Showing 84001 words to 87000 words out of 132090 words

Chapter 29 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt

yake kamar ana ka’da mata gangi ta zubawa Talatu idanuwnta da suka ka’da suka yi jazur abinda ya ka’da y’an hanjin cikin Talatun ta yi k’asa da kanta da sauri tana fatan Allah yasa ba wani abu bane daga cikin labarin nata ya b’ata ran Hajiyar. Cikin b’acin rai Hajiyar ta ce “Namiji ‘dan kunama! Namiji k’anin Ajali! Namiji tabarmar k’aya! Ta sake dunk’ule hannunta waje ‘d’aya kafin ta ce “Kin zo wajen da za’a share miki hawaye Amma da shara’di…..”

Talatu ta ‘dago da sauri don ta amsa mata sai dai abinda ta gani ya girgiza zuciyarta da sauri ta runtse idanunta tana jin wani tsoro na shigarta…….



Jikar Nashe…


(Kada a manta gobe weekend ba na posting sai dai may be za ku iya jina jibi, don kada a yi ta min waya. Nagode sosai.”)
Takaicin Uba…..

Nazeefah Nashe

41.

💔💔💔💔

Tsananin razana ya hana Talatu cigaba da kallon matar, Ba don komai ba sai don ganin yarda Matar ta zaro idanunta guda ‘daya ta sanya shi a tafin hannunta tana kallon Talatu da razanar da ta yi ya bayyana sosai a kan fuskarta. “Wannan shine ka’dan daga illar da namiji ya yi min, bisa son zuciya da zallar mugunta ya mayar da ni mai idon roba guda. Don haka wannan labarin naki ya sake tab’a ni na ji kuma ina son na taimaka miki ko don nan gaba ki taka wani matsayin da Mijinki zai raina kansa, amma da shara’di kada ki sake ki bari ya san inda kike, duk ranar da kika bari ya gano inda kike ba tare da gama cikar burikana ba ina tabbatar miki ranar za muyi hannun Riga da ke, don haka ki kiyaye duk wata hanya da zata sadaki da shi, tunda har yanzu ya mak’ale igiya guda ta aurenki kamar yarda kika ce, banda ina son na taimakeku har ku zamo wasu da a yanzu zan saka a binciko min mara mutunci in tozarci idan ta kama har uwar da ta kawo shi duniya, sai dai a yanzu idan ya bayyana na aikata masa tozarcin ina tabbatar miki ba zai bar miki yaransa ba ko don ya k’unsa miki takaici ni kuma burina yaran nasa da yake k’yama saboda an haifesu Mata su zo su zama wani abin don na gama zai yi da na sanin k’in kula da hak’kinsu da ya yi ki rik’e shara’din a ranki ban amince ko da wasa ku ha’du da Kabiru ba a fili ko a b’oye. Idan kika min haka zan ‘dau nauyin yaranki zan sanya su Makarantu masu tsada inda za su samu nagartaccen ilimi sannan zan ‘dauki duk wani nauyinsu ba tare da na kaisu aikatau ba ha’din kan ki kawai nake buk’ata, ke kuma ga Jummai nan sai ki dinga tayata aikace-aikacen gida,Allah yasa ki zamo mai rik’e amana.” Sosai Talatu ta fara zubar da hawaye tsabar farin ciki bata san sanda ta zube a k’asa ta kai goshinta k’asa ba alamar sujjuda. Kafin ta ‘dago ta zube a gaban Hajiya Kari tana mata godiya da duk wata fasahar harshenta sai da ta tattaro don jaddada godiyarta. Hajiya ta kamata ta sanyata a jikinta tana share mata hawaye “Bana buk’atar godiyar Ki Talatu, ni don Allah na yi a kuma gurinsa nake neman sakamako, ba ni da kowa ba ni da komai, iyaye sun rasu y’an uwana an kashesu sabida son zuciya, ba ni da ‘da ba ni da jika, Mijin da nake alfahari da shi tunda yaga iyayena sun mutu yake burin ya mallake abinda aka bar min, don haka ya shiga neman rayuwata ta k’arfi da yaji har ya janyo min sanadiyyar idanu guda bayan ya turo y’an fashi su min kisan gilla don kawai ya gaje dukiyata, na samu da k’yar na tsirar da kaina daga ranar ban sake saka shi a idanu na ba, sabida yarda y’an sanda suka baza jami’an tsaro suna nemansa da kaina na kai kaina kotu alk’ali ya sake ni kamar yarda shari’a ta tanadar bayan ya ‘d’au tsawon shekaru ba amo ba labarinsa, wannan shine tak’aitaccen Tarihin Hajiya Kari.

