Showing 120001 words to 123000 words out of 132090 words

Chapter 41 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt

ce ta shiga zubowa Ayra ta sake ware ido tana kallon Address ‘din da Shaheeda ta turo Abuja Gwarimfa……. “Ke! Wa yace ki tab’a min waya?” Shi ya dawo da ita daga suman wuncin gadin da ta tafi, ta ware ido tana kallonsa kafin ta ji saukar ruwa masu ‘dumi a kumatunta wanda ba ta raba ‘daya biyu hawaye ne. “Da gaske aure za ka yi Turaki?” Ya ‘dauke kai kamar bai jita ba, har ta furta ran zai amsa sai kuma ta ji muryarsa a sama yana cewa “Ko za ki hana?”



𝔍𝖎𝖐𝖆𝖗 𝕹𝖆𝖘𝖍𝖊✍️
Takaicin Uba…..


60.


Ya cigaba da b’alle mab’allan rigarsa yana hango fuskarta ta mudubi yarda kalamansa suka saka ta firgita kamar ta tsala ido. Bai bi ta kanta ba don da gaske ta ba shi haushi ya d’auke key ‘din motarsa da wayoyinsa yana zuba mata ido murya a cunkushe ya ce “Shall We?” Ayra ta saki ajiyar zuciya tana mik’ewa a kasalance ta yafa gyalen doguwar rigar da take jikinta ta mayar da siririn glasses ‘din idonta ta bi bayansa don tuni ya fice, tana fita ya ja musu k’ofa ya kulle.

A mota suna tafe tunani ne kawai ya cunkushe zuciyar Ayra, sam bata son kishiya a rayuwarta ji take kamar ta bawa Turaki hak’uri Amma wata zuciyar na sake tunzirata. Ganin ta kasa jurewa ta fara jan yatsun hannunta tana fa’din “Turaki” bai kalleta ba ya amsa “Ya aka yi?” Ta kasa furta abinda ta yi niyya sai kawai ta mayar da kanta jikin kujera ta lumshe idonta tana jin yanayin yarda sautin zuciyarta ke bugawa, kuma kowane bugu da zuciyar tata zata yi da son Turaki a cikinta, wani kyau ya mata a zahiri a yau musamman yarda yake shan kunu da tsare gida irin na mazan da suka amsa Sunansu maza wanda ba sa ‘daukar raini a wajen matansu. Daga gani yau ta kai sa bango. Duk wani yanayi da ta shiga Turaki yana ankare da ita, sai dai ko a fuska bai nuna mata ba, illa cigaba da bin karatun Alk’ur’anin da ya yi cikin suraturrahman sautin karatun Sudais. Har suka isa gidan bai sake mata magana ba, duk da hango karaya k’arara a k’wayar idanunta, so yake ya nuna mata shine Mijinta kuma Miji ba abin wasa bane kada ta yi amfani da son da yake mata ta ce zata raina sa. Ya yi parking yana kallonta don bata san sun zo ba ta zurfafa cikin tunani, jin alamar idanunsa na yawo a jikinta ya saka ta bu’de lumsassun idanunta tana wara su a kansa, gaba ‘d’aya yanayin kallon da yake mata ya sake jefa zuciyarta cikin matuk’ar rauni da tsananin soyayyarsa, har zai yi magana sai kuma ya ‘d’auke kansa yana Unlocking motar ya fita cikin takunsa na k’asaita Ayra kam ta gane kurenta don da alama yau sarautar y’an mazan ta motsa. Jikinta a sanyaye ta fito ta bi shi da sauri a baya, saboda yarda filin gidan ya fara cika da mutane da dama. Har ya ‘dan yi nisa sai kuma ya dawo ya ja hannunta ya rik’e cikin nasa, ganin kamar idanun mutanen wajen duk a kanta suke. Tattausan hannnunsa da ya gamu shi ya saka su lumshe ido da sauri Suna jin bugun zuciyarsu na k’aruwa. Suna zuwa bakin k’ofar sashen Ummeey ya saki hannunta ya sake gimtse fuskarsa ya yi hanyar b’angarensa ya bar Ayra a tsaye cikin tashin hankalin yarda zata iya zuwa ta kalli fuskar Ummeeey da wani idon? Amma Turaki ya iya tsiya bai kyauta min ba, yanzu ne zan ce da jama’a. Gaba ‘d’aya kunya ta hana ta shiga har zuwa sanda dabara ta zo mata na kiran Tayseer a waya. Tayseer tana murmushi ta amsa mata “an gama Amarcin an tuna da mu?” Ayra d’an tsaki ta ja “Ke ban san magana, ina bakin k’ofa zo ki rakani ciki.” Tayseer tana dariya ta ce “Shi Ina angon naki ba zai rako ki ba?” “Ni dai ki zo na ce Malama.” Ta fa’da tana katse wayar. Tayseer ta saki murmushi kafin ta fito daga ‘dakinsu, ta tarar da duk iyayen nasu a babban parlour da su Ya. Deejah.


