Showing 69001 words to 72000 words out of 132090 words

Chapter 24 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt

take k’waron ya fita daga jikinta shi kuwa yana tsaye yana k’are mata kallo, cikin dauriya da dake dariyar da take son kufce masa. Yayi folding hannayensa a k’irji yana kallon yarda take ihu, sai da ya ga abin nata ba na k’are bane gudun kada ta tara masa mutane sai ya yi tsaki, ya damk’eta da sauri yana saka hannayensa kan dukiyar fulaninta don son zaro k’waron da shige mata riga. Cak ta ji numfashinta na neman ‘d’aukewa bayan jin saukar tattausan hannunta a dukiyar fulaninta, shi kansa sai da ya yi azamar runtse ido lokaci guda kuma ya rik’e numfashinsa da yake k’ok’arin kufce masa jin wani yanayi da ya ritso gangar jikinsa tun daga yatsun k’afarsa har zuwa kwanyar kansa. Da azama ya janye gangar jikinsa daga rik’on da ya yi mata wanda ya janyo gamayyar k’irjinsu. Ya zabga tsaki yana fa’din “Matsoraciya!” Ya ‘dau plate ‘din da ya shak’e da abincin ya zaga ta gefenta ya wuce yana kallon yarda gaba ‘d’aya ta takure waje ‘daya kamar wacce za’a ce kyat ta gudu. Bayansa ta bi da kallo tana lumshe ido ita ka’dai ta san yanayin da ta ruski kanta a sanda ta ji hannunsa a jikinta abu ne da bata tab’a jin sa ba, yanayi ne da ba zata iya fasalta shi ba ta dinga jan ajiyar zuciya kafin ta bu’de fridge ta ‘d’au robar ruwan swan mai sanyi ta kafa a bakinta cikin wawuyar kwankwa’da ta shanye shi tas, da burin abinda take jin ya k’aurace mata, sai dai ina kamar sake rura wutar abin ta yi, cikin wata irin murya ta furta ‘Ya salam!” Kafin ta ja k’afafunta ta fice daga kitchen ‘din da kasalar jiki. Tana fita idanunsu suka gauraya cikin na juna yana zaune a dinning ya tasa plate ‘din a gaba, duk da soyayyarsa da abincin sai ya ji abincin gaba ‘d’aya ya fice masa a rai, abinda yake so yake muradi ya fi gaban abincin, ya bi bayanta da kallo yana sake sakin ajiyar zuciya ganin yarda komai na jikinta yake shaking kamar da gayya ma take aikata komai.


Ita ‘din ma kwanciya ta yi akan gado ta kifa cikinta kan filo duk wani yanayi da ta tabbatar na sha’awa ne yana amsa kuwwa a jikinta, abinda bata tab’a ji ba, tana da feeling ko a gida amma bata tab’a wannan mahaukacin feeling ‘din ba. Ta dinga damk’ar filon tana jin kamar ta je ta kai masa kanta. Sai dai ina! Ba yanzu ba bata shirya fuskantar wulak’ancinsaba.


Da k’yar ya tura abincin, amma loma biyar ya yi ya ji abincin ya gundireshi, shima ta tatan ya yi ya b’alle murfin ruwan ya kafa a bakinsa, bai kuma dire ba sai da ya shanye shi tas, sannan ya mik’e a kasalance yana ture plate ‘din abincin kamar shi ya masa laifi. Ya haye saman gidan inda anan part ‘dinsa guda yake.

Kai tsaye ya shige toilet ‘dinsa ya sakarwa kansa ruwan sanyi yana tunanin ya zama dole ya yi nisa da yarinyar nan idan ba so yake ya zubarwa da kansa mutunci ba, duk da cika bakin da ya yi.


