Showing 12001 words to 15000 words out of 132090 words
Chapter 5 - TAKAICIN UBA Book Complete by Nazifa Sabo Nashe.txt
a ciki, gaba d’aya haushin Ummeey ya gama dabaibaye zuciyarta gani take kamar tana shirin rusa mata farin cikinta ne. Ko da ta hau sama bata koma d’akinta ba don bata buk’atar hayaniyar twins direct d’akin Amma ta shige ta kullo har da murza key. Tana buk’atar kad’aicewa don samun sauk’i daga rad’ad’in da k’irjinta yake mata.
Hameeda na ganin ta gama hawa Stair case d’in ta mayar da kallonta a kan Amma da kanta yake a sunkuye. Tsam ta mik’e ta dawo kusa da ita ta sake kama hannayenta a karo na biyu ta ce “nuna b’acin ranki ba shi zai kawo warwarar matsalar yarinyar nan ba, anya kuwa babu jinnu a cikin lamarinta?” Amma ta k’ura mata ido kafin ta girgiza kai murya a sanyaye ta ce “Babu wani jinnu a cikin lamarinta, illa TAKAICIN UBA da ya gigita tunaninta ya kuma saka mata tsanar maza had’e da jingina musu suna d’aya..” Amman ta fad’a wannan karan muryarta sosai ta karye ta shiga zubar da hawaye “Mahaifinta shi ya kambama tsanar maza a zuciyarta tun tana da k’uruciyarta har ta tashi da abin a ranta, ni kuma na yi sake da na barta har yanzu ban aurar da ita ba, na bar zuciyarta a kan wancan tunanin da zaton wata rana zata fuskanci ba haka bane. Na yi nadamar hakan da na sani tunda k’ank’antar shekaru na aurar da ita, ni kuma tausayinta ne ya rinjaye ni, na fi tausayinta k’warai da gaske fiye da y’an uwanta ko don k’addarar tafi girma a kanta fiye da su.”
Shiru Hameedah ta yi tana son tambayarta wacce k’addara ce amma bata fiye son k’ure mutum ba, da ta so da kanta zata fad’a mata ba sai ta tambayeta ba. Madadin yi mata kutse cikin sirrinta sai ta kawar da wancan zancen ta sako wani “Da zaki amince da na ce miki matsalar Ayra koma wace iri ce ta zo k’arshe, ki amince a wannan karan kuma ki jajirce ki bani had’in kai mu had’a aurennan da sonta ko ba son ranta na san In sha Allah babu abinda zai faru sai alheri.”
Shiru Amma ta yi tana son ta bada goyon baya, tana tsoron tashin hankalin Ayran wanda bata san mai zata aikata ba, kada ta je zancen da take ya tabbata na kisan kanta a duk yayin da ta bud’i ido ta ganta a gidan aure, don haka ta kasa amincewa Ummeey illa jinginar da kanta da ta yi jikin kujera ta lumshe idanunta a hankali ta ce “Ki bani lokaci na yi shawara, koma me kenan In sha Allah za ki ji.” Ummeey ta saki hannayenta had’e da cewa “Allah yasa mu ji alheri ki yi addu’a sosai nima zan yi.” Ta d’aga mata kai. Ummeeyn ta mik’e tana cewa “Bari mu tafi mun ja lokaci da yawa dafatan kema zaki kawo min ziyara kuma don Allah shawarar taki kada ta d’au lokaci.” Amman tana kallonta ta ce “Yanzu kina nufin har mun gama hirar yaushe gamo? Haba Hameedah? Tun muna y’an mata fa rabon da mu had’u, baki tambayeni wa na aura ba wanene uban yara na? Baki tambayeni ya rayuwata ta cigaba da tafiya ba bayan kin tafi kin bar ni cikin matsaloli ba?” Hameeda ta sake zama had’e da dafata ta ce “Ni kaina ina son jin labarin bayan rabuwa, amma kada ki manta na sanar dake jiya na shigo k’asar nan ina da gidajen zuwa da yawa baya ga haka kuma naga alama akwai damuwa sosai a tare da ke bana son tuno miki da waccan bak’ar rayuwar, abu d’aya da zan tambayeki an ga dangin Innah bayan tafiyata? Don na san har ta rasu ba ki san kowa nata ba.” Amma ta runtse ido sosai kafin ta ce “Ba’a gansu ba, har yau ko b’urb’ushinsu ban gani ba, na yarda tawa k’addarar kenan dafatan Allah ya had’amu a darussalam.” Hameeda tausayi k’arara ya sake bayyana a fuskarta ta ce “Allah ya gafartawa Innah, ki yi hak’uri zan dawo In sha Allah ko kuma na ce sai kin zo. Ki gaida Kabiru tunda na samu labarin shi kika aura na yi bak’in ciki sosai amma da na tuna shine k’addararki sai na yi miki fatan nasara a rayuwa ki sanar masa Hameedah Daru ta zo.” Amma ta saki wata ajiyar zuciya kafin ta ce “Rabona da Kabiru da Auren Kabiru shekara Sha biyar
