Showing 126001 words to 129000 words out of 132090 words
Chapter 43 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt
motsi daga yarda yake sai Ayran ce ta zura Hijab ta je bu’de k’ofar. Tayseer da take tsaye da kaya a hannu tana kallon Ayran ta ‘dan k’unshe dariyar da take son kamata ta ce “Juliet ta romeo..” Ayra ta k’wace kayan tana harararta ta sake mayar da k’ofar ta rufe tana shirin saka kaya amma Turaki ya nuna bai san wannan ba don dole ta sake hak’ura ta biye masa. Kafin ya sake wanka ya shirya a gaggauce ya fice ‘daurin auren surikarsa. Ayra ta bi bayansa tana murmushi zuciyarta wani farin ciki take ji mara misaltuwa ta tabbata dai ta k’wace zuciyar Turakinta har abada ta cire masa kwa’dayin kowace y’a mace a cikin ransa.
__________________
Fadar ta sake d’inke wa dank’am su dai su Kabiru sai baza ido suke don har a lokacin ba su san me ya kawo su wannan aljannar duniyar ba. Ga manyan mutane da suke sake cika a fadar kowa cikin shiga ta kece raini sai busar algaita ce kawai take tashi a wajen.
Daidai lokacin Liman ya gyara zama ya ce “Za’a d’aura auren Maimartaba Waziri wanene waliyyin amaryar?” Mai martaba ya dubi mutanen Shagogo ya ce “Wanene zai zama Wakilin Talatu daga cikin ku?” Gaba ‘d’aya mutanen Shagogo suka zubo ido cikin mamaki Mai gari ya ce “Wace Talatun?”
𝖏𝖎𝖐𝖆𝖗 𝕹𝖆𝖘𝖍𝖊✍️💫
Takaicin Uba…..
Bakin da Allah ya tsaga…..
Mai Martaba yana murmushi ya zuba idanunsa cikin na Kabiru ya ce “Talatu dai Talatun Kabiru…”
Kabiru ya ji kansa yana juyawa kafin ya yi wani yunk’uri suka ji sallamar wani bafade yana fa’din “Ranka ya da’de akwai bak’o yana neman iso. Ya ce a ce maka sunansa Jabiru.” Mai martaba ya ‘d’aga kai don Talatu ta sanar da shi zuwan Jabiru “Ka ba shi izinin shigowa.” Sannan ya sake mayar da kallonsa kan Kabiru da ya yi mutuwar zaune yana jin wani sanyin nadama da dana sani yana kwaranya a b’argo da gangar jikinsa, a yau ya tabbata mara rabo a duniya idan bai yi wasa ba har a lahira matu’kar Talatu da ahalinta ba su yafe masa ba. Jikinsa ya fara rawa ya fara jin tsanar kansa musamman ganin kallon da jama’ar wajen suke binsa da shi wanda yake bayyana yarda suke Allah wadarai da halinsa ya tabbata gaba ‘d’aya labarinsa ya gama bazuwa a duniya. To tun fa anan kenan ina ga An je lahira yarda za’a tara mutane a sanar da su abinda ya aikata a kuma nuna musu su gani da idanunsu ya dafe kansa da ya ji yana sara masa kafin ya ce “Ya Allah ka yafe min.” Sai kuma ya runtse idanun nasa yana jin yarda hawaye suke kwaranya a idanunsa kamar an kunna famfo Kaico na ni Kabiru sharrin zuciya da son duniya na biyewa da kuma bin zugar aboki ya Allah ka yafe min ka tausashi zuciyar Talatu da yaranta su yafe min….” Sallamar Jabiru ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin da ya lula. Yana ganin Jabiru ya ganesa don kullum da tunaninsa yake kwana yake kuma wuni da kuma mafarkin sa don haka duk canjawar da Jabiru zai yi ba zai rasa shaida sa ba. Zuciyarsa ya ji tana neman wuntsilowa daga k’irjinsa da ya tuna bai san da me Jabiru shi kuma ya zo ba.
