai ha’dani da ita idan ta shigo ‘din ma, haka zata tattara kayanta ta tafi don ba ni na ce ta amince da auren mutumin da bata San shi ba bata San ya nake ba.Mace ‘d’aya nake ganin bayan mutuwar Matata zan sota na aureta tunda dama ita na fara so kafin k’addara ta ha’dani da Hibba… sai dai a ina zan lalubota ban san sunantaba kamanninta ne kawai suke zane a zuciyata. Ya lumshe ido yana jin yanayinsa yana canjawa a duk sanda ya tuno da kamanni da suffa ta waccan yarinyar.

Shigowar abokinsa da suke zama a gida ‘daya ne ya ankarar da shi tsawon lokacin da ya ‘d’auka a wajen, ko kafin ya yi saurin shigewa gida Mukhtar ya tarar da shi. “Tsaya mana Turaki, na san fa ka ganni ka ke k’ok’arin shigewa. Me ya faru ne two days bana ganinka. Ranar ma ina ta knocking ka rufe k’ofa.” Turaki a dole ya tsaya fuskarsa ba walwala sosai ya zuba masa ido don Mukhtar Akwai surutu yayinda Turaki magana bata cika damunsa ba. “Am too busy kwana biyun nan shi yasa.” Mukhtar ya jijjiga kai “Ai kuwa sarkin nacin naka ta zo nemanka Ya fi sau nawa, wai Turaki me yasa ba zaka hak’ura ka auri yarinyar nan ba.” Turaki Ya ‘dan matsa kansa a hankali ya furta “Shaheedah why? Ban san me zan wa yarinyar nan ta fita sabgata ba.” Mukhtar ya ja hannunsa “Let’s talk, ka San ba zan baka shawarar banza ba wallahi Shaheeda na Sanka sosai ka amince da aurenta ni ban ga aibunta ba.” “Ni na gani.” Turaki Ya fa’da cikin tafasar zuciya “Ragowar wanin zan aura? Sau nawa ina kamata da samari suna rungume da
Juna a hakan kake son na aureta ta zama uwar yara na? Ajiye maganarta a side a yanzu ma ni ba bu maganar aure a wajena ban sani ba ko idan na tsufa.” Mukhtar ya dinga dubansa yana mamakin furucinsa kafin ya jijjiga kai “To Allah ya kyauta, zan bawa Shaheedah hak’uri Allah Ya bata mafiyinka ta yi aurenta ta huta.” Ya ‘dan tab’e baki “Da ya fi mata sauk’i.” Mukhtar ya kawar da wancan zancen ta hanyar cewa “Hope kana shirin zuwa Nigeria na ga Christmas ta kusa. Gwara mu tattara mu je hutu k’asar mu ta gado.” Turaki ya sake runtse idanunsa zai so zuwa Nigeria Amma yana tsoron zuwa Ya ga y’ar da za’a mak’ala masa ya aura “Not now. Ka gaida mutanen Nigeria.” Daga haka ya shige gida. Ya bar Mukhtar yana binsa da kallo yana nazari anya abokin nasa ba aljannah bace ta aureshi? Sun da’de tare kuma zai iya shaidarsa ya yi rantsuwa akan cewa baya neman mata? To ko dai bai da lafiya? Sai ya tuna matarsa ya tuna tsananin soyayyar da suka sha kamar ba za’a Mutu ba, sai ga shi tashi guda mutuwa ta yi musu yankan k’auna, Amma shekarun ai da yawa Ya ci ace ya manta da ita? Ina Turaki bai manta da matarsa ba, ko da yaushe hotonta ne mak’ale kan screen ‘din wayarsa, System da komai ma kai har a zuciyarsa soyayyarta ke ‘dawainiya da
Shi, shi yasa duk macen da ya kalla sai ya ga bata burgeshi kamar uwar yaransa. Ita take dishashe masa y’an mata.. idan ya tuna yarda ya sameta a
Daren farko matsayin cikakkiyar mace sauran kuma matan nasa Ya same su fanko sai ya ji kimarta da darajarta suna sake hauhawa.



____________

Da nutsuwa Hameeda ta fara bawa mijinta cikakken address ‘din inda za’a samu Kamilu. “Ta yaya Babanta ya koma Kamilu bayan kin ce sunansa Kabiru?”
Tambayar da ya yi mata a bazata ita ta ka’da y’an hanjinta ta shiga In da In da. S. Turaki Ya zuba mata ido kamar yana son gano rashin gaskiya a tare da ita murya Babu wasa ya ce “Ina mahaifinta ko ya rasu ne?” Ta girgiza kai “Alkunya ce dai kawai ta fulani ya barwa k’aninsa a nemi auren a wajensa.” S. Turaki Ya girgiza kai “Shikkenan, za mu isa wajensu a cikin satin nan.” Ta gyara zamanta tana jin da’din da bai gano akwai wani abu da take b’oye masa ba “Amma na ce Abban Turaki za dai kasa Turaki yazo auren nan ko?” Ya ‘dan dubeta ka’dan sai kuma ya ce “In sha Allah, idan yana da buk’atar hakan.”
TAKAICIN UBA…….