Dariya Tayseer ta yi sosai ganin yarda Ayran take tsaye fuskarta cike da damuwa, kamar ta saka kuka ta ce “Su Ummeey suna nan ko?” Tayseer ta ‘d’aga gira, Ayra ta dafe kai ha’de da fa’din “Na ga ta kaina.” “Wai meye haka Ya. Ayra sai kace wata villager daga wajen mijinki fa kike Amma duk kin wani kin firgice kamar wacce ta kwana gurin saurayi, ki zo kawai ki maze ki shiga Ai suma sun san me zaki yi tunda suka muka aure.” Ayra ta girgiza kai “Ba zaki gane ba Tayseer amma mu je.” Ta fa’da tana sake jan mayafi ta rufe fuskarta. Sallamarta ya saka duk wajen suka d’ago kai suna kallonta Ya. Deejah ta ce “A’a ka ga Malaman Soyayya an dawo kenan?” Ayra ta watsa mata harara kamar ta saka kuka. Duk gurin dariya aka saka kafin Ummeey ta janyota “Taho nan rabu da su haka ake son Mace ta zama duk inda Mijinta ya saka k’afa tana nan, sai ki ga ta mak’ale a zuciayrsa shima ya kasa aikata komai idan bata kusa da shi. Kada wanda ya sake tsokanar min y’a.” Ayra ta ‘dan ji sanyi tana zama jikin Ummeeyn da k’arfi da yaji ta yiwa Amma fashin y’a. Adda petal dariya suka yi sosai kafin ta ce “Surikar zamani, kai Ummeey Ai kya bari mu yi miki kara?” Umeey ta girgiza kai “Rik’e kayarki karar in dai a kan y’ar ki ne, ga su nan da yawa na bar miki.” Wani farin ciki ya ratsa zuciyar Amma ta san tabbas Ayra ta dace da Uwar miji ta gari.”


Tunda ya shiga bedroom ‘din sa ya kulle ya kwanta yana jin sam yanayin jikinsa ba da’di Ayra ce kwance a zuciyarsa amma ya lura yarinyar taurin kai ne da ita sai ya b’ullo mata ta bayan gida. Ya lumshe idonsa kafin wayarsa ta damesa da k’ara ya ‘daga yana ganin sunan Shaheedah na yawa a kan screen ‘din tsaki ya ja ka’dan yana tunanin shikkenan ya janyowa kansa yanzu zata fara damunsa. Da k’yar Ya kara wayarsa a kunnensa murya k’asa sosai ya ce “Hello Shahee ya aka yi?” Ta saki ajiyar zuciya kafin ta ce “I called you several times baka ‘daga ba, hope fine?” Ya saki ajiyar zuciya Zan kira anjima yanzu am busy.” Ya katse wayar kawai. Yana jiyo yarda gidan ya kaure da hayaniyar y’an na’din sarauta, tsaki ya ‘dan ja ka’dan yana sake lumshe idonsa.

Ayra ta dinga bulayin neman ta ga ya shigo parlourn Ummeeyn amma shiru, Ummeeyn ma shirun nasa ya dameta ga kayansa da zai saka an kawo daga wajen masu aikin alkyabbar sarauta zuwa can da ta gaji da jiransa ta kalli Ayra ta ce “Maza Ayra Je ‘dakina kan gado da kayan Turaki ki kai masa ya shirya ya fita fada don tuni an fara hallara mu ma fita za mu yi, idan ya gama shiryawa sai ku tafi tare.” Ayra ta mik’e tana jin da’din Aiken da Ummeeyn ta yi mata ko bakomai zata gan shi har su yi maganar da za su yi.