Har ya saka pyjamas ya kwanta barci duk da ba barcin yake ci ba, amma a halin da ake ciki gwara kwanciyar shi ya fi alheri, ya kuma zama dole a gobe ya fara shirin barin k’asar nan kafin ya kunyata kansa a gabanta. Don ya tabbatar duk ranar da ya kai kansa gareta ranar sai ya sha gori a wajenta. Barcin yake son yi ta k’arfin tsiya sai dai idanunsa suka ce ba su san wannan ba, surar Ayra kawai suke sake hasasho masa da tudun kayan fulaninta faffa’dan k’ugu da tsukakken cikinta kamar na y’ar tsanar roba, shi bai tab’a sanin akwai mata a zahiri masu irin suffar ta ba, sai yanzu da ya yi katari da ita, ya zata ko akwai su sai dai irin masu shiga gasar sarauniyar kyau wanda kai tsaye an san surgery ake wa wasu da yawa daga cikinsu, wasu kuma tsabar workout ne yayinda wasu kuma supplement suke sha. Ya dinga duba hannun nasa wanda ya yi aikin cire mata k’waro yana tunanin ina ma hannun ya dawwama yana jin lallausan kayan fulaninta. Ya da’de a yanayin da ya kira daren dare mai wahala a wajensa don bai tab’a shiga yanayi kwatankwacin wannan ba, bai yi aune ba yana duba agogo ya ga lokaci ya ja sosai ya saki tsaki ha’de da mik’ewa ya fara laluben maganin da yake sha ya samu barci.


Ita ‘din ma hakan take a wajenta koma fiye da shi, don ita bata san yarda zata yi ta yi controlling kanta ba, abu ne Sabo a wajenta da ta rasa ya zata yi kuka ma kawai ta saka tana ja masa Allah ya isa, ga shi har a lokacin bata daina jin waiwayin hannunsa a kan dukiyar fulaninta ba abin dai kamar aikin sihiri. Sai da ta dinga addu’a ta kuma mik’e da k’yar ta shiga ta yi wanka ha’de da alwala ta zo ta fara sallah sannan ta samu komai ya lafa mata amma tabbas ta ji a jikinta.



____________


Da safe da k’yar ta bu’de nauyayyun idanunta tana sauke su a kan agogon da yake ‘dakin. Da sauri ta mik’e daga gadon da addu’ar farka wa daga barci a bakinta. Ta zuro k’afafunta da azama jin yarda cikinta yake karta da alamar ulcer tana son ta tashi ta kuma tabbata yunwar jiya ce. Brush kawai ta samu ta yi ta zura zumbulelen hijabinta don ba zata sake saken mutumin nan ya sake ganinta ba hijabi ba. Shiru falon ba kowa da alama shima bai tashi ba. Ta bi plate ‘din abincinsa da kallo wanda ya bari tun jiya a wajen ta d’an saki guntun tsaki dole nema kafin barinta gidan nan ta samo y’ar aiki don ita bata son k’azanta aikin gidan kuma ya mata yawa ita ka’dai. Fresh Milk ta samo ta sha cikin cup kafin ta yi wanka ta samu ta girka wani abin mai sauk’i ta ci. Sai da ta gyara falon tsaf da kitchen ‘din don su ka’dai ne suka yi k’ura sannan ta shiga wanka. Tsaf ta shirya cikin wata Moroccan wear mara nauyi sosai ta kawo gogaggen hijabinta da ya rufe mata jikinta ta saka sannan ta fita zuwa kitchen.