Talatu ta tausaya mata sosai kafin cikin k’asa da murya ta ce “Allah ya saka miki Hajiya, hak’ika maza da waya suna da son zuciya da rashin kyautatawa iyali Yarda kike taimakon jama’a Ubangiji Allah ya baki aljanna ma’daukakiya nagode k’warai.” Hajiya ta ‘d’aga kai kafin ta ce “Bakomai, nan sashen dama ba kowa a ciki sai ya zama naki da na yaranki. Ku dinga kwana a ciki da kitchen da toilet da komai a ciki, abincin makarantarsu su dinga dafawa a nan don ni a k’aidata bana tashi da wuri, kuma idan ina barci bana son kwarafniya. Gobe In sha Allah Zan saka Sale ya samo musu makaranta mai kyau anan kusa da mu, Sale shine babban yaro na ana kiransa Sarkin gida, sai Jummai itace amintacciyata a cikin masu aiki, sai Driver Lawal sai mai gadi Malam Rabe, Ina fatan yarda suka zamo masu amana kema za ki zamo daga cikinsu.” Da sauri Talatu ta ‘d’aga kai “To ma sha Allah, idan kika yi haka kin ceci rayuwar y’ay’anki da kanki, don kin gansu nan mun kusa shekaru ashirin da su muna zaune lafiya tausayinki yasa na amince miki zama anan idan banda haka bana son abinda zai saka min damuwa.” Daga haka ta mik’e tana daidaita zaman k’wayar idanunta da ta zaro kafin ta kalli Talatu “Ki taso maza ki amsar muku abubuwan buk’ata a store Jummai a basu kayayyakin tea da sauran tarkacen da za su buk’ata including su Sabulu toothpaste da sauransu, kada ki manta da roll on da body spray kin san bana son jin mutum yana tsami ki gaya mata ta kula a bata abin shaving ma, ki nuna mata yarda zata yi using d’insa.” Jummai cike da kulawa ta ‘dagawa Hajiyar kai tana fa’din “An gama uwar ‘dakina In sha Allah zata kula,Ubangiji dai ya cigaba da taimakon ki kamar yarda kike taimakawa na k’asa da ke, Allah ya ja mana da ranki don girman zatinsa.” Hajiyar ta amsa ba tare da nuna alfahari ko ‘dagawa don tana da zurfin ilimin addini don haka ta san illar girman kai da fankama gami da K’ifa’di irin na wasu masu ku’din.


Haka kuwa Talatu ta zauna tun a daren ta tsefewa yaranta kai ta wanke musu tas da shampoo da conditioner kamar yarda Jummai ta koya mata a nata kan, sai ga gashin yaran ya fito sai walwali yake abinka da masu suma da cikar kai. Su kansu a jikinsu suka ji sun samu canjin rayuwa ga Tv sun kunna sai kallo suke cike da nisha’di suna kuma zaune a kan luntsuma luntsuman kujera suna zuk’ar lemo da biscuit da Jummai ta kawo musu carton guda. Talatu kuwa tana gefe rik’e da carbi a hannunta tana godiya ga Allah ta hanyar jan subhanallah wal hamdulillah. Tabbas yau ta sake jaddada girman Ubangiji ashe barinta k’auyen Shagogo alheri ne zai bibiyeta ga shi nan dai rayuwa tana neman canja musu daga bak’i zuwa fari ashe suna da rabon jin da’din duniya kamar kowane ‘dan adam. Ta saka hannu ta share hawayenta da bai zamo na komai ba sai na zallar farin ciki.