kenan cif, ke dai labari sai mun had’u.” Daga haka ta hau sama don kiran twins. Ta bar Ummeey da sakakken baki da ta’ajibin abinda kunnuwanta suke jiye mata, shin wace irin k’addarace ta raba Talatu da Kabirunta duk da dama ta san ba soyayyar sa a zuciyatta? Me ya faru haka? Bata dawo daga tunanin ba taga sun dawo da y’an biyu gaba d’aya hannayensu d’auke da manyan ledodi shak’e da sutturu na alfarma. Jikinta a sanyaye ta dinga bin Amma da ido ji take kamar ta zauna ta fasa tafiyar Amman ta bata labarin bayan rabuwa. Sai dai kuma bata son k’ure mutum akwai lokaci……
Koda ta dawo daga rakasu bata bi ta kan Ayra ba, ta shige kitchen ta cigaba da ayyukanta da Dane damun kanta zata yi har sai Ayran ta bud’e d’akin ta lallasheta, yanzu kuwa tana murd’a d’akin ta ji shi a rufe ta juya abinta ya zama dole ta nunawa Ayra lokaci yazo da ya kamata ta zubar da makaman yak’inta ta yi aure, sai dai tana tsoro k’warai da gaske ta ke tsoron barazanar da Ayran ta yi akan rasa rayuwarta idan aka mata auren dole.
Sai dare can bayan Isha sannan Ayran ta fito jikinta a sanyaye ganin yarda Amma ta banzatar da lamarinta. A falo ta samu Amman tana kallon wani sabon shiri da ake a Arewa ta zauna kusa da ita, amma Amman ko kallonta ba ta yi ba illa ma sake mayar da hankalinta kan television d’in, duk da rabin tunaninta dama yana kan Ayran ta kuma ji dad’i da ta ga ta fito sumul k’alau ba abinda ya sameta.
Jikin Ayra a sanyaye ta ce “Sannu Amma.” “Yauwa” kawai Amman ta ce ta cigaba da jan carbinta ba tare da ta sake bi ta kan Ayran ba. Take hawaye ya yankewa Ayran a idanu ta sake jin tsanar Ummeey a ranta da duk ita ta janyo mata wannan matsalar. “Kada ki saka ni gaba da kukan jin da’di ban hanaki Kukanki ba amma ki koma cikin ‘dakinki, don ban ga abinda aka miki ba, aure ne ba kya so to falillahil Hamdu, sai ki tanadi amsar da za ki bawa ubangiji sakamakon b’ata min rai da kika yi.” Hankalin Ayra ya sake k’ololuwar tashi ta tabbata yau ta kai Amma tik’ewa, ina ma zata iya da ta yi shahada ta amince da auren ko da na wuncin gadi ne, ba zata iya ba tana jin zuciyarta zata fashe a duk ranar da ta had’a makwanci d’aya da ‘da namiji balle ta kai g ya kusanceta. Ta runtse idanunta tana ganin abin kamar ma ya faru, zuciyarta ta dinga bugu kuka sosai ya kece mata, da sauri ta ‘dora kanta a saman cinyar Amman tana kuka na gigitar hankali. Duk dan ta yi nasarar ‘daga hankalin Amman sai dai bata nuna mata ba, ta dai cigaba da kallonta tana jin tausayinta yana tsirga mata sosai, a hankali ta cigaba da jan addu’oi a bakinta da niyyar Allah ya sauk’ak’awa Ayran ta samu sauk’in zuciya. So take ta rarrasheta amma tana gudun aikata hakan, gani take kamar wannan hanyar data b’ullo shi zai saka Ayra ta amince ta yi auren ko bata so. Kukan sosai ta yi kafin ta share hawayenta ta mik’e a sanyaye karo na farko a rayuwarta da take kuka a gaban Amma bata rarrasheta ba abinda ya ki’dimata kenan a sanyaye ta koma kan kujera ta lafe, ba zata iya cin abinci ba duk da yunwar da take sasik’ar hanjinta. Amman ta bita da kallo kafin cikin k’arfin hali ta sake d’auke kanta ta cigaba da jan Addu’oin da suke bakinta.
