Showing 81001 words to 84000 words out of 132090 words

Chapter 28 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt

su Five star Hotel da ke garin Moscown anan yake son ya kafa mata tarihi mai wuyar gogewa a kwanya. Ayra kam gaba ‘d’aya ta tsure da jin furucinsa kawai daurewa take kuma a yanayinsa bata hango zai janye daga alk’awarin da ya ‘d’auka ba, babu alamar haka don kallonta kawai yake yana sakin murmushin da kai tsaye ta kira na mugunta.



D’aki ‘daya jal ya kama musu mai masifar kyan tsiya an gyara gadon da katifa mai wani irin laushin tsiya ga k’amshi da sanyi ko ta ina yana tashi daga ‘dakin. Ayra kamar ta yi kuka ta shiga kallonsa murya na rawa ta ce masa “Nan ‘din nawa ne ko naka?” “Namu ne.” Ya bata amsa yana tsalle a kan gadon cikin nisha’di kafin ya mik’e kansa a kan hannunta ya ce “Madam di Madam ya dai na ga bakin tsiwar ya mutu.” “Ba zan iya kwana ‘daki ‘daya da namiji ba.” Ta fa’da tana kallonsa narai narai da idanunta “Yau kika fara? Ai kin Riga kin haddace yarda ake kwana ‘daki ‘daya da namiji tunda har kina banbance rago da gwarzon namiji, don haka ki saki jikinki Malama bana son wani pretending just like you don’t know anything.” Ya fa’da yana tsareta da wani irin kallo da bai tab’a mata ba sai yanzun. Ayra ta saki ajiyar zuciya kafin ta kalli ‘dakin ta ga ko y’ar kujera babu alamar dama da gayya ya kama ‘dakin ko kuma don masu honey moon aka k’irk’iresa. “Duk ba wannan ba ni dai ka taimakeni ka kama apartment.” “Ban ga dama ba.” “Bari naje ni to na kama.” “Bismillah.” Ya fa’da yana kashe mata ido ha’de da nuna mata hanya da sauri ta ‘d’au hand bag ‘dinta ta zuge tana addu’ar Allah yasa ta taho da Dollar card ‘dinta sai dai wayam bata gansa ba, sai tarkacen Atm card da ba zasu mata amfani a k’asar ba, ta saki tsaki tana cillar da jakar, da mamakin yarda aka yi dollar card ‘din ya yi b’atan dabo bayan da kanta ta saka shi a ciki. Shi kuwa yana kwance yana sakin dariya k’asa k’asa don tuni ya sace Dollar card ‘din saboda irin wannan kada ta zo tana masa tak’ama da ku’di.