Sanda ta fito falo ta tabbatar yana wajen, don yarda k’amshin turarensa ya mamaye falon. Shi ‘din ma nata turaren ya sanar da shi zuwanta sai dai bai ‘dago ya kalleta ba don ya lura kallon nata shi yake haddasa masa tashin hankali da rashin nutsuwa ya kuma ji kamar magana’disu yana jansa zuwa gareta. Ta gefensa ta wuce ta shige kitchen ‘din ba tare da ta masa magana ba. “Idan akwai abinda kike buk’ata wanda za’a siyo miki ki rubuta a takarda zan je shopping don jibi zan bar k’asar nan.” Cak ta tsaya hannayenta a kan handle ‘din k’ofar kitchen ‘din jin maganarsa kamar daga sama. Kamar wacce aka yiwa umarni kuma sai ta juyo ta sauke idanunta a kanta “Amma dai ba da aurena za ka bar k’asar nan ba ko?” Sai a lokacin ya ‘dago ya zuba mata idanunsa da suke tabbatar da yanayin da ya kwana, da ace ita mai ganewa ce tsaf zata hango tsumammiyar soyayyarta mai caku’de da sha’awarta a cikin idanuwansa, sai dai da yake ba sani ta yi ba, don ba soyayyar ta tab’a ba sam bata gane ba, ya da’de yana binta da kallo kafin ya saki dogon tsaki ya ce “Ki shirya anjima mu je ki maimaita wannan maganar a gaban Ummeey don ita ta auro min ke, ba mamaki idan ta ji furucinki ta tabbatar ba kya son auren ta saka na sake ki na fi kowa burin hakan.” Ya fa’da yana fighting da zuciyarsa mai k’ok’arin k’aryata kalamansa. A zafafe ta ce “Idan ka yi niyyar saki na Ai ba sai Ummeey ta sani ba, tunda ba ta da hurumin sakin aurena kai ne mai wannan hurumin.” “Kin kuma taki rashin sa’a bana k’etare Umarnin mahaifiyata. Kin gane ai na San muhimmancinta don haka duk munin abu Idan ta ce na yi nake aikata shi ko da hakan zai zame min illa a rayuwata, ko da zan dawwama da bak’in cikin hakan. Idan kin shirya sai mu je ki mata bayani nima kin hutassheni.” Ya fa’da yana ka’da key ‘din hannunsa ya fice ya barta a tsaye tana jin wani turnik’in b’acin ran kalamansa da gaske ya sake hura wutar bak’in cikin da yake zuciyarta. Ta rintse ido tana fa’din “Allah ya kai mu anjimar zan tabbatar maka ba ni da kunya zan bika wajen nata na kuma fa’da ba na son ka sai me?”





_______

Kafin ya dawo tsaf ta shirya cikin wani zafafen Hkg lace da ya ji bu’da’dden ‘dinki Half boubou da siket, duka a cikin irin ‘d’inke-‘dinkenta na gida da aka mata don ta k’i yarda ko ka’dan ta tab’a masa kayan lefe. Tsaf ta fito lace ‘din ya sake haska fatarta duk da ba fara bace tas, ta kafa ‘daurin ta ture ka ga tsiya sannan ta baza gashinta a saman kafa’darta ta ajiye matching bag ‘d’inta kusa sa gyalenta red maha’din lace ‘din nata. K’amshi kawai take zubawa ta koma falo ta kame kan kujera tana jiran ta ga ta yarda zai shigo don da gaske ta yi shirin zuwa sanar da Ummeeyn a raba auren nasu don kuwa ba taga alamar duk wasu plans nata za su yi tasiri a kansa ba.


Tsawon nawa guda cur ta zauna a falon kafin ya shigo falon yana ‘dora idanunsa a kanta, duk da yarda gabansa ya tsananta bugu bai nuna hakan a saman fuskarsa ba, ya shanye a ransa yana ha’de fuskarsa lokaci guda a zahirance ya kawar da kansa a bad’inance kuwa sake k’issamata matsanancin kyanta yake sai kace aljanna nema kike tilas sai kin tarwatsa min zuciya. Ya yi furucin a zuciyarsa yana harararta k’asa k’asa “Allah yasa ba ni kika yiwa wannan kwalliyar ba?” Da sauri ta ‘dago itama tana kallonsa kafin ta ‘d’auke kai cikin zafin rai ta ce “A wane dalilin zan maka kwalliya?” “A dalilin kina son siye zuciyata” ta sake tunzira da kalamansa sai ta hau furzar da huci kafin ta ce “Kada Allah ya nuna min ranar da zan yi wani abu don kai.” Ya ji zafin furucinta amma sai ya shanye ta hanyar yin k’wafa ya kama k’arfen staircase ‘din da zai kai shi sama yana fa’din “Sai dai kar a kuma.” Ta yi saroro tana kallonsa kafin ta ji takaicin kanta ya kamata me ya kaita ma yin kwalliyar. Hawaye ta ji yana son zubo mata saboda yarda ta ji ta muzanta da kalamansa sai dai ta shanye tana cizan leb’enta “Komai ma yau zai zo k’arshe ka yi da wata ba Ayra ba.”


Ya da’de kafin ya sauko k’asan idanunsa a kanta ya fita ba tare da ya ce mata komai ba, duk da ya san jiransa take su fita. Da sauri ta mik’e ta bi bayansa don dama ba motarsa zata shiga ba a tata Motar zata bi bayansa don bata san gidan Ummeeeyn ba.