Haka ta ratsa corridor ‘din da zai sadaka da ‘dakin wajen shiru sai sanyin a’c da yake tashi da k’amshin turaren wuta. Ta mur’de handle ‘din k’ofar da zata shigar da kai ‘dakin da Turakin yake, lumshe idon ta yi tana shak’ar k’amshi turarensa da ya gauraye parlourn ganin ba ya parlourn kai tsaye ta nufi bedroom ‘dinsa ta mur’da k’ofar. D’akin ba haske dun’dum yake da duhu sai azababben sanyin A.c. Shiru Turaki ya yi duk da ya ji motsin mutum ya kuma tabbatar Ayra ce don jikinsa ya ba shi. Wayar hannunta ta kunna fitilar tana haska ‘dakin tana sallama a hankali.
Hango shi ta yi a kan gadon don haka ta k’arasa a hankali da tunanin barci yake. Ta zauna bakin gadon tana sake haske kyakykyawar fuskarsa duk abinda take Turakin yana jinta ya yi shiru kawai yana amsar gashin da dafin idanuwanta yake saka shi jin wani iri a gab’bansa. Ta saka hannu a hankali tana ‘daukar wayarsa da take ta faman ringing tana jin wani takaicin ganin sunan Shahee yana yawo a kan screen ‘din. Ji ta yi kawai ya ja hannunta ya cire wayarsa ya kara a kunne yana magana k’asa k’asa. Ayra ta fara jin hawaye na neman zubo mata, Turaki ya juya mata baya yana kunna fitilar ‘dakin murya k’asa k’asa yana magana da Shaheedah. Kafin ya katse wayar ba tare da ya kalleta ba ya ce “Menene kika shigo min ‘daki, ko kin zo ki sake birkita min tunani ne?” Ayra ta lumshe ido tana girgiza kai “Ummeey ce ta ce na kawo maka kaya.” Ta fa’da muryarta na rawa ta sauka daga gadon sai dai kafin ta yi wani motsi ta ji ya fisgota ta dawo samansa ya saka hannu ya ‘Daga hab’arta yana kallo kafin ya kai yatsansa kan hanwayen da suke zuba a idonta murya a cunkushe ya ce “Tears? Na menene?” Ayra ta kawar da kanta. Sai kuma ya tab’e baki yana mik’ewa ya ce “Tashi ki tafi tunda kin kawo sak’on?” Zama ta sake yi a kan gadon fuskarta a ha’de ta ce “Cewa ta yi I should wait for you mu tafi tare.” “Ni kuma nace ki tafi.” Ta ‘dago tana kallonsa kafin ta mik’e jikinta a sanyaye tana tunanin yanzu Turakin ba ya sonta. Har ta kai k’ofa ta ji ya janyota yana ha’data da bango ya ce “Wipe those tears off Malama kafin ace na miki wani abin.” Kukan sosai ta saka Turaki bai hanata ba kawai samun kansa ya yi da tsura mata ido kafin ya saki ajiyar zuciya ya ce “Kee wai kukan me kike yi Malama?” Kawai sai ta fa’da jikinsa Turaki yaji wani yarrr a jikinsa tsawon lokaci yana jin yarda ‘dumin jikinta yake kassara duk wata garkuwa ta jikinsa. Ya ‘dan janyeta kafin ya ce “Ki min shiru in don nace ki tafi ne kike Kuka zo ki zauna.” Ta janye hannunta da sauri tana fita a guje. Turaki ya bi bayanta da kallo yanzu kam ya san meye damuwarta kishi ne shi kuwa ba zai fasa abinda ya yi niyya ba, haka kawai ya zauna da ita ita ka’dai ta kashe shi.


Ko da ta koma ‘d’aki kwanciyarta ta yi tana jin yarda zuciyarta take k’una ga wani irin Soyayya Zazzafa da takewa Turakin da ta lumshe ido shi kawai take gani. Ta kowane side Turakin ya isa ya amsa sunan Mijin Ayra don shine mafarkinta tunaninta da kuma burinta! Ta ina zata hana shi aure? Shine kawai damuwarta a yanzu.