D’an k’asan gadon ta samu ta raku’be ta zauna tana jin kamar ta saka hannu a kai ta kurma ihu wannan wace irin masifa ce? Wato shikkenan bata da mafita kenan sai ta zama k’ark’ashinsa ya juyata kamar yarda yake so, da ace da Dollar card ‘dinta da sauk’i zata iya booking flight ta wuce Nigeria idan taga dama, to yanzu ko tarkacen numbers ‘din da suke ciki bata haddace ba. Tana kallo ya ta shi ya zaro towel a trolley ‘dinsa fari tas da shi daga ganinsa Sabo ne. Ta runtse idonta ganin yana shirin cire kaya a gabanta duk abinda take yana kallonta ta mudubi ya tab’e baki a ransa ya ce ka ji y’a kamar bata tab’a ganin namiji a tub’e ba. Ya cire kayan daga shi sai boxer ya shige toilet yana jin wani nisha’di a ransa ko abinci a hotel ‘din za a basu ba inda zai je. Tana jin ya rufe k’ofar toilet ‘din ta mik’e da sauri ta hau binciken kayansa ko zata ga card ‘dinta sai dai ko alamarsa bata gani ba. Har ta gaji ta zauna tana haki yanzu kam ta amince bata da mafita, lamarin sai addu’a. Wanka ya yi sosai sai zabga k’amshin turaren wanka na companyn Makari yake harta da kansa sai da ya wankeshi ya fito sanye da rigar wanka yana tsane kansa da hand towel. Ita kuwa tana jingine da gado a takure barci ne yake fisgarta ga shi tana jin yunwa ga gajiya wanka take son yi amma ta Ina zata fara shiga toilet yana cikin ‘dakin. A kanta ya tsaya yana combing kansa hakan yasa take jin ‘d’igar ruwan kansa a fuskarta, ta bu’de idonta mai nuna alamar gajiya ya ce “Ki tashi ki yi wanka bana son k’azanta.” Murya a raunane ta ce “To don Allah ka fita ka bani 20 minutes na shirya sai ka shigo.” “Ashe kuwa ba za kiyi wankan ba, idan baki yi wasa ba da kaina zan shiga toilet ‘din na cu’deki, me kike b’oyewa ne jikin da wasu banza suka gama ganewa?” Ta ‘dan turo bakinta tana bu’de akwatinta gwara ta ‘dau kayan ta shiga toilet ta yi wankan ta shirya a can. Takaici ne ya kusa kasheta ganin kayan da suke cikin akwatin, sai lokacin ta san da tsiyar da Deejah ta shuka mata. Ganin yarda ta yi kasak’e tana kallon kayan ya saka shi matsawa shima yana dubansu “Ya dai? Ko ba kayanki bane?” Cikin takaici ta rufe akwatin tana fa’din “Nawa ne, amma ba ni na shirya kayan ba.” Da mamaki yake bu’de akwatin yana fa’din “Then so what? Kayan ne ba su miki ba.” Ya fa’da yana ‘d’aga kayan kafin ya saki murmushi “Godiya dubu ga wacce ta ha’da kayan kamar ta san irin wanda nake so kenan.” “Ni kuma ba zan saka su ba.” Ta fa’da kamar ta yi kuka tana hawa Deejah Allah ya isa a zuciyarta “Me ye sabo a cikin kayan da dama su kika saba sawa ki zumbula hijabi sai kin je wajen Mazan banza ki bu’de jiki, ko nine kike min bak’in cikin ganin halaliyata? To wallahi sai kin saka ko ki yi yawo tsirara.” Kife kanta ta yi a cinya tana sakin kuka don ta kasa danne kukanta, duk da kukan ya tab’a zuciyarsa haka ya danne ya maze yana fa’din “Ki tashi Malama ki je ki yi wanka, ko na ‘dauke cak na miki don wallahi a wannan daren sai na nuna miki asalin ragon namiji.” K’irjinta yana dukan uku uku ta ‘dago tana kallonsa. Ba ta yi aune ba ta ji ya ‘dagata cak ya nufi toilet da ita. Ta fara wutsil wutsil da k’afafu Amma ko gezau bai yi ba har sai da ya direta a ha’dadden toilet ‘din kafin ya ja k’ofa ya rufe yana fa’din “20 Minutes na baki ga abinci nan an kawo ki ci ki k’oshi don ba ‘daga k’afa..” ya zauna gefen gadon yana sakin murmushi shi ka’dai kafin ya fara fesa turaruka a kowane gab’a lungu da sak’o na jikinsa. To fa! Wannan dare akwai kallo Allah sarki Ayra za’a shiga hannun Maza zaki san kin kira Turaki Ragon Namiji… kafin ta fito daga wankan bari mu lek’a Nigeria mu ji wainar da ake toyawa.





______________

Tsaf Amma Talatu ta shirya cikin tsadaddiyar atamfarta super wax. Sai zabga k’amshin turaren gabbasa take wanda ta turara kayanta da shi. Gidan Hameeda take son zuwa, don ta gaji da k’orafin da Hameedah take mata a kan rashin zuwanta. Drivernta da suka ‘daukar mata shi yake janta a motarta suna tafe tana saurarar karatun alk’ur’ani cikin suratul mulk k’ira’ar Sudais.

Sai da suka je bakin gate ‘din sannan ta kira Hameeda ta sanar mata zuwanta. Murna da farin ciki suka ziyarci fuskar Hameedan da sauri ta kalli Tayseer da take shirin shiga kitchen ta ce “Maza bu’dewa Amma k’ofa.” Ita kuma ta mik’e ta isa anthem ‘din gidan ta tsaya tana tsimayin zuwanta.