Jabiru ya k’araso cikin shigarsa ta kamala ta had’adden yadin fitex da aka masa ‘dinki iya gwiwa sai gajeran hannu da ya sake bayyana dattijantakarsa sai dai idan ka gan shi ba zaka je zai lamushe shekaru arba’in da ‘doriya ba, saboda yarda shekarun suka yi gaddamar nunawa a jikinsa da kamanninsa. Fuskarsa ba walwala sosai ya shiga fadar inda hankalin y’an shagogo gaba ‘d’aya ya dawo kansa. Ba za su mance da fuskar Jabiru ba fuskar da suka kora suka yi wa tofin Allah tsine. Jabiru ya zubawa Kabiru ido yana jin duk wani b’acin rai da ya taho da shi ya na zagwanye wa kamar aikin sihiri. Bai sani ba ko don ganin Kabirun a cikin wani hali na abin a tausayawa gaba ‘d’aya k’afafunsa sun shanye da alama kuma b’arin jikinsa ba ya aiki ma’ana ya samu paralyze. Sai dai yana kauda idonsa sai ya dinga hango hoton wancan lokacin da Kabirun yake cikin tashensa har yake aikata musu rashin mutuncin da ya ga dama. Idanunsa suka sake hasko masa ranar da ba zai tab’a mantawa da ita ba ranar da Kabirun ya runtse idanunsa ya musu sharri shi da Talatu matar da yake ‘daukar ta kamar mahaifiyarsa. Murya a cunkushe cikin ‘dacin rai ya yi furucin “Ba zan tab’a yafe maka ba.” A hankali yarda kowa ba zai ji me yake cewa ba. Sannan ya durk’ushe gaban Mai martaba yana jin kamar ya tashi ya shak’e Kabiru da ahalin da suka rakosa daga Shagogo. Da idanunsu ya dinga bin su da kallo ‘d’aya bayan ‘d’aya jin suna ambatar sunansa cikin mamaki suna fa’din “Jabiru dama kana raye?” Ya d’an saki murmushi mai ciwo kafin ya ‘daga musu kai yana mayar da kansa a kan Maigari yana tuno idanun Maigarin da suka dinga masa kallon tausayi sanda y’an garin suka jefe su da wancan mummunan sharrin. Murya a tausashe ya sunkuya gaban mai garin yana gaishe sa. Maigari ya d’an yunk’ura a hankali yana dafa Jabirun ya ce “Hukumullahi La ajabun, jama’a kun ga ikon Allah ko? Kun yarda da girman Allah ko? Ga shi nan cikin shekaru k’alilan Allah ya sauya rayuwar bayin Allahn nan, Wanda da ba’a yi musu duk abinda aka yi musu a Shagogo ba da tabbas ba su samu albarkar da Suka samu a rayuwarsu ba, a yau na yarda da maganar Malam bahaushe da yake cewa Wani Hanin ga Allah baiwa ne. Kabiru kai kuma ka ga ishara kai da abokinka ga shi nan tun a duniya ubangiji ya k’ask’antar da ku ya kuma fifita Talatun da Jabirun zuwa wani matsayi da baku isa ku taka shi ba.” Mai martaba ne ya yi gyaran murya jin wajen yana neman ya kaure da hayaniya ya ce Liman ya ‘daure aure. Ai kuwa nan da nan aka ‘daura auren Talatu da Baba Waziri akan sadaki dubu ‘dari biyar lakadan ba ajalan ba. Lamarin da ya sake gigita Kabiru da mutanen Shagogo jin yawan sadakin da kuma irin Mijin da Talatun da zata aura. Zuciyar Kabiru ta sake nauyi yana jin da yana da iko da ya tariyo Rayuwarsa ta baya ya gyara abinda ya gurb’ata a cikinta, sai dai tuni wannan damar ya kufce masa ya Riga ya aikata abinda ba zai tab’a gyaru wa ba har yaumuttanadi. Yarda wajen ya yamutse da hanayaniya da ihun marok’a yasa wani ba ya jin abinda na kusa da shi yake cewa har sai da Maimartaba ya tsawatar sannan ya mayar