Showing 30001 words to 33000 words out of 132090 words
Chapter 11 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt
dukiyoyin Iyayensu da shanunsu da kuma iyayen nasu kan su,ashe sun da’de suna bibibyarsu ba tare da saninsu ba, sai a wannan lokacin da suka far musu cikin dare. Ayarine na fulani masu yawan gaske sai dai Sam basu da Makamin kare kai, dalilin a wancan lokacin k’asa lafiya k’alau take ba’a fiya samun irin wa’dannan matsalolin ba. Matsala ‘d’aya ce da take addabar mutane inda ake zuwa a mamaye gari mutanen ciki wa’danda suka yi saura kuma a kame su a matsayin bayi, a je a siyar a masarautu ko a siyarwa manyan y’an kasuwa, wasu kuma su kan kaiwa iyalinsu su dinga musu bauta ko kuma su yi k’wark’wara da su.
Ganin yarda suka tunkari ayarin su Mahaifiyarta sai suma
Mutanensu na Fulani suka taso don kare kan su sai dai ba su da k’arfin wa’dannan jama’un. A wannan lokacin Innar Talatu ba zata wuce shekaru goma ba tana ji tana gani aka kashe iyayenta Yayyenta maza guda hu’du suka gudu. Ita da yake mace ce tana da rauni ganin mutuwar iyayenta sai ya sanyayar mata da gwiwa ta kasa tafiya ta durk’ushe wajen gawarwakinsu tana kuka mai tsima zuciya. A wannan lokacin ne mutanen suka Ankara da ita suka kuwa kamata suka na’deta da igiya kamar yarda ake wa bayin wancan lokacin suka ha’data da sauran mutanen da suka kama a wajen suka saka a wani Babban abu kamar amalanke suka tafi da su, bayan Sun kwashe tulin dukiyoyin iyayensu da shanunsu.
Ba mai magana har suka kawo kasuwar da ake cinikin bayi. A ranar da suka iso shi kuma Malamijo kakana ya shigo kasuwar don sarar bayi ya kai gidajen masarautu kamar yarda suka Saba.
Su biyar ya siya ciki kuwa har da Mahaifyar Talatu. Haka ya ‘d’unguma da su wani k’auye a kano tun kafin Gaya ta zama gari tana daji a sannan anan yake zama shi da almajiransa koyarwa yake yi sai kuma cinikin bayi. Yana zaune a garin shagogo tun kafin kafuwar wannan garin tun mutanen cikinsa ba su fi a k’irga ba.
Tunda ‘dansa ya k’yalla Ya ga Innarta da ake kira Danejo ya kafewa mahaifinsa a kan shi yana son Innarta ta kada a siyar da ita. Malamijo ya san shi da son mata don haka ya zabga masa harara ya na fa’din “Ina zaka kai mata uku Moddi?” Ya fa’da masa da yarensu na fulde. Amma Ya ce shi ya ji ya gani yana son Inna ta. Haka Malamijo Ya hak’ura ya bar Mahaifiyarta Danejo a gidan sa da zummar idan damuna ta fa’di za’a yi aurensu da Moddi.” Wannan shine mafarin shigarsu duk wata masifa a rayuwa saboda halin da suka shiga sun gwammace ace can gidan sarautar aka kai Mahaifiyarta. Duk da a lokacin su ayarin da aka ha’do da Danejo murna suke mata suna cewa ta rabauta daga bauta. Ashe da rayuwar da zata shiga gwara mata rayuwar bauta.
Tana ji tana gani ranar Malamijo ya saka sauran y’an uwanta a gaba da zummar zai kai su masarautar Kano a siyar idan an siyesu shikkenan idan kuma ba’a siyesu ba sai ya k’ara gaba da su.
Mahaifiyarta sam bata samu soyayyar surukartaba ba don k’iri-k’iri ta dinga nuna rashin son auren, Amma da yake Malamijo mutum ne tsayayye mai kafewa a kan ra’ayinsa sai ya dage da cewa sai an yi auren. Haka aka ‘daura auren bayan fa’duwar damuna ta kuma tare a gidan Moddi b’angare ‘d’aya da sauran matansa da suke ji tamkar su saka wuk’a su kasheta saboda tsana.