Da farin ciki ta tareta suka isa cikin falon tana fa’din “Ai dama na saka a raina in dai baki zo ba ni da kaina zan je a satin nan, don na k’agu na ji k’arashen labarin Kabiru Wallahi da kuma irin k’addarar da ta afkawa Ayra da yasa mata tsanar Maza. Ina son jin wani laifi Kabiru ya mata har haka?” Amma da ta shigo da karsashinta tuni duk wata fara’a da walwalar fuskarta ta arce, idanunta suka ka’da suka yi jazur ba abinda take sai sauke ajiyar zuciya tana kokawa da numfashinta da yake neman barin k’irjinta. Ba labarin Ayra bane bata son bayarwa, sai dai a duk labarinsu shine labari mafi muni da ko son tunawa ba tayi balle ta furta da bakinta. Yanzu me Hameeda take son tace mata, da zata iya tabbas da ta yi mata k’arya don ko kad’an bata son fitar labarin da ta kira bak’in labari daga bakinta. Sai dai ba abinda zata iya b’oyewa Hameeda tana jin Hameedar kamar y’ar uwarta ita take kalla Makwafin y’ar uwa ta jini da ta rasa don haka murya na rawa cikin hawaye ta ‘dago tana kallonta kafin ta yi k’asa da kanta ta ce.




JikarNashe ce!
Takaicin Uba…

Nazeefah Nashe.

40.


💔💔💔💔

Idanun Talatu na ‘disar da hawaye ta dubi Hameeda da ta zuba mata ido cikin tarin jin tausayinta, don dai ta san ko mai ma Talatun zata fa’da ba zai zama mai kyau ba. Ta ja ajiyar zuciya itama tana jin taruwar hawaye a nata kwarmin idon, dafa Talatun ta yi cikin muryarta mai bayyana raunin da zuciyarta take ciki ta ce “In dai ba kya son tuna labarin Talatu ki bar shi nima na hak’ura da ji, daman abinda yasa nake son jin don na ‘dauke ki kamar y’ar uwa ne ga maganganun da suke ya’diwa a gari na mutanen da suke ganin ba kiyiwa Kabiru adalci ba, don haka ni dai na hak’ura.” Talatu ta girgiza kai ha’de da share hawayen da yake kwaranya daga idonta kamar k’orama murya a raunane ta ce “Fa’da miki ba zai zama aibu ba, nima hakan da zan yi zai saka na samu sauk’i a zuciyata don tunda abin ya faru ba wanda na gayawa ina ta fama da shi a zuciyata na tabbata kuma barinsa a raina shine yake assasa min ciwo a zuciyata, don haka na shirya fa’da miki don ina jinki kamar y’ar uwata ta jini…”


GA YARDA LABARIN ZAI CIGABA….



Jin furucin Kabiru na cewa ya bar mata yaran yasa ta ji wani taratsatsi a zuciyarta ga shi har yana ikirarin siyar da gidan zai yi. Ta dinga kallonsa kamar mutum mutumi ta ma kasa motsi saboda tsananin b’acin rai da girgizar zuciya, Ina Kabiru yake son ta kai yaran da yake ik’irarin ya bar mata halak malak har duniya ta na’de a ina ake haka a rayuwa bayan tana sane da cewa musulunci shi ya k’allabawa wahalarsu cin su shan su, suturarsu duk suna k’ark’ashin Kulawarsa ne, duk da hakan ba sabon abu bane a wajenta dama ta saba duk wani nauyinsu a kanta yake, abu mafi ciwo a wajenta maganar cikin da yake neman sheganta mata. Murya a raunane ta ce “Kabiru ka ji tsoron Allah, kai da kanka ka san cikin jikina naka ne, kuma ka san ban tab’a kusantar wani ‘da namiji ba me yasa kake son sheganta shi tun kafin koma meye a cikin yazo duniya?” “Saboda bana son koma me za ki haifa? Shi yasa na gwammace na sheganta shi ‘din kuma maganar na ji tsoron Allah idan ban ji tsoron saba tsoronki zan ji? Kin ga wannan ba zata fishsheki ba ki tattara yaranki ku yi gaba ko bara ku je ki yi a birni ki ciyar da su ba matsalata bace, abu ‘d’aya da nake son ki lura da shi ki kuma ajiye a ranki duk inda za kije ki dinga tuna sark’afaffiyar igiyar aurena a kan ki, don ba zan yi saken da zan sake ki gaba ‘daya ni kuma na talauce ba.” Hawaye ne kawai yake bulbula daga idanun Talatu kafin ta samu k’warin gwiwar cigaba da tattara kayansu don yanzu ta tabbatar ba su da wani gata sai nata sai na Allah, ta amince ita zata maye musu gurbin Mahaifi da Mahaifiya gaba ‘daya, tana fatan Allah ya agajeta ya bata ikon ‘daukar duk ‘dawainiyarsu da tarbiyyarsu gaba ‘daya. Zuciyarta ta bushe ta ji gaba ‘d’aya garin Shagogo ma ya fice mata daga rai bata burin ta wayi gari a cikinsa. Da sauri take komai su Majeeda suna tayata da wasu aiyukan.


