Showing 1 words to 3000 words out of 132090 words

Chapter 1 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt

*********************


TAKAICIN UBA……📝📝📝

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️


Na

Nazeefah Sabo Nashe..


Daga k’ungiyar Elegant Online ✍🏽


Arewa books
@nazeefah.

Wattpad
@Nazeefah381.

08033748387.


(Alhamdulillah cikin hukuncin ubangiji na sake zuwa muku da wani sabon littafi masoyana, da nake fatan ya faranta muku fiye da na baya a kullum da ku nake alfahari. Ina sake mik’a godiya ta gareku dafatan Allah ya karb’i ibadunmu.)

Daga alk’alamin marubuciyar


Me Zan yi da ita?

Da

Ya abin yake?


Mafari……………..


******************************


Page 1


A zafafe ta fito daga office d’in Cikin sauri tamkar zata tashi sama. Da sassarfa sosai ta isa wajen tarin jerin motocin da suke fake a parking lot d’in da yake ma’aikatar. Ba tare da damuwa ba suke ta darewa suna bata hanya don ba sabon abu bane a wajensu a tarin lokuta suna yawan ganinta a haka, cikin wannan yanayin mai firgitarwa. Sai da ta tattare zumbulelen bak’in hijab d’inta da ya zame mata tamkar uniform saboda duk wanda ya san AYRA GAYA da wannan shigar ta dogon black hijab mai jan k’asa ya santa, da kuma black nik’ab. Da wuya a samu mutumin da ya san zallar kamannin na AYRA GAYA in dai ba makusancinta ba shak’ik’i ko kuma daga cikin y’an uwanta sai kuwa abokanta na makarantun primary da secondary da wanda ya santa shekaru goman baya da suka wuce, don na jami’a ma d’aid’aikune suka san zallar kamannin na AYRA GAYA.

Da zafin nama sosai ta finciki kan motor, haka yanayinta yake komai a zafafe take yinsa tamkar namiji so take lallai sai ta maye wa mahaifiyarta haushin rashin haihuwar d’a namijin da ake cewa ba ta yi ba. A gareta duk abinda wani d’a namiji zai aikata za ta aikata irinsa koma kai tsaye ta bugi k’irji ta ce zata aikata wanda ya fi shi. Ta fi yarda da cewa What Man can do woman can do better, fiye da what Man can do woman can do. Duk wanda yake cikin ma’aikatar bin ta suka yi da kallo suna tabbatarwa da kan su cewa yau ciwon AYRA ya motsa don sun fi danganta ta da mai cutar jinnu ko tab’in hankali saboda yanayin yarda take mu’amalantar mutane halayenta gaba d’aya ya farrak’a da na mutane sai dai masu shafar jinnu. Yanzu zaka ganta da sanyin hali anjima kaga ta murd’e ta zama wata iriyar mace mai bak’ar zuciya mai zafi da saurin fushi.

Ta ko ina take jefa motar har zuwa sanda Allah ya kawota unguwar Rail way inda anan ne suka tanfatsawa mahaifiyarsu gida ita da y’an uwanta su hud’u har ita cikon ta biyar d’in kafataninsu zallar mata.


Horn d’in da ta dinga dannawa Mai gadin a zafafe ne ya tabbatar masa da cewa yau Uwar d’akin nasa ba lafiya ba, don da lafiya take idan ta yi sau biyu bai zo ya bud’e ba da kanta take zuwa ta tura gate d’in ta kan ce masa “Yi zamanka Baba na san hutawa kake bana son katsewa mutum hutunsa musamman idan barci ya d’aukeshi balle kai da shekaru sun ja.”

Yau kam ya san tunda take wannan gigitaccen horn d’in ya tabbata aljannun uwar d’akin nasa sun motsa. Sai da ya ja Innahu min sulaimanu sannan ya bud’e gate d’in abinda ya ke zargi ya tabbata domin dai ko glass d’in motar bata sauke ba balle ya saka ran samun gaisuwa kamar yarda duk ta saba idan tana cikin sukunin zuciya da walwala. Madadin haka ambaleshi da iska ta yi a zafafe ta kai kanta ma’ajiyar motocin gidan.