********************************
A bakin faffad’an windown mai d’auke da glass mai girman gaske yake tsaye hannayensa sanye cikin aljihun jibgegiyar rigar sanyinsa, don garin canada akwai muku-mukun sanyin da har dusar k’ank’ara yake zubarwa (Snow). Sanyin yake ji sosai sai dai ya kasa barin wajen windown duk da windown ba’a bud’e yake ba. Yana tsaye yana hango yarda ko ina ya lullub’e da dusar k’ank’ara kamar ma ba’a halicci k’asa a wajen ba. Ya saki ajiyar zuciya tunawa da ya yi marigayiyar matarsa ta fi k’aunar yanayin fiye da komai, saboda yarda take kanainaye jikinta a nasa kamar mage. Ya lumshe ido a hankali ya ambaci sunanta a saman lab’bansa “Hibbah!” yana jin tamkar ta amsa cikin duhun idanunsa yake hango fuskarta tana sakar masa kyakykyawan murmushin da yafi so daga gareta. Ya da’de idanun a lumshe yana tuno memories d’in su masu da’di da suka kasa barin kwanyar kansa. A hankali ya bu’de idanunsa da ya ji sun masa nauyi kamar ‘dan maye wani feeling na muguwar sha’awa na taso masa. Yanayin da ya da’de bai riski kansa a cikinsa ba tun bayan aurensa na uku da Lubna ta ribace shi ta saka masa desired tablet a cikin coffee ‘din da ya saba sha duk dare. Tabbas ranar ta samu kansa domin kuwa kasa mallakar kansa ya yi sai da ya kusanceta sai dai abin haushin ya tarar da ita fanko ma’ana bata kawo budurcinta ba, kamar dai wancan Auren da yayi na Sa’eeda itama fankon ya tarar da ita shikkenan ya saka wa kansa cewa duka y’an matan yanzu hakan suke, ai kuwa ta jawowa kanta daga ranar ya saketa yana takaicin ha’da jikinsa da nata da ya yi.
Da sauri ya fa’da toilet baya son yanayin ya cigaba da zagaye jikinsa yazo yana rasa inda zai saka tsananin buk’atarsa. Ruwa sosai ya sakarwa kansa kafin ya fito ya zari car key ‘dinsa ya fice daga gidan bayan ya gama k’arewa hotonsu da Hibba kallo.
TAKAICIN UBA…….
Na
Nazeefah Sabo Nashe.
08033748387.
8….
Driving yake yana sauraron Karatun Alkur’ani daga k’ira’ar sudais. Shi ka’dai ne abinda yake saurare ya rage masa zugi da ra’da’din rashin Hibbarsa. Ko da ya yi parking a makeken wajen shak’atawar kasa shiga ya yi ya shiga cusa hannayensa cikin tarin sumar gashin kansa da ya gadota daga gurin Ummeeynsa. Ya dinga cukuikuye gashin yana jin kansa na sara masa kafin ya mayar da seat ‘din kujerar ta sa ya koma ya kwanta tunanin rayuwarsu da Hibba na sake bujiro masa….