Na

Nazeefah Sabo Nashe.

08033748387

Page 11




Haka aka yi kuwa Mahaifin Turaki da wasu daga cikin danginsa suka je Har k’auyen nemawa Turaki aure. Sun yi mamaki k’warai ganin mutumin da Ya zo amsar ku’din auren.

Da mutunci da kamala ya tarbesu, Ya kuma amshi ku’din ba tare da Ya sanar da su mahaifin Ayran yana nan da rai ba. A tunaninsa Mahaifin Ayran ne Ya turo su nan wajensa kasantuwar shi ba shi da lafiya. Haka nan aka tsayar da maganar biki sati biyar masu zuwa.

Don haka kashegari ya shirya takanas Ya taho Kano, don ya kawowa Kabiru ku’din auren y’ar tasa. Sanda Ya isa Gidan Kabirun yana kwance shi ka’dai ba matar gidan, balle Yaran gidan da kowa Ya kama gaban sa. A wannan karon tausayinsa Ya kama Kamilu sosai ya dinga tsinewa Matar tasa da yaran nasa. Kabirun yana hawaye daga gefen idonsa Kamilu Ya mik’ar da shi sosai ya zauna akan yagulalliyar katifarsa da ta sha jiki, Tabbas duniya a wannan karan ta juya masa baya…. Kamilu Ya dinga jinjina lamarin girman Ubangiji ko shi da yake k’auye dai ya fi Kabiru wadata da jin da’din rayuwa.

Bayan Sun gaisa a tausashe Kamilu Ya tambayi jikin nasa? Kabiru jinjina kai kawai ya yi don ba zai iya cewa da sauk’i ba, domin Har ga Allah babu sauk’in. Ya dai ja bakinsa da ya ‘dan karkace ya yi shiru don maganar ma wahala take masa. Kamilu Ya zaro uwar ku’din da yake aljihunsa Ya zube a gabansa. Da mamaki Kabirun yake kallonsa kafin cikin karyayyan harshensa ya ce “Na Menene?” Shima Kamilun da mamaki yake kallonsa “Ban gane ba? Ba kai ka tura a kai min ku’din Autarka ba na aure?” Kabiru yana hawaye Ya girgiza kai Ina yaga wannan darajar da Talatu zata saka a kawo masa ku’din auren y’ay’ansa balle wannan da lamari mafi nuni da ko tunawa ba ya son yi ya afku kanta…… Ya ja hannunsa da k’yar ya goge zufar da take goshinsa ga k’walla da ta cika masa kwarmin ido. Ya kalli Kamilun cikin takaicin abin ya ce “Yaute aka kai maka Allah ya tanya alheri, Ban tani ba.” Tausayinsa ya kama Kamilu sosai a karo na farko tun bayan faruwar lamarin ya dafa shi cike da kulawa ya ce “Ka daina saka damuwa a ranka, In sha Allah wannan karan zan daidaitaka da y’ay’anka zan gaya musu ibtala’in cuta da ya sameka, na kuma sanar da su tarin nadamarka, idan an dace shikkenan. Lamarin ne da ciwo kuma na tabbata Har yanzu wannan tabon bai bar zuciyarsu ba. Sai ka toshe kunnuwanka daga duk abinda Talatu zata fa’da maka, ta cancanci ta gaya maka duk maganar da ta zo bakinta tabbas k cucesu ka zalincesu ka bar musu bak’in tabo mai wuyar gogewa musamman Na Auta.” Kabiru wannan karan kasa hak’urcewa zuciyar sa ya yi sai da ya saki kuka sosai Kamilu yana rarrashinsa. Shigowar matar gidan ce ta farkar da su daga zaman jigum jigum da suka yi kowa zuciyarsa ba da’di. Ta zube magananta a kansu kafin ta ja dogon tsaki tana kallon Kamilu da yake mayar da ku’di aljihu ya so ya yafitarwa Kabirun wani abu daga cikin ku’din amma ya san yana ba shi muguwar matarsa ce zata amfana don haka ta tura su aljihunsa yana muzurai don sam shima baya raga mata duk da ya san babu laifinta a rabuwar Kabiru da Iyalinsa.

Daga haka Ya mik’e ya yiwa Kabirun Sallama akan ya je ya samu Malam Hadi shi ya san gidan ya raka shi su kaiwa Talatu ku’din auren.


A bakin layi Ya tarar da Malam Hadin suka gaisa, sannan ya sanar da shi buk’atarsa ta son ya raka shi gidan Talatu. Malam Hadi cikin fa’duwar gaba ya dubeshi “Wa? Ni da zuwa wanann gidan ai sai dai idan gawata aka kai…..” nan ya dinga ba shi labarin abinda ya faru a ranar Kamilu ya dinga dariya har da rik’e ciki “Sun yi maganinka kenan, ai shikkenan mu je na tsari Adaidaita sahu ka masa kwatance yarda zai gane sai ya kai ni.” “Wannan kuwa” Malam Hadi ya fa’da yana murza gemu.


Shi kansa Kamilu sanda aka nuna masa gidan aka ce nan ne gidan Talatu sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login