Da k’arfi ta tura k’ofar da zata shigar da kai ainahin harabar tsakargidan kafin shiga main parlour na gidan. Tun a waje dama ta shaida zuwan y’an uwanta ganin motocinsu duka a wajen.
Ta sani sun zo don su d’aga mata hankali kamar yarda suka saba su saka mahaifiyarta ta kwana tana mata mita akan rashin aurenta kamar a kansu take zaune. Kafin ta shiga sai da ta tuge nik’ab d’in da yake fuskarta sannan ta tura k’ofar. Ga hasashenta kuwa suna zaune zagaye da mahaifiyarsu, yaransu a gefe suma.
Hutun makaranta ake ta san shi yasa suka zo da su.

Tsam ta d’inke sauran annurin da yake fuskarta ta tattare ta waje d’aya kamar ba a tab’a halittar dariya a fuskarta ba. Cikin wani irin taku mai nuna a shirye take da tunkararsu da duk wacce suka zo ta isa wajen su. Kafin ta zauna tana cin magani tana kuma amsa gaisuwar da y’ay’ansu suke mata tamkar bata so, don gaba d’aya idonta ma Akan screen d’in waya yake. Sai da ta runtse ido ta bud’e Kafin ta zare bak’in shade d’in da yake idonta. Su Kansu ba yaran ba Sai da suka razana da ganin yarda k’wayar idanunta suka jirkice zuwa launin ja. Murya a cunkushe ta zube idanunta cikin na Babbar yayarsu kafin ta ce “Ina yininku?” Tana nufin gaba d’ayansu don bai Zama lallai ta bi su d’aya Bayan d’aya ba. Jikinsu a sanyaye cike da kulawa suka fara amsa gaisuwarta. Suna sonta sosai fiye da duk tunanin mai karatu, wani irin so suke nuna mata da gata da yasa ko kad’an ba sa son ganin b’acin ranta, burinsu gaba d’aya a kanta yake suna burin kyautata rayuwarta da samar mata da farin ciki fiye da nasu farin ciki ba su sani ba ko don kasancewar ta taso da wani tabo a zuciya mai wuyar gogewa. So suke su d’auke mata wancan bak’in fentin na mahaifinsu da ya yi naso a zuciyarta har ya haifar da rud’ani da k’iyayyar jimillar maza a zuciyarta, har hakan yasa ta yiwa maza kud’in goro ta kuma k’addara ba zata tab’a aure ba a rayuwarta, duk da tarin baiwa da Allah ya bata na wani irin kyau cikar haiba da zati hakan yasa take b’oyewa maza jikinta da fuskarta don kada ma su kwad’aitu da son aurenta, ba ta son ko kad’an a mata zancen aure duk da kasancewar a shekarunta ya kamata ace tana da auren shekara ashirin da shidda cif. Ta sha alwashi a zuciyarta duk sanda y’an uwanta suka mata aure ba tare da amincewarta ba tabbas za su d’au gawarta a washegari a gidan mijin, don tabbas sai ta kashe kanta.

Sab’anin nata burin, y’an uwanta burinsu ta yi aure burinsu yau ace ga mijin AYRA, su duk tunaninsu jinnu ne ya aureta duk da suna tunanin wancan bak’in fentin da mahaifinta ya shafa a zuciyarta ne yake biyayyar ta sai dai hakan ba zai saka ya zama gamsashshiyar hujjar k’iyayyar maza a zuciyarta ba. Duka-duka shekarunta nawa a duniya sanda lamarin ya faru? Bai kamata ya zame mata hujja ba da zata tattare duka maza ta saka su a mizani d’aya ba.

Sakin ajiyar zuciyar da mahaifiyarsu ta yi shi ya dawo da dukkansu daga tunanin da suka afka. Yaya Dija da tafi kusa da ita da sauri ta dafata “Please Ammaty kada ki saka damuwar da zata zame miki lalurar da zamu rasa ki mu shiga uku kin dai san ke kad’ai muke gani ki zame mana farin ciki a rayuwa AYRA bata da asara tunda tana sani take saka ki b’acin rai,ki godewa Allah tunda dukkanmu muna d’akin mazajenmu ita kad’ai ce mai kafaffiyar zuciyar da ta kasa gusar miki da b’acin rai itama kuma da ikon Allah lokacin ta yazo k’arshe za mu sadata da d’akin miji ko sadakarta za mu bayar.”