K’arar da wayarsa ta yi ne ya farkar da shi daga wancan tunanin, ba sai ya kalli screen ‘din wayar ba ring tone ‘din ya sanar da shi wacece ‘Ummeey’ ya fa’da yana sakin murmushin gefen kumatu kafin ya jawo wayar ya kanga a kunnensa. Cikin muryar shagwab’a kamar yarda ya saba mata magana ya ce “Hayateey!” Ummeey daga ‘daya gefen ta saki murmushi tana jin da’din sunan da yake kiranta da shi. “Amin ya gida hope dai kana lafiya, muma kwanan mu uku a Nigeria.” Ya ‘dan yi dum da waya a kunne kafin ya ce “Nigeria kuma how comes? Ya aka yi Abeey ya barku kuka je?” Dariya ta yi sosai kafin ta ce “Da kansa ya sauko ya ce mu je. Yauwa ba wannan yasa na kira ka ba, Amin bu’de kunne da kyau ka ji lokaci ya yi da ya kamata ka yi aure.” Wani irin dum ya ji k’irjinsa ya buga, Ummeey zata sake janyo masa wani jidalin kenan shi tun yaushe ya cire maganar aure a rayuwarsa, ya Riga ya gama da wannan babin an gama samun mata na gari tun bayan da Hibba ta rasu. “Ba ka ji ni ba ne?” Ummeey ‘din ta fa’da with a serious tone. Sakin ajiyar zuciya ya yi kafin ya ce “Na ji Ummeey, amma ina neman alfarma, not now please, wallahi ban shirya aure ba, ko kuma na ce na gama buk’atarsa a rayuwata tunda dai Hibba ta haifa min mai yi min addu’a.” Cikin b’acin rai Ummeey ta ce “Ko da nice nake so?” Muryarsa a cunkushe ya ce “Don Allah Ummeey a bar maganar, please!”
“Ka yi k’arya kuwa in bar maganar aure, haka kawai da ranka da lafiyarka in dai ba mu’amala kake da matan banza ba ai ya kamata ace zuwa yanzu ka ajiye iyali, don haka magana ‘Daya da zan maka na samar maka mata y’ar aminiyata ta yarinta da nake yawan baku labarinta wato TALATU, don haka umarni na baka ba shawara ba..” kafin ya ce komai ta katse wayar don ta san idan ba haka ta yi masa ba,
Ba zai ‘d’au zancen serious ba.
Gaba ‘daya ji ya yi zuciyarsa ta karye, ya tabbatar tunda ta fa’da ‘din sai ta cika alk’awarinta. Ya runtse idonsa yana tunanin menene mafita? Wannan karan kam ya zama dole ya bijirewa umarninta, shi kam da zata bar shi haka ma tsaf zai iya rayuwarsa har ya koma ga lillahi babu aure. Wajen shak’atarwa da bai shiga ba kenan, ya da’de a zaune a motar kafin ya ja motar da sauri ya fice daga garden ‘din.
____________
Tun Asuba da ta mik’e bata farka ba, ta shiga gyaran gidan da abincin da ta san Amma ta fiso, gurasar larabawa da alkubus sai kunu da k’osai. May be idan Amman ta ga wannan hidimar da ta mata ta sassautawa zuciyarta daga fushin da ta tsiri yi da ita tun jiya da bak’uwarta da ta kira bak’ar bak’uwa ta zo gidan.
Sai da ta jera kayan akan dinning table da taimakon mai aiki. Sannan ta kunna sunnah t.v tashar da ta san Amman ta fi muradin kallo a koda yaushe.
Tsaf ta fito cikin shigar alfarma. Ta dinga bin falon gidan da kallo ganin yarda aka canja masa tsari. Ga dadda’dan k’amshi da aka baje falon da shi, na abinci da na k’amsashshen turaren wuta mai sanyaya ruhi na mutanen chad. Murmushi ne ya so sub’uce mata sanin cewa Ayra ce duk ta shirya hakan sarai ta san neman sulhu take tun jiyan tana lura da ita fushin da take da ita yana damun zuciyarta, sai dai ba zata bari ta fuskanta ba.
Ta zauna tana sake addu’ar fatan alheri ga Ayran kamar yarda ta kwana tana yi a cikin sujuda, ji take kamar warwarar matsalar Ayran ce ta zo. Ita kanta ta ji tana son Ayran ta yi wannan auren ko da sonta ko ba son ranta.