Innar ta ta ce ta sha matuk’ar wahalar zaman aure gidan don duk wasu aiki na su sai da ta zama ita take yi, wahalar da take sha ta tabbata ko bayin da aka tafi da su bai zama lallai su sha ta ba. Ita ce surfe nik’a daka a turmi sannan ita zata yi yo musu itace ta ‘dora Sanwa bayan ta ‘debo ruwa a can wani rafi mai nisan gaske. Duk ta k’are ta koma’de dama ita ba jikin arziki ba. Duk tsananin kyanta mai fisgar hankali sai ya fara dishewa dalilin bata samun kula da kanta kullum a cikin aikin wahala take. Kamanninta sak da Ayra don gaba ‘d’aya Ayra ita ta ‘dauko idan ta kalli Ayra sai ta ga kamar ita take kallo.
Sau biyar tana samun ciki cikin yana b’arewa duk da soyayyarta da samun ‘da haka ta zubawa sarautar Allah ido tana tunanin ba mamaki bata da rabon ganin k’wanta a duniya. Burinta ya ta’allak’a da ta samu haihuwa don bata da mai ‘debe mata kewa sai maigidanta shi kuma bai isa ya shigo wajen ta ba ko ta masa magana dole sai ranar girkinta, don haka sai ta kwana hu’du ba tayi magana da kowa ba don ko ta yi maganar ma Babu mai kulata tsana da tsangwama suke nuna mata muraran.
A kan Talatu haihuwa ta fara tsaya mata, bayan ta burne yaranta biyar wasu sai ta fara saka rai da su sai su mutu, wasu kuma tun kafin su zo duniya suke mutuwa a ciki. Idan ta tashi haihuwa ita ka’dai take haihuwa a ‘daki Babu mai taimakonta ga shi ita ba dangi ba, ita zata yiwa Kanta wankan jego ta gyara y’ar sai an ci mugun sa’a ne za su shigo mata barka, dangin Mijinta ma ba sonta suke ba balle ta saka ran samun salama a wajensu.
Sanda ta samu ciki ne uban mijinta ya dage da mata rubuta da addu’oi cikin ikon Allah sai cikin ya tsaya ta kuma haifi jaririyar ta lafiya mai cikakken lafiya.
Bayan wata guda da haihuwar yarinyar da ta sakawa Bo’ddo Malamijo ya amsa kiran Ubangiji daga nan ta San cewa ta rasa duk wani gata, tunda Ubangiji ya amshi surikin nata mai tsaya mata tsayin daka, musamman ta fannin matarsa da ta zama Uwar mijinta.
Bo’ddo ta taso da kazar-kazar ga farin jini wajen jama’a, sai dai zuwa lokaci k’ank’ani sai farin jinin nata ya kau, don duk inda ta shiga sai kyara da hantara kamar wacce aka yiwa asiri. Don dole ta koma ba inda nake zama ta ji da’di sai wajen Mahaifiyarta kullum tana jikinta a rakub’e itace abokiyar hirarta da ita ka’dai ta Saba don mahaifinta ma sai taga kamar baya sonta ko kallonta baya yi, sau tari idan ta matsa jikinsa sai ya hantareta har ta sakawa kanta cewa Mahaifiyartace ka’dai take k’aunarta a duniya.
Sanda take shekara bakwai a lokacin aka fara ginin gidan su Hameeda, da aka tabbatar ‘dan hakimin garin ne da ya je k’asar Saudiya karatu shine zai dawo aka dinga zuwa kallo dalilin ginin bulon suminti ake ginawa ba na k’asa ba kamar yarda aka Saba a duk sassan garin, don haka gidan ya ‘dauki hankalin jama’a tun kafin ma mamallaka gidan su bayyana kansu.
Sanda aka gama ginin aka zuba fitilu sai gida ya zama abin kallo, kullum k’ofar gidansu Hameeda a cike yake da jama’a, kowa burinsa na Shafa fentin da aka ranga’da wa gidan yake. Da fitilu da suke amfani da engine generator don ko gidan mai garin babu su, dalilin ba’a Kai wuta garin ba a wancan lokacin.