Mamaki ne ya kusa kashe shi a tsaye ganin yarda ta shiga motarta ta tayar cikin zafin nama, wato ‘dan iska ta mayar da shi da ya zauna yana jiranta. Ya ja k’wafa yana gyara sit ‘dinsa ya kwanta abinsa cikin motar idan ta san wata Ai bata san wata ba, idan ta san hanya sai ta kai kanta. Ayra ganin abinda ya yi sai itama ta saki murmushin a cikin tata motar ta mayar da sit baya ta yi kwanciyarta tana fa’din “Daidai nake da kai zamaninka.” Tsawon mintuna talatin suna zaune a hakan ba wanda ya yi k’ok’arin yiwa ‘dan uwansa magana. Ganin hankalin masu hidimar gidan yana neman dawo kansu sai ya saki ajiyar zuciya ya yi tsaki kawai ya fita daga motar yana fa’din “Ba zaki jawo min raini ba shashashar yarinya.” Cikin takun isa da gadara ya isa wajen motarta a zafafe ya bu’de murfin motar b’arin driver ‘din ya jawota da k’arfin gaske har tana shirin samun makwanci a k’irjinsa sai ta yi saurin ja ta tsaya tana masa kallon hadarin kaji “Menene haka?” “Ke zan tambaya menene haka? Kina son jawo ma kan ki raini ne wajen mutanen can?” Ya fa’da yana nuna mata masu gadi da suke ‘dan kallonsu k’asa-k’asa “Idan ke kin shirya karb’ar raini ni ban shirya ba, so that ki nutsu ko don ki siyawa kan ki respect ba don Turaki ba.” Ya yi furucin k’asa-k’asa idanunsa cikin nata kuma har a lokacin hannayensu sark’afe da juna bai saki ba kamar wasu masu kallon soyayya duk wanda ya gansu a lokacin abinda zai kawo wa ransa kenan, ma’aikatan kuwa murmushi suke saki k’asa-k’asa saboda yarda abin ya musu kyan gani. Hannunsa rik’e da nata har ya isa wajen motarsa ya tura ta a mazaunin driver sai sannan ya saki tsaki yana harararta k’asa k’asa ganin yarda take k’ok’arin janye hannunta tun kafin ya saki “Sai kace wani abin arziki ne a hannun naki, hannun da ya gama shan ruk’o gurin kowane k’ato.” Ya fa’da yana k’ok’arin tayar da motar “Hannayen garadan sun fiye min naka masu kama da na mata.” Cak ya tsaya daga k’ok’arin tayar da motar da yake yi. “Ba za ki daina suffanta ni da mata ba ko? So kike sai na bayyana miki b’acin raina ta hanyar da zaki banbancin Turaki da duk namijin da ya tab’a kusantar ki ko?” Ya ciji leb’ensa “Banda bana son ratsa gonar da wasu suka tab’a shuka yau da kin banbance tazarar da ke tsakanin sama da k’asa ina tabbatar miki akwai banbanci mai nisan gaske ki kiyaye harshenki.” Ya yi furucin in a serious tone fuskarsa a ha’de da alama da gaske yana jin zafin ha’da shi da jinsinta da take. Har suka je bai sake magana ba driving ‘din da yake kansa ya san ransa a matuk’ar b’ace yake, suna tsayawa ya danna lock ba tare da ya kalleta ba ya ce “Ina tabbatar miki ki san hanyar da kika bi Ummeey ta amince na sake ki shine kwanciyar hankalinki idan ba haka ba…. Mhmm Wallahi zama gidan Turaki zai zame miki zaman kabari a matakin farko.” Ya fa’da yana lumshe tsumammun idanunsa “Ruwanki ne kina shiga ki k’unduma min zagi a gabanta idan ta yi magana ki bayyana rashin kunyarki k’iri k’iri ta hanyar zaginta itama ina tabbatar miki ko gware kuka yi da ita kuka zo duniya k’arewar soyayya sai ta saka na sake ki, shawara na baki kyauta.” Ya fa’da yana dukan sitiyari.