Wani kallo AYRAn ta kafe Dija da shi don dama duk ciki tafi raina ta musamman kasancewarta sak’uwarta ta mik’e a zafafe tana wurga mata kallo kafin ta ce “Idan kun tashi sada ni da d’akin miji Ku tabbata kun tanadi likkafani da duk wani abu da kuka san mamaci zai buk’ata don ina tabbatar muku tabbas suna na gawa a gidan duk uban da ya yi tsautsayin aurena, haba ku k’yaleni mana rayuwarku ko tawa shin ban tsare kaina bane? Ko rashin aure ya saka ni aikata zina? Ba zan aure ba na sake jaddada muku tunda auren ba wajibi bane a musulunci balle ace ya zama farilla.”

Yarda take maganar sosai zuk’atan su suka sake samun rauni don zahirin abinda yake k’ark’ashin zuciyarta take fad’a da kuma duk wani tarin confidence d’inta a yarda take tabbas idan aka mata auren zata iya aikata kashe kan nata kamar yarda take fad’a ba wai iya kan harshenta abin nata ya tsaya ba a’a har k’asan ranta iya zallar gaskiyar kenan. Kafin su yi wani yunk’uri tuni ta burma kanta cikin d’akin da ya zama mallakinta ne a gidan ta kuma rufo k’ofa da k’arfin gaske wanda ya yi daidai da kece wa da kukanta.

Amma tabbas yau ta yarda bata tantama AYRA jinnu ya aureta. Kuka take tana fad’in Ya Allah ka taimaki ne akan yarinyar nan ni ba wani namiji tsayayye da zai tsaya min akan lamarinta ba, Ubanta kuwa da shi da babu a wajena duka d’aya Ya Allah kada ka d’au raina ban ga auren AYRA ba.” Eesha ta ja ajiyar zuciya kafin ta kama tafin hannun Amman tasu ita kanta kukan ne yake son k’wace mata ga shi nan dai yanzu auren yaransu za’a fara amma ita AYRA ta k’i ta bud’e fuskartata ma maza su ganta balle su sota kullum fuska a dunk’une cikin nik’abi, jiki a na’de cikin burgujejen Hijabi, bata hoto ma balle ka nunawa wani ko zai so ta, duk da su kansu sun san gangancin gaske ne su aurar da ita ba da son ranta ba, yarda Ayran take da zafin zuciya kamar siya mata tikitin tafiya lahira ne, ko bata rantse ba sun yarda da tace ko an yi auren ma kashe kanta zata yi wa ya aikesu wannan ganganci gwara su zuba mata ido har zuwa sanda Allah zai yi ikonsa a kan ta.

Kaf d’in su hawayen suke har da y’an matan y’ay’ansu da ake zancen aurar da su nan da watanni kad’an masu zuwa lamarin AYRA kowa da shi yake kwana yake tashi. An sha yi mata ruk’ya amma babu alamun jinnu tare da ita, kawai ta d’arsa wa kanta tsanar maza ne a zuciyarta tun tashinta.

To fa! Ko mai Uban AYRA ya aikata mata da ya d’orata a tubalin k’in maza da aure ma gaba d’aya. Za mu ji anan gaba kad’an Ku dai Ku biyo JIkar Nashe.



Ku shiga link ‘din nan don samun labarin a sauk’ak’e a can kawai zan dinga posting. Daga yau nagode.


https://chat.whatsapp.com/EZyeAwHEGGhJz1pRBmmale
Takaicin Uba…..

Na

Nazeefah Sabo Nashe..


08033748387.

❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

2..