Wata rana suna zaune kawai sai suka dinga juyo hayaniya a waje ana ‘dan hakimi ya dawo amma ya dawo da mata balarabiya Har da y’a. Jin haka yasa ta fita a guje don itama ta je ta ganewa idonta. Ai kuwa dai sai ga shi ta gano Hameeda fara sol da ita, Hameedar da ta zame mata tsanin farin cikinta kafin rabuwarsu ta hangota a jikin Babarta a shekaru zata iya bata shekara biyu don dai ita Hameeda tana da girman jiki ne, yara suka dinga kallonta ana janta ganin yarda aka Mata kwalliya da riga da wando Har da wata hula mai fa’di mai kare rana. Tana kuka babanta ya ‘dauketa ya sanyata a kafa’da Ya kaita gida, don da alama tsoron mutanen take ji. Ta bata sha’awa lokacin sosai ta koma gida tana bawa Inna labari, tana murmushi ta Shafa kanta ta ce “Ke ma Bo’d’do babanki ai yana son ki.” Girgiza Kai ta yi da sauri tana ‘d’an zubar da k’walla don a lokacin ta fara sanin ciwon kanta. Ta ce “Baya so na Innah, kowa ma na duniya baya so na ke ka’dai kike so na shi yasa nake burin na girma da ke na samu ku’di don ki huta, na kuma nemo Miki y’an uwan ki” Ta girgiza Kai “Kayya Bo’ddo na fitar da rai da ganin dangina, ta ina zan gan su bayan duk kowa tarwatsewa ya yi, ke dai ina son ki dage ki yi karatun muhammadiya ki kuma koyi sana’a saboda ko bayan Raina kada ki zama abin tausayi.” Ta saka kanta a jikinta tana kuka “Inna ba zaki Mutu ba, in sha Allah sai na tsufa.” Sai taga ta yi murmushi ta girgiza Kai “Mutuwa ai dole ce Bo’ddo, tana kan kowa, sannan kada ki sake cewa kowa na duniya baya son ki, yaushe kika zagaye duniyar balle ki sani? Nan dai na kusa da ke ba sa son ki, Allah zai kawo mai son ki kin ji ko bayan Raina…” kalma kenan mafi muni da ta tsani ta ji ta a bakin Inna, sai kawai ta kifa kanta a cinyarta ta rufe ido, so take ta bar maganar, sai ta jawo mataji ta shiga kunce mata kitso dama ita take mata kitso da komai da ya danganci mata Lalle da sauransu.
Da daddare suna raku’be a cikin ‘dan akurkin da za’a
Kira shi ‘dakinsu to akurki mana don na matan gidan duka ya yi ukun nasu. Moddibo da muke kira Baji ya shigo da sallama idanunsa a kanta, ya ‘dan yi tsaki “Ke kuwa Danejo baki da aikin yi sai ki saka y’a a gaba kina hira ko fulako babu.” Da sauri Inna jikinta na rawa ta tureta daga jikinta ta mik’e zaune “Ka yi hak’uri Moddi ban San da zuwanka ba.” Ta fa’da don har ga Allah bata San da zuwan nasa ba don ba ranar girkinta bace, to ko ranar girkin nata ne bai mayar da ita komai ba saboda an Zare masa son ta a zuciyarsa. Ya sake sakin tsaki “Ki shirya gobe ki je sabon gidan can na yaron Mai gari za ki fara musu aiki.” Da sauri Inna ta ‘daga kai kanta a k’asa don bata isa ko idanunsa ta kalla ba, ya sake rataya sandarsa ya fice da sauri.
Sai taga Inna ta lumshe ido ta ‘dan rik’e k’irjinta da yake matsa mata da ciwo a lokacin. Ta saki kakkaurar ajiyar zuciya.
Da sassafe haka ta tashi bayan gama aiyukan da yake gidansu ta tasa Bo’ddo a gaba ta tafi makarantar Allo, ita kuma ta tafi gidan yaron mai gari.
Wannan zuwa gidan su Hameeda da take yi ba k’aramin bak’in jini ya sake jawo mata ba, dalilin mahaifiyar Hameeda mutuniyar kirki ce, kuma tana taimakawa Inna sosai, wani lokacin har Kayan Hameeda take bayarwa a bawa Bo’ddo tunda aka je Da ita gidan sau ‘d’aya ta k’yalla ido ta ganta sai jininsu ya ha’du idan ma Inna bata je da ita gidansu ba sai ta saka an zo har gida an tafi da Bo’ddo ko ta saka a rakota.