K’arfe 4:00 na dare suka bar garin Shagogo, garin da ba zasu k’arar da farin ciki ko ‘d’aya a cikinsa ba sai tarin bak’in ciki, ko a mafarki Talatu bata fatan ta sake ganin garin na Shagogo ‘daid’aikun mutane ne ba zata manta da su a cikin su ba, ba kuma zata tab’a mance alherinsu ba cikinsu har da Mai gari.


Bus da take shirin tashi ta shiga garin kano suka shiga, ta kama musu kujera biyu suka gwamutsa suka tafi ba tare da ta san inda zata dosa ba, kawai dai ta san garin na Kano akwai girma akwai kuma bayin Allah masu taimakon jama’a.


Tunda suka sauka a garin suka fara yawo lungu lungu ba tare data san inda zata yada zango ba, kawai tafiya take yaran suna tare da ita, idan Deejah ta gaji sai Majeeda ta goyata har suka isa wata unguwa masu manyan gidaje kana ganin unguwar ka san masu hannu da shuni ne. Ta jikin layukan unguwar Majeeda ta karanta sunan unguwar Shara’da phase 2. Gajiya ce ta sa ta fara musu yawa ga yunwa ga kuma k’ishirwar da ta addabesu. Talatu ta samu wata mai masara a bakin titi ta siya musu da ragowar y’an ku’din da suke hannunta ta kuma siya musu ruwan leda sannan suka kutsa cikin layukan unguwa addu’oi fal a bakinta dafatan Allah ya kaita gidan da za a agajeta da y’an y’ay’anta ta amince zata rabasu aikatau a cikin gidajen da suke unguwar idan yaso ta rik’e Deejah kawai a wajenta. Wani gida suka wuce shi ka’dai ne kuma gate ‘dinsa a bu’de da mutane almajirai a bakin gidan da alama sadakar abinci suke karb’a. Haka kawai Talatu ta ji hankalinta ya kwanta da gidan ko aikin abincin sadakar zata rok’a ta dinga yi, don haka ba tare da wani tunani ba ta k’arasa bakin gate ‘din. Suka amshi abinci kamar yarda suka ga kowa ya amsa a cikin bak’ar leda har yaranta sai da aka bawa abincin. Talatu ta jasu
Gefe suka fara cin abinci hannu baka hannu k’warya. Suna nan zaune sai ga Maigadi a guje yana fa’din “Kai bayin Allah ya da haka kuka zauna anan kuna cin abinci to ku tashi maza Hajiya zata fita da mota.” Talatu ta mik’e da sauri tana janye hannayensu suka rakub’e a gefe. Daidai fitowar wata zundumemiyar mota bak’a wuluk k’irar jeep. Har motar ta wuce sai kuma suka ga ta dawo da baya. Hajiyar da kanta ta sauke gate tana kallon Talatu fuskarta da mabayyanin tausayi “Baiwar Allah daga ina?” Da sauri Talatu ta zube a gaban Hajiyar murya cike da ladabi ta ce “Hajiya a taimaka min aikatau nake nema don girman Allah.” Hajiya ta yi shiru tana kallon Talatun sama da k’asa nazarinta take sosai kafin ta saki ajiyar zuciya “Yanzu ina sauri Amma ga driver nan zan saka ya baki wajen zama kafin na dawo muga yarda za’a yi.” Ta fa’da tana k’walawa Drivern kira “Rabe zo mana.” Ya k’araso da sauri “Maza shiga da su Guess side idan na dawo zan gansu ina da urgent meeting ne.” Rabe ya ‘d’aga kai da sauri yana fa’din “Shikkenan ke kakarki ta yanke sak’a Hajiya da kanta zata ganki Ai ganin Hajiya alheri ne.” Ya fa’da yana shigewa gaba su kuma suka bi shi a baya. Talatu tana fatan abinda Rabe ya fa’da ya zama hakan In sha Allah, tana fatan Allah yasa k’arshen wahalarta ne ya zo.