da kallonsa kan Kabiru ya ce “A da na yi niyyar idan aka kawoka na ‘daureka anan ‘daurin da ba me iya belinka a bursuna, amma a halin da na ganka na tabbata hukuncin Allah ya Riga ya sauka a kan ka tunda yanzu Allah shi tun a duniya yake hisabi saboda ba ya yafe hakkin wani a kan wani, haka ka’dai da Allah ya mayar da kai ya isheka ishara ya kuma nuna maka girman Hakkin Talatu da ka ci ba na wasa ba ne, ba’a tab’a bayin Allah Ubangiji ya kyale, saboda Allah da kansa yakewa bawansa yak’in musamman idan bawan nasa ya zama mai mayar da dukkan lamarinsa gareshi sai Allah ya dinga masa yak’i a kan duk wani abu na cuta da zai tunkaro shi ba boka ba Malam sai ka ga mutum ya gagari mak’iya da mahassada har a yi zaton da wani abu da yake aikatawa ta bayan fage alhali ba abinda yake aikatawa sai tsananin dogara ga Ubangiji da mayar da dukkan lamarinsa gareshi don haka y’an uwa mai rik’o da addini da bin abinda Allah ya umarcemu da kuma gujewa sab’a masa shine abinda zai sa ka ka gagara irin gagarar da za ka ji ana Ya gagari gasa. Zan saka Talatu da yaranta su yafe maka har Jabiru ma don tun a duniya ka ga shaida girman hakkin wani ka kuma shaida Allah yana amsa addu’ar wanda aka zalunta don ka zaluncesu kuma na tabbata daka zaluncesu sun yi addu’a sun ce Allah ya saka musu ga sakayyar nan ka na gani Allah yasa y’an baya su yi koyi da darasin da ya sameka idan suna da niyyar cin zali su san ba abu bane mai kyau. Allah ya kyauta yasa kuma wannan ya zamewa duk wani mai hali irin naka Ishara.” Kabiru da Hadi sunkuyar da kansu kawai suka yi Jabiru ma ya sake bin su da kallo ya ji har a zuciyarsa ya yafe musu don a yanzu sun zama abin tausayi duk da ba a san gawar Fari ba Amma ya tabbata ba za su ja lokaci mai tsawo ba.
Mai martaba ya saka aka mayar da su fadarsa ta cikin gida kafin a kai musu abinci da ruwa da lemo aka musu tarba dai ta alfarma sannan yasa a kira Talatu da yaranta su zo su gaisa har ma da Mazajen yaran Talatun da duk suma suka zo Gombe a safiyar yau ‘din. Ayarin Talatu suka sak’o ta a gaba har da Ummeey suka nufo fada Ayra ma Turaki ya saka mata alkyabba sannan ya rik’o hannunta suka nufi fa’da cikin takun k’asaita yana tafe yana murza hannayenta da ya sake jin sun yi taushi na masifa.
Gaba ‘daya ahalin Shagogo zuba ido suka yi suna kallon zuri’ar Talatu shi kansa Kabiru kallon yaransa yake cike da k’auna yana mamakin yarda y’ay’an nasa suka hayayyafa suka samar masa da kyawawan jikoki, Jikokin Talatu 18 maza da mata daga yaranta guda hu’du nan gaba kuma ba’a san me Ayran zata haifa ba da sauran Da ba su daina haihuwa ba. Yara kyawawa da su kalolin y’ay’an hutu yaran da ake kira ajeboters. Kabiru ya dinga kallonsu kamar ya janyosu duka ya rungume su yana tunanin yaran mazan da ya dinga alfahari da haihuwarsu a yanzu ba wani da zai nuna ya yi alfahari da zamowarsa ‘dansa har gwara Ahmad shine mai dama dama a cikinsu. Ayra ta zube idanunta cikin nasa tana jin zuciyarta tana sake tafasa musamman da ta runtse ido tana gano shi a kanta yana k’ok’arin keta mata haddi. Kawai sai ta ji jikinta