_________

Daga ranar rayuwa ta canja musu gaba ‘daya. Yara har sun fara k’iba cikin tsawon sati biyu a gidan fatar su ta sake murjewa an kuma saka su a makarantar IMAN da take nan shara’dar makaranta ce mai kyawun gaske, Hajiya ta siya musu kaya kala biyar biyar na zaman gida. Abinci sam baya yanke musu, suna cikin farin ciki sosai. Ita kuma Talatu cikin da yake jikinta yana ta girma da k’ara bunk’asa ga watsalniya da yake yi alamar yana cikin k’oshin lafiya kuma tun a ciki Ayra ta nuna mai kazar kazar ce ita. Don sau tari Talatun tana jiyo watsalniyarta a ciki kamar zata fito ta tilas. Ta kan shafa cikin ta ce “Oh, ni dai tunda nake haihuwa ban tab’a ciki irin wannan ba to ko namiji ne?” Sai kuma ta yi saurin yin istigfari ta ce “Allah koma me ka ban ina farin ciki da shi ina kuma murna fatana Allah ka musu albarka.”

Bata nuna son jikinta ko ka’dan haka take zagewa ake aikin gidan da ita, kuma sun saba sosai da su Jummai da ma sauran ma’aikatan gidan Talatu jin su take tamkar y’an uwanta, haka nan ta dauki hajiya kamar mahaifiyarta.


Cikinta wata tara daidai da watansu biyar a gidan, Ciwo ya kama Hajiya Kari, duk wanda ya ga ahalin gidan ya san ba k’aramin tashin hankali suke ciki ba, musamman jin labarin ciwon nata cuta ce ya Daji da ake kira Cancer ta mahaifa ta kamata, sun firgita matuk’a ainun da lamarin ciwon nata sai dai ita ko a jikinta gaba ‘d’aya ta sake kusanta kanta ga Allah ibada take sosai ta kuma cigaba da kyautatawa mabu’kata. Sai dai asibiti sun buk’aci a kaita k’asar waje ta amince zata je a ka fara mata processing visa da komai da za’a tafi da ita Egypt don duba idan da hanyar da zata samu lafiya. Ana jibi za ta tafi ta tarasu gaba ‘d’aya ta bar musu amanar gidanta musamman Talatu don Jummai da su za’a tafi ita da Sarkin gida. Tashin hankalin da ya dirar wa Talatu shi ya tayar mata da nak’udar da bata shirya ba a kuma daren cikin huwacewar Ubangiji ta haifo santaleliyar y’arta mai kama da Mahaifiyar Talatu sak, tun tana cikin jini ta ce “Na sanya miki suna Fatima Allah ya raya min ke Hajiya Kari.” Wato ta yiwa uwar ‘dakinsu ma gajiya. Sai da ta gyara y’ar da k’yar ta mayar da kai ta kwanta tana jiran asuba ta yi ta je ta sanar musu ta haihu.


Ba k’aramar murna Hajiya Kari ta yi da jin an mata takwara ba, ta ‘d’aga Jaririyar tana sumbata a hankali kafin ta ce “Na ji da’di Talatu wannan ya nuna min ko bayan ba ni ba zaku manta da ni ba, nagode sosai da wannan karamci don haka tukuicina ga takwara wannan companyn nawa na kayan gine gine ko bayan raina na mallaka mata shi halak malak, sannan na ra’da mata suna Shuayra don na da’de ina burin na sakawa y’ata irin wannan sunan sai dai Allah bai bani ba, ashe Talatu ce zata haifa min y’a don dai wannan y’ar in dai na dawo da raina da lafiyata to ta dawo tawa Talatu.” Murmushi Talatu ta yi cikin karsashi da murna ta ce “Na bar miki halak malak Uwar Marayuz.” Hajiya ta rungumeta a k’irjinta tana karanta mata addu’oi a kunnenta, kafin ta sauketa nauyayyen barci ya ‘dauke Ayran da da take ta mutsu mutsu. Hajiya ta mayar da kallonta kan Talatu ta ce “Kin min alk’awari kin bar min ita ko? Jummai ku zama shaida?” Jummai tana dariya ta ce “Ai kuwa nice Shaida Hajiya muna dawowa za ki amshe a barki.” Ta zari check ta yi rubutu tana mik’awa Jummai “Maza aje a sake mata siyayya tunda takwara ce kuma y’ata ce kayan da duk wasu y’an gata suke sakawa zata saka itama…”
Takaicin Uba..