(A min afuwa sakamakon wa’dannan kwanaki da suka riskemu In sha Allah daga wannnan posting ‘din zan k’ara posting ‘d’aya sai kuma Allah ya kai mu bayan sallah, kowa ya san girman wa’dannan gwala Gwalan kwanakin da suka rusko mu, bai kamata bawa ya shagala da duniya ba bai rub’anya aikin da zai samu dacewa ranar gobe k’iyama ba, karatun novel ba namu bane Karatun k’ur’ani shine abinda ya kamace mu a wa’dannan ranaku don haka y’ar uwa ina tunatar da ke da barin shagala da duniya mu ribaci kwanakin mu ta hanyar rub’anya nafilfili da karatun alk’ur’ani ya fiye mana karatun novel dafatan za ku fahimce ni nagode k’warai daga gobe sai bayan sallah In sha Allah.

Tafiyar mai nisan Zango ce Kada ku damu In sha Allah za mu cimma ga ci. Jikar Nashe ta ku ce Ayra da Turaki suke cewa Allah ya bamu ladan aikin da zamu yi a wannan ranakun yasa muna daga cikin bayin da za’a y’anta daga wuta. Astagfirullah min kulli zanbun. Love you all.❤️❤️)
Takaicin Uba…

Nazeefah Nashe✍🏽

35.

💔💔💔💔


Tsam ta yi da ranta tana bin sassan falon Ummeeyn da kallo, da jiran ta inda zata fito. Shi kuwa yana zaune daga gefe fuskarsa ba yabo ba fallasa. Sai ta ga ya mik’e yana murmushi ya isa inda hotonsa da Marigayiyar matarsa Hibba yake, wanda aka ‘dauke su ranar biki. Ya zubawa hoton ido yana ‘dan sakin murmushi kamar kuma wanda aka ingiza sai ya ciro hoton duk da girmansa ya iso wajen Ayra da shi. A fuskarta ya nuna mata hoton “Dubi ki ga Matata. First love ‘dina salihar mata ta gari, mai nagartattun halaye da tarbiyya wacce ta kawo min budurcinta har gida ba irin ki ba da ta zubar a waje…..” cak Ummeey da take shirin shigowa ta tsaya jin munanan kalamansa a kan Ayra, ita kanta kalaman sun yi girma a wajenta bai kuma kamata ace ya gayawa Ayran ba. Ta ‘dan runtse idonta cike da takaici a tunaninta tuni suka daidaita kan su, ashe akwai sauran rina a kaba. Duk wani annurinta ya ‘d’auke tsaf ta fara tunanin ko da gaske Ayra bata kai budurcinta ‘dakin Miji ba. Shikkenan ta tabbata Turaki ba zai so Ayra ba amma dole ta yiwa tufkar hanci. Ayra kuwa lumshe ido ta yi daga zaunen duk da ta ji ‘dacin kalamansa sai dai bata sake ta nuna masa ba ko a kan fuskarta ta saki ‘dan murmushi kafin ta furta “Kowa da k’addararsa ina tayaka jimami na rashin managarciyar mace da kuma auren ballagazar Mace a karo na biyar.” Ummeey ce ta saki gyaran murya hakan yasa da Sauri Turaki ya matsar da hoton daga fuskar Ayra Yana kallon Ummeeyn fuskarsa a ‘dan daburce. Bata nuna masa ko a fuska ta ji kalamansu ba illa murmushi da ta yi tana duban Ayra da ta mata wani kalar azababben kyau. “Daughter ya gida? Zo mana taso maza.” Ayra duk sai ta ji gwiwarta ta yi sanyi a sanyaye ta isa wajen Ummeeyn ta ‘dan rungumeta ka’dan, Ummeeyn ta hau shafa bayanta “Hope kina lafiya mhmn?” Ayra ta ‘d’aga kai tana ‘dan zamewa k’asa sosai don gaishe ta, haka kawai yau sai ta ga girma da mutuncin Matar kamar ba zata iya fa’dar abinda ta zo da niyyar fa’da mata ba, kunya sosai ta rufeta. Ummeey ta ja hannunta ta zaunar da ita a gefenta tana duban Amin Turaki da yake tsaye ya zube hannayensa a aljihu yana kallonsu k’asa-k’asa. “Kai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login