ya fara rawa Lura da hakan Turaki ya sake damk’ar hannunta yana janta kujera ya zaunar da ita a gefensa yana ‘dan Petting bayanta. Hawayen da ya gani a idanunta shi ya sake b’ata ransa shima ya dinga kallon Kabirun cike da tsana don Ummeey ta ba shi labarin Kabirun in briefly. “Relax Ayra! Ba abinda zan bari ya cuceki in dai ina nan.” Ayra ta kwanta a jikinsa sosai tana jin yarda amai yake k’ok’arin zubo mata da gaske bata son ganin fuskar mahaifinta da ta san kuma shi zata gani ba abinda zai kawota nan. Amma kuwa ko kallon Kabirun bata sake yi ha tunda ta masa kallon farko. Ta ‘dauke kanta cike da takaici tana k’arasawa gaban Mai gari jama’ar wajen na kallonta cike da sha’awar yarda ta koma ta durk’ushe a gaban Maigarin tana gaisheshi. Murmushi ya yi yana amsa mata cike da kulawa ya ce “Allah Ubangiji ya miki albarka, ga Kabiru na kawo miki don Girman Allah ku yafe masa ko a haka aka tsyaa yaga isharar rayuwa ba zan so ya tafi lahira da wannan babban zunubin ba. Ki tuna Allah ya miki komai a rayuwa ba abinda ki ka nema kika rasa shi kuma ki ga yarda Allah ya mayar da shi a rayuwa ki yafe masa Talatu idan kika aikata haka ko a wajen Ubangiji kin fi shi.” Talatu ta runtse idanunta tana ha’diyar wani abu ga wani sanyi da yake ratsa zuciyarta tana jin wancan b’acin rai yana melting yana zama farin ciki a zuciyarta, hannayen Baba Waziri ta ji a cikin nata ya mik’ar da ita tsaye ba tare da la’akari da mutanen da suke wajen ba ya zaunar da ita a kujera ta musamman inda yake zaune a gefenta murya a tausashe ya ce “Bu’de idonki Bod’do ba abinda zai sake tayar min da hankalinki matuk’ar ina kusa, ki yafe masa kawai kin ji Gimbiyar Waziri.” Ya fa’da yana mik’a Mata handkerchief ‘din hannunsa Talatu ta saki murmushi a hankali tana mayar da kallonta kan mutanen da suke wajen Musamman Kabiru da ya kafeta da ido yana jin zuciyarsa kamar ta b’alle ta fito don turirin bak’in ciki, a yanzu kam ya san Talatu ta masa nisa har abada ta kuma samu Miji na kere sa’a. Talatu ta sake gyara zaman ta tana fa’din “Ya ci albarkacin Mai gari ya ci albarkancin Uba na Mai martaba ya kuma albarkacin Mijina na yafe masa, ina kuma rok’a masa yara na su yafe masa Allah ya yafe mana baki ‘d’aya.” Gaba ‘d’aya wajen aka ‘dau Kabbara Kabiru ya saki wata ajiyar zuciya yana rik’e k’irjinsa da ya damesa da ciwo ya koma ya jingina da keken guragun da yake zaune a kai ya lumshe idanunsa yana jin hawaye na sake shatata daga idanunsa.
Haka nan Taron ya watse bayan Maimartaba ya tabbatar da Yaran Kabirun sun yafe masa har Ayra duk da dai a da ta turje Amma daga baya da Turaki ya dinga lallashinta ya na nuna mata mahaifinta ya kusa rasuwa yafiyarta kawai yake nema sai ta ji zuciyarta ta karye ta ce ta yafe masa hawaye yana zuba a idanunta. Zuciyar Kabiru ta ‘dan yi sanyi daga zafafar da ta yi sai dai yana jin yarda zuciyarta da take aiki kamar ba daidai ba don tana tsayawa cak a lokaci guda kamar zata daina aiki.
Ganin dare ya yi Maimartaba ya hana su tafiya ya saka aka bu’de musu wani b’angare ya ce su kwana zuwa da safe su tafi.