Tana jin takun tafiyar Ayran, ta kawar da waccan fuskar tata mai yalwar fara’a ta saka wacce ta aro tun yammacin jiya, mai wuyar kallo a wajen Ayran mai fa’dar mata da gaba da sakata ‘dimuwa. Zuciyar Ayra ta buga sosai ganin har a lokacin waccan caku’da’ddiyar fuskar tana nan tare da ita. Ta yi k’asa da kanta tana jin yarda zuciyarta take bugu a hankali take furta ‘Wannan bak’uwa ta cuceni na shiga uku, ban tab’a ganin fuskar mahaifiyata a haka ba kamar yau.’
Jiki a sanyaye ta isa gefen Amman kamar yarda ta saba ta rab’a jikinta da nata a hankali ta bata sumbata a kumatu “Ammaty Ina kwana?” “Lafiya” ta fa’da tana sake ‘d’aure fuskarta sosai, Ayran gabanta ya fa’di sosai ganin ba sassauci da da ne sai ta janyota itama ta ha’da goshinta da nata kafin ta ce “Lafiya lau Auta ta, kin tashi lafiya.” Ta dinga wasa da hannunta kafin murya a raunane ta ce “Amma I cooked your favourite dish.” Ta ‘dau tsawon lokaci kafin ta yi jarumta ta kawar da tausayin Ayran daga ranta ta ce “Ana sa’im.” Ayran ta dinga kallonta wani iri kafin ta ce “Sa’im kuma Amma? Yau fa laraba idan ban manta ba.”
Zuciya a dake ta ce “Na sani. Kuma ki k’yaleni haka bana son magana.” Tuni idanun Ayra ya fara tsiyayar da hawaye ta dinga bin ta da kallo kafin ta fashe da kuka ta fa’da kanta. Amman bata hanata ba amma fa bata saka hannu ta rarrasheta kamar yarda ta saba ba. Duk da zuciyarta tana bugu haka ta mayar da idanunta kan T.V a zahirance kallon take amma a ba’dinance kukan Ayra ne yake tsaya mata a zuciya. Ta da’de tana kukan kafin Amman ta saki ajiyar zuciya ta ‘dago kanta. Idanunta cikin nata ta ce “Saurareni Ayra, idan kina son ganin walwalata ya zama dole wannan karan ki yi ya’ki da zuciyarka ki amincewa auren nan, idan ba haka ba kin bar ganin walwala ta. A kullu yau min ina gaya miki ba duka maza ba ne halinsu ‘daya akwai wa’danda halinsu ya Sha banban da na mahaifinki yanzu yayyenki ba duk sun yi auren ba, duk da ta ki k’addarar ta fi ta su girma, kada ki manta ni kaina idan na tuna lamarinki abin yana min ciwo wani lokacin kwana nake ban yi barci ba saboda tsananin b’acin rai kuma ma ba wannan ba, ki tuna wani abu ‘daya mana yau ace na mutu na barki ina za ki kama? D’an uwana ‘daya tak da nake da shi kina ganin dai shekaru ashirin ba mu ji labarinsa ba, aurenki fa shine abinda ya fi cancanta..” Hawaye take idanunta ba k’akkautawa ita Kanta Amman danne zuciyarta take bata bayyana nata kukan ba, amma wanda take yi a zuciyarta ya fi na Ayran yawa ya fi shi kuma ciwo. Ayran da sauri ta mik’e ta shige wani k’aramin falo da yake k’asa. Kuka take sosai tana tunanin ina ma zata iya da ta amincewa aurennan tunda yanzu ta lura burin Amma gaba ‘daya ya tattara ga son aurar da ita, sai dai ina har a lokaci zuciyarta bata karkata da neman rushewar wancan adawar da takewa aure ba, ba zata iya ba ba zata iya ha’da makwanci da namiji ba…. Ba zata iya bawa namiji lokacinta ba balle ta masa girki ko ta nuna masa wata kulawa Menene Mafita? Shine kawai abinda take tunani ta runtse idanunta kawai tana hango wata mafita da take tunanin ita ce zata tserar da ita daga wannan auren ba tare da kowa ya zargeta ko ya k’alubalanceta ba…. Ta dinga sakin ajiyar zuciya tana jin cunkoson b’acin ran da zuciyarta ta