Nazeefah Nashe

42.


💔💔💔💔


Jummai ta amsa check ‘din tana murmushi a zahiri, a ba’dini kuwa bakinciki ne ya cika mata da zuciya, abinka da shaid’an tuni ya rinjayi zuciyar ya shiga k’issima mata abubuwa da dama, me yasa Tunda suke da Hajiyar ita bata mata kyautar ko da fili ba, sai yanzu da Talatu tazo daga sama cikin watanni biyar kacal da zuwansu har an dank’ara mata company guda. Ranta ya b’aci matuk’a ainun ta shiga k’issimawa a ranta ta yarda zata bi ta kori Talatu da yaranta daga gidan itama ta ‘dauko jikokinta Hajiyar ta dinga wahalta musu kamar yarda take wahaltawa yaran Talatu. Sam Hajiya da Talatu basu ankare da yanayin Jummai ba, suka cigaba da hirarsu Hajiyar na sake jaddadawa Talatu ta kula da gidan sosai duk da b’angarenta ba a bu’de zata barsa ba, za dai ta bar musu duk wasu abin buk’ata dangin su Abinci. Ta sake Aikawa aka kira Sarkin gida ta bashi ku’di ya siyowa Shuayra ragon suna a yanka mata.


Jummai tunda ta fita take sak’e sak’e abin duniya ya taru ya mata zafi, ina ma zata ga Mijin Talatu da ta nuna masa gidan ta tabbata hakan ne kawai zai raba Hajiya da Talatu da take nema ta zame musu k’arfan k’afa. Ina dalili su da suke zaune shekara da shekaru suna wahala ba a basu company ba sai wata Talatu. Allah dai ya dawo da su lafiya da kanta zata ja Sarkin gida su je har k’auyen Shagogo da ta ji Talatun ta basu labari ta nemi Kabiru ta gaya masa inda Talatu take, idan yaso ya zo ya tafi da matarsa da yaransa. Ta saki murmushi tana jin da’din shawarar da zuciyarta ta bata, hankalinta Kuma ya kwanta, kafin nan kuma zata yi k’ok’ari wajen ganin Hajiyar bata bawa Talatu takardun companyn ba kai koma ta bata sai sun k’wace ita da Sarkin gida bayan rasuwar Hajiyar don dai ta san Talatun bata da ilimin da zata nemi hakkin ta koda ta kai su kotu ne, Hajiya kuwa ta san tazo gangara kawai lokaci ake jira ciwon Cancer Ai da wuya a warke. Jummai kenan banda abinki wa ya san gawar fari?