Duk abinda Inna ta samo mutanen nan ta k’arfin tuwo suke k’waceshi su raba a tsakaninsu. Inna Sam bata damuwa kullum cewa take na rasa dangina ma balle abin duniya.
Ana haka Wata rana Inna ta tafi gidansu Hameeda, Bo’ddo kuma ta sawo Kai kenan zauren gidan su sai ta ji kamar ana ambatar sunan Inna don haka sai ta rab’e ta ji zancen da ake tunda ta ji ana ambatar danejo maganar Kulu da ake kira Inna wuro ita taji tana cewa “Wallahi Malam ya tabbatar min idan na burne layar nan a cikin ‘dakinta to sai buzunta don ciwo zata kwanta sosai har kwananta ya k’are.” Sai ta ji Sun yi dariya Inna Habi ta ji ta ce “Yanzu kin bisne kenan?” Ta yi shewa ta ce “Ai ba a bori da
Sanyin jiki..” jikin Bo’ddo na b’ari ta yi sallama ta shiga gidan, duk sai ta ga Sun zubo mata ido ba tare da Sun amsa sallamar ba. Gaba ‘daya a ru’de ta fa’da ‘dakinmu burinta ta gano inda ta binne abin kafin dawowar Inna, sai dai bulayin duniya ta rasa wajen ba inda bata tona ba, Amma babu labarin laya ba zancenta.
Tana k’ok’arin tone waje ‘daya da ya rage mata Inna ta zabga sallama ta shigo.. cak ta tsaya a
Bakin k’ofa tana k’are mata kallo “Bo’ddo! Me kike yi haka?) tana k’ok’arin tashi ta turata waje ta sako kai, Bo’ddo ta saka ihu ba ta San sanda ta ce “. “Kada ki shigo Inna za su kasheki” sai dai kafin ta rufe bakinta ta ga Inna ta dafe kanta sai kuma ta ga ta yi luuuu zata fa’di, da sauri ta k’arasa wajenta ta fa’do jikina tana wani irin mak’yark’yata….
Takaicin Uba.
Paid pages 15
Na
Nazeefah Sabo Nashe
Ta dafe kan Innar tata da taga tana rik’e wa tana fa’din Bo’ddo…. Sai dai duk abinda take son fa’da ya tokare tsaf a mak’oshinta, harshenta ya karye ta kasa furta koda kalmar ‘a’ sai ido data zubawa ‘diyartata cikin wani irin matsanancin hali take fitar da nishi da wani irin yawu a bakinta. Ganin furucin ba zai yiwu ba sai ta koma yiwa y’arta nuni da hannu irin maganar bebaye, Bo’ddo ta gane mai take nufi so take a kirawo mata mijinta Moddi don haka da sauri ta ajiye kan Innarta Akan matashi, ta fita a guje, ba tare da ta kula da lab’ewar da matan gidan suka yi ba a bakin k’ofar ‘dakinsu, fuskarsu ‘dauke da matsananciyar fara’a da alama burinsu ya cika, burin da suka da’de suna Neman hanyar kammaluwarsa sai yau Allah ya yi, Sun tsani Danejo Sun tsani su bu’di ido su ganta a cikin gidan tun a farkon fari da Moddi ya nuna mata wani irin so, su suka jirkitar da soyayyarta a zuciyar Moddi zuwa matsananciyar k’iyayyar da shi Kansa ba zai iya fasalta ta ba, sau tari idan ya ganta a cikin wahala ya kan ji wani sashe na
Zuciyarsa yana tausaya mata, sai dai a duk yayin da ya yi nufin taimaka mata sai ya ji zuciyarsa ta kasa, sai ya ji kamar an yiwa gangar jikinsa dabaibayi. Ganin hak’arsu ta kusa cimma ruwa sai kowacce ta shige bigirenta suna jiran su ji an fasa kukan Danejo ta Mutu.