B’angaren bak’in da Rabe ya saukesu waje ne mai kyau shi ‘din ma don su dai su Majeeda ba su tab’a ganin irin ginin gidan Hajiya ba, gidane canca’dede zubin ginin turawa daga wajen gidan har da swimming pool da Garden. Nan ‘din ma babban falo ne da ya ji manyan kujeru masu kyan gaske da Babbar Tv plasma ga Ac tana sanyaya Falon. Talatu ta sauke ajiyar zuciya mai nuna tsananin gajiyar da take ciki kafin su zube a kan carpet don da kunya su zauna akan kujerar abinda ba su tab’a gani ba. Su Majeeda sakar baki kawai suka yi suna nuna k’auyancinsu zalla don har gaban Tvn da Rabe ya kunna suka je suna tab’awa suna ganin mutanen ciki kamar za suyi musu magana. Sai da Talatu ta tsawatar musu sannan suka dawo suka rakub’e suka zauna. Rabe da kansa ya kawo musu ruwa mai sanyi da wani kalar lemo da basu tab’a sha ba har da kilishi da dambun nama duk daga umarnin Hajiya Dubu. Komai sai da suka masa cin wawaso kafin su koma su Majeeda suka baje a saman carpet suna barci abin su, itama Talatun barcin take ji Amma sai ta mik’e ta shiga inda take zaton toilet ne ta ‘d’auro alwala duk da ta sha wuya sosai kafin ta iya kunna famfon. Sallah tazo ta gabatar kafin ta zauna tana lazimi da addu’ar samun dacewa a wajen Hajiyar.


Sai bayan Magriba Hajiya Dubu ta shigo gidan, bata nemi su Talatu ba duk da suna ranta sai da ta isa b’angarenta ta yi wanka tukunna ta ci abinci da Sallah, sannan ta nufi b’angaren da ta saka aka sauke bak’in nata cikin takunta na nutsuwa gefenta kuma mai kula mata da hidindimun gidanta amintacciyarta kuma. K’amshin da ya cika falon ne yasa Talatu ta ‘dago daga dogon tunanin data tafi da sauri ta mik’e tana gyara zamanta ta nutsu sosai tana gaishe da Hajiyar cikin k’asa da kanta. Hajiya ta zauna tana amsa gaisuwarta don Macece ita mai tausayi musamman ga mata masu rauni. “Baiwar Allah ya sunanki kuma meye mak’asudin zuwanki nan?” Talatu a nutse ta gaya mata sunanta ha’de da cewa “Hajiya taimaka min za kiyi ko aikatau na dinga miki a kuma raba min ‘ya’yan nan suma su yi aikatau ‘din a wasu gidajen.” Hajiya ta ‘d’aga kai tana duban su Majeeda da bata hango wani aikatau da k’ananan yaran nan za su iya ba. Ta saki ajiyar zuciya ha’de da cewa “Yaranki ne?” Da sauri Talatu ta ‘d’aga kai “To ina Ubansu don dai ga ki na ganki da ciki..” Hawaye ne ya fara ‘diga daga idanun Talatu tana sakin ajiyar zuciya ta ji ta aminta da Hajiya zata iya kuma bata labarin ta ba zata b’oye mata komai ba don haka murya da rauni ta fara bata labarin. Kafin ta gama tuni duk wani annurin fuskar Hajiya ya b’ace b’at jikinta sai tsuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login