Bata yi bak’in ciki ba ta zage ta siyowa Ayran tsadaddun kaya duk da dai ta samu rarar canji sosai ta kwashi kayan cike da bayan boot ta nufi gida. A falon Hajiya ta zuba kayan Hajiyar ta dubasu sosai ta ga sun mata yarda take so sannan ta ce Jumman ta kai mata Talatun. Jummai tana tattara kayan ta ‘dan dubi Hajiya a kaikaice kafin ta ce “Amma Hajiya da zan baki wata shawara, sai dai ina gudun kada ki ce na miki katsalandan.” Hajiyar ta ajiye littafin Azkar ‘din da yake hannunta tana duban Jummai cike da kulawa ta ce “Ina jin ki Jummai, ai duk mutumin k’warai yana son a bashi shawara, ba kiji mai mutane suke cewa ba aikin me shawara ba ya b’aci.” Jummai ta saki ajiyar zuciya tana ‘dan wasa da zoben hannunta. “Maganar companyn da kika yi kyauta da shi dama nake son miki. Kina ganin hakan bai yi sauri ba? Musamman ganin ba wani jumawa aka yi da su ba, har wa yau kuma ba a tabbatar da sahihancin labarin da ta bamu ba, ina tsoron kada labarin ya zama k’anzon kurege ko ta yi amfani da halinki na tausayin jama’a ne ta zo miki a haka.” Hajiya ta da’de tana kallon Jummai tana nazarin kalamanta, har Jummai ta fara jin tsoron kallon ta yi k’asa da kanta cikin rawar murya ta ce “Allah ya huci zuciyarki Hajjaju, idan shawarar tawa ta b’ata miki rai ne..” Hajiya ta saki ajiyar zuciya tana girgiza kai “Sam ba b’ata min rai ta yi ba, abinda kika fa’da haka yake ‘dan Adam abin tsoro ne, sai dai ni zuciya ‘d’aya nake abu idan ka cuceni kanka ka yiwa tunda ni don Allah na maka, don na bata company ba abinda zai girgiza daga dukiyata ke da kanki kin san a cikin kadarorina wannan companyn shine koma baya, ina da kadarorin da ni kaina ban san adadinsu ba, Iyayena sun bar min, y’an uwana da Mijina ya yi sanadiyyar su zuwa duniya suma sun bar min dukiya mai tarin yawa tunda ana gaf da aurensu ya saka musu guba suka ci duka su biyun maza rus suka mutu, duk don ya ha’de dukiyar mu ya handame, ban san me Zan Yi da dukiyar na musamman a yanzu da nake gargarar mutuwa don haka na rubuta duk wata wasiyya na yarda za’a kasafta dukiyata na bawa amintaccen Lawyer na wanda na san ko bayan raina ba zai haince ni ba, zai aikata abinda na saka shi, don haka ba damuwa idan tazo ne don ta cutar da ni ita da Allah, sai kiga kuma Allah ya kareni daga sharrinta tunda ni ban nufeta da sharri ba. Don haka ki kwantar da hankalinki, duk wanda yake k’ark’ashina zai samu kwatankwacin abinda Talatu ta samu bayan raina In sha Allah.”

Jummai ta saki ajiyar zuciya jin abinda Hajiyar ta ce duk da wani sashen na zuciyarta ya sanyaya bai hana Hassada tasiri a zuciyarta ta ba, ita fa wannan Kamfani da aka dank’arawa Ayra shine babban Tashin hankalinta, don haka sam wancan k’udirin da ta ‘dauka a zuciyarta ba zata barsa ba, da zarar sun dawo in dai ba ran Hajiya zata isa garin Shagogo ta gayawa Kabiru yanda suke.


Fuskarta ba yabo ba fallasa ta shiga inda Talatun take, daidai lokacin Talatun na zaune da Ayra a jikinta tana gasa mata cibiya. Ganin Jummai yasa ta washe mata hak’ora tana fa’din “Sannu da k’ok’ari nagode sosai.” Jummai ta gya’da kai ha’de da fad’in “Ai ki godewa Allah kin zo a sa’a, lokaci guda a dank’ara miki company.” Talatu ta ‘dan saki murmushi kafin ta ce “Wai Jummai Hajiya bata da y’an uwa ne?” Jummai ta kalleta shek’ek’e kafin ta ‘dan tab’e baki ta ce “Idan ma tana da su Ai kin fiye mata su yanzu tunda ban ji ba, ban kuma ga wanda Hajiyar ta bawa company ba sai ke, wai ni Talatu ya kika ce sunan uban mijinki a garin Shagogo?” Talatu ta ‘dan yi Jim kamar mai son ta gane abinda Jummai take nufi sai dai ba abinda ta gane don bata da wani wayon gane makircin mutane. Jummai ganin yanayin Talatun sai ta yi saurin gyara zamanta ta ce “Akwai wasu y’an uwana da suka tab’a zama a garin naku ne? Nake son sanin ko wajejenkune shi yasa kika ji na tambayeki sunan sa.” Talatu ta mik’a mata Shuayra tana fa’din sunansa “Iro Na Lami, duk wanda kika tambaya an san gidan duk da dai baya raye Amma an san shi ya yi suna sosai a garin.” Ra’dam Jummai ta haddace sunan a kanta, ta kalli Ayra tana murmushi kafin ta ce “Wannan y’ar taki duk tafi sauran kyau, yarinya kamar ‘d’iyar larabawa Ma sha Allah.” Talatu tana murmushi ta ce “Kamarsu ‘daya da Innata kwabo da kwabo har wannan lotsawar hab’ar da kumatunta na Inna ne.”

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login