Turaki ya fita wajen ya dinga zagaye idanunsa yana son ganin inda zai gan ta amma ba labarinta. Sai kawai ransa ya ba shi tana cikin ‘d’aki murmushi ya yi kafin ya hana zuciyarsa zuwa inda take.



Da daddare ya samu Ummeey da Abeey d’insa zaune a parlourn Abeey ‘din su Amma suna sashen Umeeey. Kulawa da tarairaya Umeeeyn take ba shi don in dai suna tare bata son ya tuna yana da wata matar. Turaki cike da sha’awa ya dinga kallon yarda Ummeeyn take feeding Abeey ‘din ya shiga da sallama yana fatan su amince da abinda zai je musu da shi d’in. Ummeey ta amsa masa tana ‘dan janye jikinta daga abeey ‘din suka mayar da hankalinsu kan Turaki da ya durk’usa a gefe yana gaishesu. Sannan ya cigaba da murza hannunsa murya cike da damuwa ya ce “Abeey na samu mata zan k’ara aure….” Cup ‘din
Hannun Ummeey ne ya sub’uce ya fa’di sabida yarda sautin bugun k’irjinta da ki’dima da ta shiga suka sanya hannunta rawa. Maganar ce ta zo mata a sama, ranta a b’ace ta soma kallon Turaki kafin ta saki murmushi wanda ya bayyana zallar b’acin ranta ta ce “Allah ya sanya alheri, a ina matar take?”




𝔍𝖎𝖐𝖆𝖗 𝕹𝖆𝖘𝖍𝖊
Takaicin Uba…

Nazeefah Nashe…



Gangara💫
__________________


Kamilu ya ji da’di sosai da furucin Abeey, a yanzu kam tabbas yana tausayawa ‘dan uwansa abinka da jini da shi yake kwana kuma yake tashi a ransa don haka ma suka shirya da Jummai a kan su biyo Talatun har a Gombe duk da ba su san y’an uwanta ma aka gani ba, sai bayan zuwansu hakan yasa Kamilu ya ga ba abinda ya dace irin ya saka dangin Talatu su sake rok’a masa ita ta yafewa Kabiru don hakika yana cikin jarrabawar rayuwa kuma daf yake da rasa rayuwarsa. Duk sanda kuma zaka je wajensa rokonka zai yi ka nema masa afuwar Talatu ko zai samu sassauci a cikin kabari, duk abokansa sun gujesa Hadi ma yana cikin bala’in rayuwa ya dawo kamar almajiri saboda rashi, ga abin kunya da ya faru a gidansa ta yarda ‘dansa ya yi lalata da y’arsa har ciki ya bayyana duk Shagogo an ‘dauki maganar Y’ay’an Hadi sun yi lalata da junansu, har ciki ya shiga wannan shine abinda ya saka Hadin shima ya fa’di warwas. Sanda Jummai take gayawa Talatu murmushi kawai ta yi ta ce Hakkine Ai shi Allah ba azzalumin sarki bane ka’dan ma ya gani.” Jummai dai Shiru ta yi bata sake magana ba.

Kamilu ransa wasai ya mik’e ya fice daga parlourn da suke ganawa da S.Turakin. Yana jin kamar warakar ‘dan uwansa ta zo.