Zainab da tun shigowarsu bata ce komai ba, don tana da zafi idan ta ce zata biye ta Ayra fes zata mata mugun duka, sau tari Ayran ta fi shakkarta fiye da kowa a cikin y’an uwanta, don da wuya ta kulata amma duk ranar da ta bari ta kaita bango ranar Zainab d’in marinta take. Itace Yarsu ta biyu amma ta fi shakkarta fiye da Majeeda Babbar Yayarsu. Huci kawai take tana jin takaicin Ayra na sake katantawa da zuciyarta. Bak’in cikinta d’aya yarda za su fara aurar da d’iyoyin cikinsu Ayran na zaune a gida kuma ba wai rasa mazajen auren ta yi ba, tun bayan da ta fuskanci kyanta da jikinta ya na janyo hankalin maza gareta tun kafin ta gama Secondary school sai ta k’irk’irarwa kanta sanya dogon zumbula zumbulan hijabs kuma bak’ak’e wuluk da su. Ta bi kuma fuskarta da nik’ab ta k’unshe harta da hannunta sai ta sanya masa hand gloves da k’afafunta idan ka ganta sai ka zata d’aya daga cikin y’an k’ungiyar Shi’a ce.

Ajiyar zuciyar da ta ja mai k’arfin gaske ya dawo da hankalinsu kanta. Ta d’ago fuskarta a had’e sosai kafin ta ce “Ammaty da laifinki kema, ya kamata ki nunawa Ayra ke kike iko da ita kuma kin isa ki zartar da hukuncin da ya wajaba ta bi shi da son ranta ko babu umarni ne Allah ya bata, kina da damar da zaki aurar da ita ga duk wanda kika so.” “A aurar da ita ba da amincewarta ba ta kashe kanta kenan ko?” Babbar yarsu Majeeda da ta fi su sanyin hali kusan duk ita ta d’auko halayen Amma ta fad’a idanunta cikin na zainab k’anwarta mai bi mata.
Cikin takaici Zainab ta saki murmushi kafin ta ce “K’aryar banza ce ba zata kashe kanta ba wallahi kawai don ta saka mu k’i mata auren ne take wannan furucin, kuma raina mu ta yi don taga Amman bata da wani tsayayyen namiji da zai jajirce a kanta, ina ma Kawu Saddi zai dawo da naga uban da zai hana shi aura mata duk wanda ya yi niyya.” Amma kallon Zainab kawai take kafin ta girgiza kai “Tsaf zata aikata kisan kanta, kamar ba ki san kafiya da taurin zuciya irin na Ayra ba, da wannan tunanin fa ta tashi a zuciyarta, K’iyayyar maza a ranta take tun bayan da mahaifinku ya d’arsa mata hakan a ranta, ku cigaba da yi mata addu’a dai Allah ya kawar da wancan lamarin a zuciyarta ya sanya mata nutsuwa da tunanin cewa mazan ba duka suka taru suka zama d’aya ba, Allah ya mata jagora ya sa naga auran Ayra kafin kushewata.”


Ayra kuwa tana shiga d’akin cikin b’acin rai ta tub’e suturun jikinta daga ita sai underwear ta shige toilet ta saba a yanayi irin wannan sai ta sakar wa kanta ruwa take samun sukuni. Gaba d’aya ta ware shower d’in a kanta tana burin zuciyarta ta sassauta daga yanayin b’acin ran da take ciki, amma ina kamar ana sake angizo mata b’acin ran, hotunan lamarin suna sake mama ye ganinta tamkar yanzu abubuwan suke faruwa ta runtse idanunta ta shiga dukan bango da dukkan k’arfinta kai kace zata ruguza duka tiles d’in toilet d’in ko zafin hannunta bata ji, hawaye kuwa zuba yake sosai a idonta. Ta tsaneshi ta tsani mahaifinta tsana mafi muni, bata jin har ya koma ga ubangiji zata yafe masa tarin laifukansa, bata ji ko mutuwa ya yi zata d’aga hannu ta rok’a masa gafarar Ubangiji. Tsawon lokaci tana cikin wannan yanayin kafin ta fito daga cikin tub d’in sanye da rigar wanka bata damu da tsiyayar ruwa da gashinta yake yi ba, ga wani irin kakkarwa da jikinta yake saboda ruwan sanyi ta sakarwa kanta duk da kuwa muku mukun sanyin da ake. Ba abinda ta yiwa jikinta illa towel da ta saka ta nad’e gashin kanta haka ta shige cikin blanket ta k’udundune kanta tana rawar d’ari sosai zazzafan zazzab’i ya rufeta ban da Amma ta hanata da tuni ta maka wancan Uban nasu a kotu.. tunanin da take kenan tana cizon leb’en bakinta da har suke fitar da jini Saboda datsesu da take yi.