A can gona ta tarar da Moddin, tana hakin gudun da ta sha ta zube a gabansa, yanayinta ka’dai ya duba ya ji wata irin fa’duwar gaba ta sameshi da sauri ya ce “Ke Bo’ddo k’alau kuwa?” Hanyar gida ta nuna masa tana haki da k’yar kalmomin Inna…’ suka fito daga bakinta sai kawai ta sake juyawa a guje, shima bai yi k’asa a gwiba ya bi sahunta da sauri yana addu’ar kada Allah ya tabbatar da hasashensa na rasuwar Danejo, me zai ce da Allah? Akan irin wahalhalun da suka bata, baya so Danejo ta mutu bai nemi gafararta ba, ya San ya gallaza mata gallazawa mafi muni… da kwatantuwa.
Ko kafin ya je gida tuni ya jik’e sharkaf da gumi, zuciyarsa tana wani irin duka da fisga kamar zata bar k’irjinsa. Isar sa k’ofar ‘d’akin Danejon ya yi daidai da lokacin da ta amsa kiran Ubangiji cikin ambatar sunan Allah, da Allah ya bata dama ta fisgo shi da k’yar a harshenta. Shikkenan ji kake ‘dif Danejo ta wuce kushewa inda ba a dawowa.
Duk da yarintarta bai hanata gane ta rasa Innanta ba har abada, wani irin kuka zata yi babu! Gani take kuka ma rahma ne tunda ga shi tana son ta yi ta kasa, wani irin k’unci take ji a ranta tana kallon Gawar Innanta da Moddi ya zubawa ido, yana hawaye ji yake da yana da iko da ya dawo da ran Innajin ya gyara kuskuren da ya aikata sai dai ba dama…
Shigowar Innawuro cikin ‘dakin ya tunatar da Bo’ddo waccen maganar da ta ji suna yi, da sauri ta mik’e idanunta a warwaje tana duban Innawuron tana fa’din ta kasheta… wallahi su suka kashe min Inna su suka bisne wani Abu a cikin ‘dakin nan.. Moddi ne ya jawota jikinsa a tunaninsa zafin mutuwa ne yake Neman zautar mata da k’wak’walwa “Ki yi shiru Bo’ddo..” ya fa’da yana kallon Inna wuro cikin tsananin firgita da kallon da take wa Bo’ddo sai Kuma kamar an tsikareta ta
Mik’e ta fice daga ‘d’akin. Bo’ddo ta sake binta da
Kallo tana tunani cikin ranta.
Shigowar Hameeda da mahaifiyarta ne yasa kukan da bata shirya yinsa ba ya fito mata, Mahaifiyar Hameeda ta jata jikinta cikin tausayawa ta dinga buga bayanta tana mata nasiha mai ratsa zuciya. Haka tana ji tana gani aka fita da mahaifiyarta don kaita kushewa shikkenan Sun yi sallama da Inna ba zata sake ganin Inna ba.. hakan yasa kukan ya sake kece mata…
⭐️⭐️
Watannin da suka biyo baya, masu muni ne a wajenta, watannin da ba zata taba’ mantawa da su ba cikin tarihin rayuwarta, sai yanzu ta san menene maraici? A lokacin ta San kalmar da ake fa’da ga Wanda ya rasa iyaye wato sai hak’uri. Tabbas ta yarda sai hak’urin domin bata da sukunin zuciya ko ka’dan zuciyarta ta zama a k’untace sau tari ta kan ji wani abu ya tokare k’irjinta.
Bata da kowa bata da komai Kowa ya juya mata baya, babu mai kallonta da idon rahma ta ji sanyi, ita take kula da kanta sannan aikin da mahaifiyar ta take yi kacokam ya dawo kanta, ba su duba k’ank’antar shekarunta ba, ba su duba rauninta ba duk aikin da suka ga dama shi suke bata.
Mahaifiyar Hameeda jigo ce a rayuwarta, matar da ba zata tab’a mantawa da ita ba, ita ta Maye mata wani gurbi daga guraben da Innarta ta bari, sau tari tana bak’i in cikin yarda Bo’ddon ta lalace, har kaya take bata Amma a banza don ba zasu barta ta mora ba. Yaransu masu ido da kwalli suke bawa.
Da kanta ta yi tattaki ta je Har gida da zummar ta karb’i