Sai dai cikin daren Kabirun wani irin ciwon k’irji ya matsa masa ga shi zuciyarsa ba ta bugawa yarda ya kamata. Numfashinsa ma sama-sama yake fita yana furzar da wani irin haki mai bayyana halin da yake ciki. Kamilu a guje ya je kiran Jabiru sai dai ko kafin Jabiru ya zo Ran Kabirun ya yi halinsa sakamakon zuciyarsa da ta daina aiki ta tsaya cak da alama ya samu heart attack. Jabiru da ya k’araso a ki’dime hankalinsa a tashe ya dinga duba Kabirun, sai dai ba numfashi ba alamarsa. Idanunsa sun ka’da sun yi jajir ya ‘dago yana kallon Kamilun da ya shima ya kafa masa nasa idon cikin tashin hankali “Jabiru me ya faru ka yi magana mana.” Jabiru ya ‘dan d’auke kai murya a dakushe ya ce “He passed away. Allah ya gafarta masa.” Wani irin kallo mutanen wajen suka dinga bin sa da shi a ru’de suna duban agogo da yake buga k’arfe 4:00 na asuba daidai safiyar Alhamis. Kamilu ya runtse idanunsa yana sake bu’dewa ya ware su a kan Kabirun da ake kira gawa. Shikkenan yanzu Kabiru ya mutu ba zai sake jin muryar ‘dan uwansa ba, shikkenan rayuwar fa shikkanan an yi an gama, ashe Kabiru yana da rabon sake ganin zuri’arsa y’ay’a da jikoki shi yasa suka zo Gombe ashe rabon ganawarsu ta k’arshe ne, rabon Talatu zata yafe masa ne Ya Allah ka yafe masa don girman zatinka Allah ya ji k’an ka Kabiru.” Kamilu ya fa’da yana jin zuciyarsa na karyewa tsoron Allah na sake shigarsa. Ya ja mayafi ya rufe fuskar Kabirun da shi.
Sai da aka fita sallahr asuba, sannan suka sanar da rasuwar Kabirun. Ba wanda bai girgiza da lamarin girman Ubangiji haka nan mutuwar ta dinga kara’dawa a masarautar har sanda Talatu da ahalinta Suka
Ji. Ayra ce ka’dai bata ji ba tana can ‘b’angaren Turaki tana barci don bata samu cikakken barci ba dalilin zazzafan zazzab’i da amai da ya sakata a gaba. Turaki mutuwar ta daki k’irjinsa ya dinga kallon Jabiru da yake sanar masa da mutuwar kawai sai ya ji hankalinsa ya tashi. Ana idar da Sallah ya ja k’afafusna da suka masa sanyi ya isa gidan yana tunanin ta yarda zai sanar da Ayra mutuwar mahaifinta Mahaifinka komai ya yi maka dole zaka ji mutuwarsa. Cikin sanyin jiki ya tura k’ofar d’akin. A bakin gadon da take kwance ya tsaya yana bin fuskarta da kallo ya ‘dan shafa wuyanta ya ji still da zazzab’in a hankali ya saki ajiyar zuciya yana saka hannayensa ya ‘dagota kafin ya ha’data a jikinsa a Kunne ya dinga kiran sunanta. Ta bud’e idanunta da suka mata nauyi tana kallonsa. “Sallah.” Ya fa’da a hankali “Tashi kada ki makara.” Da k’yar ta mik’e sai da ya taimaka ta ta shiga toilet ‘din ta yi wanka sannan ta yo alwalar ta zura doguwar rigarta bak’a da ta shigo da ita a daren jiyan ta tada sallah kakkarwar da jikinta take tana k’aruwa. Turaki na ankare da ita. Sai da ya barta suka yi Azkar don shima bai yi ba sannan ya mik’ar da ita “Tashi mu shiga cikin gida idan Abba Jabiru na nan ya duba jikin ki zazab’in nan da amai ya takura miki.” Ta saka kanta a kafa’darsa a hankali ta ce “Abban Amaan don Allah ka k’yaleni na yi barci.” “Mu je mu dawo sai ki yi barcin.” Ya damk’i hannunta ha’de da sakata a b’arin jikinsa d’aya ya rungumota ta sake lafewa a jikinsa tana jin kamar k’afafunta ba za su iya ‘daukar ta ba. A haka ya dinga jan ta a hankali har suka isa b’angaren Ummmeey nan Ayra ta ga kowa yana ta kuka musamman y’an uwanta su Zainab. Hankalinta a tashe ta fara ware ido tana neman in da Amma take don kawai sai ta ji zuciyarta ta tsinke saboda kukan da suke ya yi kama da wanda ya rasa Uwa ko Uba….
𝔍𝖎𝖐𝖆𝖗 𝕹𝖆𝖘𝖍𝖊✍🏽
Takaicin Uba.
Episode finale…..
Komai ya yi farko zai yi k’arshe yau ne na kawo k’arshen book ‘din Takaicin Uba, ina rok’on Ubangiji ya yafe min kuskuren da na yi a ciki. Ku da kuka samu damar karantawa da ba ni lokacin da kuka yi da dukiyarku Ubangiji ya saka muku da alheri. Nagode sosai da sosai musamman y’an group