Kamar Amma ta san za’a yi haka ta biyo bayanta ita da Dijah da Majeedah. Suka ci sa’a k’ofar d’akin a bud’e take bata rufeta ba hakan yasa suka shiga kansu tsaye, da sauri Amma ta k’arasa gadon don daga inda suke suna juyo sautin had’uwar hak’oranta da suke bayyana alamar halin da take ciki. Amma na k’ok’arin yaye bargon Ayra na ja tana sake k’udundune jikinta murya a shak’e alamar kukanta ya tsananta take cewa “Barni na mutu Ammaty, tunda ba kwa son rayuwata, wallahi da na yi aure na zauna k’ark’ashin wani namijin gwara na mutu tun yanzu zuciyata suya take da zafi daga zancen auren ma ina ga an yi auren na tabbata idan ban kashe kaina ba zuciyata kuwa zata buga da kanta na mutu ku huta.”

Cikin azama Amma ta jata jikinta ta rungume ta tausayi sosai take bata kuma laifinta ne da bata wayar mata da kai tun tana k’arama ba ta bari abin ya girmama a zuciyarta bata sanar mata Mazan ba halinsu d’aya ba kowa da halinsa, yanzu y’an uwanta ba gashi suna zaune da mazajensu lafiya ba cikin so da k’aunar juna, tun a lokaci bukukuwansu Ayran ta sha fad’ar ba zata tab’a aure ba, kuma ko mazajen nasu bata wa magana a zaton Amma duk wasa take bata san lamarin ya yi tasiri a zuciyar Ayra ba ta yarda ta dunk’ule maza waje d’aya ta lak’kaba musu halaye guda. “Kunna room heater Dija jikinta da zazzab’i sosai. Ki kuma kira min y’an uwanki na sake kafa musu sharad’in da duk wanda ya k’etare sai dai ya nemi wata uwar ba ni ba, ba zaku hallaka min yarinya ba tunda ba a kanku take zaune ba, ba kuma ta tab’a jawo min abin magana ba.” Amma ta fad’a cikin b’acin rai zuciyarta cike da tausayin Ayran. Da sauri ta ja Hand dryer tana busar mata da gashin kanta kafin ta shafa mata mai a sassan jikinta ta zura mata doguwar Riga mai nauyi sannan ta saka mata rigar sanyi shayi mai zafi ta saka Dija da suke tsaye jigum jigum ta had’o mata haka ta tilasta mata ta sha duk da tana turjewa sai da ta gama Amman ta hau murza mata k’afa sannan ta kalli sauran yaranta da suke tsaye musamman Zainab da ta fisu uzzira wa Ayran akan aure “Kada wanda ya sake mata maganar aure bana so, tunda ba a kanku take zaune ba, duk cikinku ba wanda ya fuskanci irin matsalolin mahaifinku fiye da ita a rayuwa ta taso da abin a ranta don haka tilastawarku ba zai sa ta mance da wancan k’addarar ba har ta yi aure ku barta haka nan idan Allah ya nufa zata yi aure zata yi idan bai nufa ba ku k’addara hakan Allah ya rubuta mata ba kuma wanda ya isa ya canja k’addarar bawa. Ba y’ay’a za ku aurar ba ko
Jikoki ku aurar shi Aure lokaci ne ko bayan raina kuma ban amince muku ku tialsta mata ba doka ce na saka musamman ke Zainab na fad’a na sake fad’a.”
Tsit d’akin su kayi, ita kuwa Ayra farin ciki ne ya kamata duk
Wani nauyi da zuciyarta ta yi tuni ta yi k’asa a yau Kam ta tabbata Ammaty ta tace tana kuma gudun b’acin ranta. Ji ta yi kamar ta tashi ta taka rawa ta dinga kallon Zainab tana dariya k’asa-k’asa kafin ta ja bargo ta kwanta bayan ta sha maganin saukar da zazzab’i ta lumshe idonta barci mai dad’i yana d’aukarta. Amma ta tisa k’eyarsu a gaba suka fice. Ko a falo jajanta lamarin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login