_______________


Ya ja bargon da sauri Ayra ta sake ja tana k’udundune jikinta fuskarta ‘dauke da murmushi duk abinda ya wakana a daren yana dawo mata tiryan-tiryan da irin kalaman da ya dinga gaya mata a kunnenta masu saka nisha’di ba wanda ta rik’e irin yarda yake ce mata “Ba Shaheedah ba har abada Ayra Wallahil azeem ba zan miki kishiya ba! Ni ka’dai na san irin ni’imarki da na ‘dan’dano please ki min alk’awarin ba za ki sake min rowar kan ki ba.” Ta ‘dan lumshe idonta Turaki yana tsaye yana sake bin ta da kallo ji yake kamar ya mayar da ita ciki ya huta da zazzafar k’aunarta da take masa walagigi da zuciya “Tashi mana, Sweet ko so ki ke na koma ruwa.” Da sauri Ayra ta mik’e tana kawar da kanta don bata son ha’da ido da shi. Ya jawota jikinsa yana ‘dago hab’arta ya ce “Kunyar ta mecece? Bayan kin gama rikita min kwanya.”
Ta sake runtse idonsa Turaki murmushi kawai ya yi yana ha’deta da jikinsa ya sake rungumeta tsam yana sakin ajiyar zuciya ya ce “Allahumma barik, Allah ya sake ninka miki ni’ima akan ni’ima ki dinga hauka tani kina susutani sai ki ji ana Turaki ya koma Mijin kan ta ce.” Ayra dai ba ta yi magana ba illa sake k’udundune kanta da ta yi tana sake jin k’amshin jikinsa da yake tado mata duk wani dafin k’aunarsa Turakin ma lunshe idonsa ya yi yana jin dama su dawwama a haka har abada ba zai tab’a gajiya da jinta a jikinsa ba.” Tsawon mintoci kafin Ayra ta zame jikinta tana duban agogo ta ware ido ganin k’arfe 11:00 shima idanunsa ya kai kan agogon ya ‘dan ware ido ganin lokaci ya ja. “Ayra kin shigesu? Me za ki ce da mutane?” Ya fa’da yana kwaikayar maganarta. Da sauri Ayra ta bi shi tana cillinsa da pillow har kan gadon da ya koma, yana ganinta ya sake janta jikinsa yana fa’din “Shikkenan kin sake kawo kan ki.” Ayra ta bu’de baki Zata yi magana ta ji kawai ya Aika mata wani salo da ya sata jan bakinta ta k’unshe don ta kasa bijirewa Turaki lamarin mai girma in dai har ya cigaba da yi mata haka bata jin zata iya bijirewa umarninsa zata bi shi sau da k’afa fiye da tunaninsa.



Ummmeey dai da ta gaji da jiransu kawai sai ta aika musu da abincin breakfast parlournsu ita ka’dai ta dinga sakin murmushi don ko bakomai burinta ya gama cika, Ayra da Turaki sun zaman tif da taya. Daga haka ta ja Amma suka nufi fa’da gaida mai martaba da su Deejah da suke shirin tafiya ranar su kuma su Amma da su Ummmeey sai jibi za su rankaya su koma Kano.


Sanda suka je gaida Maimartaba yana murmushi ya mik’e yana amsa gaisuwar su kafin ya kai dubansa kan wazirinsa yana fa’din Kaya ya tsinke a gindin kaba ga Talatun da kake min magana a kanta.” Waziri ya kai dubansa kan Talatun yana murmushi ya ce “Ai mun gama magana da kai, ka ce in dai har ka isa da ita kada na ji komai.” Haka kawai sai Talatu ta ji gabanta ya fa’di ta zauna dai jiki a sanyaye tana gaishe da maimartaba Ummeey da fulani kuwa sai murmushi suke don sarai sun gane inda maganar Maimartaba ta dosa.

Bayan gaishe-gaishe Maimartaba ya dubi Talatu yana murmushi ya ce “Alhamdulillah Y’ata na miki mijin in dai ban miki shigar sauri ba.” Da sauri Talatu ta sunkuyar da kanta tana jin wata fargaba na dirar mata ita fa ko kalmar aure bata son ta ji an ambata mata balle ina zata kai aure da shekarunta da komai duk da shekarun sun yi gaddamar nunawa a jikinta. Sai dai ba zata iya kallon idon maimartaba ta wofintar da maganarsa ba musamman yanzu shi take kallo a matsayin Uba mahaifi. “Waziri ku daidaita da ita in dai har ta amince a gobe juma’a zan saka a ‘daura muku aure In sha Allah.” Murna ce ta bayyana a fuskokinsu gaba ‘d’aya har su Deejah in dai Amman zata yi aure a inda zata huta suna murna da haka don ko bakomai ya cancanta Amman ta ji da’din da ake samu a rayuwar aure in dai ka yi dace da Miji na gari, don haka zuciyoyinsu ba su ji komai ba sai na murna suka yi za kuma su rok’i Amman ta amince ko da zuciyarta bata so. Suna ganin hakan shi zai k’ara mata kima da martaba a idanun mutane tunda dai ba wuce auren ta yi ba. Mai martaba ya sallamesu sai dai kafin su tashi Kamilu ya rok’i alfarmar yana son magana da su. Suka zauna duk da yana jin nauyin maganar bai b’oye komai ba ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login